Showing 6001 words to 9000 words out of 328222 words

Chapter 3 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

yan uwa da
abokai ita ba zata yarda ya barta zaria ba don ba sakarai take irin Asmau ba miji
yana lagos ita ta zauna a gida.
Sai bayan ta shigone taso nuna hakan amma uwar miji tace bata kai can ba yadda
ta sama sun tsara abinsu haka zata bi dole shine wanan rawan kan nata ya dan fara
lafawa tun lokacin.
Saboda ta fahinci ashe a karkashin iyayyensa yake wanan yasa Asmau dake gabata
bata motsa ba take biye dasu a zauna lafiya.
A cewan mama ba zata bari ya dauki iyali yaje zaman lagos ba don kada ya
shagala da dukiyan marayu dake hannunsa .
Haka zalika zaman shi a can din zai iya dauke masa hankali da gida dudu nawa
Jafar din yake inbada rigima yaushe ma ya isa iya aje mace daya balle yace biyu.
Allah ya taimaka jafar da yan uwansa mutanene dake matukar girmama iyayyensu a
yadda suka taso da tsoron mama da iya kakarsu har girmansu haka suke masu biyayya
sau da kafa.
Zaman iya a wani bangare na gidan yayi tasiri sosai a rayuwansu dontane suke
rage wani iya shege idan su fara yanzune iya zata tsaya tayiwa wace bata da gaskiya
fes hakan yasa suke dan ragewa.
Rayuwan malam bahaushe akwai kalubali da yawa a cikinsa inda wani zubin ake
yawan tauyewa mace incinta da sunan aure.
Akwai part din da babu kowa a cikinsa instead daya ta zauna a cikinsa amma iya
tace sam hakan ba zai yuyu ba wanan din dai shine kasonsa don haka shida ya dauko
auren mata biyu lokaci guda dole ya zauna a cikin nasa hakana.
Sani Allah sani ma,aiki aka samu kawu Dauda ya rokan masa wanan filin daya
fadada girman ginansa har ya bambanta dana yan uwa saboda kara fadin wajesa da
akayi.
Saboda raba gado da akayi yasa yaran mama Dubu tun bayan auren yayansu Jafar da
hjy Iya ta koma gidansa da zama suma kusan rayuwansu a can gidan suke da zaran sun
dawo hutu zasu tare a wajen kakansu suna tayata zama wanda shi jafarne ya tilasta
masu yin hakan.
Haka kuma idan suna gidan wajensa yana da wuya ka samu gida kaca kaca a cikin
kazanta don suna tsayawa su gyara tsakani da Allah.
Tsab mama Dubu ta gama shiryawa don zuwa ta dubo mahaifiyarta da iyalan danta
don tana hasashen Asmau ta samu karuwa a jikinta yadda hjy Iya ta fada mata .
Idan zata zakice ba a gari daya suke zaune ba don shiri takeyi sosai sayi wanan
sayi wancan taje masu dashi sai kice tazo daga kauyene ganin su.
Saida ta gama shirin da komai ta fito tana fadawa mutanen gidan nasu zataje ta
duba su iya ta dan kwana biyu wanan ba bakon abu bane sunsan data saba yin hakan .
A zaton suma basu dauka zata zauna kamar take zaune din nan ba a cikinsu da Allah
ya albarkaci yayan nata sosai fiye dakowa a gidan kusan ace dai sune sukaci moriyan
gadonsu da aka raba na marigayin.
Tunda wasun su har sunka ga saida kadaran da suka gada din sun koma rabe rabe
duk da mahaifin nasu bai wani dade da kwantawa dama ba sosai.
Dama ance mai zari a wajen rabon gado shine nasa bai faye albarka ba kusan haka
dinne ya faru don kuwa su yan dakin hjy babba da aka tsaya masu suka samu kaso mai
tsoka sune suka fara wullakanta dukiyan nasu.
Wanan ya jawo tsaiko da iyayyen mata suka hana yayan nasu raba wanan baban gidan
da suke zaune ciki a yanzu inda sukai rayuwa da mijin nasu.
Tunda gidan mata hudune ras irin ginan malam bahaushe duk da ko wace bangarenta
a kewaye yake sai babban falon marigayin inda turakasa yake a nan yayi rayuwa har
Allah ya karbi ransa.
Don haka har gobe idan ka shigo kaga yadda suke rayuwansu zakice ko maigidan
nasu yana rayene amma kuma kowa a yanzu yana cin gashin kansa sai dan abinda ke
shigo masu da akan kasa kamar yadda dai aka sabayi tun baya Allah yasa mu dace ya
jikan iyayyen mu da rahama Allahuma Amin.
Daki daki tabi tana masu sallama da sai ta dawo yadda kowansu keyi idan zai dan
fita sukai mata Allah ya kiyayye zakice ba wani abu na rashin jittuwa a yadda
sukeyi din.
Saidai hakkurin wani ya dara na wanine a zaman don anyi ba daidai ba an nuna
hadama da zalama daga bayane suka sulhunta kansu kan hakan.
Yan jikokin gidan da almajirai suka dauko mata kaya suka nufi bakin titi inda
zata hau keke zuwa unguwar su iya din.
Fitanta soma zancen ta ukkunsu dake fadin yau kuma ta haka aka fito muna ba Habu
yayi tafiya ba kada ya dawo ya sauke abinda ya dawo dashi mugani a bamu tabon mu .
Sai ita amaryansu tace aiko yaya bata da haka kowa ya sani nan gaskiya ko bamu
gani ba sai an bamu in rabon mu ya ratsa.
Ni bance bata bamu ba ai maganace kawai nakeyi ta fada a hasale don ba a kama
mata yadda taso aja zancen da nisa ba ta katseta.
Yaran da suka rakata zuwa titi ta sayawa rake sai dari dari data basu suka dawo
gida da murna hakan yasa data dau kaya zata fita suke taso durrrr subi bayanta da
sunan rakiya don dan wanan ihisanin da take masu.
Itama hakan yana mata dadi tana jin dadin rakiyan yaran wani lokaci takan
daukosu suzo su wuni su koma in Jafar na gari mota tana a wadace .
Daidai kofan shiga gidan mota ya ajeta da kayanta sanin da mai adaidaita din
yai mata yasa ya taimaka har cikin get ya shigar mata da kayan kuma bai tsaya
karban kudi ba duk da tsawan da take mashi akan ya tsaya ya karbi hakkinsa amma
yaki saboda mutunci.
Kauyen Zakuwande ya samu halartan baki daga sassa na duniya mu sanman a yan
nahiyar africa manoma da masu kiyo da suka cika wanan gari dam ko ina bakine dake
halartan taron mafi girma da akeyi bayan shekaru.
Engineer Abubakar daya gama hada duk wani na,ura da zai hasko masu tauraron dan
adam dinsu ya sauko daga saman motan yana kara duba saitin dayayi da kyau kafin ya
nufi bayan mota ya bude yana dauko goran ruwa ya balle yana kokarin zuba don
dauraye hannunsa.
Hankalinsa sam bai kaiga dandazon mutanen da suka kewayesu suna kallon aikin
nasu ba sai lokacin daya gama wanke hannun ya kwankwade sauran ruwan ya cillan da
goran gefe .
A lokaci ya kula da jama,an dake waje ashe akwai inda yafi Nageria kauyanci don
goran daya cillan suka taru suna wasoson dauka .
Har da manya wani dattijo daga cikin masu rige rigen daukan gora da aka tureshi
tare da kekensa yasa Habu din fadin subbahanallahi yaje da sauri ya kama tsohon
yana tayar dashi tare da kekensa yana mashi sannu.
Tare da tambayan baba bakaji ciwo ba ko yace banji ba dana naso dai in samu
wanan jallon nasaka ruwa a ciki yara kuma sun hana.
Ina zuwa yace ya koma ya dago gora biyu cike da ruwa ya kawowa dattijun ya bashi
cikin girmamawa godiya tsohon ya fara mashi sau ba adadi yaja kekensa ya tafi.
Juyawa yayi yaje gun yan uwansa da suka zubo mai idanu saida ya karaso ibrahim
ke fadin wanan yasa danasha ruwa saina jefa gora a bayan mota.
Tausayi tsohon yabani yana bukatan gorance da ganin haka yafada ibrahim yace
tun dazun yake tsaye ai yana kallonka .
Watau wanan gari gashi dai babbane cike da jama,a kuma amma kullum basu wayewa
su kasan abinda ya kawo hakan yace ina zansan hakan ni dana fari shigota yau din .
Yace gargajiya donsu har yanzu gargajiyansu yana nan basu yarda sun dauki akidar
nasara sunsawa kansu ba aikinsu ke nan noma da kiyo komai arzikin mutum ata wanan
hanyar zai nuna halinsa.
Gaga kuwa ba zasu taba cigaba ba matukar basu yarda da nasara ba a rayuwansu
gargajiyace tsantsanta a garin nan ka duba ko tsarin shigarsu mafa dabanne kuma
kowa da irin al,adansa wajen nan.
Hakan yafi masu sauki kallo daya zakai masu kagane basuyi sakaci da addinin su
ba har yanzu yawan kabilu kuma ai duk zubin fulanine garesu ko larabawa.
Haka sukai ta hira tsakaninsu suna jiran lokacin da zasu fara gabatar da shirin
nasu don komai a yanzu hada lokaci kadai suke jira.

Kuyi hakkuri mu dauko tushen labari don fahintarku masu karatu nagode.

ZAINAB IDRI MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f

MARFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



Sallaman mama Dubu yayi daidai da jefo plate din shimkafan da Saiba tayi ya fado
saman hijjab din jikinta kafin ya gangara ya sauka kasa daidai kafanta ya tsaya.
A hankali mama tabi plate din da kallo haka kuma take kallon yadda sauran
shimkafan dayake gangarowa daga saman jikinta zuwa kasa.
Kaita girgiza ta dago ta saukewa Nusaiba kafin ta mayar kan Asmau data dafe baki
cikin tsoro da firgici kai ta sada kasa tana mai tsananin jin kunyar uwar mijin
nasu.
Da kyat mama ta iya budan baki tace yaran nan har abin yakai haka a gareku daga
haka ta juya don bari part din taga hjy Iya a tsaye itama cikin takaici take
kallonsu.
Gara dai da kuka gwada ga uwarku yau tunda ni kun raina min arzikina mata kamar
dabbobi kullum fada dan abu kadan fada kamar karnuka.
Akanku aka fara zaman kishine wai in ba auro mata ana haihuwan ku kun mayar da
gidan yaro gidan yan tasha gidan dambe .
Badon makwabta na tsoron jidalina ba da yanzu gidan nan ya cika da yan kallo
tunda kun zama mutanen bamza.
Kishi haukane wai mijin ku yana wajen nemawa kansa rufin asiri ku kuna nan kuna
tona masa asiri a cinkin unguwa sai yaushe zaku bar wanan bakin kishin nakune
wai ?
A hankali mama da ranta yake bace ta zagaya Iya tani dake masifa ta karasa
ficewa daga part din zuwa nasu wajen kokarin cire hijjab dinta da suka bata takeyi
kada ya lalace ban daki ta nufa taja bucket ta jikashi tare da yayafa omo ta barshi
a jiki.
Fita tayi waje don bata zauna ba kayanta dake can ta waje ta shiga kwasowa zuwa
cikin falon mahaifiyar ta din a daidai lokacin Iyan tani ta kara fada ta juyo zuwa
wajensu rai bace.
Ta samu mama na kokarin zuge zip din dan jakar kayanta data dauko wanda zatai
dan kwana biyu dashi a nan zani ta dauko daga ciki tana sauyawa.
Wuri ta samu ta zauna iyace ta soma magana tana fadin yau naga yaran banza a
gidan nan yara kamar tashin gareji ace babu wanda zakaiwa fada yaji.
Sallaman Asmauce data shigo tana sune kai hannunta dauke da cooler abinci tazo
ta dire a gaban mama a daidai lokacin kuma itama Nusaiban ta shigo da ruwan data
surka da postard cleak ya rine a cikin jug ta aje gaban mama din cikin girmamawa.
A,a ku dauki abinku ni a koshe nake daga gidan mijina nafito yanzu koda bai
raye bayansa basu barmu a cikin yunwa ba Alhamdullahi nagode.
Zaune Asmau takai tana dan dukar dakai Allah ya gani tasan mama mace ce mai
kawaici da kawar da kai daga abinda sukeyi bata kulawa koda ance ga abinda sukeyi a
kullum nasihanta dasu shine su zauna lafiya suba mijinsu farin ciki ga nemansa.
Fitansu koma bayansane ga harkokinsu tasan zaman kaunace ya hadasu da danta don
haka suma dul biyun tana kaunarsu tunda dantane ya daukosu ya kawo matasu amana a
cikinsu.
Yau sai gashi iya shegensu yakai har plate din abincin danta suka watsa mata
saman jiki ya watse a tufafinta ita yanzu me zatace da boyar Allah nan mace mai
zurfin tunane da kawar da kai irin mama.
Kaita kara sadawa kasa ta soma magana mama don,,,,,,
Asmau jeki kawai kuci gaba kada ku bari zaman nan dai ina son ku sanin na bautan
Allah kuyi akwai hakki da amana a tsakanin mu daku da mijinku dake can yana neman
abin rufin asirin mu.
Idan kun zauna lafiya kuji dadin hakan idan kuma kunki kome ya biyo bayan hakan
kuka da kanku kada ku kuka da wanin mu nan Allah ya gani munyi iyakar yinmu akan ku
kun kasa kwantar da hankalinku ku daina wanan shashancin kishin a tsakanin ku.
Sauran mata da suke zaune da kishiyoyi ake ganin kamar zaman lafiyane a
tsakaninsu kokari suke suna danne kishinsu a idon jama,a kowa da kuke ganin yana
zaune lafiya danne abin yake kasan ransa shin ku ba zaku iya hakan ba don Allah.
Mama wanan yarinyar yar rainin wayauce waini Asmau zata zubawa abinci a plate a
kawo min don ta raina min wayau kome Saiba ke fadan hakan ga mama.
Hannu mama din ta kara daga mata tana fadin ban tambayi ba,asiba don Allah komai
mutum yayi kansa yaiwa ina dai son ku sani ba a wullakanta abinci a zauna lafiya.
Wanan shine maganata dukkan ku nan ba zance bakusan abinda nake nufi ba tunda
kowacen ku uwarta tana da kishiya a gida.
Mama bani wullakanta abinci wullakancintane kawai ya mota innice nace ta ban
abinci cewa take naje cikin tukunya in daba shin laifine ni har na zuba mata a
plate mama ?
Amma dai kinsan niba wullakantata bace da zaki ban abinci a cikin plate kamar
nazo bara a wajen ki kema kinsan nafi karfin hakan wallahi.
Yanzu dai sai kuyi ai garara ku nunawa uwar naku halinda kuke kwana kuke tashi
dashi a cikin gidan nan ta gani ksllon Iya din mama Dubu tayi tana fadin mama kin
hada kayan na soma wankewa ?
Don dama duk aka kwana biyu mama tana zuwa gidan ta gyarawa mahaifiyarta waje
tayi mata wanki da sauran gyaran waje sai idan yan matanta sun dawo hutu suna gari
suke dauke mata hakan.
A cikin matan Jafar din babu wace zatace bari ta dan gyarowa Iya part din ta
matukar basu din bane sukazo sukayi wurin zai koma fes.
Ganin mama din ta fita batunsu yasa Saiba fita cikin hasala tabar Asmau nan
saida zata mike take kara fadin mama kiyi hakkuri don Allah.
Jeki Asmau a kula don Allah kece dai babba a gidan nan kanninku da abinda kukeyi
sukr koyi don Allah Asmau arika tausan zuciya idan rai ya baci.
Fita tayi tana tunanen irin halin mama dubu na sanyi hali macece datake rike
girmanta da kawar da ido akan duk abinda ke faruwa danta dasu iyakarta nasihan da
zaiwa mutum amfani gaba idan yabi.
Saidai ko tayi kokarin bin nasihan da ake mata hakan bai samuwa don Nusaiba taza
fito da sabon fitinan da sai tabiye mata sunyi fitina.
Ita wanan tana da dama sosai fiye da wacan fitsarariyar da tafita duk wani
fitina daga wanan nusaiban yake fitowa a gidan nan Iyace ke wanan maganan bayan
fitansu.
Taron yarane kurciya shike rudinsu a wanan lokacin wanda sukeyi a kansa yana can
baima san suna yiba zasu zauna su halaka kansu haka a banza kan namiji.
Wata rana ko ance suyi hakan ba zasuyi ba ai don girma yazo a lokacin saidai su
koma kishin mumuke wanda yafi wanan da sukeyi zafi.
Mamace take fadan hakan ta mike ta dauko tsintsiya don ta fara gyaran dakin Iya
din da yayi kaca kace ga kura ko ina a falon har makewayin data shiga yana bukatan
gyara idan zai samu.
Komai a wajen taron nan yana gudana daidai sun fara hasko wa duniya abindake
wakana wanda hakan yasa hankalinsu daukuwa da aikin don abune da yake son
natsuwa don kada a samu kuskure.
Sallah ya tayar dashi da yunwan da yakeji ya fito daga cikin motar tasu mai
na,ura zuwa lokacin wajen taron ya cika makil da jama,a tare da Sahabi suka nufi
masalacin sukai ibada ya jima kafin suka fito tare da dan zaga wajen suna kallon
irin baiwan ni,iman da Allah ya shimfidawa yan Africa.
Malam Habu zokaga kayan nono a wajen nan Sahabi ya fada ya doshi wani hanya
dashi yana biye dashi a bayansa koreni gasu nan birjit iya ganin mutum da matan
fulani dake ta kaida komo a wajen.
Sahabi din ya tsaya yana taya wani kwaryan nono hakan yasa Abubakar ya fara
raraban ido yana bin ko ina na wajen da kallo direct ya nufi wajen wasu da suka
tsabtace nasu da komai a cikin tsabta gwanin ban shawa .
Malam zoka saya baida tsami ko karni lafiyanyyen nonoce tatsin yau din nan
muryan wata bafulatana ke fadan hakan ya karasa gabansu cikin mamakin jin yadda
take hausanta na yan Nageria sak a bakinta.
Sahabine ya karaso yana fadin aina fadama sai inda kallonka ya kare a wajen nan
yaji matar fulani din na fadin wanan na shanune wanan kuma na rakumi ga wananshi da
akecewa wara da wani hausan nonoce sahihi ake dafawa ya hade haka.
Sai wanan kuma cikwai ce mai dadi baida mixed a cikinsa zakaso ka kara idan kayi
amfani da kayan don babu algus a cikinsa ko wani mixed .
Kai amma ke yar Nageria ce ko sahabi ya tambaya tace meka gani tana murmushi a
fuskanta.
Kafin tace dashi daga dai can muke ta fada tana juyawa da alaman neman wani
takeyi alokacin a cikin harshen


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login