Showing 63001 words to 66000 words out of 328222 words
Chapter 22 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
muna baya.
Mun koma damu da bayi bamu da bambamci a idon yan uwan mu nan dai nashiga bata
labarin rayuwan da mukayi a wajen baffan mu har zuwa lokacin da Yanda suka hadu da
mijinta.
Kafin muka samu yanci daga kangin bautan baffan mu da iyalinsa da mukeyi muka
dan murje a yanzu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
2️⃣2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Sai daren sallah ya J ya dawo zaria don haka Habune ya gudanar da duk wani shirin
sallah a gidan kamar yadda al,ada yake ga musulmin bahaushe.
Part din iyayyensu dana yayanshi komai ya tanada musu a nan da daren kuma ya
dauki mama ya mayar babban gida inda tace dakin mijinta zatayi sallah tare da yan
uwanta.
A can ma suyi hidima sosai daga sutura kudin cefane shimkafa dasu mai duk Habu
yakai masu kowa nason samun albarka duk da karfin abin Jafar ya turo da kudn yi
amma ya dora da nasa don samun akbarka.
Nama kuwa a can aka kada shanaye biyu kamar yadda mahaifinsu keyi a baya shida
mutanen unguwa a hada a saye a raba ko idan kana da hali ka yanka kai daya ka bawa
wa,yanda Allah yaci dasu rabonka.
Suma wanan karon dai sunyi hakan shanu daya nasu da babban gida daya kuma mutanen
unguwa da yan uwansu masu aure aka yayyana sai albarka ake saka masu da fatan
gamawa lafiya, Allah yasa mu dace Allahuma amin.
Duk,da da dare mama dubu ta dawo bayan shan,ruwa hakan bai hana mutane suji
dawowanta ba suka dinga shigowa masu godiya nayi masu yan koken abinda zasuci ta
bude shimkafanta aka dinga diban mata don yanzu Nafisa idan mama bata nan itace ke
zama a part dinta don haka koda ta dawo bata koma wajen uwarta ba nan mama din tace
su zauna tare da ita.
Saiga Jafar ya shigo wanda dawowanshi ke nan ya dai shiga gida sun gaisa da iya
da matarshi Asmau daya samesu a waje da wasu mata da iya biyu da iya tasa aka dauko
daga unguwarsu su taimaka masu da aikin gida dan aikin yayi yawa.
A ranan Ramaah tasha ambata a bakinsu saidai ba Ramaah don tana can inda aka
san darajanta wurin da ko kamshin aikon da akeyi bana ji saidai a debo anunawa
matar gidan ko yayi idan bata nan kuma nice zasu tambaya ko yayi ?
Tunda ya shigo ya zube saman kujera ya dafe goahinsa da hannunsa daya uwarta
dubeshi tana fadin lafiya kake kuwa Jafar ?
Saida ya nisa ya sauke hannu ya dubeta da idanuwansa da sukai ja jajir yake cewa
uwar kansa ke masa wani irin ciwo wani irin ciwon kai da bai taba jiba yakeji da
kyat ya iso Zaria yan,zuma dayasha ruwa saida ya hade magani ya samu fitowa.
Allah ya sauwaka uwar tayi mai kafin ta dora da fadin aidole kayi ciwo Jafar
tunda baka hutu ga azumi ga yawan tafiye tafiyen da kukeyi ga rana da zafi.
Cikin karfin hali ya murmusa yana fadin dolene mama idan ka zauna sai a cuceka
ai tafiyan da sauki tunda da jirgi nakeyi bada mota ba.
Sallama akai mai ya fita wanan yasa bai dawo ba ya wuce zuwa gida da kyat yakai
gida zuwa dakin shi cikin dare ya kira dan uwansa Habu da waya dole sukaje asibiti
dashi a daren.
Allurai akai mai da magani masu karfi aka bashi suka dawo gida don zaiyi barci
sosai akace idan yasha maganin .
Ba wani barcin ya samu ba amma ya danji sauki sosai zuwa safe haka yai karfin
halin zuwa sallah idi a dadafe ya dawo gida ya kwanta.
A kullum isan sunje sallah a ka,ida zasu wuto gidansune direct su gaida
iyayyensu da makwabta da ake zaman arziki da iyayye tare da sauran yan unguwa.
Wanan sallah rashin ganinsa yasa ake tambaya anan mutane suke jin baijin dadin
jikinsa abokansa suka fara tururuwan zuwa gaidashi harma da manya.
Mama dubu sunzo da abokan zaman ta da Habu ya kwasosu sunzo gaidashi suga
yanayin jikin nasa suka sameshi a falo zaune inda abokansa suka barshi.
Suka shiga yi mashi sannu da jiki basu jima ba don sallahne aka mai dasu gida
har mama din don tabar Nafisa tana mata aiki a gida.
Zuwa yamma kuma saiga Habu ya kirata yana sheda mata zasu koma asibiti da zafar
don kan nasa ya matsa da ciwo.
Sai lokacin hankalin mama dubu din ya soma tashi da zancen ta fahinci wanan abin
ba karamin abu bane ke nan tunda za a koma asibiti kuma again .
Da zatazo Nafisa ta boyota suka zo tare don asibiti suka nufa suma a lokacin suka
samesu a can kai dai yake fadi yana mashi ciwo sai dafe kan yakeyi yana juye juye
cikin damuwa da yadda yake jin wani irin azaban ciwo .
Tun safe da nayi wanka na bude ledan kayan da aka sayo min din ina duba wani
zan saka a jikina cikin jallabiyan dana ya saya min din.
Don bandasu banda wasu sabbin kayan da zan saka a jikina lokacin inyi fitan
sallah dasu na azo agani haka masu kyau gashi zamu tafi sallah idi gidan.
Tsab kayan suka karbi jikina simple makeup nayiwa fuskana nayi rolling din
gyalena ka,idan anty Salma nabi da take fadin idan zan fita na gyale kawai zan
sakawa dan kamshi mai taushi yadda ba kowane zaiji ba sai idan nabar wajen za a iya
gane hakan.
Ire iren roll on oud din data ban na murza na koma gaban madubi ina kallon kaina
a cikinsa ni kaina a ranan nasan na fito diya mace sak dani.
Kila rabona da tsayawa inyi kwaliya irin hakan tun ina karama a gidan daddy da
anty salma da hjy suke tasa mu a gaba dole muyi gyara.
Don acewarsu ba a ganinsu fes a samemu a kazance cikinsu don dole ake gyaran mu
fes a lokacin a gaskiya wasu mutane tun a duniya kake sanin su din na dabanne .
Don wallahi nidai ba zan iya ko kwatanta alherinsu gareni ba tsakani da Allah
bansan ta ina zan soma fada ba gaskiya saidai haka a ciki labari na dinga tsankwaro
alherinsu garemu.
Rita yar aikin antyce tazo kirana wai idan na shiriya in fito inji anty din nace
gani tafe muka fita tare da ita na jawo kofata muka fice a dakin.
Falo na samesu zaune harda mijinta da yaransu biyu ko wanin su yasha kwaliyansa
gwanin ban sha,awa dasu sai photuna sukewa kansu .
Gaida mijin nayi wanda anty salma tafishi hausa sosai a bakinta yake fada cikin
hausan da bakuwar fulani kina gidan nan yau nake tambayan anty ki ai?
Akwai wasan barebari da fulani shi yakan so ya zolayeni da hakan amma ban saba
da in sake da mutum haka inta zuba ba saidai inyi murmushi kawai in soke kai.
Na fita daban a cikinsu donsu bakakene sosai ni kuma din bafulatana don haka da
gani ba sai an tambaya ba za a gane ba hadin kifi da kaska.
Bamu jima ba muka fito shi ya dauki dan nasu babba na dauki karamin muka nufi
wajen motanshi kusan kowane a gidan za a tafi mota biyu nagani a jere don haka aka
bar mutum biyu sune basa sallah ta musulunci a ciki mu.
Mota daya muka shiga dasu ni ina baya da yara su kuma suna gaba zuwa idin da
baida nisa sosai mun samu an kusa tayar da sallah don haka bamu waji nima ba aka
tayar da sallah.
An sauko lafiya muka nufi mota aka dawo gida sai lokacin akewa juna barka da
sallah gwanin ban sha,awa kudi masu yawa mijinta ya bawa kowa na gidan sai ince
nawa yafi nakowa yawa a cikin mu har wa yanda basu sallah su Rita an basu goron
sallah a ranan kuma ya wuce maiduguri wajen iyalansa nacan.
Don ita tana tare da mahaifiyarshi bata zama a abuja sai maiduguri din a yadda
anty salma ke fada min bayan wucewansa take fadin shine dalilin aurensu don ita ta
zauna a nan Abuja kuma zaman nasu gaskiya akwai sauki sosai don kusan dukkansu yan
uwane dama.
Abincine na alfarma muka zauna akaci kafin dan wanan jigilan kowa ya nemi wajen
hutawa don sun fita zata saukeshi a airport saina koma dakina na kwanta.
A ranan na gwada amfani da wayana wajen kira layin nan na cikin wayan da bantaba
kiran kowa a cikinsu ba na danna na salima yayi ringing gab da tsunkewa ta daga
tana sallama tare da tambayan waye ?
Nice Ramaah na bata amsa daga bangarena sai naji tace a,a Ramaah yau an tuna
damu dadin abuja ya hana ki kira ko koda yake nasan ba waya a hannunkima.
Dan dariya nayi nace abuja akwai dadi gaskiya anty salima na tambayeta kowa
nagidan tace duk suna lafiya saidai ya J ne ya dawo jiya ba lafiya amma da sauki.
Nayi Allah ya sauka nace ta gaida kowa ta amsa da insha Allahu zasuji muka kashe
wayan yar uwata na kira muka gaisa na tambayeta jikinta tace da sauki ta ban ummah
mun dade muna hira ina bata labarin anty salma din.
Bayan mun gama waya nace Yanda ta turo min number ya habu in gaidashi da sallah
ba a jima ba kuwa ta turo min muka gaisa a yadda naji muryanshi kamar yana busy a
lokacin .
Zan kashe naji yana fadin nagode Rahama gamu nan mun dawo asibiti ne da J da
baida lafiya idan na shiga wajen Maria zan kiraki ku gaisa naji ya kashe wayan nasa
dip.
Tun lokacin nima naji hankalina ya tashi kuma lokacin sallah azahar nayi sallah
na kwanta sai barci sai gashi ina mafalki da baffa.
A wajena gaskiya mafalki baffa bai zama alheri a wajena don baffa ya tsaya min a
rain har ya zamo shine singn of bad luck dina.
Idan wani abu zai faru da na kusa dani ko wanda nasani zanyi mafalki baba yana
aikata mugun abinsa to kwana biyu sai wani abu ya faru da wani na kusa dani ko
wanda na sani.
Baffa mugun bafulatanin dajine ba arabi ba boko sai duhun kai da yake amfani
dashi dip yake baida imani ko na miskara a rayuwansa .
Inda na shamaceshi kuma sai yafi ji dani saboda zafin namana don haka lokacin
zaman mu wurinsa nice mai masa dake dake da kula da wasu kayansa na tsubbu da
tarkacen tsafinsa Dage dansa daya biyo halinsa wajen mugunta.
Shine kan nuna min aikin da sake sakin da nake dakawa baffa amfaninsu da aibunsu
don yana bashi siri sosai kamar shine maganijisa dai zance.
Don haka nima da zanyi amfani dasu da zan iya ba wani taimako akan hakan saidai
ba wanan a gabana don na dauki hakan da tsubu shirka sukeyi a wajena.
Tashi nayi na kasa komawa barcin ina faman tunanen wa kuma wani bala,in zai
sama inda nakai raina shine yanda don itace a asibiti don haka hankalina ya kara
tashi sosai da mafalkin.
Bayan nayi sallah la,asar na fito falo anty salma na dakinta barci tayi tun
bayan dawowanta sauke daddyn Imran ta kwanta.
Sai wajajen biyar ta fito daga daki har lokacin ina zaune a falonsu ni daya da
wayata a hannu ina game.
Muryan ta naji a kaina tana fadin tsiyan abuja ke nan fa ranan sallah ba wani
gurin da mutum zai fita yawo saidai kaje park da sauran wajajen yara saiko gidan
yan uwa da abokai.
Na dago ina gaida ita da fitowa wanan dabi,an gidansune muka gada ko wanka mutum
ya fito sai angaidashi da fitowa .
Zama tayi tana fadin wai Ramaah kinsan wanan rigar taki mai bala,in tsadane kuwa
kwanaki nayi ta neman irinsa in saya ban samu ba sai gashi na gani a jikin ki.
Murmushi nayi ina fadin yaya J ya saya min da zamu zo saboda ban samu dinkin
sallah naba aiko wallahi yayi maki kokari sosai rigan nan yakai seventy fa Ramah
gaskiya guy din yayi kokari.
Anan muke dan hiransu jefi jefi har nake bata labarin yadda zaman mu yake gidan
da yadda matansa suka tasamu a gaba da nuna kiyayya har yadda sukai mun kafin inzo
Abuja da dalilin dayasa mijin nasu ya saya min kayan.
Mesuke nufi dayin hakan nace sunce kamar ni zai sayawa lace mai tsada hakana
matsayina baikai hakan ba.
Don ya saya masu abu su da kannesa zai saya min ai rikona akeyi a gidan in
gaskiyane Habu ya saya min mana ai dalilishi nazo gidan.
Kaji jahilai zasu batawa mata tsarin diyanta idan mijin maria ya saya maki ai
zaiga kamar ya shiga gaban dan uwansane tunda kansu a hade yake yadda na fahinta.
Kin mun daidai wallahi laifin uwarsu bagani a nan don itace ya kamata ta fara
magana ba wanan salima din ba gashi ai yanzu ya saya maki wanda kila yafi wanda
suke fada a kanshi din.
Kishine fa kada ki dada kishine irin namu na mata kawai suka dora akanku ku fita
zancen su kawai yan iskane.
Ni dai abu daya zan fada shine kada ki yarda ai maki aure bakije gaba kin kara
karatu ba idan maria batayi ba ke zaki kara gaba din insha Allahu tunda kun fito
wajen wanab mugun mutumin.
Ai wasu yan yankin kune suka fadawa daddy lokacin yafita zancen ku don mutumin
nan na iya halakshi da asiri wana yasa daddu ya bar zancen ya barku can zube a
hannunsa amma idan bashi ba daddy yaso dawo daku hannunsa nan.
To an fada mashi shine ya kama kurwan baba fillo shiya kasheshi don haka daddy
ya barku ko ba mutuwa wahala ai baida dadi Ramaah.
Mun dauko hiran baffa sosai a wajen har nake tunane kodai wanan hiran nasa da
zamuyine yasa nayi mafalkinsa a ranan.
A Zaria kuma abu ya koma tashin hankali sosai don ya J yana cikin wani hali ba
barci ba zama sai kugi da yakeyi anyi mai allura amma a banza.
Dole kawu yaje wani waje dama yan zaria badaga nan ba shirya suke da unguwa na
malamai don akwai kasuwa a irin hakan .
A wanan wajen ya karbo wani hayaki akai mashi shine har ya samu ya dan ci abinci
da barci yayi ya kafin hankali ya kwanta amma a asibitin suka kwana dashi.
Washe garima jikin da sauki saidai wajajen rana kuma lamarin ya kara dawowa
sosai sai kugi yake yana kiran wai shi kansa zai mutu babban mutum yana raki yana
kiran sunan Allah.
Hankalin mutane ya kara tashi sosai kawu dauda ya shiga nan ya fada can kowa da
kalan nasa aka samu ya samu dan sauki kawu yace a basu sallama tunda ba abin
asibiti bane.
Lokacin hankalin mama Dubu ya tashi sosai a wanan dawowan gidan dole Nusaiba ta
dawo dakin ta ba shiri saidai basu ga maciji da Salima da take ganin itace ta sanar
da dan uwanta fadan su har ya dauki mataki haka akanta.
Salima bata damu ba itama shere Saiban tayi tunda ta fahinci me take nufi a kanta
nan gida sukai ta magani har ya dan samu sauki ya daina buga kan nasa da yakeyi
yana fadin ciwo kamar a cire mashi kan ya huta yake ji.
Sai daga baya bayan munyi waya da salima data kirani take ban labarin irin halin
da suke ciki na tashin hankali kan jafar din inda ta kare zancen da fadin amma
yanzu abinda sauki yauma ya fita sallah jumma,a ya dawo.
Sai banji dadin hakan ba ko banza ance ka damu da wanda ya damu dakai akace sai
naji na damu da jin hakan hankalina ya koma Zaria din tunda a karkashinsu nake kuma
ni banganin laifinsu akaina.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
2️⃣3️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Satina biyu Abuja na dawo a cikin mutunci tare da goma hataran arziki da mama da
anty salma suka hadoni dashi.
Nida naje da jakka daya karami sai gashi na dawo da jakkuna maya har biyu makil
da kaya na mutunci da alfarma ire iren kayan anty Salma da sakawa daya wasuma ko
sakawa batayi ba wai angama yayinsu a wajenta.
A part din Iya na sauka don part din mu yana rufe sun nuna farin cikinsu da
dawowana musan,man iya daketa fadin yar nan muji kewanki sosai a gidan nan .
Gamu gida ya koma muna wani iri sai kace taron tsofi ba don zuwan Iyatu gidan
nan ba aida bola ya rufemu tas don babu wanda yake iya gyaran gidan nan yanzu.
Iyatu na samu tazo ta wuni min idan zata koma na hadata da abinci da kudin mota
a raina nace yanzu ko ga boyanku ta dawo bako zan hana iyatun nan cin abincinta ba
gaskiya.
Saare ce tana shigowa ta ganin zaune gaban mama sai tarin kayana dake