Showing 132001 words to 135000 words out of 328222 words
Chapter 45 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
Saidai zanso ki haifa min ya mace mai kama dake sak mai irin tsayinki da hancin
nan naki da gashin nan yakai hannu yana kokarin taba gashin kan nawa nayi saurin
gwaucewa ina murmushi.
Falo muka fito tare zuwa dining ya zauna na fara bude abincin ina kallon sanda
ya lumshe idanunsa naci gaba da hada mai na aje komai na zagayo na duka a gabanshi
yabini da kallo.
Takalman dake kafanshi mai belt don na kula yana son saka irinsu shi din dan
gayune na karshe idan yai shiga saikin tsaya kina satar kallonsa wani lokaci.
Komai nasa a nutse yakeshi nasan kuma shida kansa ke tsayawa yiwa kansa lalura
wani lokacin koda wanda ya kamata ace mace tayi masane ya rigada ya saba da hakan.
Kafafuwan nasa ya kara miko min na karsa zare dayan ina kokarin mikewa naji ya
dafa kaina yana fadin sharp kinga na manta da takalma a kafana na zauna.
Allah ubangiji yayi maki albarka Rahama sunan ki yayi daidai da halinki na kirki
da sanin ya kamata daidai da addini yadda ake son mace ta kasance harta bawa yara
tarbiya ke nan.
Nidai dai murmushin iya baki na sauke na juya da takalman zuwa dakinshi naji
yana fadin wai ina Nafisane ?
Ta tafi gida dazun nan ta wuce wai zataje ta duba su inna sai yayi dan murmushi
ya kada hannu a ruwan dake gefenshi yana dauraye hannunsa .
Na juya nakai takakman dakin na dauko mai wasu sifas masu kamar gashi a jikinsu
wanan duk hikiman anty Salmace saida ta jaddada min kan wanan akidar na kula da
bashi takalman tafiya a cikin gida ta kuma nuna minsu din hakan yasa na fara amfani
da nasihar nata a lokacin.
Na zo na aje masa a gefe inda inya daga zai saka na zauna a kujeran dake
gefenshi abincin naga ya debo ya nufo bakina dashi na noke kaina ina fadin zanci ai
idan ka gama.
Bai tsaya saurarena ba ya mika min dole na bude baki na karba a haka mukaci
abincin waya ya mikar dashi daga wajen wanda na fahinci daga matansace dake mashi
cin mutunci a cikin wayan a kaina.
Kayan na shiga tattarawa na nufi kitchen dasu ban fito ba saidana dauraye na
kife na dawo nagoge dining din na nufi dakina don ya shiga dakinshi tun lokacin.
Kayan jikina na sauya na kara muke jikina da dan kamshi mai saukin shaka na
dauko riga cotton bubu mai gyale na daura a kaina lokacin wayata tadauki kara ina
dubawa anty Salmace a layin.
Na dauka da sauri muka fara gaisawa ina tambayanta yara da gajiyan hanya take
fadin suna lafiya suna wajen lesson .
Kafin naji ta dora da fadin to yaya ashe ango ya dawo sai ta kwashe da dariya
nima a bangarena murmushi nayi kawai a lokacin.
Take fadin komai daidai ko murmushi mai sauti na sake kawai tace ato na dai fada
maki yanzune zaki koyi narkar mashi da zuciyanshi akanki kada ki tsaya wanan sanya
da kauyanci.
Kiyi kokari ki kafa taki gwaunatin a zuciyarsa ta yarda zai mata da irin ukuban
daya saba dashi wajen wa yan can garorin matan nasa.
Duk abinda kika sai zai farauta masa Rahama ki daure kiyishi don Allah kicire
duk wani kunya da nauyi ki nuna masa kulawa fiye da zatonsa tunda abinda yajashi
gareki kenan dama samun natsuwa a wajenki din.
Muryanshine ya katse muna hiran da yashigo yana fadin kin kwantane Rahama ina
son na leka gidancan in dubusu ban samu tsayawa dazun ba dana shiga abubuwa sunyi
min yawa a lokacin.
Saika dawo yaya agaidasu dasu dasu hajjaju da iya ya amsa da zasuji har yakai
kofa ya juyo yana fadin kada kice zaki sake wani girki ki huta hakana sai gobe don
Allah zan riko muna abinda zamuci da daren.
Saida yakai kofa nake fadin da anty Nafisa zaka dawo ko ?
Sai naji yace kina son ta dawone shiru nayi na kasa cewa ehh don irin kallon da
yake jifana dashi lokacin ya juya yana fadin banjin hakan su dan huta a gida kwana
biyu.
Yana fita muka cigaba da hiran mu da anty salma din dake min sherin a,a komai
zam kan ga alama nan naji da kunnuwana .
Kin gane yanzu fa abin kamar compertion ne a tsakanin ku kowa ya biya allonsa ya
wanke suma zasuyi kokarin ganin kin zama banzace a wurinsa don haka shiga gidan
mata biyu akwai hatsari babba ga mace sai ka iya takonka sosai dasu.
Mun dai dauki lokaci zancen ke nan guda akan zamantakewan aure ta yadda zan
zauna da kowa kafin mu dauko hiran su hjy yabi muna dariya wanan ya shagal dani na
manta da komai saida aka kira sallah na mike zuwa alwala.
A gidan su kuma yana isa yaran ya sama a kofan ya Habu suna wasa da Abba ya
fito mota ya nufi wajensu.
Zaune yayi ya dorasu saman jikinshi yana dan jansu da hira irinta yara jin shiru
yasa maria bude falon don taga ko Abba yana kusa.
Sai tayi arba da ya J din ta dan daburce don tunda abin ya faru basu hadu ba sai
wanan karon suka hadu dashi din.
Shine ya fara gaida ita wanan karon taji abin wani banbarakwai tana fadin sannu
da dawowa yaya ya hanya lafiya yaya gida dasu Abba koda yake gashi nan yana fada
min wai yana son karatu .
Tayi murmushi ta juya zuwa ciki ta barsu a wajen yake fadin gashi ai zamu shiga
ciki take fadin dama wanka zan mashi nake nemanshi.
Ya iza yaron zuwa gareta ya rike hannun yaransa zuwa part dinsa inda ya samu
matan basa a zaune falo duk da suna a waje daya kowa da abinda takeyi a lokacin.
Sallamanshi ma da yayi sai Asmauce ta amsa mashi da kyar itama dai a cikin
basarwa tayishi bai kula da hakan ba ya zauna a tsakiyansu
Yana fadin ya Asmau ya karfin jiki kuma sai saiba taja tsuki ta mike kafin ma
asmaun tayi magana tabar falon a cikin hasala binta yayi da kallo ya dawo da dubasa
ga Asmau sake fadin lafiya gamu dai muna ja ai.
Ai watan haihuwan ki ke nan zai kama ko tace haka akace saidai idan Allah ya
raba kawai yanzu Allah ya rabamu lafiya ta amsa da amin.
Badai wani matsala ko tace da sauki gaskiya kinje asibitin da kikace tace naje
naga likitan shima yake fada min edd dina ok ya fada.
Yarshi data hau saman cinyarsa tashishi ya biye mata suna hira kafin ya mike
ya shiga wajen saiban dake kwance ta kafawa siling din dakin ido tana tunane.
Nusaiba ya wai meye matsalankine haka ta dago daga yadda take ta watso mashi
harara tana fadin matsala matsalan me kagani a wajena ?
Naga kin gani kina basarwa mana kamar baki ganni ba tace oh so kake in daukeka
in goyaka tunda ka tuna damu kazo garemu yanzu ?
Yayi murmushi yana zama a bakin gadon daidai kafafunta ta wani jaye kafanta da
sauri gefe daya ya sake fadin wai meye hakane wai ?
Cikin kyarmar murya ta soma magana tana fadin me kuwa ko kagawani abune a
wajena kaje wajen wace kake tunanen ta fimu wani abin daka zabi tozarta mu a idon
mutane .
Tozarci kuma ya fada tace koma meye dai kaika sani da abin kunyanka tunda baka
daukeshi komai ba ya mike yana fadin Allah sarki auren da nayine abin kunya kuma
yau Nusaiba ?
Ashe aure yana zama abin kunya a wajen ki don na auri wace kika sani na hadaku a
waje daya a matsayin matana ?
Wanan kuma kaiya shafa don ni wanan figagan yarinyar karamar yar iskan da kake
kallo a mata bata isheni ko kallo ba balle .
Allah ko niko kinga ko gajiya baniyi da kallonta da tayi min dari bisa dari ko
kifta ido idan tana kusa ban iya yi yanzu .
A hakan kai har kaga mata ke nan ita dai Ramaah din dana sani ko ancanza mata
kamane kuma ?
Ya gyada kai yana fadin itafa yanzu ai in ba itaba banganin kowa a mace yarinyat
data san zafinka tasan ciwon ka ako wani hali ka shiga ina zanga daidai da ita.
Don haka inma kushe min mata kike kokarin yi gara ki daina don ita din
tauraruwanace a yanzu tunda ba zata taba guduna ba duk halin da nake ciki kuwa yasa
kai ya fita ya barta tana ta zunduma ashar.
Ya jima a falon kafin ya shiga wajen iya daga can ya wuce masallaci bayan an fito
sallah ya dan sayo kayan sanyi da nama ya shigo masu dashi ya aje a falon yayi masu
saida safe baijin akwai wace ta iya amsawa a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
4️⃣5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Mummy zulaihat Allah ubangiji ya baki lafiya yasa hakan ya zamo kaffarane a gareki
ubangiji Allah yasa anyi aiki cikin nasaran ubangiji Allahuma Amin ya Allah.
Mama Amina kema Allah ubangiji ya baki lafiya yasa kafarane yasa hannu ya warke
a cikin kuduran ubangiji Allahuma amin sauran uwayena da bab kira ba da yayyun mu
ya Allah ka basu lafiya masu damuwa Allah ka yaye masu kamai dashi alheti a garesu
Allahuma amin jumma,at mubarak gareku yan uwa musulman duniya.
Fada yake sosai gaban matarshi hafsatu tana kara zugashi akan Habu wanan karon
fushinsa ya sauka don Habu din yake zagi saboda yana ganin shine ya kawo mashi
cikas a ranan.
Idan badon shawaran da habu ya kawo ba da duk yadda akayi a ranan saiya mallaki
wani abu daga cikin kudin nan ranan.
Amma ga kudi yana gani ido da ido amma dan banzan yaron nan Habu yai masa bakin
cikin su shigo hannunsa saboda wata akidarsa ta banza dayace wai sai ankira wasu
malamai can .
To kai malam waisu yaran nan dake gagawan fadin yadda za ayi da tasu kason a
sakebawa yayan nasu me suke nufi da hakan yanzu matarsa hafsatu ke tambayashi cikin
katse mashi tunanen da yakeyi.
Sai daya nisa ya kallota ta sake fadin yanzu kyalesu zakuyi da shawaran ya asake
karban kudin kuma a hannunsa ?
Kafa san idan suna hannunsa ba zai yarda agani ba balle a taba yakamata kayi
wani abu akai hakana malam koda baka da gadon mai fata ai kaima dai ka wahala dashi
gashi
Yaron nan Jafaru fa malam kana sane ko kashi ya rika ya shiga kasuwa dashi sai
sun zama kudi a wajensa na rasa wani irin albarka Allah yaiwa yaron nan haka ?
Dan banza gashi da iya boyon kurwa wai ace akwai wa yan nan kudin haka amma yake
daukan dan kudi ya mika maka kaine baka iya kashin kudi ba ke nan ?
Abin ne da daure kai kema kin sani hafsstu ba irin karba da bayin da sunan yaran
nan amma kamar ina aika dutsene ba abinda suka canza saima gaba gaba suke karawa.
Wai, kinji yaron nan ashe harda gidaje yake kokarin ginawa yan uwansa bai fadawa
kowa ba sai yau din nan yake fada a wajen haduwar nan.
Sai nake ganin yanzu kamar ya fara fahintar manufarmu akansu don ya fara yin
abubuwa ba tare da sani ba da farko ba haka bane na samu kansu fiye da tsamanina.
Amma sai gashi yanzu da nake hango kudi sun zauna mashi haka yana kokarin ya juya
min baya a tafiyan yanzu.
Harshi ya isa malam wallahi bai isa ba komawa zakayi a kara nemo makashi a
hannunka sai yadda kayi dashi a rayuwansa .
Shi wanan Habu dai tauraronshi bai haskawa kamar nasa nake gani don har yanzu bai
kaiga samun irin na Jafar din ba amma duk da hakan tunda bakinsu gudane shima ba
barinsa zakuyi ba ai malam.
Dole ai insan abin yi a yanzu ya zama dole na sake sabon shiri akansu kafin
komai ya jagule muna don ina ganin wancan na farkon ya dushe .
Kwance ya sameni da waya a hannuna har barci ya soma daukata lokacin ya shigo
cikin dakin da sallama tsaye yayi a waje daya yana kare min kallo kafin ya tako
zuwa bakin ya karbi yawan yana dubawa gamen din engela yana ta playin da kansa.
Dan murmushi yayi yana kashewa kafin yakai zaune a gefe daya yana aje ledan
daya shigo dashi a hannunsa sai lokacin naji motsin zaman mutum a kusa dani na dan
zabura kadan naganshi .
Komawa nayi ina sauke numfashi tare da dago fararen idona na kalleshi ina furta
sannu da dawowa a bakina .
Sai naga ya lumshe ido yana amsawa yace har kinyi barci by this time sorry na
tsaya da iyane ban fargaba ashe lokaci yaja haka ban sani ba.
Allah sarki Iya suna lafiya a cikin hamma dake nuna kasala ya amsa da lafiya lau
suna gaida ke nayi dan murmushin da nasan zan tsokaleshi na yunkura da niyar tashi
zaune .
A lokacin naga ya dadirce da kyat ya iya sassauta muryansa yake fadin ina jin
yunwa fa Rahama ?
Na juyo da sauri ina fadin kace kada nayi girkin dare kuma yace ehh muje falo ki
ban abu yana can na aje hakan yasa na yunkura na mike zaune daga kwancen har jikin
mu yana gugan juna dashi na samu na mike tsaye.
Zanin dana daura saman rigar barcina na gyara dauri zan fita ya bini da kallo
tare da ajiyan zuciya ya mike ya fito falon shima ledan na hango saman center table
din falon na nufi wajen ledan har na duka zan bude kuma na dago zuwa kitchen na
dauko plate da su knife da ruwan wanke hannu irin wanan sallon mazan nasanshi a
gidan anty sallama ai.
Na samu ya zauna ya baje saman kujera irin zaman a bude kafa din nan ya dafe
goshinshi da hannu dayan shi yana murzawa.
Na duka na fara kiciniyar budan ledan naga take away irin wanda kake iya hango
abinda ke cikin roban da alama dai kamar ganyece da wasu tarkace haka.
Saidana bude naga rabin kazace da ganye da aka gyara yaji hadin turawa sai dan
shinkafa manne a gefe daya ko wani roba haka yake da abin.
Dayan ledan na jawo dake ta maiko da kamshi kayan cikin ragone a cikinsa mai yawa
sai kamshi yakeyi anyi mai irin gashin zamani din nan dayan kuma shima dai namance
ta rago gassassa a cikinsa yaji su albasa da kabeji da kayan kamshi.
Saidana gama hada komai yadda ya dace na dago kai na kalleshi ina fadin
bissimillah yaya sai naga ashe duk hankalinsa yana kaina shima a lokacin.
Sai naji yace ki zauna tare zamuci ai dake nasan bakici komai ba na noke kai
cikin kunya ina fadin idan ka gama zanje daki inci ai.
No no wai kunyata kike jine yana magana yasa hannusa daya ya jawoni zuwa jikinshi
ya zaunar dani saman cinyarshi.
Noke noke na farayi ina kokarin zullewa don hakan da yayi min din bakon abune
tunda ban saba hurda da namiji ba haka ko yan uwanmu maza ba tare muke rayuwa ba a
rugga yunda su suna yawon cinrani.
Kokarin kaimin a bakina yake a dole saina karba na dai karbi na farko amma
taunawa na kasa hadewa a gabanshi ga idon daya tsura min wanda yasa na fara kwarewa
lokaci guda.
Ruwa ya miko min na dan kurba bai duk da haka bai yadda ya sakeni ba a rikon da
yayi min dole ba sarki sai Allah na biye mashi ina karba a kunyace ina hadiyewa a
cikin kunya.
Saida yaga na koshi ya barni na koma gefe ina kallonshi yadda yake cin abincin
ya tabbatar min daba karamin yunwa yake ji ba lokacin.
Ya gama na kwashe kayan zuwa kitchen na dauraye na fito har lokacin yana zaune
yana waya a wajen dana barshi daki na nufa harya gama wayan nasa ashe barci ya
daukeni.
Har ya gama ya shigo dakin ban sani ba a cikin barci naji ana tabani hakan yasa
na dan yi niyar dagawa sai naji ya matseni a jikinsa yana wasu maganganun da na
kasa iya tantancesu a lokacin.
Ga kasa daya dora a kafadana ya sakarmin nauyinsa ban gama mamakin hakan ba naji
yana sumbatar wuyana hakan jikinane ya fara rawa lokaci guda.
Abinda ya kara dumatani jin wasan yau bambanta dana dareb jiyan da yake min yafi
na daren jiyan don ya bambanta da wasan da zan tsaya fada da baki a nan.
Sai karfe shida da rabi ya samu sallah safe balleni da saida nayi da gaske na
iya lalabawa zuwa bandaki na tsabtace jikina.
Ga zuciyana da tayi min wani irin nauyi da ba zance ga daliliba don nasan wani
abu daga rayuwata ya tafi ke nan sabon rayuwa yazo min a yanzu duba ga yadda bani
samun natsuwan barci a dan tsakanin nan.
Har na idar da sallah na samu na mike na gyara gadon na sauya shimfida da kyar
na koma na kwanta don zazzabin da nake jin yana son kamani a lokacin.
Hakan yasa ina gamawa na koma na kwanta da niyar gari ya dan kara wayewa in
daure in fito kitchen ashe barci ya daukeni mai nauyi irin barcin wahala din nan
bana dadi ba dai kam.
Sau biyu yana shigowa dakin yana samu ina barci gashi ko karyawa banyi ba ga
abin kari dsyasa