Showing 180001 words to 183000 words out of 328222 words
Chapter 61 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
barakha ta fada hannun baragurbi azo ana dana sani
daga baya ido ya raina fata shine ya dawo yasa namike zan fito sai gashi ya shigo
yana fadin kina nan ashe ?
Na amsa da ehh yake miko min goran ruwan dake cike da ruwa nabi goran da kallo
kafin na karba don ruwan ciki bai min kama da ruwan goran ba.
Ganin na karba da mamaki yake dan wuceni yace ruwan da akace a samo na hadin
maganine ai nace au ruwan doki ko ?
Ya amsa shine Auwal ya samo min a gidan makwabcin su yanzu ya kawo minshi daga
inda iya ke zaune take fadin ruwan doki kuma ?
Yace iya banjin dadin jikin nan nawa wallahi shine wani yace mu samo ruwan a hada
magani dashi ina jin kamar wancan ciwon yake son ya dawo min kuma a yanzu.
Muna ga rasulu ni yar mutum biyu kaga abinda nake fadawa uwarku ko amma ta kasa
fahintana sai shirme ta tsaya yi ita da wanan shashan dan uwan nata.
Wai yanzu ace kamar dauda zai kara aure don jaraba mace tazo ma da goyo har da
yayyu a gida ka wani haukace kana sabari kamar karamin yaro ?
Jiya nan hafsatun take ai tana muna kuka wai dauda ya juya mata baya kan ya kara
mata da yaya ko yaushe yana rugume da dan da akazo mai agolanci dashi.
Har yana batun sabawa Hafsatun da yaranta kaji min abin kunya waya saura wanan
auren kazantan yanzu banda shi mara hankali ?
Ba rashin hankali bane iya abinda yake ra,ayine kinsan mu maza idan muka hangi
abinda muke so sai aga rashin hankalin mu kan abin da zuciyarmu ya zaba.
Kaiya ba irin haka bane wanan yarunyar daya kwaso yar duniyace kaji banda
duniyanci da samun waje zakizo aure da yaya ukku ?
Sai kace wani attajiri dashi a zamanin nan da kowa keta kansa ina dai dan dukiyan
nan daya kwamsa na uwarku da yan uwakane ya ke rudansa har yake ganin shiya isa a
yanzu baijin has ?
Kawu aiya canza gaba daya iya ni har abin nasa yana ban mamaki wallahi zai baka
kuwa kaida kasan kanka amma dama ai haka dauda yake kune baku ganesa ba dai sai
yanzu.
Kaga matar nan nasa hansatu to makiran matace tun aurensu gaba daya lamarinsa ya
canza bari naga abu zama da wanan yarinyar.
Don akanta nasan dan kauye bala,ine duk abinda ake fadawa bakauye gaskiyane ko
wanan zancen auren naka waya zuzutashi ga uwarku haka banda ita da mijin nata ?
Duk wani makirci da aka kulla nasan ga hansatu ya fito kallon su nakeyi kawai
sai ranan da dubu ta gano gaskiyan zancen da idonta.
Don yanzu kowa baida kima ko mutunci a idanunta banda dauda a duniyan nan ko
kara dauda ya gitta dubu bata iya ketara mashi shi a yanzu na dauka zumuncine na
tsakani da Allah sai yanzu na fahinci makircin hansatune hakan.
Habiba taso muje falo na fada don wani zancen da suka somayi ba jin Biba bane
harni wanan yasa na fadi hakan muka fito don mu basu waje su samuyin zancen da
kyau.
Aikuwa dai sun samu kuma har ya amaryar mata da abinda ke damunsa din inda yace
mama taki fahinta a tsaya ai bincike kan zancen gashi duk inda yaje magana daya ake
fada mashi.
Jikin iyar yayi sanyi cikin damuwa tace Jafaru kasan da wanan maganan baka fada
min tuntuni ba ta ina yanzu zan somashi dole a zauna dasu muji yadda abin yake ?
Ka bari nasan yadda zan bullowa wanan zance din dauda dauda na fada maku kune
baku san dauda ba ai komai dauda zai iya idan akace tunda yana rayuwa da muguwa.
Kirikiri kaika sani saida Allah ya kawo rabuwan muna dawo gidanku da zama na samu
sa,ida da kaidin wanan yarinyar duk da hakan ta riga tayi min illa a rayuwa saidai
aina musulinci kawai a zauna lafiya.
Abincinsa nan nakai masa yaci don har biba tayi barci a nan falo da muke kallo
saida ya fito daga dakin na tayar da ita taje ta kwanta na rufo masu kofan dakin
nina na sameshi a dakinsa.
Washegari dole zan fita school ga kuma iya a gidan donshi tun karfe biyar
natashi na fara aiki kafin gari ya haska na hada mata abinci har na rana na samu
nashiga wanka saidana shirya na shiga mu gaisa da ita.
Inda na sameta zaune a kasa tafi ganewa zaman kasan nake gani muka gaisa nake
fadin zan shiga makaranta iya gashi zamu barki ke daya na wani lokaci a gidan .
Allah dai ya tsare ya kare tayi min na koma kitchen na kwaso kayan abincin ta na
kawo mata dakin na jera take fadin duk yaushe aikai wanan aikin haka yar nan ?
Murmushi nayi ina fadin yanzu da safe nan na girka ai har na rana don kada
infita in jima a can din ban dawo da wuri ba.
Allah yai maku albarka ta fada tace kwarai magananki gaskiyane mijinku yana
cikin damuwa yar nan jiya mun zauna dashi ya fada min komai kuma hankalina ya
tashi.
Tun za a ke shiri ba sai an dawo ba habu nake son yazo garin nan ina gidan nan
ya tara min iyayyenku muyi zancen dasu muna kallo yaro zai halaka ba a dauki mataki
ba ?
Sam basu da tunane wallahi dan nan shine jigo a garemu kaf amma sun kasa tsayawz
su fahinci gudun kada in makavjqra nace ina zuwa don ina biyewa zancen iya ba zan
samu class ba ranan.
Dakinsa naje na sameshi yana barci na fito wayan yaya ibrahin na kira shi yazo
ya kaimu school ranan din ban tayar da shiba muna tsaka da lectures ya kirani yana
fada na bashi hakkuri na kashe wayan nawa gaba daya.
A gidan kawu fadane sosai sukayi ashe ranan da iya tazo gidan mu har saida mama
dubu ta kaiga zuwa gidan don sulhuntasu inda take fada sosai kan yadda abubuwa suke
taso mata a yanzu .
Cikin fada take fadin abin yayi yawa mana zaman lafiya yana nema ya kaurace muna
ayanzu shigowan yarinyar nan cikin mu ni bai min dadi ba wallahi.
Na kula da zance nan nason zama gaskiya don tun ranan da jafar yace ya auri
yarinyar nan Rahama abubuwa suke nemansu tabarbare muna.
Ko sam hakan ba zai yuyu ba wallahi ba zan bari akan wanan abinda mutane suka
camfa ace kan mu ya tarwase ba dole yasan yadda zaiyi da ita ya rabu da ita.
Yar uwa mai karatu Ina kike tunanen wanan zance na mama ya fito da har mama din
ta riks tansa bakin saratu data fara furta hakan a lokacin aurena da abin yai mata
zafi take fadin .
Iren fulani irin tsiya zasu tara muna a gida fulani da akace aurensu matsalane
don sai gida ya watse ta dalilinsu shine su zasu kwaso muna su suna cika gida ?
Ko ita yarta banda matsala da fitinan tsiya meta kawowa mutane ga ya habu nan
kullum jiya wa yau ba a ganewa samunshi haka aurensu yake kamar auren buzaye
wallahi baban wata kawarmu yayi ai mungani.
A take zancen saratu din yayi tasiri a zuciyar mama don a ganin ta gaskiya
saratu take fada don gashi habu dai ba ruwanshi da taimakawa kowa saishi da
matarshi suke cin abinsu.
Hakan kuma itama matarshi YANDA bata yarda kowa yasan sirinta ba balle aji a
zauna gulma sai haushin hakan ya zamo biyu ya hade ga saratu din .
Wani lokaci kiyayyan abin hannunka yanasa a kika, haka kuma kiyayya kan baiwa ko
daukaka da Allah yayima yana sa mutane suji sun tsaneka.
Abubuwa da dama suna saka mutane sukika saboda hassada da bakin ciki da kyashi
da sukeji naka ,wani lokacin kuma rashin gamon jini nasa kaji haka kawai ka tsani
mutum a ranka irin wanan yana cikin dabi,an saratu don idan mutum bai mata ba zata
fara bakin ciki dashi dole kuma dole kaida ke tare da ita ka nuna kaima baka kauna
wanda ta tsana din.
Exam din mu yazo dole na maida hankali ga karatuna idan na fita gida sai yamma
zan dawo gida cikin irin haka wata rana shi yazo daukana lokacin matarshi nada sati
biyu da haihuwa.
Bayan mun kama hanyane naji yana fadin Rahama ina ganin yau a can gidan zan
kwana ba sai kinyi girki ku dani ba.
Duk da naji zancen a bazata amma na daure ina fadi a fili Allah ya bamu alheri
iya abinda na iya fada a bakina kenan lokacin.
Shiru ya dan biyo baya kafin yace mama ta matsa min akan Saiba ta karbi girki
zuwanta biyu ke nan gidan ki wajen iya akan hakan yau iya tace bayi hakkuri nabi
abinda take so din.
So don Allah kada ki dauki hakan wani abu a zuciyarki haba dai yaya ni hakan ma
yayi min dadi don laifina da ake gani kan hakan ?
Na banza tunda sunsan bakece kikasani yin hakan ba ai duk wanda zai zageki ya
rage maki nauyine ya daukarwa kanshi alhaki don ra,ayinane naga daman hakan.
Ko yanzu kuma hakan bashi zaisa ta samu yadda take so a gareni ba na fada masu
har Asmau din ta karbi girkin ta .
Allah ya kyauta na fada ina gyara zama cikin dan siririyar murya sai naji yace
me kuke bukatan a sai maku ne a gidan ?
Dan kallonshi nayi nace ba komai kamar a hasale yake don yadda ya hauni da fada
yana fadin ya zakice ba komai ?
Komai ke nan kuna dashi a gidan nace to yaya me zance tunda nasan komai muna
dashi yanzu saidai in za a karo munane mun gode amma ba abinda babu gaskiya.
Alright bari in naje masu sayayya sai a hado da naku barin saukeki sai in fita in
duba abinda ya dace kinsan iya na gidan yanzu.
Duk da nasan banda matsalan hakan don kina iya kokarin ki a kansu amma ina son ki
kara kula don Allah iyace makamina Rahama kin sani idan ta tsaya muna komai zai
tafi yadda muke so don haka nake son ki kara kula don Allah har ta gama zaman ta
kada ki yarda a samu wani matsala daga wajen ki please.
Ni dai banda insha Allah ba abinda na iya fada lokacin don na fahinci kamar
akwai matsala ko kuma ranshine a bace dai yake hakan.
Koda ya saukeni bai shiga gidan ba ya juya ya fita na shigo na samu su iyan da
Biba a falo zaune gaidasu nayi na zauna suna min sannu da dawowa.
Bayan na zaunane take fadin aina fada baki tsayawa ko ina yanayin karatunkine
kawai haka amma baki barin mu da yunwa ko wani abu.
Dazun uwarku tazo gidan nan naji dadin da bata sameki a gida ba duk da taso ta
dauki hakan da zafi ta juya zancen da wai baki zama gida ?
Nace ba inda kike zuwa banda makaranta ai tazo ranan da ba karatu idan bata
sameki gida ba wai banson a fadi zancekine nace hakan.
Wa yan can gantalalun da take magana meye amfanin zaman gidan nasu ba moriya ke
ai neman abinda zai zama maki alheri ga rayuwa kike fitayi.
Su kuma fa da zaman gidan bai amfana masu komai sai komawa baya a kullum miji na
kumsan bakin ciki a kansu.
Batayi fadan hakan ba sai ke da kike fita gun amfanin rayuwanki su yayanta da
sukai karatun har wani gari waya matsa masu ?
A raina nace aisu yayantane basu laifi niko tsintana sukayi daga sama dole ta
kyashewa karatuna din don tun farko ai bataso hakan ba Allah dai ya nufa da sainayi
kuma in zauna a karkashin danta da bata so.
Ni dai a fili mikewa nayi ina dariya nace iya bari in dan rage kayana in watsa
ruwa na nufi dakina ina kwalawa biba kira data dauko min ruwa insha.
Naji iya din na mata fada akan hakan da bata ganin yadda nakewa duk wanda ya
shigo ai kaba mutum ruwa arzikine ba sai ya roka ba.
Wanka nayi na fito na zauna ina cin abinci muna dan taba hira da iyan take fadin
mijinki ya fada maki yau matanshi zasu karbi girki ko ?
Don sun kaishi kara yafi a kirga wai yazo ya tare a gidan ki ya fita batunsu
nace yayi hakkuri ya koma can din Allah ya isar masa da duk tsiyar da zasuyi mai
tunda haka uwarsa ke so.
Ga abin magana da zata tsaya tayi magana akansa ta kasa sai inda ake ganin
mutuncinta nan take neman barar da mutuncin nata.
Yaron nan Yazidu ya kyauta min ashe duk dadewan nan aurensa yayi a can bai fadawa
kowa ba sai kwanan nan ya sanar da yayansa hakan.
Harda haihuwansa yanzu gashi zai dawo gida saita sake maki mara ita da magoya
bayansa su farwa matar nasa kuma tunda karuwane basu so cikin zuria.
Yayi aure iya na tambaya cikin mamaki tace yayi aurensa wallahi matarsa harda
haihuwa biyu tayi mashi mace dana miji yara masu kyau kamarki haka ?
Taso tayi fada nace fadan me zakiyi abinda yake sone yayi banga dalilin sakawa
yara ido kan zama da iyalinsu ba don ita aiba haka mukai mata ba.
Zai dawo dai yanzu wanan gidan na kusa daku da ake gyara a nan zai zauna shima
habu ashe duk nan zasu dawo din da zama.
Ai Jafar shine maganinta da yake abinsa yanzu ba shawara sai ya gama yake fada
masu wai kuma sun samu hakan sun tsaya fadan jin dadi.
Nayi masu tas yau haka kuma nace dashi munafukin yayi gagawan kai yar uwarsa
inda sukaje can wai wani bakin ruwa wajen wasu masunta masu bin ruwa .
Har can yaje ya samo abinda ya zama wahala a yanzu garesu tun lokacin na fada
mai suyi hakkuri komai na Allah ne amma basuji ba Allah dai yasa su samu matar a
raye ?
Amin na amsa dashi yayin da gabana ya fadi don in bata raye hakan yana nufin
rayuwan yaya yana cikin matsala ke nan ?
Har ya dawo da kaya niki niki Biba ta fita tayi ta kwasowa har abinda muke
dashi da yawa duk ya karo muna anzuba a kitchen din mu na mike mukai ma komai
muhalinsa nan yayi magariba da isha,i sai wajajen tara ina daki kwance ina waya ya
shigo dakin nawa.
Kamshin da yakeyi yasa na dago kai duk da nasaba ganin hakan amma na danji ba
dadi a raina kishi kumallon mata watau kishin nan akwai ga ko wata mace saidai ka
danne kawai shine mafita.
Ni zan tafi ya fada ya tsaya akaina ban dago ba nace Allah ya bamu alheri sai
naga yayi tsaye yana kallona.
Ganin hakan yasa na dago na kalleshi ni din yake kallo yayi murmushi ya
girgiza kanshi yana fadin in fasa zuwa ke nan ko ?
Da sauri nace nina isa in samesu da mijinsu ince kada kaje gunsu ai sai ace da
gaske nice ke hanaka kulasu din da ake fada.
Ok kin yarda ke nan kema ban kulasu ko nace ai haka ake fada don na fada shine
na yarda to haka zaki sallemi idan ba fushi kikeyi ba ?
Har lokacin fuskana ba annuri nace to wani irin sallama zan maka yaya ok to
barin zauna idan kin tuna sai kiyi min in tafi.
Ganin yana kokarin kaiwa zaune mannin jikina hakan yasa na dan zabura ina fadin
wallahi ba ruwana kada kasa gobe mama tayi muna sammako a gidan nan.
Bai kaiga karasawa ba naji ya hade bakin mu waje daya danasa yana tsotso na samu
na kwace kaina gareshi yana fadin rowan jikin ki kike min ke nan yau ko ?
Banice da jikinka ba shiyasa ban maka rowa ba aika sani haka dai ya gama dan
kame kamenshi yana fadin naje na rakashi dole na taso har wajen mota na rakashi
nayi mai saida safe ya tafi.
Dakin iya na leka ina mata saida safe take fadin Jafarun ya tafi ko nace ehh iya
na dan zauna na dan wani lokaci kafin na mike zuwa daki na kwanta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
6️⃣0️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Nagama shiri zan kwanta kiranshi ya shigo min nayi mamakin ganin kiranshi na daga
tare da sallama a bakina ya amsa yana fadin baki barci ba ke nan har yanzu ?
Na amsa mai da fadin yanzu dai zan kwanta ina wajen iya muna hira yace keda
kike da exam gabanki zaki tsaya hira da iya ?
Murmushi kawai na iya yi ba tare da furta mai komai ba sai naji yace nima gani
nan ina kewarki yau duk sai naji dakin nawa daban kamar ban saba kwana a cikinsa
ba.
Na miji ke nan wanda keda mata biyu a kusa dashi ya fake da fadin hakan don
dadin baki irin na maza don kawai ya faranta min rai nasan ya fadi hakan.
Ban karasa mamakinsa ba na sake jin yana fadin kilama zan dawo nan in kwanta
abina don kewanki a kusa dani da banji ba duk ya kashe