ENGLISH DESCRIPTION
BINTA YAR JAGALIYA: THE STRUGGLE OF LIFE
In a forgotten corner of poverty and hardship, Binta was born into suffering, rejection, and a life without privilege. Some call her the Girl from the Slums, while others call her a Female Thug because of her fearless spirit and extraordinary courage.
Her life has been one endless battle. A battle against poverty. A battle against oppression. A battle against people determined to use her for their own selfish ambitions.
On the other side stands Mu'azzam Bilal Kura, a wealthy, respected, and influential politician. As he prepares to rescue his nation from corrupt leaders, powerful enemies begin plotting to destroy both his reputation and political future.
But what happens when Binta Yar Jagaliya is chosen as the weapon to bring him down?
Will money and power conquer Binta's heart?
Or is destiny hiding a secret that will unite the lives of the poor and the powerful?
Filled with romance, political intrigue, betrayal, suspense, heartbreak, and shocking revelations, this unforgettable story follows a young woman the world looked down upon as she becomes the center of a battle that could change countless lives forever.
BINTA YAR JAGALIYA: THE STRUGGLE OF LIFE
A gripping Hausa romance and political drama that will make you laugh, cry, rage, and keep turning pages until the final secret is revealed.
Will Binta become the hero everyone needs?
Or will she be the reason everything falls apart?
HAUSA DESCRIPTION
BINTA YAR JAGALIYA: GWAGWARMAYAR RAYUWA
A wani lungu na talauci da kowa ya yi watsi da shi, an haifi Binta cikin ƙunci, raini da rashin gata. Wasu na kiranta Yar Jagaliya, wasu kuma Yar Daba saboda tsananin jarumta da ƙarfin hali da Allah Ya huwace mata.
Rayuwarta ta kasance cike da yaƙi. Yaƙi da talauci. Yaƙi da zalunci. Yaƙi da mutanen da suke son amfani da ita domin cimma mugun burinsu.
A gefe guda kuma akwai Mu'azzam Bilal Kura, hamshaƙin ɗan siyasa mai tarin dukiya, mutunci da farin jini. Yayin da yake shirin ceto ƙasa daga hannun azzalumai, wasu manyan mutane masu iko sun shirya makircin da zai rushe rayuwarsa da siyasar sa.
Amma me zai faru idan aka zaɓi Binta Yar Jagaliya a matsayin makamin rusa Mu'azzam?
Shin kuɗi da iko za su rinjayi zuciyar Binta?
Ko kuwa ƙaddara tana ɓoye wani sirri ne da zai haɗa rayuwar talakawa da ta masu mulki?
Cikin wannan labari mai cike da soyayya, siyasa, makirci, cin amana, tashin hankali da asirin rayuwa, za ku shaida yadda yarinyar da duniya ta raina ta zama jigon sauya tarihin mutane da dama.
BINTA YAR JAGALIYA: GWAGWARMAYAR RAYUWA
Labarin da zai sa ka yi dariya, ka yi kuka, ka yi fushi, sannan ka kasa ajiye wayarka har sai ka gano ƙarshen sirrin Binta.
Shin Binta za ta zama jarumar da za ta ceci rayuka?
Ko kuwa ita ce za ta zama sanadin rugujewar komai?