Showing 69001 words to 72000 words out of 328222 words
Chapter 24 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
matan yaya din
da abin ya kara daure masu kai suka maishi alheri yace dari biyu kawai zasu bashi
sadaka in an samu lafiya su dawo su bashi abinda Allah ya hore a garesu suka fito
suna mamakinshi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
2️⃣
2️2️⃣
4️⃣4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Basu iso zaria ba sai goma na dare nayi barci a lokacin don mun dan samu sabani da
anty Saare inda Iya da anty Nafisa suka shigan min da cewa.
Idan banyiwa yar uwata abinci nakai mata ba wa zai kula min da ita tunda
mijinta lalura ya kamashi yanzu bai cikin hankalinsa akan dan uwansa.
Hakan kuma sai ya zama laifi saratu ba dole bane duk abinda ta dafa ace saita
zubo muna tunda abincin asibiti takeyi abinda mara lafiya ke ra,ayine ai ta dafa
mata ni inama ganin kokarin yarinyar nan wallahi nafisa ke fadan hakan .
Saare ta kallota tana fadin kada tayi kokari mana wa tayiwa ba kanta ba nifa
dole in fada yarinyar nan tunda taje Abujan nan ta dawo ta canza gaba daya a gidan
don taje Abuja zatayiwa mutane daukan kai kamar wace taje london.
Abinki dai hassadane Saare inbashi ba wani daukan kai yarinyar nan takeyi gidan
nan yarinyar da bata ko saka kanta cikin sha,anin kowa ?
Dama ai hassadane hakan kada ki dada ki kara indai anty Saarece yanzu haka acan
lungun yaya J akai haka tazo ita ta ara ta yafa abinda bai shafeta ba.
Ramaah tun wancan case din da akayi na kayan sallah da kuka hana a bata ta kama
kanta a cikin gidan nan sai tacewa yar uwar nata salima dake magana.
Wa zata kamawa kai mufa nan gidan mune ba cin rani mukazo ba wanan yasa na fito
daga dakin iya dana idar da sallah magariba nake fadin.
Anty Saare nima gidan mijin yar uwata nazo idan ba haka ba aiba zaku ganin
gidanku ba nasan baki kaunar zaman mu gidan nan kuma Allah yayi mu zauna daku din
tunda Habu ya dauko yar uwata dole ki ganni a gidan in baki son ganina yau kisa
Habu ya saki Yanda gobe idan kin ganni ki fadi abinda kikeso a kaina.
Ke nikike fadawa magana haka Rahama ke yar gidan uban waye nace yar gidan ubana
malam Aliyu bafillace rugga da kika fada.
Shi kenan kun dauka mu fulani dabbobine bamu da wayau ko hankali kowa sai yaso ya
raina muna hankali girmanki nake baki don abubuwa amma tunda baki so muje a hakan
ai kowa ya iya rashin mutunci.
Yanzu kin samu abinda kike so ai tunda kikaiga fada yarinyar nan ta fada girma
kuma ya fadi ba salima ta karbe iya data soma maganan a lokacin.
Bata daiji dadin kowa ba a cikin zancen donshine tunda na shiga daki ban fito ba
tunda naji kawu na fadawa iya ba zasu kwana ba donshine banje part din su Yanda ba.
Sun gaji da zaman jira suka kwanta sai anty Salima dake zaune tana kallon
film wayanta itace taji dawowansu maigadi yana bude masu get.
Ta tayar da iya tana sheda masu sun dawo taji maigadi na budan get din yana
gaidasu da dawowa a lokacin hakan yasa suka bude kofan ni dai ban fito ba don idona
biyu ina hadiyan bakin cikin Saare a zuciyana a lokacin kinsan bafulace da bakar
zuciya dama.
Sai washegari dana fito na gaida mama dake zaune falo tanawa iya bayani abinda
mai magani ya fada ta juyo tana amsawa kafin na mike nakoma daki tabini da kallo.
Kodai yar nan malamin nan yake nufi dai don wanan kunun tsamiyan da take damawa
shi kadaine abinda Jafar yake sha ya zauna a cikinsa.
Kai ba ita bace dai nafi sa ran Nafisace dai bata kai karshen zuci ba da takeyi
taji iya na fadin jiya Saratu bata kyautawa yar nan ba.
Akan abinci ta zauna taci mata mutunci a gidan nan wai tayi girki bata zubo masu
ba ta zuba min ta kwashe takai asibiti zokiga yadda tayiwa yar nan falle falle a
gidan nan jiya.
Garin yaya haka ya faru kuma me saratu ke nema da yarinyar nan don Allah ai jiya
takai ga bata amsa ta fada mata ba,a daji aka daukosu ba suma suna da uba ai dalili
yasa ta ganta nan din tasa habu ya saki yar uwarta idan ta sake ganin fuskanta a
gidan nan.
Ai gaskiya ta fada idan ba dalilin yar uwarta ba ta yaya zamu ganta gidan nan da
tana zaune ta mike kafa habu ya kawo masu yar aiki ko ?
Bafulace zaka rainawa wayau ka zauna lafiya don ma yaran nan nada wayewan kai
suna amfani da iliminsu aida ta dajinne datace data gane bata da wayau gobe ba zata
kara raina masu wayau ba.
Murya tasa tana kirana daga falon na fito take fadin Rahama daga yau nayi maki
iyaka da sa,insa a gidan nan kinji nasan an bata maki rai amma kiyi hakkuri itama
zan fada mata wanan halin banzan nan data koyo ba alheri bane ga mace tagani ta
gaza shiru komai kace sai kayi magana akansa kana tare da wahala bance kuma
inkiyiwa yar uwarki abu sai kin dibawa kowa ba tunda suna da hannayesu kiyi hakkuri
kinji Rahama.
To fadane dai gashi nan irin ta uwa mai son yayanta bata goyi bayana ba bata kuma
nuna nayi laifi ba wanan shi ake fadin wanka da jurwaye ke nan.
Na daiji amma nace nagode mama tace ba komai kinji gaba zai maki amfani yar nan
hakkuri baya baci gabawa.
Allah yaba yar uwanki da Jafar tare da sauran al,umman musulmi lafiya na amsa da
amin nashige daki ashe ta samu Saare a can tayi mata ba dadi a gaban kowa.
Saiba ke fafin amma mama kada kuba wanan yarinyar garati da yawa ta dauka daya
take da mutane a gidan nan ko banza ai duk sun girme mata don me zataki masu girki.
Ya J dake kwance sama dogon kujera mai ci mutum uku ya dago yana fadin wanan
wani irin maganan banza kikewa mutane ?
Kinfi nama sanin abinda ya dace tayine akan mu ko kinfi yarinyar wani darajane a
wajenta ?
Koko an fada maki boya aka kawo masu ina da niyar wanan maganan mama ta rigani
don aikin da yarinyar nan keyi a gidan nan babu wace cikin ku dake yinsa tafiku
wawiya kawai ko ta zauna tayi girki aci hankali kwance wanan ba daraja bane banda
cin mutunci me kika koya ke ?
Zancen nan dai ba naka bane jafar ka barta aina san abinda nakeyi ba zan zuba
ido su saka yarinyar mutane a gaba ba ina kallo aiki ya wuce nawa da iya kona yar
uwarta ba zata kara kauda kara a gidan nan ba.
Wanan ma da iya ta dauko kwanan ta uku batazo ba son bata iya kallon ga mata
zube amma basu iya komai wa zai zauna yana wanan wahalan haka ?
Suna cikin wanan zancen muka shigo da Iya a cikin jam,i na gaidasu kafin nace
yaya ina kwana ya karfin jiki ya amsa da Alhamdullahi .
Yadda naga fuskokinsu yasa na fahinci akwai abinda ya faru don haka ban zauna ba
na mike don barin falon don kusan ni dayace bare a cikinsu.
Kin hada abincin asibitin ne Rahama mamace take tambayana na juyo ina fadin na
rana zanyi masu yau sunce abar na safe zasusha shayi.
Ai shike nan sun hutar dake aiki naso naje na dubasu saidai abinda hali yayi
zuwa anjima tunda jikin jafar din da sauki sosai yau insha Allahu.
Ya dace aje a dubasu kada suga rashin hankalimu iya ta fada mama din ta sake
fadan insha Allahu zan kekasu yau ina ganin can Habu ya nufa tunda safe.
Ban tsaya ba na fita naje aikin gabana sun dan jima zaune kafin ya mike zuwa daki
yana fadin zai kewaya.
Sumama suma suka bar falon don gaskiya maganin da alaman ya karbeshi sosai ba
bugun kai da yakeyi a lokacin nafisa ta rigasu barin falon ta koma part dinsu.
Salima na zaune tana dakilan wayanta suka fara magana Saiba tace dole tayi hakan
don ta danje Abuja tayo clean baki ganin daga kan data fara yiwa mutane tunda sun
iya asiri .
Babu asiri sai iskanci a ina wanan zata samu asirin balle tayi Asmau take fadan
hakan haka kike gani da asirinsu ake haihuwansu.
Yar kauyece fa kibar yan kauyen nan inda kike ganinsu sis haka suke kiran junan
su tun farko yanzu in ana dadin rai hakan ake furtawa juna sunan na sis idan fada
yazo kuma za a kira mutun da sunansa na yanka.
Boni ya tabbata ga mai zunde yanzu me yarinyar nan tayi maku da zaku sakata a
gaba da zaki harda wanan irin zargin inma asiri tayi ai baku tayiwa ba dai ko ?
Salima inma tana asiri tasan wanda zatayiwa nikan nafi karfinta har kowa nata
kuwa haka dai kikace idan baka damu da mutum ba ai baka zaman kushesa haka ?
Ke Saare bar part din nan kafin ranki ya baci yayan nasu ya fada yana nuna mata
hanya don ransa ya gama baci da wanan halin nasu.
Ke kuma Nusaiba abinda yarinyar ta tsare maki saiki kokarta ki koreta a gidan
ki samu sanyin a ran ki tunda zamanta ya tare maki wani abu.
Salima ce ke ban labari daga baya zamuce Alhamdullahi don gaskiya jikin nasa
yayi sauki sosai sati daya ya iya yi a gida ya soma harkokinsa na yau da kullum.
Haka salima da Saare sun koma wajen karatunsu ya rage gidan dagani sai Nafisa
da zance zamanta ya dawo nan dai ke nan don tafi ganewa zama a nan din donko da
mama zata koma gida bata bita sun tafi ba tace sai mama ta dawo ita tana nan ba
yawan hayaniyan nan na gidansu.
Shakuwa sosai na tsakani da Allah ne a tsakanina da Nafisa don tankar yar uwa
ta daukeni inda har dan fi min salimama zance dadin zama don bata da son kanta tare
muke komai da ita.
Ba irin rayuwansu bane ita ba sai ta jira kayi mata abuba ita zata tashi tayi da
kanta dama aikin dai iya girkine kawai inyi na safe tayi muna na dare wani lokacin
idan tana gida tare zamuyi aikin da ita.
Watan haihuwan yar uwata ya kama kowa hannunsa a gaba duk da likitoci sunce
babu matsala ga hakan saidai komai a hannun Allah yake ai ba a wajensu ba.
Allah cikin yardansa ta haifi danta lafiya lau ba tare da aiki ba ranan munyi
murna sosai da haihuwan .
Ya habu bakinsa yaki rufuwa duk daurin fuskan nan nasa a ranan babu wanan halin a
wajensa sai washe baki yake kallo daya zakiyi mai ki gane yana cikin farin ciki.
Matan yaya Jafar kusan sune sukazo a karshe daga gidan duban maijego da jariri
sun samemu a dakin zaune tare da ita muna hira su mama suna waje da ummah mu zaune
don an dauke wuta.
Sun shigo sunyi barka basu zauna ba duk da dagawan da mukayi muka basu wajen
zama sukace sauri suke zasu koma gida iyace da mai aiki suka bari a gidan.
Bayan fitansu mama ta aiko Nafisa tazo sai gata ta dawo tana fadin zata bisu su
sauketa gida ta karbo sako a wajen innansu.
Don haka suka tafi tare dasu a hanya suka fara zagin yar uwata harni basu barni
ba da uwarmu duk sun hada sun zagemu tas a lokacin kishin (saure) ke nan wasu suce
dashi (Facal) matar wa da kani ko dan uba.
Yafi zafin kishi wani lokacin ga mata har gara kishiyar da kuke mijin ku daya da
matar dan uwan miji koda ko ba a gida daya kuke rayuwa da juna ba ana samun wanan
matsalan sosai a ko wani kabila a duniyan nan.
Mukan bamu san sunayi ba abinda dai na sani shine basu kaunan mu wanan yasa
gaba daya bani shiga tsabgansu yanzu ko part dinsu tunda mijinsu ya samu lafiya
rabona da wajensu ke nan sai inyi kwana gamu gida daya amma bamu hadu ba.
Ina dakin nasan dai ya dawo garin tunda naga motar dayake amfani dashi haka kuma
anshigo da tsaraba akace shine ya dawo.
Sai asibiti muka hadu daya shigo ganin jaririnsu jikinshi a lokacin ya dan dawo
sosai zakice bashine yayi wanan ciwon bala,in ba a watannin da suka shige.
Gashi a yanzu yadda nake ji a wajensu arzikinsa sai habbaka yakeyi don har su
mama da iya na kiran dan yar uwata da arzuka wai yaya J yace ana sanar mashi da
zancen haihuwan kuma aka kirasa kudadenshi sun fito masu yawa daya saka hannun jari
a wani harkan mai a can kudu.
Don haka komai baja baja akeyinsa a gidan alherinsa ga mutane kuma bai daina ba
kamar ma kada yai ciwom nan abin ya nunku masa.
Ya shigo da mutane a bayansa yuuuu da suka taka masa naji Nafisa tana gaidasu
nidai sau daya na gaidasu na mike tsaye na koma can wajen gado na tsaya.
A cikin yare anty Yanda take min magana da na dauku dan nabasu don haka nake
fadin nikan ina nasan haka akeyi.
Yar fillo anyi da sintirin zuwa asibiti ya kare sai karatu yanzu ko abinda yaya
j ya fada min ke nan a lokacin na danyi murmushi ina mika mashi dan cikin ladabi.
Amsan shi yayi yana kallo ya jima dashi a hannu sai daga baya na fahinci addua
yakewa yaron ashe naga yana mashi ikima da bin sassan jikinsa yana tofewa har dai
ga al,auran yaron ya mikawa na kusa dashi yana fadin Allah ya raya muna Alh mu bisa
kan sunna sunan baba na saka mashi dama alwashina ke nan idan na samu da in saka
mai sunan baba sai ga habu ya rigani hakan.
Ai duk nakane wani mai banbadanci ya fada basu jima ba suka mike don tafiya
akwaisu da son kanninsu don haka ya yafito Nafisa da hannu ta biyoshi kome ya tuna
naji yana fadin yar fillo zo muje mana.
Dole na biyo bayanshi sam ba zan iya yadda suke da yan uwansa ba sosai suke
sakewa dashi fiye da Habu donshi Habu ko yaushe fuskansa babu fara a cikinsa.
Shiko yana da dama sosai yakan zauna dasu yayi hira su fada mashi korafinsu kuma
yayi masu maganin hakan a take matane kawai za ace bai dace dasu ba.
Amma yana iya kokarinsa ba zaki gansu da tufafi da bai dace ba saidai yanayin
gyaran ne da basu tsayawa suyi kawai gara Saiba yar kadunace iya kwaliya a wajensu
yake sai dai ita kamar bata amsa sunan yar kadunan ba.
Mun fito yake fadin to yaya Nafisat party zamuyi ko walima ta kwashe da dariya
tana fadin party kuma yaya kamar wata yarinya karama au to ke in bakiyi yar fillo
zatayi ai ?
Ko sai ki hada muna taron fulanin ku ayi sharo ayi rawan sanda nayi murmushi ina
fadin yaya ai sai za aje neman aure ake sharo ba a haihuwa ba.
Au ashe akwai kallo kuwa ranan da zaki kawo muna miji don sai munyi masa shadin
nan dubu kafin mu bashi mata.
Abokansa suka kwashe da dariya wani ke fadin ka ganta kuwa sai jarumi zai iya
zuwa don wanan za a kashe nagge a kanta kana ganinta nan.
Au Allah dai kace mu shirya kwasan nagge ke nan nidai sai murmushi kawai nakeyi
don ban iya cewa komai idan yana min irin ba an nan.
Yanzu ke Nafisa sai mun hadu a gida ke nan ko yar fillo dai wasan Nagge zatayi
muna da kiwo ke kuma kince bakyayin party sai walima ?
Tana dariya take fadin sai mun dawo yaya Allah yasa kana gari ba tafiyan zakayi
ba mukai masu sallama har bakin mota bayan ya gama da su mama suka tafi.
Da muka dawo dakin Nafisa ke muna hiransu irin rayuwanshi da yadda suka taso har
wani labarin danake tsakwaro maki nasu da akayi bani wajensu.
A gurin ta na kan danji tarihin rayuwan mama dubu da iyalinta don takan fada min
komai salima ma takan fada sai da komai har haka ba.
Hidama sosai yayiwa sha,anin sunan zakice matarshice tayi haihuwan farko haka
kudi ya raba muna har anty Salima dake kara a birnin minna don ita bata samu zuwa
ba ya tura mata da kudinta Saare kuma da ita akayi sha ,anin bukin.
Babban yarsu tazo daga zamfara don da yayi ciwo a lokacin kuma mijinta yayi
accident ya kare a hannu sai wanan zuwan muka santa dai zance amma muna gaisawa a
waya da ita.
Ummah mu ana gama hidimar suna ta nuna tana son komawa gida a lokacin saidai
mama ta hana hakan sai anyi arba,in tace yan uwan mu sunzo mutum biyu da namiji
guda .
Sunzo da nasu abin arzikin daidai iyawarsu an kuma yaba mukan bamu da abinda
zamucewa hardo daya rungumemu hannu biybiyu a yanzu .
Sai a bakin iya nake ji wai ai ummah mu ta samu manemi a kaduna zatayi aure wani
abu naji ya daki zuciyana nace iya ummah tamuce zatayi aure kuma ?
Muna ga rasulu yar nan me zai hanata aure wanan da bata wuci