Showing 303001 words to 306000 words out of 328222 words

Chapter 102 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

ita yana
fadin wanan warin fa tun safe nake jinshi a part din nan ?
Asmau ta fito da danta a hannu tana fadin kadawo ashe yaya mai jikin kuma yace
da sauki ashe an sauka Allah raya ya amsa da amin yana fadin.
Wanan warin fa na meye do Allah yaya zaku zauna cikin warin nan kuna ji zai iya
illanraku amma kun kasa duba kome ke wari haka don Allah ya fada yana bin falon da
kallo.
A,a warin ruwan waken da Saiba tayi alale dashi jiyane na fada mata yana wari
ta dauke taki to munafuka kina fada mashine don ya dakeni kome ?
Hauka nayi da har na fara duka waike Nusaiba wace irin macece da baki son zaman
lafiyane komai naki nacin mutuncine ke ?
Yanzu ina shigowa asibiti na fito amma kika bini da kallon wullakanci din kina
yar rainin wayau ko ke gaki issasa ki shiga ki dauke ruwan nan yanzun nan kafin na
fito.
Ina ruwana da ka fito asibiti tunda ban aike ba asibiti wanan ruwanka kai ya
shafa bani ba name zaka kuma dafa min wai nayima mugun kallo ?
Ai nasan ruwana tunda bai shafeki ba niko daya shafa ai kinga naje har kuma kin
gune da hakan ni yanzu na gane ki sarai kanki kawai kika sani ke saukin abin kowa
dai na ciwo aiko ?
Wata sabuwa za a dora min laifin da banji ba bangani ba akai kaje kaji da wace
ta jaka zuwa asibiti ta kwanta don samun waje bani ba ?
Ai kinji nace niya shafa kuma naje ba sai kinyi hakan zaki nuna min ranki a bace
yake ba ai dani taje ta kwanta kuma naje na tsaya din anyi mata aiki ina shike nan
koda kudinki nakai ta asibitin ?
Meye nawa malam mu dai da aka raina idan munyi magana ace damu babu kudi gashi
yanzu anyi kudin kai mata asibiti ai tunda tana yar gwal.
Au bakin cikinki ke nan ashe na samu kudin dana kaita asibiti akai mata aiki to
kije ki kwanta kema asibitin sai in kashe maki kudin ko ?
Kai kai kai wai haniyar meye kukeyi hakane kai da kake da mara lafiya kazo nan
kana wanan hayaniya haka kuma kuna saida hali ?
Yarinyar nan mama yar rainin wayauce ya juya yana fadawa mama din yace har da
asibiti mutum ya dawo ba zata barshi ya huta ba nina gaji wallahi tunda bata da
ranan gyara halinta ?
To ka gaji mana sai me keko kikan fara halinki ke nan wallahi tunda kinsan
hankalinshi na a kwance yake ba baki kyaleshi koma meye ?
Mama kodaya fita gidan nan bai fada muna matarshi tana asibiti ba ko zai kaita
asibiti don ina tsoronsu yanzu sai ince mashi yaya jikinta ko an haihu ?
Kallon mama din yayi cikin mamaki yaji abinda zata fada sai yaji tace towa ya
fadawa ga abinda ke nan muma saida yaga za ayi aikin aiya kiramu tunda bamu da
amfani a zancen ?
Ina dai fadama kayi hankali da mace balle irin shu,umar yarinyar nan data iya
kisisina iri iri tun bata kai nan ba.
Mama kin goyi bayanta ke nan fa zancenki ke nufi ba zancen goyon baya a nan
tsoranka akeji daba za a fada maka gaskiya ba tunda an nayar daku shanun tatsa ko
yaushe kuke nan cikin wahalan mata ?
Yarta ta kwanta tace bata iya daukan ciki balle haihuwa yanzu gashi itama ta
tsiri hakan farawa da iyawa saika koma kaita kashe jiki ana tatsanka kaiga mata
asibiti.
Ballema ita bata haifo a sa,a ba tunda taszo da kissan ba kudin ta gaji da kwanci
ta taso don kanta idan taga ba abinda sukewa din ta makara wajen wanan kissan.
Kai ya girgiza ya juya zuwa dakinsa ya rufo ya barsu tsaye cirko cirko a wajen
sai nusaibance ta kawar da shirun take fadin wallahi Asmau muna fukace ta karshe
wai mutum bai fada muna komai ba take mashi wani kashe murya yanzu .
Wanka yayi ya koma asibitin Nafisa ya kira yake fada mata taje can gidanmu ta
shiryo abinci a kawowasu mama nan ya bata kudin mota ta tafi.
Koda ya shiga dakin ya samu na farfado ina ina kwance mama tana gefe da jaririn
a hannunta tare da sauran yan family house dinsu da sukazo ya shigo suna gaisawa
dashi suke mashi barka da arzikin fitan kai lafiya.
Ya amsa kafin ya aje masu ledan daya riko dan abinda zasuci a lokacin ya nufi
wajen gadon yana min yaya jiki na lumshe ido cikin gajiya tare da amsawa da kyat
nace da sauki.
Ya juya gurin mama yana tambaya yace wai kuwa matar habu tazo mama mama din tace
yanzu na kare zancenta a raina da ban ganta ba nima.
Waya ya dauko yana bugawa habu din wayan ta kusa katsewa ya dauka yana dauka
yake fadin sorry J wallahi kudin ne basu samu ba kajini shiru.
Yace nerve mind nace ka fadawa Matarka cewa muna asibiti anyiwa kanwarta CS an
cire da dazun ?
Wai dama aiki za ayiwa Rahama din na zata kunje ganin likitane kawai fa ya
katseshi da fadin don Allah fada mata anyi aikin an cire da tun dazun muna nan
Royal da ita ya kashe wayan .
Ya juyo gareni nake fadi a hankali dama ka kyaleta ai yace No a dai fada mata
din kada ayi laifi donshi bai fada ba wai baisan aiki za ai maki ba.
Shigowa likita yasa sauran fita aka bar mama dashi a dakin likitan na fita mama
ta soma fadin matanka fa da dubu koda yake ga iya ai da salima sunzo ba zance basu
sani ba.
Sun sani mama ya fada a cikin wani irin yanayi na bacin rai kafin ya juya zancen
da fadin yaron yanzu mai za a bashi ga dai ruwan zamzam nan na sayo da dabino a
leda.
Nagani salima zata bashi likita ya shigo barci ma yakeyi tun dazun dai yayi dan
kuka kuma aka lalasheshi yayi barci.
Likitan yace ya gaji da yawa hutu yake so ai an auna arzikine aka sameshi raye
yarinyar nan tana da taurin kai mama tana nakuda tun cikin dare amma bata kirani ta
sheda min ba ?
Murmushi mama tayi tana fadin bafulatancefa Malam aiko inba ta zama bafulatanan
zamani ba baka taba jin ta bude baki tacema ga matsalan ta wanan halinsune alkunya
da kawaici shi mutane suke dauka rashin wayewa nan ko alkunyace irin tasu ta fulani
da akasani.
To mama kana cikin wanan cindition din baka kikirana kunya hardani zata hada
mama haba mama tayi murmushi tana fadin daga ita har matan habu ai basu yarda
akidojinsu na fulani ba.
Mama ni yau ai ina a cikin mamaki sosai wallahi ashe idan baka dashi ba kowa
kake a wajen ko yan uwanka ba mama ni habu zauwa haka.
Ban gama mamaki ba kuma naje gida na samu wanda yafi wanan abin mamaki ace maman
mu har da asibiti take adawa akai wai da gangan Rahama tazo ta kwanta akai mata
aiki.
Don kawai a kashe mata kudi da ganganfa mama ta katseshi da fadi yace wallahi
mama ita kuma shashashan nan mai bakin kishi ta dora nata sai Asmau ce tayi min
Allah sauwaka kuma sukaga laifinta.
Ita dubu har abin yakai haka gareta to Allah ya sauwaka don abin nata sai addua
iya fa ta fara ban labari dazun ashe ta fada maka hakan kaima Allah ya sauwaka toh.
Mama ni habu zai hanawa kudi sai wani banza can na waje bare aboki dana
taimakawa taimakon da baikai nasa danayi mashi ba shine zai dauko kudi ya ban masu
yawa inyi lalurata dashi.
Amma ko habu bai kyauta ba barshi insha Allahu ko talauci zai kasheni bani kara
tambayanshi komai a duniyan nan in Allah ya yarda.
Habu ko bai kyauta ba ko ana mashi kirarin rowa har dakai zai hada yayiwa rowa a
duniyan nan meye bakai masu ba a rayuwansu kaf dinsu gidan nan.
Barshi babu komai mama ya fada cikin wani irin murya ina kwance ina jinsu ya ban
tausayi a yadda yake fadi yana bata labarin yadda yabar mashi aikinsa na farko na
mai da habun keyi yanzu .
Haka kuma suka kama dukiyansa suka durmuye dashi dasu kawu har kayansa suka
salwanta baiyiwa kowa korafin hakan ba kuma.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

[6/7, 20:37] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

9️⃣4️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Kwana biyu muka samu sallama dama da iya da mamane sai salima muke zama asibitin da
inna dake zuwa itama ta wuni damu wace a yanzu na fahinci taga kamar mama ta karbe
matani don da farko itace muke tare da ita.
Amma zamanmu jiyar yaya dasu maman tudu din sai muka saba sosai da ita fiye da
inna duk da dukkansu suna da halin sukan mama dubu da iyalinta a gabana saidai ina
nuna masu hakan bai damuna don ba halina bane zama yi da mutum.
Wanan kuma nasan cewa halin kishin mu na matane yasa suke hakan tundai mama
gaskiya tana yawan magana da korafi kan halin mama amma wanan matsalansuce ta manya
ai bai shafeni ba amma kuma tana da fadin gaskiya dasa mutum a hanyar da zai
fusheshi.
Din haka koda muka dawo gida mama tudu itace ta biyo mu zata zauna dani ke nan
yan kaduna sunzo tun washe garin haihuwan sun dubani hakama Yanda a ranan da dare
tazo ta dawo kuma washe gari har dare tana wajena kafin ta tafi.
Duk da bai fadi ba kana kallonsa kasan akwai damuwa a tare dashi a yanzu ba
lokacin da zai iya fada min ko maye don ko yaushe muna tare dasu mama idan zai
shigo wurina.
Yayi kokari sosai zamana asibiti haka abokainai da yan uwa suma sunyi nasu rawan
ganin a lokacin gaskiya gashi wanda duk yazo da alherinsa mama ke karba idan yazo
ta mika mai da farko ya nuna abarmin aimu aka ba.
Amma mama ta nuna mai ai damu dashi dayane don haka ya karba ya rage lalura dashi
ga asibitin na kudune sai demand suke saka mashi na kawo kudin kaza kawo kawo dai a
asibitin har aka sallamo mu muka dawo gida.
Ina barci da dare ranan yaya habu yazo dubamu ya jima suna hira dasu mama don
lokacin yana gida nabar labari a baya don kuwa mama dubu itama sun shigo a ranan da
aikai min aiki ita dasu Asmau da Nusaiba .
Ta dauki dan ta kare mai kallo mama ke fadin dubu kinga farin miji kin kasa ba
uwayensa su dauka su gani budan bakin mama sai cewa tayi ga faein miji kam amma
yazo a yanayi.
Baizo lokacin daya dace ace fari yazo ba walwala ba maman tudu tace jam meye na
rashin walwala kuma dubu ga yaro da uwar kafiya kalau dasu.
Ummm,hummm yaya ke nan nabar zancen don ba zaku fahinta ba Allah dai ya raya
muna shi ta amsa da amin tace mikoshi kada ki shaye zakin angonane dai ni kadai ko
Ladi tayi ta barni da abina da cewa inna.
Da haka aka wasance zancen nata lokacin iya tana waje tana sallah akai hakan
suma suka karba sai Asmaucema ke fadin kai lalai mama kinyi ango wanan aiya kosa a
ciki sosai tubbarkallah masha Allah ta juyo tana min sannu nayi murmushi ta mikawa
Nusaiba ta dan karbi dan a dakile ko minti daya baiyi a hannuta ba ta mayarwa matar
yazid dashi ta fice daga dakin wai tana waya.
Basu jima ba suka tafi wai yaya na gida yana jiran a kawo mashi mota ya fita don
dayan motan tashi da suke fita ta lalace lokacin.
Haka zancen mama ya tsaya min a rai don na kasa fassara abinda hakan ke nufi
lokacin saina bar zancen a raina.
Tare da mama muka kwanta a gado iya kuma falo ta tsaya don lazumin da takeyi da
dare washegari tunda safe mama ta tayar dani nayi wanka don anty Nafisa na gidan
har lokacin.
Ya shigo suka zauna da iya a falo suna gaisawa mama ta fito suka gaisa yake
tambayansu dare tace Alhamdullahi maigidan nawa ai bawan Allah neshi baida fitina
ko kadan.
Kamar dai sak nacewa dubu kai ya biyo amma take fadin wai baku da kama yaron
nan kaine ai sak babu inda yaron nan ya rageka gaba daya diyanka ba wanda ya
daukoka irinsa duk da uwayensu sukai kama sauran ba dai kamar wanan mai yawan ciwon
ita bata rage uwarta ba ko ina ?
Ya mike da zuman zuwa daki wajena wayanshi yai kara ya tsaya daukan wayan yana
karawa a kunnensa a cijin harshen turanci ya soma magana da maishi har ya shigo
dakin ina zaune nayi zufa na gama shan tea ke nan a lokacin.
Hannusa yakai yana share min zufan tare da fadin eh nine kwarai kuwa nike magana
ya tsaya ya saurra da kyau ga bayanin da mutumin yake mashi na daiji yace Allahu
akbar kabiran .
Jin hakan yasa na dago na dan dubeshi daga inda nake zaune din ya hannusa yana
rike da nawa har lokacin godiya ya somayi kafon ya kashe wayan yana rungumeni ya
furta Iam back Rahama in sha Allah kayana da suka salwanta anganosu yanzun aka
kirani daga can.
Farin cikine ya kasheni ina murmushi na furta Alhamdullahi Allah abin godiya wai
Allah mun godema.
Ya sakeni ya juya falo zuwa falo wurinsu mama yana shiga ya daga hannu yabawa
Allah kirari da godiya ya duka yayi sujadan godiya ya dago yana fadin me zance mama
wanan mijin naki lalai arzikine an gano kayana da suka salwanta a can kasan aka
kirani ana sanar min.
Masha Allah suka dinga furtawa a cikin murna budan bakin mama sai cewa tayi
Allah ka rufa wanan asirin dama na fadawa dubu hanya Allah yawa gareshi yanzu me
zatace don Allah kuma ?
Tace wanan dan bai zo a sa,a ba don yazo ba a cikin walwala don haka ita batayi
dashi nace mata hanyan Allah da yawa yake yanzu gashi ?
Ita dubun ta fadi hakan yaushe tayi wanan zancen banzan haka banji ba a ranan
da sukazo asibiti mama taba iyan amsa tana labarta masu yadda akayi.
Yoo kuji zancen bamza don Allah jininka zaka tsaya fadawa wanan zance haka abin
kunya abin takaici wai meke damun dubune kamar wace kwaro ya hau kanta don Allah
jinin ja zakaiwa wanan furcin ?
Wanan kam saidai a kirashi da arziki yaci babban suna mohammad za,a saka mashi
insha Allah dama dashi nayi mashi hudu babane ya dawo .
Gaskiya kam yaci wanan sunan wanan da arzkine yasha sara da suka da sassaka da
kushe tun yana cikin ciki har fitowanshi duniya ba a bari ba kai jama,a Allah na
gwadawa mutane isharanshi tun a duniya.
Dubu dubu meya samu jan yarinyar nan ne nikan sai ince ko mutanen boye sun
shafetane wai ba a sani ba dariya taba kowa datake zancen nan .
Kubar dariya don Allah iyan ta kara fada tana fadin nifa abinta ya fara daure min
kai jama,a kutayani duban zancen nan na dubu jininka yazo duniya ka nuna bakin ciki
a fili kana wanan furcin haka abin dubawane zancen nan ?
Ta fada don nima abinda tace min ke nan a lokacin wai Rahama bata da sa,a gashi
ta haifo da a cikin rashin sa,a yazo babu komai sai wahala.
Duba fa wanan zance haka ina ya fito ki kyaleta iya komeya faru kaddaratace a
hakan ai Rahama tayi hakkuri sosai da abubuwan nan don haka ki kyaleta muyi mata
addua inma wani abin ne ya hau kanta Allah ya yayye matashi iya.
Ina ganim gobe insha Allahu zan tafi lagas zan bar nan zuwa Abuja inshiga jirgi
don suna nemana ai ina ganin suna ba satin nan ba ko yake tambayan mama.
Ina sai maijego ta kara samun lafiya dole a dage sunan nan don aikin da akai
mata saita mayar da karfin jikinta .
Haka nayi tunane ban fada bane kada ace wani abu ya fada mama ta bashi amsa da
fadin haka abin yake ai sai an mayar da sati daya ko biyu maijego ta murmure ake
suna idan aiki akaiwa mace.
Sun zauna nan suna hiran yadda abin ya kasance haka lokacin daya kwanta ciwo
yana processes din fitan kayan nasa ciwo ya kadashi sai wani abokin hurdanshi
kirista ya dauki kayan ya boyr a can da suka isa.
Nan kuma ankira a tura kudi habu yabi don kada kayan ya salwance yace ba kudi a
hannusa a turo mai daga wajensu sun turu din kuma aka kama amfani dashi wajen
magani.
Har kudin sukai rauni koda habu ya samu zuwa kuma ba issasun kudin da zasubi
kayan shi kuma baiyi dabaran karawa da nasa ba a samu kudin su fito don maganan su
saiba a lokacin kan yana tausan dukiyan su kadai shida yazid ba a basu komai.
Ke mai karatu kinsan harkan wani zumunta da zama a babban gida gidan yawa yana
tara mabanbantan mutane masu banbancin ra,ayi sai a cakude ayi ta zaman tsama a
tsakaninsu.
Irin wanan halin shiya shafi habu donshi dan no case ne suna wanan maganan ya
shafi dan uwashi har kowa nasa ya hau fushi tun a lokacin ya fita batun komai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login