Showing 18001 words to 21000 words out of 328222 words
Chapter 7 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
yake ita bata son yawan hayaniya .
Sunyi mamaki kwarai da irin abinda mama Dubu ta aiko masu dashi nan gidansu su
raba ke nan yana can gidansu baja baja ke nan tunda har ta iya basu haka ?
Kai tsaye ya Jafar motarsa yabada wanki a nan kasan unguwarsu ya hau mashin zuwa
gidan kawu Dauda da sakon tsarabanshi cikin buhu.
Ya samu baba din ya fito zai fita ganinsa hakan ya dakata yana fadin malam kaine
tafe yaushe garin ?
Yace jiya da dare kawu yana fada yana kokarin dauko buhun da mama ta bashi ya
shiga masu dashi cikin gida kai tsaye nan suka tsaya gaisawa da matarshi tana mashi
yaushe gari ?
Sai bayab sun gama gaisawa yake fadin mama tace a shigo da wanan au ka biya ta
gidanta ke nan kawu ya tambaya yace tana wajen iya ai.
Kace tayi tataki zuwa kwasan lada nimafa yau nake zancen naje nagonasu na kwana
biyu ban lakasu ba kawu ya fada ya kara da yaya wajen iyalin naka suna lafiya Jafar
ya bashi amsa.
Fita sukayi tare da kawu din dake tambayanshi baizo da mota bane wanan karon
yace nazo da ita kawu tana wajen waki nakaita can tudun wanda.
Ai hakanma na dakyau wuri suka samu suka tsaya daga kofa kawu din ke fadin naga
kamar kazo da magana a bakinka ?
Yadan kara rankwafawa kafin ya fuskaci kawu yana fadin nazo dashi kawu shawara
nazo nema akan wani harka da nake son fadawa shine nace barin nemi shawaranka muji
indan hakan zai yuyu ?
Nan ya kwashe yadda sukayi da Meiambe ya fadawa kawu din shiru kawu yayi inda
Jafar din yaga yana kokarin tsugunawa kasa shima yabi sahunsa suka kai kasa din.
Can yanisa yace tau malam Jafar bakin wanan abin ba son hanyar karuwace saidai
ina tsoron harkan kudi a yanzu .
Don rikon amana haka abune dake son taka tsantsan duk da banda shamakin hakan a
kan Jafar saboda kai ko ince har yan uwanka kuna da natsuwan zuciya sosai kan
duniya don gwargwado kuna da kamun kai har yau Allah ya tsare ya kara karewa babu
dan daya taba dauko muna magana a cikin ku.
Don haka Jafar ba zanki shawaranka ba tunda hanyace ta samu amma shawaran da zan
baka shine kafin muyi komai ya kama mu binciki idan ba wani matsala ka bari zanje
gidan yaya sale na kusfa na fada mai a roka muna Allah a cikin lamarin .
Saida Jafar din ya sauke ajiyan zuciya kafin ya karawa Kawu haske akan yadda
abin zai gudana da kuma irin yadda yake so shima a ta bangarenshi abin ya kasance
kawu yace ya fahinta insha Allahu zaiyiwa yayansa magana zaiji komai da yardan
Allah kafin ya tafi da haka suka rabu da kawu din kowa ya kama gabansa.
Suna fita daga cikin gidan nasu ya kama fabanshi yafi ganewa wanan unguwan daya
taso a cikinsa don ana kowa nasu yake wancen wajen a yanzu ya zama kamar sabon
wajene garesu.
Abubakar din shagon sanusi ya nufa sukai daidai da sanusi din yana shagon nasa
ta sayar da waya a kofa ya tsaya bai shiga daga ciki ba duk da ya saba shiga din
amma a yau daga kofa ya tsaye.
Sanusi yaji dadin ganinsa sosai sai faman washe baki yake yana fadin kai mutumina
kace min har kun dawo ashe tafiyan bamai jimawa bace dama ?
Tafawa sukayi suka soma hiran bayan rabo inda shi sanusi din ke bashi labarin
abinda ya faru cikin unguwa sai yaga hankalin Abubakar din baya tare dashi lokacin
sai waya hannunsa dayake faman dannawa hankalinsa ya dauke dashi.
Yasan halin abokin nasa don haka ya bashi lokaci tun safe yake faman kiran layin
ta amma baya shiga sai kuma hakan ya daga mai hankali a zatonsa an karbe wayan ne
don yadda yake tunanen suna cikin matsi akan hakan.
Dafashi sanusi yayi yana fadin lafiya kake kuwa abokina naga kamar kana cikin
damuwa niko naso na gama baka labari in fada ma riban da aka samu bayan tafiyan ka.
Barshi kawai zuwa gobe idan nashigo ya fada ya juya ya soma tafiya hankali tashe
har lokacin yana gwada sa,anshi ga kira ko zai shiga.
Garba sadauki garba gagare Abubakar mazan fama irin ku biyu ke gyara gari kwana
biyu ashe ka dawo daga tafiyan ?
Kai ya daga a hankali ya kurawa matar ido yana son tuno ta kwalan kanta yasa
yayi saurin ganeta ita matar ranan da sukai tafiya data shiga da maciji gidansu.
Fuska ya tsuke a waje daya sai dai duk da hakan saida yaji kawai ya gaida ita
don baisan wacece ita din ba da take faman bibiyan shi tambayan daya fara yiwa
kansa kenan a zuciyarsa.
Baabba ina wuni ya fada sai tayi murmushi tace dashi kada kaga na kulama yarona
akwai abinda nake son ka sani game da rayuwanku na fadama ka fada wa mahaifiyarku
inda nake ko baka fada bane yasa bata zo ba ?
Yanzu haka naga hankalin ka a tashe yake don baka samu mutumiyar ka bako kada
ka damu zuwa yamma insha Allahu ka gwada zaka sameta.
Saidai ka kula da amana taraiyanku akwai nasara don kusan ince ka tsira daga
sherin magautanka habu.
Saidai yan uwanka amma a gaskiya in mahaifiyar ku batayi da gaske ba za,a dukar
daku gaba dayan ku .
Ka maida hankali akwai alheri da nasara daga wanan yarinyar daka hadu da ita
acan saidai iyayyenta mutanen banzane shine kadai matsalan da zaka dan fuskanta.
Habu yau fiye da sati fa ina cigiyan ka garin nan muryan Sabi,une abokin shi
yake fadan hakan ya juya yana cewa sabi,u yaya nima ai naso ganin ka sai na danyi
tafiya ina zuwa ya fada ya juya girin wanan matar don yace yagode.
Saidai wayau baiga kowa a wajen ba cikon mamaki ya juyo ga abokin nasa sabi,u
yana fadin ina wanan matar tabine sabi,u ?
Wace mata ke nan fa sabi,un ya tambaya matar daka samemu mana magana a nan mana
naga kamar nan tabi ya fada suka juya gaba dayansu har sabi,un suna kallon hanyar
cike da mamakin ta.
Ikon Allah kasantane ya girgiza kai alaman a,a amma dai ranan tashiga gidan mu
anan taji sunana ta rike sai ya canza topic din don ba zaiso ya matsa mai da
tambayan daya fara ba yasan halinsa bakinsa baida sirin rike magana.
Yanzune ma zai iya juya zaicen zuwa wani tsiga ta daban ya dauko mashi zancen
magana da soka soma dashi a ranan zasu hada kudi su sayi wani shago anan cikin
unguwa suba da haya.
Ire iren hakan yanayi sosai da abokansa na kut da kut dama yan zaria basu da
wasa wajen sana,a rigima da naci kawai kanawa suka fisu 😍.
Har suka rabu da Sabi,u a wajen sallah yana tunanen zancensu da wanan matar
dake yawo da kwalla tana tallan maciji a cewarshi.
Saidai abinda ya daure masa kai shine zancen data soma ta katse ta yaya tasan
cewa yana gwada kiran layin Yanda tun safe bai samu ba.
Gabanshine ya fadi lokaci guda wanan wata irin matace take kokarin bibiyan
rayuwatane wai meyasa ta lake min hakane ?
A iya tunanesa baiga alaman tana nemam wani abu a wajensa ba tunda bata tsaya
karban komai garesa ba yauma amma kuma me take son fadawa mamane wai ?
Data matsa tana son yin magana da mama me zata fadawa mama din akan shi shirme ya
dauki zancen da sallon yaudara irin na mutane.
Wata zuciyace ta bashi shawara ya gwada abinda tace mana ya gani idan hakan
gaskiya har yakira yanda ya sameta da yamma to akwai kamshin gaskiya a cikin zancen
ta ke nan yake fadawa kansa.
Zama ya gyara yana fadin abu sai kace almara meye hadina da wanan matar da take
son shiga min rayuwa ya akayi tasan dana hadu da Yanda ?
Gaskiya dole ya sanarwa mama barazsn matar nan a kanshi kada sai abu yazo ya faru
dashi ba yadda za ayi a lokacin yace zai sanar da ita daga baya.
Anan cikin unguwar yai sallah magariba da isha,i yana fitowa kuma suka dauki
hanya da sanusi daketa kokarin masa bayani kan shagon nasu na saida waya da kayan
wayoyi din wanda ba kowane yasan da kudin habu a cikon shagon nan ba sai iyayyensu
kadai suka sanda wanan.
Kusan lokaci guda suka iso gida da yayansa do zakice tafiyarsu gudane yadda suka
shigo din shi jafar part dinsa ya nufa shi kuma habu ya tsaya nan jikin motar
yayansa yana gwada kiran layin Yanda da son ya kure karyan wanan matar don ya samu
madugaran yi mata kashedi akansa.
Ga mamakinsa yana kira kiran ya shiga mamakine karara a fuskanshi yaji ta dauka
tana sallama da muryantan nan mai nuna sanyi hali irin nata.
Kamar kullan yadda take fadan amincin Allah ya tabbata a gareka hakane ko
lokacin ta fada gareshi a cikin sanyin murya daya sakashi cikin wani irin yanayi
shauki.
Tare dake sahibata ya fada ba tare da yashirya furta hakan agareta ba sai yaji
sautin murmushinta na jin dadin abinda ya fada a gareta da Sahibata.
Tun safe nake gwada kiranki baya shiga da fatan dai lafiya hakan ko take bashi
amsa da fadin lafiya kalau kasan da zaran bakwai yayi muna daji muna kiyon dabbobin
baffan mu nida sister .
Duk da kuwa a kwai maza da yakamata suje kiyo amma mu baffa ya zaba da mu dinga
fita mashi da shanunsa wajen kiyo acewarsa don mu koyi wahalan ruga da bamu taso a
cikinsa ba a baya.
Shi wani irin mutum ne da zai yanke hukuncin hakan yasan abinda gobe zatayi a
kanku hira dai sukayi sosai dashi wanda a cikin irin hiran yake tsuntan wani abu
daya shafi rayuwansu na baya ita da yan uwanta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Yanda wace akafi sani da maria kamar yadda aka rada mata zanen sunnanta tun
haihuwanta inda sunan nata ya samo asaline ga sunan kakarsu kasancewar hakan da
uwar bata iya kira saboda sunan sarakuwartace sai ta juya sunan a cikin harshen
yarensu da yan mata.
Dama sunan da mahaifiya ke kiran da dashi shine mafi karbuwa a bakin mutanen
dake kewaye dasu don suma da wanan sunan zasu dinga kiran yaro saboda agane.
Yanda yariyace natsatsiya ga ilimi da Allah ya bata na addini dana boko wanda
sanadin samun hakan zaman da mahaifisu yayi a Abujan Nageria ne dasu.
Inda yake sana,anshi na sayar da kayan masarufi wanda daga baya ya dan samu
kariyan arziki saiya koma gadin gidan wani dan majalisan taraiya mutumin maiduguri.
Zamane na amna a tsakaninsu don matarshi mutumiyar arzikice dama ance silan
gyaran gida yada a wajen mata don ko hjy itace tasa Yaro ya dauko iyalinsa ya dawo
dasu gidansu a inda suke wani unguwa a cikin masaka.
Zuwan yairo birni da kuma kariyan arzikinshi kuwa ya samo asaline daga kiyayya
irin na yan uwa daya taso a cikinsa kusan bafulatani da riko haka kuma duk
bafalatin asali suna da wani hanya irin ta kaucewa da suka rike dimun dimun a
zuciyarsu wanda ba kowane zaisan wanan ba sai su yasu yasun su yan wajen.
Zaki gansu adaji suna rayuwa kiyi ta tunanen ko basujin tsorone wai idan kika
zauna kikai nazarin fulani da kyau koda a birni suke kuwa zaki fahinci asalin
fulani yana da wani boyayyen siri nai kama da surkin jinnu a cikin halaiyansu.
Wanan zancen ba karya bane haka zancen yake duk da fulanin yanzu ba damuwa da
irin abubuwan haka sukayi ba suma don wayenwa kai a yanzu.
Zakiga tsofin fulani ba kasafai zasu iya barin daji ba saboda anan Allah ya
halicci rayuwansu tare da dabbobinsu da tsuntsaye da sauran namun daji dake kewaye
dasu da kuma sauran abin boye.
Kiyiwa kanki tambaya ke mai karatu su basu tsoron dajine wai ko basu tsoron dare
da abinda ke cikin darenne wai wanan amsan yana ga balafulatanin asali daya san
kansa wanda bai iya ruwa ko a cikin mutane sai gefen daji zai zauna shi kadai.
Irin hakane da Allah ya tsamo Yairo daga ruga don yawan tsagwaman yan uwa ya dawo
birnin ya fara sana,a sai suke ganin ai yaro ya lalace a yanzu ya zama dan duniya.
Abu ga Allah haka sukai ta jefo masa asiri tun bayan da sukaga da gaske yaro keyi
da zaman birni tunda har yazo ya dauki matanshi da tsohon ciki zuwa birno to tabbas
zaman Yairo birni ya tabbata tunda har ya iya daukan matarshi dele suka koma birni
da zama.
To tanbada ya hau kan yairo ke nan a yanzu ka,ida wanda suke ciki daya zai
tattara dan sauran abinda ya bari ya hade da nasa na tsawon wasu shekaru idan bai
dawo ba sun zamo nasa ke nan ladan kiyo.
Haka baffa sa,idu ya tattara sauran dabbobin mahaifisu ya hade da nasa ga bakar
asirin dayai ta jefawa Yairo din wanda gida ya fita ransa baki daya har yakai yayi
haihu hudu duk bai tako gida ba.
Allah ya rufa mashi asiri rikon amanansa yaja mashi farin jini sosai ga Alh da
iyalinsa da suka rikesu amana a tare dasu da farko zuwa yake shi kadai sai bayan
wata yace zai tafi dubo iyalansa.
Ranan Alh da hjy ya samu a tsaye yazo sallamansu akan yana son ya dan leka
iyalinshi don bashi dayane maigadi ba sukan shirya a tsakaninsu sai mutum daya ya
tsaya ya fake gida har dayan ya dawo irin hakane yazowa Yairo din .
Kudin mota Alh ya bashi yana godiya har ya dan daga hjy Falmata ke fadin wai
kai Yairo har ina iyalinka suke zaune kai din mutumin wani garine wai ?
Ya dawo ya gurfana ya soma fadin hjy ni mutumin nan Gembo ne nan wajajen tasanwa
kasan Camero saidai yan uwana da kowa nawa sun ketara yanzu suna kasam ccamero din
da zama.
Iyalina kuma suna nan masakane zaune inda na kama haya a nan na barsu suke zaune
nan masaka na Abuja ko ince nan Nasarawa yace kwarai hjy nan na kama masu haya suke
zaune don yafi min kusa da zuwa can gida.
Matarka dayace yara nawa yace dayace hjy da yarinya daya da take goyo kallon
mijinta tayi don a gaskiya suna jin dadin zama sosai da yaro mutum ne mai mutunci
da kamun kai sosai mutumin.
Ai ina ganin Alh basai na dako wata yar aiki ba indai matarsa zata iya min
komai ai gara ya daukota nan tunda ga wuri zaifi sauki.
Yafi muyi tafiya mu bar yaran nan a cikin zullumi ko yaushe ina ganin haka yafi
ai ko meka gani kai yaro ?
Hjy nikan in anyi min haka ai banda bakin godiya a hakan Allah ya kara daukaka
da nisan kwana nagode kwarai Allah kara rufa asiri amin hjy din ta fada.
Ta dora da fadin yanzu kaje duk shawaran da kuka yanke sai muji ko mu ganku tare
ya kara mata godiya donshi mijin yana ta faman amsa waya a lokacin.
Wanan ne sanadiyan zuwansu zama gidan Alh inda hjy taji dadin zama da Ashatu
mata mai kirki bata da kiuya ga tsabta da mutunta kowa har yara .
Jin dadin zaman nasu yasa hjy batayi kyashin sakasu boko ba tasa aka hada Yanda
da yaranta suna zuwa makaranta haka kuma ta islamiya da suke zuwa a tare da ita.
Wanan yasa yaran suka taso cikin jin dadi da natsuwa ba zaki taba sanin su din
yayan tugga bane don basu taba sanin wani abu rayuwan ruga ba.
Sun dauka Alh dan uwan mahaifisune don su kadai suka sani a danginsu lokacin
kwatsan ranan mahaifisu ya samu labarin rasuwan tsohonsu hakan yasa ya roka da
zasuje gida har yaran.
Ba jin komai hjy tasa aka kaisu har garinsu cikin motan gida wanan zuwan shine
yayi silan komai garesu.
Don kuwa mahaifisu bai dawo gida ba saida dafi da aka jefashi dashi inda ya dawo
yayi ta jinya daya zamo ajalinsa akarshe.
Anan babban asibitin Abuja Allah ya dauki rayuwansa ganin halin da iyalin yaro
suka shiga yasa Alh da hjy suka kaisu gida da kansa da niyar suje suyiwa yan uwansa
ta,aziya su dawo dasu daga baya.
Saidai tun zuwansu budan bakin baffa fara tambaya yayi ina dukiyan dan uwansa
daya tara abuja din ?
Mamakine ya kama Alh yace shidai a saninsa baisan Yairo yana da wani dukiya ba
yasan dai duk wata yana bashi hakkinsa kuma yaransa kaf sun dauke masu laluran
karatunsu suke biya shida matarshi.
Karshe dai ba a rabu da dadi ba tsakaninsu da Alh saima sukace zasu bar iyalansa
a nan don za a dinga zuwa gaisuwa ana tambayansu daga baya in komai ya lafa zasu
nemesu.
Sukan tunda suka roko ko yanda dake shirin zana jerabawa a bari suje da ita
sukaki suka fahinci ba su son yaran su koma hannunsu ne.
Haka suka tafi suka barsu a wajen yan uwan mahaifinsu karshe da suka gano ashe
dukiyan da suke zaton na yairone ba nasa bane ashe sai haushin hakan ya koma wajen
yaransa.
Nan wanan baffan nasu ya rufe ido yana fada yana fadin indai hakane dole su
biyasu hakkin kiyon da Yairo ya gudu bai karasa ba ya koma birni da zama don
iyalinshi suji dadi .
Wanan dalilin yasa suke zaune a hannunsu cikin