Showing 78001 words to 81000 words out of 328222 words

Chapter 27 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

dan
uwan a yanzu.
Zuwan ummah biyu daga kaduna suna wuni a nab su duba jikin nasa ita da
maigidanta sai ya ajeta ya shiga gari wurin yan uwansa.
Ba wani rashin jin dadi ko takura a jikinta tayi fes da ita dama gwanar tsabtace
ita don haka gyara a yanzu ya samu waje.
A kullum ummah tazo takan min korafin yaushe zanzo naga mazaininta saidai inyi
dariya kawai banyin magana.
Ni damuwana yan uwan mu da muka baro a gida duk yadda birni ya lalace yafi kyau
mu muna nan muna jin dadi su kuma suna can bamu san halin da suke ciki ba .
Don ni a nawa ganin banga abinda zaisa ummah ta barsu a can hannun hardo ba
tunda ita dai ba haihuwa take nema a yanzu ba.
Har yakai na kasa magana da zata tafine nake fada mata damuwana akan yan uwan
namu maza tunda ba wasu manya bane dai.
Shine take fadin mijinta ya soma maganan hakan yana son su dawo wajenta don suci
gaba da karatunsu itace bata bada goyon bayan hakan ba kada yan uwansa suce tana
son mamaye masa gida.
Ummah ai yasan kina da yara ya yarda ya aureki don haka a taimaka masu su samu
suyi karatun nan suma bata dai ban amsa ba har ta tafi gashi ko wayansu muka kira
ba,a samun su wasan dadi suna daji inda ba service.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,

2️⃣7️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Wai habune aka fada a bayanshi jin hakan yasa ya tsaya cak yana dube dube ko zaiga
wani fuskan sani ya kirashi.
Saidai ba alaman wanda ya sanshi a wajen hakan yasa ya dauka bashi ake nufi ba ya
kara yunkurawa zai shiga motan.
A daidai lokacin ta karaso tana fadin Garba sadauki garaba gagare Abu bakari
mazan fama baka shedani ba ko ?
Yanzu kan yasan dashi take magana a lokacin don haka ya dakata tare da juyowa
gareta duk da baudaden halinsa dabiansune gaida nagaba dasu.
Ina wuni yayi mata cikin ladabi ta amsa tare da fadin kwana biyu shekaru da yawa
Habu ba zaka shedani ba duk ku din kuna a raina don abinda na hango a zurian ku.
Uwarku tana da yawan sakaci ga mantuwa habu tun a lokacin naso tazo na fada mata
abinda ke faruwa bata zoba har nabar garin ku.
Banfa ganeki ba boyar Allah ya fada yana kara kallonta sai tayi dan dariyan manya
tace kagani na ganeka kuwa ni mutum ce da bani raina alheri komai kankantarsa idan
anyi min.
Balle alherin ka dakai da uwarka yasa naji ina dai son in taimake ku duk da nasan
abin ya faru ko dan uwaka yanzu.
Don yanzu haka yana kwance a gida rai a hannun Allah kuna shiga kuna fita kuna
bata kudin ku a banza.
Duk da kamar warkansa yana hannunka a yanzu amma baku san da hakan ba don
mantuwa irin naku.
Haka kuma cutarshi na jikin ku habu yana biye daku sauda kafa ako yaushe matukar
ba wanan sadakan aka bada ba.
Duk da akwai hannun maki don abune da yayi yawa a tare dashi shiya nasa ya kaishi
kwance amma ko ku baku tsira ba gaba dayan ku matukar ba wanan sadakan aka biya ba.
Ba na fada maka a ranan tafiyan ka a kofar gidanku ba na fadama alherin ka da
nasara yana inda ka dosa a lokacin tabbas nasan zaka hadu da wani abin alheri a can
da zai iya fin karfin abinda ke bibiyan ku.
Wanan kawun naku yasan komai kuskuren daga gareshine shiyasa yake jin nauyi a
yanzu yadda zai gyara kuskuren nasa.
Haka kuma ku din kuna da kariya daga Allah don kuna da alheri sosai kaida dan
uwanka harma ince shiya fika.
Cikin yardan ubangiji kuma kayi nasara a nan Habu don baka bar alherin naka ya
salwanta maka, ba a lokacin don a yanzu haka kana tare dasu a hannu .
Matsalan saidai kada ka yarda kai sakaci irin na dan adam kamar yadda iyayyen ku
sukayi a baya11q.
Kallonta yayi kafin ya katseta da fadin Mama kece matar nan mai maciji da tazo
gidan mu a baya ko ya tambayi matar cikin mamaki ?
Sai yaga tayi murmushi tana fadin nice naso fada maku komai a lokacin tun hakan
ba faru ba amma mahaifiyar ka bata maida hankalinta ba.
Zanso kubar yarinyar nan ta bashi maganin hannunta don mai gaba daya akai mashi
itace zata iya kwatoshi ba tare da komai ya sameta ba koya sameshi.
Amma bayan ita duk wanda zaice zai taimaka maku akan matsalarsa karyane hakan
saidai maishi yaci kudin ku kawai.
Nata dai din shine maganinsa don shi wanda ya bata makarin bai san iya amfanin
shiba dabai bata ba itama tayi arziki dauko wanan abin daga wata kasa zuwa wajen
ku.
Ka tambayi dan uwanka dake kwance zai fada maka komai don yasani a yanzu babu
maganin da yake sha da yake mai amfani kamar wanan da take bashi a boye.
Mahaifiyar ku kuma ka fada mata nace inda ta nemo haihuwata tayi gagawan zuwa ta
biyansu sadakansu idan ba haka ba an dinga bibiyan ku a cikin sauki sauki ana
halaka ku.
Su kuma wa,yan nan yaran dake cikin ku a yanzu sune saukinku dob kamar kariyane a
wajenku.
Saboda abinda ke bibiyan naku basu iya masu komai akwai alkawari a tsakanin su
dasu tun na asali amma suma basu sani ba akwai dafa,i a jikinsu dashi kuma ake
haifansu .
Ko wani mahaluki daka gani a duniyan nan akwai wani sirin rayuwa a baya a tare
dashi tun na kakaninsa saidai yai ta mafalkin abin ya dauka mafalkine kawai.
Saidai mutanen yanzu basu sanshi ba kamar na da saboda wayewan kai da suke amfani
dashi a yanzu sun watsar da komai na baya.
Wanan yasa kaga ciwo yayi yawa ga dan adam naba gaira ba dalili da asibiti
saidai su camfa kawai don su lalaba mutum.
Don haka kuma muddin suna tare daku a gida daya wani mugun abu ba zai taba cin
maku ba sai alheri saiko idan aka samu akasin hakan kamar yadda ya samu dan uwaka
din.
Falkawa yayi yana zufa duk da sanyin AC dake dakin amma zufa yakejin yana
tsiyayya mashi abinda ya gani a mafalkin nasane ke dawo masa wace yarinya ke nan
wai ake nufi ?
Amma zai gwada tambayan J din kamar yadda ta fada yaji idan da wata yarinya
dake bashi magani basu sani ba ?
Idan har hakan gaskiyane dole ya fadawa mama dubu wanan magana asan abinyi shi
wanan maimagini na Niger abinda ya fada masu ke nan duk yadda akayi wanan abin yana
da salsala daga mama din ke nan.
Allah Allah yake gari ya waye ya nufo gida don yana katsina yai wanan mafalki
duk da ya dauka karyan mafalkine hakan don dadin barci amma zai gwada tambayan J
din kamar yadda matar mafalkinsa ta fada.
Abinda ya faru tun haduwansu da matar ya kama dawo mashi sabo gashi kuma shi J
wani lokaci saiya kama salinta jikinshi na saba irin na macizai.
Abinda da daure kai a cikinsa duk yadda mutum yai tunane abin ya wuce hakan
gareshi Allah dai ya bada lafiya kawai za ace.
Watau akidar nan ta mutanen baya kakannin kakannin mu da sukai ta shirka wa yan
nan abubuwa suke bibiya wani lokaci don suna biye da zuri,a har karshen duniya don
alkawarin da aka dauka a kansu.
Shine zakiji ana fadan wani nada iska ko wance iskansu na gadone ai ko wani ciwo
ya kamashi ba a san takamaimain ciwon ba Allah dai ya kyauta kawai za ace.
Mafi A,a lah shine bawa ya koma ga Allah a kula da addua da sadaka da taimakawa
bukata nakasa dakai komai kankantan alheri wata rana sai hakan yai maka rana.
Da irin wanan tunanen a zuciyarshi ya shigo garin zaria kai tsaye gidansu yaiwa
tsunke inda maigadi ya bude mashi get yai arba da kawu dake tsaye yana waya.
Suma ido suka zubo mashi suna mamakin dawowanshi a ranan don ya fada masu sati
daya zaiyi a can saiya tsaya yaga komai ya kankama ga aikin gidan man nasu da
akeyi.
Sai gashi kwana guda sunga ya dawo garin kuma koda ya fito mota wajensu ya nufa
suna mai barka da hanya ya runsuna ya gaishesu.
Lafiya dai ka juyo yau kawu ke tambayansa yace lafiya kawu wasu takarda zan
dauka kuma sai an bincika yasa na dawo da kaina.
To aida sauki hakan sannu da hanya na dai dauka don jikin dan uwan naka kajuyo
kuma ince Jafar kan jikinshi Alhamdullahi jiki a na samun sauki sosai ai.
Mikewa yayi zuwa part din ya J din inda ya samu Nafisa na shara ni kuma ina
mopping a bayanta ya shigo muna gaidashi da hanya.
Ya amsa muna tare da shigewa dakin da dan uwan nasa yake kwance da sallama dan
juyowa yayi yana kallonshi yace Habu ka dawone ?
Na dawo J ya fada yakai zaune saman kujeran dake gaban kadon yana fuskantarshi
yayi mai ya jiki shi kuma yana tambayanshi hanya ?
Jiki da sauki ya fada a hankali cikin yanayin ciwo ya dan kura mashi ido na dan
lokaci kafin yace J akwai wata yarinya dake baka maganine bayan su mama ?
A hankali ya juyo kanshi ya kurawa dan uwansa ido yana nazarin fuskansa da
tambayan daya jefa mashi kafin ya mirgina kai gefe daya yana fadin .
Meyasa kake tambayana hakan ina son in tabbatar ne kawai don wanan zancen na
dawo garin nan amsa kawai nake son ka bani ?
Shiru dakin yayi na dan lokaci kafin ya furu iska daga bakinshi bayan dogon
nazarin daya gama a kasan zuciyar shi don bai san dalilin tambayan da dan uwan nasa
ke mashi ba ?
Akwai ya fada a takaice yana kawar da kansa gefe daya don sauraren abinda zai
fada din game da zance.
Wacece ita J ya kara jefa mai tambayan shiru na dan lokaci kafin J din ya juyo
gareshi cikin tsare gida yana fadin kai inda aka fadama basu sanar dakai ko wacece
ba.
A,a sun daice in tambayeka kasan hakan zaka fada min ina son sanine don a tsaya
ga magani daya ba tare da dora wani ba akan hakan.
Ok to Rahama ce ta wajen ka tace daga gida aka bata makarune amma sirine bata
son wani yasan da tana min amfani dashi kada a fahinceta ta bai bai amma gaban
Nafisa ta fada min don kafa hujja koda wani abu ka iya tasowa.
Rahama dai Rahama kanwar maria Rahaman nan dai dake waje na itace kuma naji
sauki sosai don tunda na fara shanshi gabban jikina suka daina ciwo hakama kaina .
Da wanan abin dake rike min makogorona duk yanzu na daina jinshi sosai a jikina
karfin jikin ne dai da banda.
Rahama ikon Allah Rahama dai dama abinda ake yawan nuna min ke nan akansune
shine alherin da ake nufi tabbas hakan ne kuwa don a wanan tafiyan na hadu da
maria.
Kana yawan mafalkin ke nan kai ma ban taba dauka ita bace amma ina yawan ganin
rabin fuskan maishi tana neman taimako a waje.
Idan nazo in taimaka mata sai kuma inga nita taimaka saidai ban dauki wanan
mafalkin da ma,ana ba sai yanzu da kake wanan maganan .
Amma idan Rahama ce kuwa ,,,,,,,
Me Rahaman tayi muryan mama dake shigowa ya baiyana a dakin da sauri ya habu ya
dago yana fasin zancen aikin da yaran nan keyi mukeyi mama .
Ki duba yadda cikin yan kwanakin nan yaran nan biyu kacal sun gyara wajen nan
haka gwani ban sha,awa dashi wallahi.
Ai kaidai bari kawin kuma saida yai wanan maganan jiya ni yaran nan na rasa irin
haukan kurciyan su yanzuma kawun ku a kansu yake min magana waje.
Wai mahaifin ita Asmau ya matsa da zuwa gidansa akan ya ban hakkuri kaga dai
rashin su yasa munyi magani a tsanake so nake kowacen su takoyi hankali a gidansu.
Duk da ita wanan Nusaiban da alama ba hankalin zata koya ba tunda ta saba zuwa
gida ta zauna shiyasa wanan karon nake son su dauki lokaci a gidajen nasu har
iyayyensu su fahnci rayuwan da sukeyi a dakunan su.
Mata ku zauna baku iya komai ba sai kazantar tsiya da sherin duniya kala kala
bayan wanan basu iya komai ba sai daukan kai su wata tsiyace.
Aiko yanzu sun horu mama ki barsu su dawo hakana don Allah abinda takaici shi bai
gujesu ba don halinsa sai sune suke kyamatarshi habu ?
A gaban mu wanan yarinyar ta nuna hakan fa haba dai don kwatoshi cikin bari a
horasu tunda ba tsoron su akeji ba mana abin yayi yawa shege da hauka.
Idan dai zasu dawone su dawo kawai duniyace ai zata gyarasu gaba ina kawu ya
tafine habu ke wanan maganan shi jafar yana kurum baice uffan ba a lokacin tunda
aka dauko zancen matan nashi.
Ya tafi kaidai wai yana da daurin aure bayan sallah kuma muka tsaya muna magana
bai fargaba har lokacin ya dan shige.
Ok mama wai nace ba don Allah wani tambaya nake son nayi maki kuma kada ki damu
tambayane kawai jin hakan yasa ta zauna tana kallon dan nata.
Nace mama ko a baya kin taba yawon neman haihuwa haka ko amsan wani magani kan
haihuwa a wajen wani ?
Magani kuma gaskiya kona taba ba zan iya tuna hakan ba wani abune akace game da
hakan eeh to ance gaskiya.
Don yadda aka fada min kamar kin karbo maganin bisa ga sharadin cewa idan bukata
ya biya zaki koma ki kai masu wani abu .
Sai kuma da bukatan ya biya mama baki koma ba wanan yana daga cikin abubuwan dake
damun J a yanzu in ma ba ai hankali gaba dayan mu wanan matsalan zai iya shafan mu.
A ina kaji wanan zancen Habu tana tambayan dan nata cikin zuba mata idanuwanta
don jin amsan da zai bata don zancen ya taba mata zuciya sosai.
A baya kan lokacin da bata haihu ba anyi neman magani duk wanda ya kawo kuma tana
gwadawa ita yanzu yaya zata iya tuna hakan.
Mama ina son ki tuno kafin kiji yadda zancen nan yake san nan kuma zancen
maganin da J yake sha a yanzu duk za a dainasu akwai wani wanda zan ba Rahama ta
kawo maki yana a mota shi kadai za,a dinga amfani dashi har kwana biyu a gani.
Ko me kikace mama shiru tayi kafin tace a sanyayye a gwada din aiba a ki ta
magani ba sai an gwada akansan na kwarai inji ba haushe .
Yanzun ai lalube mukeyi a cikin duhu Allah yasa a dace din ya bashi lafiya shida
sauran al,umman Annabi baki daya suka amsa da amin.
Sai aiwa kawu bayani ya dan tsagaita zuwa wajen karbe karben da yakeyi din yanzu
a gwada wanan din sosai a gani ta amsa da insha Allahu.
Sun dan jima kafin ya mike zuwa part dinshi a gajiye anan ya sameni dauke da
Abbati dakinsa ya shige matarshi ta bishi hakan yasa na fito zuwa part dinsu iya
don nasan anty nafisa tana part din.
Ina shiga na samu Saare tazo nasan kuma a nan zatayi weekend tunda alhamisce
Allah ya gani duk da gidansune banyi maraba da ganinta ba.
Haka na gaida ita a darare ina kokarin zama take fadin kai dan fillo miko
minshi nan kafin na kaiga mika mata iya ta karbe da fadin dan fillo kuma kun basune
?
Ai dole mu basu dan nema baisan kowa ba sai uwayenshi bakin kiuyane dashi iya
baya yarda da kowa a gidan nan.
Ki daina fadan hakan ran mahaifisa ba zaiyi dadi ba ranan dayajiki da aida gidan
ubansa aka san asalinsa ba fannin uwa ba.
Ai fulanin basu kadai bane ko ita Asmau asalinta ai fulanine saidai sun zama yan
garin nan yanzu don ko yare basu iya ba gidan su.
Nafisace ta fito daga daki tana fadin Ramaah mamace kadai a wurin yaya wallahi
ban sani ba anty nafisa tunda na fito ban koma part din ba ina shiyan mu.
Saida ta mede baki take fadin yanzu kune kuma masu kula da ya j din duniya tai
maku dadi matanshi sun tafi kun maye gurbi.
Haba dai Saare wanan wani irin maganan banzane zaki fada haka idan munyiwa yaya
hidima laifine yaya mukaiwa ko kan mu ?
Shike nan don matansa ba zamu kulashi ba ko suna nan ai dole mu kulashi tunda
lalura ya kama na hakan kin taba gani mutum ya guji dan uwansa ?
Zaki mayar min da zance wani abin kuma niba nufina ke nan ba gani nayi dai bai
dace ba inda baku kulawa din ai mama ba zata iya ita kadai ba ?
Oky hakan laifine ko to ba don wani abu mukayi ba don Allah da mama dashi ya J
din mukayi inma kina zaton wani abune.
Ta mike tana fadin nifa Nafisa ba wani abu nake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login