Showing 192001 words to 195000 words out of 328222 words
Chapter 65 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
a tsakanin mu tun a yanzu din.
Idonta ya fifito na masifa ta soma jefa muna zagi na wullakanci ina rama abinda
take fada min din cikin hikima da nasa mata bakin ciki a rayuwanta dama ance magana
zaran bunu.
Nasam karshe tace zata dora min hannu a jikina don haka takewa kishiyarta a baya
nasani kuma hakan yasa tunda naga tana nufoni na mike tsaye cikin masifa nima ina
jiran karasowanta a kaina.
Sai fadi take yau zan murji rashin kunyar nan taki da kyau dana jima ina jiran
wanan ranan zan gwada maki nafiki iskanci ke karamar yarinyace wallahi .
Yariya ai tana bayan uwarta kin sani nikan ai daidai nake dake saiba kafin
hannunta ya sauka jikina don yanda data shiga tsakanin mu hakan yaban daman samun
shammatarta nakai mata wawan mari a tsakiyar fuska tauuuu.
Saida ta duka kasa kokarin kare yar uwata don kada mu illantata nayi nakai
gareta muka hade ana gwadawa yar filo mai kiwo a daji kokawa ?
Ai kunya garemu badai tsoro ba sai gashi Allah yaban sa,a na dagata sama na zuba
saman kujera nabi na danneta ina aikawa fuskanta naushi a iya karfina da bansan na
saura dashi ba har lokacin .
Ihun yanda ya fito da mutanen gidan mama a rude babu kallani akanta tana rige
rige da yayanta suka nufo part din cikin tashin hankali.
Salimace ta soma fadin ayya girma ya fadi ke Rahama daga mata hakana don Allah
garin yaya haka ya faru kuma yaushe kika shigo gidan nan ma inji mama ?
Jin abinda suke fadi din yasa na daga akanta ga idanuwanta sun firfito waje
tana haki ta soma fadin wallahi ba zan yarda ba yau gidan nan za ayi bala,in da ba
a taba yiba kuwa kun tarar min ke nan ?
Da keda yar uwarki ko nace kunji munafuka har me za a tarwa anan mace haka kamar
faifai ba nauyin komai nidai din da kikace zaki murza na murjeki son raina yau din.
Tayi kukan kura akaina tana fadin wallahi baki isa ba kizo har gidan nan kice
zakiyi min haka karyane wallahi na tattare bujena zuwa gwiwa don kada ya takura min
nako here hannuna nakai mata wani naushi sai a gefen fuska duk suka jaye baya dama
salima da Asmauce ke rikeni mu din don sunfi kusa damu.
Na kara samun sa,anta na taushe a kasa amma wanan ai zaluncine ku dagata mana
tunda kunga bata in mata kun tsaya kuna lallonsu kuma tana dukanta ?
Saarece ke fadan hakan cikin hasala tayi kaina wai zata dagani jinta kasa yasa ta
kai min duka nako juyo na aza mata duka iya karfina saida ta saka ihu tana fadin
kika dukeni Rahama ?
Keda kika dukeni fa ina can ina bata amsa ta samu sa,ana ta kai min cizo a
hannu tana dagowa na koma na kaimata shaka a makogoranta ta soma kakarin kamar zata
shude.
Haka na zama masu yar daban gaske a gidan inkaiwa saratu duka inkaiwa saiba maria
ta dora hannu akai tana kuka duk da suma suna dukan nawa amma Allah bai basu sa,ata
ba yadda suke so don na fitarwa kowa da jini .
Saida kyat mama da su salima suka samu rabamu fadan salima ke fadin an daiji
kunya yau tunda har kuka tararwa mutum daya ke Saare meya kaiki shiga fadan su don
Allah ?
Ke rufa mana baki mama ta fada a cikin tsawa tana fadin mara zuciya kawai da iya
fadan tsiya ki tsaya kina kallo kin kasa rabasu daga rabon fada zata hau yar uwarki
da duka haka kina tsaye ?
To mama so kike mu zama daya meyasa takai mata duka haka ake raba fada kakaiwa
mutum duka muko muna can muna aikawa juna zagi na tashin hankali ido a rufe duk a
gabab mama din data kasa komai .
Sai ranan na fahinci waye mama da kyat suka samu na fito daga part din cikin
masifa don banson na bar gidan su mayar da abin akan yar uwata dake fama da kanta
aiki daba kan ranan sungashi wajena don ban raga masu ba.
Asmau tazo har inda nake tana fadin kizo ki bar gidan nan don Allah don in baki
tafi ba fadan nan ba karewa zaiyi ba wallahi.
Na budawa idona yaji nace ba inda zan tafi saina tashi so nake tazo ta murjeni
kamar filawan datace an fada mata shiru shiru tsorone dama niba maria bace da take
kyalesu duk wanda yai min zan mashi nima ban kaunar a zauna lafiya din.
Kawune ya soma zuwa cikin wanda mama ta kira tun a get ya soma fadin asshaaa
subahanallahi garin yaya haka ya faru kuma ke dubu ?
To kadai gani ace yarinyar nan ta biyosu da masifa har gida irin haka don ta
rainawa mutane wayau komai ?
A,a mama inda ita ta biyosu ai part din mu zata nufa ko amma a wajen yar uwarta
fa ta sameta saida nace kada Saiba ta fito don Rahama taba yaran nan abu shine wani
abu don Allah ai,,,,,,,
Kaji munafunci ko zaki juya zancen yanzu Saiba datace taje ta shirya tafito da
wani bakin dogon wando da t,shirt ajikinta take fada ta nufoni kawu yana mata
tsawa.
A lokacin kuma motan su yaya ibrahim ya tsaya suka shigo gidan ankira mazajen mu
an fada masu abinda ke faru shine yace yan uwansa din suzo gidan.
Tare dasu na koma gida inda suka jawa kowa kunne kan duk wanda ya kara tayar da
zancen wallahi su zasu dauki mataki mumuna akan mutum.
Jin hakan yasa na yarda na bisu badon naso barin yar uwata ba da naga suna da
niyar illanta muna ita haka kuma mijinta dake kusa ya kamo hanya zuwa zaria hankali
a tashe kar wani abu ya samu matarshi din.
Gaba dayan su na barsu da tabona a jikinsu zakice ko wani abu na samu nayi masu
illa haka dashi duko hannunane yayi masu wanan aikin haka ?
Ana gwadawa bafulatani hanyar keta muda in muje daji muke gwada karfin mu da juna
don gudun ta taso a garemu .
Kodana koma gida daki nashiga bance da iya komai ba jin hannuna yana son takura
min da tsami yasa na gasa jikina da ruwan dumi na shafa rob na sauya tufafina
wajajen karfe biyar na fito falon.
A lokacin kuma kawu ya shigo gidan shida mama sukayi sallama sai lokacin iya
kejin abinda ya faru a bakinsu don irin fadan da mama din take min akan me zan hada
har saratu don tana rabamu ?
Dakata Dubu ban fa fahinciki ba shin da saratu akai fadan nan koda yar nan
Nusaiba don zancenki yana nuna da mutum biyu akai fadan nan haka ?
Iya dasu biyun nefa duka tayi fada haka daga maganar fatan baki zaki dinga kai
masu duka kamar kina jirace dasu dama ?
Kaiya iyan ta fada ta kara fadin nace kaiya dubu ina hankalinki ya shigane wai
har hakan yakai ga faruwa ?
Ba yau ba kinsan halin yaran nan haka suke wanan dabi,an takaiwa yar uwarta duka
daga magana kadan sai duka ita saratu ya akayi ta shiga zancen shine ban gane ba ?
Wai rabasu takeyi shine kawai ta,,,, dakata muji daga bakinta ai tana da hujjan
yin hakan tunda ba hauka tayi ba ko ?
Jin abinda iya ta fada yasa na soma magana banji nauyi ko tsoron idon mama ba
don zuciyana daya bushe a lokacin komai zai faru ya faru shike nan nace.
Ina school Maria ta kirani tana fada min zancen rashin lafiyanta shine na kira
yaya nace zanje na ganta dana isa ina jin yunwa na dauki youghout ina sha nan dai
na fada masu komai tas har dukan da saratu din takai min.
Kaiya iyan ta fada a hasale ta kara da kin min daidai gobe ta koma in halintane
tunda bata da mutunci ita a fakaice ta shigarwa masoyiyarta fadan ko saita hadu da
fulani sukai mata maigaba daya.
Ta dauka ta hada fada zataci bulus ko tunda ta zata irin sakarancan ne da suka
saba tauyewa su zalunceta tayi ta kuka ana dariya gobe su kara in halinsune iyan ta
fada.
Amma iya wanan abu yayi yawa ta yaya zata bisu har gida tayi masu wanan aikin
kamar an turota tayi masu hakan sai iya ta dubi mama tace kila nice na turata tayi
masu hakan ko ?
Bakiji kunyar wanko kafa zuwa gidan nan kina wanan maganan ba dubu aure fa ba
bauta bane dubu duk abinda ya faru dama an shirya a tozarta yarinyar nan ne sai
Allahnta yafi nasu ya dorata kansu duka shine kuma yanzu don an daki yarki data
saya aka sayar mata kikazo fadan haka ?
To ki bari mijinta ya dawo dubu sai kisa a ranan ya saketa ina shike nan tunda
kina da power hakan a hannun ki idan bashi ba wanan abin kunyan ina na taba jin
haka ?
Fada ya hadata da abokiyar zamarta yarki ta shiga ta saya an mata dukan tsiya
yanzu kinji haushin hakan tunda ba ita bace aka samu sa,anta akaiwa hakan ?
Iya na yarda yaran nan da goyon bayanki suke haka tana ganin tafi kowa a yanzu
don an nuna mata fifiko akan abokan zamanta har take ganin zata iya dukan saratu a
gabana ko ?
Yau muna ga rasulu shine zancen mamakin iya idan abu ya daure mata kai shi kuma
ta furta a lokacin cikin mamakin mama dubu din dake gabanta.
Tace yanzu ai gata nan idan kinzo sakintane saiki bata takardanta kowa ya huta
ina zance ya kare tunda baki iya tsayawa can ki tsawata yarki datayi abin kunya ba
haka ?
Iya ai abin bakai can ba don dai kawai abinda ya faru kar a koma hakan ne yasa
mukazo mu tsawata mata don gaba kada a ,,,,😑😑 kai dakata don Allah ta fadawa kawu
daya soma magana.
Tace bakinku daya kowa ya sani kunji zafi ba itace akaiwa duka ba don baku da
kunya kuka kwaso jiki zuwa nan kuciwa yar mutane mutunci ko ?
To Dubu kin kai ga yadda kike so ai yau gari ya dauka ga abinda yarki dake kuka
taru kukaiwa matan danki har da kishiyarta abin kunya kamar yar nan zakuyiwa taron
dangi haka dubu ?
Ganin yadda iya bata basu daman magana ba yasa mama ta soma fadin iya kinsan
dole in tsawatawa saratu ai duk abinda ya faru itace ta jawoshi.
Don anba yaran nan abu zataje ta fadawa uwarta ita kuma don bata da hankali
takwashi jiki zuwa fada duk nayi masu fadan hakan amma yadda yarinyar nan tayine
bata kyauta ba tunda muna wajen muna tsawata mata ai.
Daga gefe na bude baki nace mama kuyi hakkuri don Allah amma ni banje gidan nan
da fada ba itace tazo ta sameni ta soma zagina ganin tana da niyar kai min duka
nima nakai mata.
Amma da nazo yakamata ki dubi tsufana ki ji me nake fada aiko ayi hakkuri nayi
kuskure hakan ko gobe ta kawo maki kada ki kyalesu tunda da niya sukai hakan iya ta
fada.
Keko iya inji kawu ni tayi min daidai yau don Allah ya nuna masu mugun abinsu a
fili gobe su kara in halinsune gida kuma ba zata fasa shiga ba tunda gidan
mijintane kuma yar uwarta na gidan zaune dole ta shiga.
Ai don haka muka taso iya amma kin hana ayi magana kamar kina zugatane fa iya
irin abinda kike fada yanzu ?
Dauda so kake su daketa taki ramawa kome don ban fahince kaba har yanzu yarinyar
nan kowa yasan halinta magana ba magana ba duka ne zata kaiwa mutum .
Ba haka tayiwa Salima ba wani lokaci kan dan maganan fatan baki kuma yarinyar nan
tasani suka dai samu suka tafi don magariba daya kawo jiki lokacin.
Tunda na shiga daki ban fito ba don gaskiya jikina yayi tsami abinda na dade
banyi ba biba tashigo ta sameni take tambayana ta kawo min abincine nace tea
zansha.
Zata fita nace ta miko min wayata a jaka ta dauko min miscal din dana gani a
lokacin bana lafiya ba duk kuma nasan akan abinda ya faru dinne ake kirana din.
Nasa kiran kusan goma sha hudu gana yaya habu har ukku sai na Nafisa da anty
salma na anty Salman na fara dauka .
Tana dagawa take fadin ke Ramaah meya kaiki hada jiki da kishiya ashe bana fada
maki hakan tsiya yake kawowa ba ga mutum ko ga miji ?
Idan ban dauki mataki ba dukana zatayi anty tace taci bulus aida kikayi kadan
sai ki bari amma duka haka kamar wace taci tauri Rahama ?
Maria tace min taji tsoronki dazun ta dauka ko kina da iskane tace fuskansu da
jikinsu kin masu illa sosai a wajen fadan ?
Na kwashe yadda abin ya faru na fada mata sai naji tace kin min daidai wallahi
ya kirani hankali tashe yake fada min shi a zatonshima wai ciki gareki kikaje kina
fada haka ?
Tsuki naja jin abinda ta fada tace Allah yace with dis condition naki zakije
kina fada a illantashi idan wani abu ya samu cikin jikinki fa ?
Kyashi anty ni banda komai a jikina na fada muka kuma koma zancen su din inda
tace wani lokacin irin haka idan ba haka ya faru ba dama ba a samun natsuwa ai.
Yanzu tunda ta gwada hada jikin taga baci zata koma wani sallonne kuma in bi a
hankali don zata fara makirci tunda taga uwar mijin tana kama mata.
Ita kuma yar iskan nan sai taji a jikinta ai nace na dauka ai sakina zaiyi idan
ya dawo tunda haka uwarshi ke so na daki yarta a gabanta ke kin min daidai wallahi.
Maria tace ai mijinta ya dawo ya zo ya karanta masu hauka iya son ransa yace
wallahi duk wani abu ya samu matarshi sai yayi karasu kuma yace zai bar masu gidan
ya koma gidansa ya gaji da jidali kullum.
Ashe ya dawo a gurinta nake ji tace ai ya dawo kuwa yayi masu cin mutunci sosai
don saida ita Saiba ta rufe daki akace saboda yayi niyar dukanta dakyat aka samu ya
hakkura amma yace zai bar gidan don ba zai yarda ba.
Mun kai wani lokaci da ita wayan shi dake shigowa ne yasa na katse kiranta din
na dauka don inji me zai fada a ranan kowa ina iyawa dashi don abin ya isheni
gaskiya gara dai kowa yasan matsayinsa zai fi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join
my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
6️⃣3️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
A sanyayye na amsa mashi murmushi naji yayi sabanin fadan dana zata zai min a
lokacin yana fadin ashe yar kokawa na aje agida ban sani ba ?
Abinda ya fada din yasa na sauke murmushi lokaci guda yace baki kyauta min ba
Rahama with your condition zakije kina fada haka idan wani abu ya sameki fa baki
tausaya min ne don Allah ?
Kayi hakkuri don Allah ya daurone idan ban rama ba a lokacin sai su dauka ina
tsorone shiyasa na rama dukan da sukayi niyar yi min din.
Nasani amma kinsan illan hakan ai ina daukanki mai hankali sai gashi kuma kina
son kifi Saiba hauka agaban kowa kuka dinga fada kuna zubar da mutuncin ku why zaki
biye masu kuyi hakan don Allah.
Na sake fadin kayi hakkuri yaya muryata tana nuna alaman karya a lokacin is ok
amma don Allah kada a maimaita hakan naji komai nasan ba laifinki bane zuwa gidan
kuma har in zai kawo matsala idan ban nan don Allah Rahama ki daina.
Katseshi nayi da fadin saboda su ba zanyi zumunci da yar uwata ba ke nan banje
donsu ba kuma ban takalesu ba sune suka kirkiro abinda zamuyi fitina har haka ai.
Nasani amma itama Maria din dole subar gidan ai tunda har haka ya fara faruwa
yanzu haka mun gama magana da habu zai gyara gidansa su koma ciki zuwa next week in
sha Allahu .
Bance kicewa kowa komai ba duk da ance mama da kawu sun sameki a gida saidai
banda fargaban hakan tunda iya tana gidan a tare dake yasa wanan bai dameni ba amma
ki kula don Allah hakan ba mutuncin ku bane please ?
Nagode na fada sai nayi shiru shima dan shirun yayi ina jin yadda yake sauke
ajiyan zuciya a bangareshi kafin yace ina dai baki ji ciwo ba kema ?
Banji ba na fada a takaice yace sure nace umm,umm Allah ya tsare ya jikin ita
maria din duk da ance kun dai fasa mata kaya amma ba a tabeta ba kinga illan fada
ke nan bakyau don Allah.
Tausayi ya bani yadda yake maganan sai naji ba dadi a raina karon farko da nayi
nadaman faruwan abin kenan a kasan zuciyana wanda hakan ya ja na rage irin zafin da
nakeji kasan zuciyana nasu.
Washegari saiga maria a gidana ita da yaya Habu sukazo nan muka zauna falo dasu
da iya nan naji yadda ransa ya baci ya fada ya kara zai bar gidan tunda mama bataga
laifinsu ba sai na matarshi da yar uwarta.
Habu kuyi hakkuri akwai abinda ku baku sani ba game da uwarku ina nan