Showing 93001 words to 96000 words out of 328222 words

Chapter 32 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

zakizo nan ne na girgiza kai ina
fadin banda yan gidan mu ban fadawa kowa ba.
Suma kuma sai yau din nan suka san da zancen tafiyana ai da zan wuto kila dai ba
daga can bane kodai kuma mijin anty Maria ne amma shi yana bauchi akace.
Saiga dan sakon ya shigo yana fadin yace nace dake yayankine Jafar na gidan ku
can zaria din wanan yasa na mike ina fadin ya J kuma meya kawoshi kuma ?
Wanan me mata din na anty salma ta tambaya kai na iya gyada mata don bansan me
zance ba ta dan tsuke fuska tana fadin je kace ance ya shigo.
Yana zaune yana waya Isah ya sameshi a mota yake fada mashi ance ya shigo daga
ciki jin hakan hakan yasa ya dan kalli Isah din dake fada mai sakon ciki mamaki
yana fadin maigidan yana nan ne ?
Baya kasan hjy ce da kadai sai yan aiki a ciki dan jim yayi kamar yana tunane
kafin ya bude motan ya fito da kafansa daya ya tsaya gyara yanayinsa.
Ya fito wanan isah din yayi mashi iso har zuwa falon na anty lokacin mun bar
falon don tace dani tashi kije ki kimtsa yasan akwai banci da nan da can da basu
daukeki da daraja ba.
Idan basu kaunan ku mu muna kaunan ku tunda munsan darajan ku munsan kuma
muhinmancin ku a rayuwan mu.
Hakan yasa na mike zuwa daki na dan sauya kayan jikina din kamar yadda tace na
fito fes dani sai kamshi nakeyi da daukan ido bakina na asalin fulanin mu na
Cameroon ya kara baiyana sai golden eyes dina da samansu yake kamar ansaka min
eyelashes garza garza dasu suka kara min ma,ana tsayina yasa ban saka takalma mai
tsini a kafana sai yan ma daidaita haka.
Yana tsaye cikin falon ba tare daya zauna ba ya juya baya yana kallon kofan
shigowa daga falon kamar me tunane yana shakan kamshin da falon keyi a lokacin ga
komai na falon white tsab dashi kamar ba mahalukin dake rayuwa a cikinsa saboda
tsabtan wajen.
Haka na fito na sameshi a tsaye na danja na tsaya ina kare mashi kallo duk daya
ban baya amma ba zakice shine a yan kwanakin da suka shude yake cikin bautan Allah
haka ba.
Yar siririyar sallama nayi ina karasowa ciki hakan yasa ya juyo gareni ya zuba min
idanuwanshi da har sukasa tafiyana ya fara hardewa lokaci guda saboda tsarguwa da
irin kallon da yake min din.
A hankali nace ka zauna mana yaya ai anty tana daga ciki ya dan kalli inda
kujerun suke ya nufa ya zauna a daya yana fadin nagode fuskanshi har lokacin dauke
da damuwa a cikinsa.
Tiren dake hannuna na dire tare da jawo dan side table din zuwa gabanshi na
durkusa a gabanshi na balle murfin goran na fara tsiyaya mashi ruwa a cikin
tumbulan glass mai kyau da tsada.
Ya miko hannu ya amsa tare da fadin thanks lokacin na mike can nesa dashi na
zauna a darare ya zuke ruwan yana aje glass cup din ya sauke ajiyan zuciya.
Idon da ya tsura min na wasu yan lokaci hakan yasa na dukar da kaina kasa cikin
jin nauyin shi yadda ya kura min ido din a lokacin.
Akwai damuwa sosai a yadda na kula da irin kallon da yake min din a lokacin don
yanayin annurin nan nasa da babushi shimfide a fuskansa lokacin.
Har tsawon wani dan lokaci muna zaune a hakan ganin wanan yanayin yasa na zamo
saman kujeran nakai zaune kasa ina mai sada kaina.
Ganin hakan yasa ya soma magana a cikin murya mai taushi kamar ansa shi dole ya
furta ya soma fadin Rahama meyasa kika taho Abuja kika zauna ?
Me zaisa ki bar gida ki dawo nan ba tare da sanin mu ba kina ganin hakan da
kukayi ke da maria kun muna adalci ke nan ga amanan ku da aka bamu riko ?
Fuska na dago na dago da hanzari na dan kallesa yace yes amana kuke a wajen mu
don hardo bai boye muna komai game da kuba ya kuma roke mu da mu rike masaku amana
kuma mun karbi hakan.
Sosai naji hankalina ya tashi ga kalaman nasa dayace sunyi alkawari da hardo
akan mu don nasan hardo zai iya hakan don yadda ya damu da lamarin mu.
Kada kika ban dauki mataki akan abinda matana suke maku ba ki dauka sunfi
karfinane a hakan ?
A,a akwai matakin da nake son dauka wanda duk sai sun raina kansu a karshe kan
wanan rayuwan banza na kazafin da suke kokarin maki.
Dago kai nayi na kalleshi don jin abinda ya fada din ke nan shiya tsame kansa a
ciki nice ma suke batawa ke nan hakan yasa hawaye ya soma zubo min don zuciya daya
kawo iya wuya .
Koma me suka fada maki nasan Allah zai wankeki ga sherin su Rahama don Allah
yayi hikimarsa daya bar shari,a a hannunsa akan bayinsa.
Ni nasan kin taimakeni taimakon da ko mama data duka ta haifeni ba taimin irinsa
ba tunda ta kasa tsamoni cikin halaka saike Allah yaba wanan dama da ikon data
sanadin a yau gani a saman kafata tsaye.
Banda Allah waya isa hakan ga bawan shi Rahama toni na sani kuma ba butulu nake
ba dan hakin da ka raina shike tsone ma ido inji manya.
Suna maki kallon dan haki a wajensu ni kuma ina maki kallo na mutum sak a
idanuna don wanan sirin banda habu da Allah ya nunawa dagani saike sai nafisane
muka sanshi.
Shiyasa nake matukar girmamaku a cikin lamarina girman da a gaban kowa kuke ba
zan iya boye hakan a raina ba sai na fitar fili kowa ya sani.
Yau kin kwaso kin dawo Abuja wajen anty ki Rahama kin zauna yaya kike son na
kasance a can quite sure basu fadi karya ba a kaina nina sani Rahama.
Akwai wani fleeling da ban iya boyewa a kanki matukar zan sanya idona a kanki ko
a gaban wa kike kuwa zan kasa controlling din kaina a lokacin.
Ina kike son kai alhakin hakan a kanki Rahama a yau nazo maki da wata tsiga ta
dabance banzo nan da sunan dan uwa ko yaya a gareki ba na zo makine a matsayin
jafar din da kowa ya sani.
Don haka kiyi hakkuri kada kice zakiyi fushi da gidan mu Rahama ki dawo nan
Abuja da zama akan laifin da bamu muka aikata maki ba .
Su basu isa su fitar dake gidan muba sunzone kamar yadda kema a sanadiyan aure
Allah yayi zaki zauna damu din haka suma suke zaune damu.
Kaina yana kasa na dukar lokacin mukaji takon anty Salma ta nufo falon tana
waya kafin ta karaso tana sallama.
Shi ya amsa mata don ni kona amsa ma ba zataji ba a sannu da hanya ta fada tana
zama kallo daya yayi mata ya kawar da kansa gefe daya.
Dan zaria ina fatan ba kazo dauke min kanwata bace ya danyi murmushi yana fadin
banzo daukanta i hope muma ba dauke muna ita kikayi daga can ba ?
Eh to kusan haka gaskiya don ka canka da kyau saboda matanka sun saka min kanwa
gaba da haushi ba zan lamuci hakan ba gaskiya har yaushe nawa Ramaah take balle
wanan zancen banza ya taso kanta.
Bakai naso kazo ba don banda case dakai da mijin Maria da aka bashi amana don
aure amanane ya tsaya ana yi masu hakan yana kallo kai kan ai matankane ba zasu
taba laifi a wajenka ba don da an dauki mataki.
Hjy ko yanzu daukan matakin da nake son yi shine yasa kika ganni a nan zaune .
Ok to muna jin ka nima abinda ya fito dani ke nan yanzu ka fada min manufar
biyotan da kayi don ina da bukatan ji idan hakan zai gamsar dani.
Amma taya don Allah bawan Allah mata zasu zauna suna ciwa yarinya fuska haka amma
a rasa wanda zai daukan mata mataki a gidan har kai da abin ya sha ?
Allah da nayi niyar yin karansu kan zancen nan amma sai nayi duba ga maria dake
zaune daku naga rashin dacewan hakan da zanyi din.
Shine yasa na daukota baki a laikum zuwa nan komai iskancin da suke ji ba zasu
taba biyota ba nan suyi mata ai ?
Ya langabar da kansa gefe daya yana saurenta sai da yaji tayi shiru ya soma fadin
da kinyi hakan kin dauke ta hjy baki kyauta min ba donni abin zai shafa a karshe.
A daiyi hakkuri ina mai bada hakkuri a both side amma a gabanta aina fada masu
matakin da zan dauka ga hakan da sukai min ba zaiwa ko wacen su dadi ba a rai .
Wanan yasa naki daukan komai da zafi hjy don in gasa masu kwakwansu a hannu
kafin na kai ga daukan matakin ni zuwata nan ai yayi min dadi tunda acan boyewa
takeyi bani ganin ta.
Ba anty salma ba ni kaina saida na dago ina kallonshi da mamakin abinda yake
fada ko banda hausa zan fahinci wanan magana amma kuma bai fadi dalili ba.
Shike nan ai tunda har kayi tunane kamar nawa sai a je a hakan Ramaah dai zata
zauna a waje na sai hutu ya kare insan abinyi a kai idan haya zan kama mata anan
zaria din har ta karasa karatun ta tadawo nan ko kuma idan a hostel zata zaune dai
zanyi shawara a san abin yi ko ita maria bata san kudirina ba a yanzu.
Shike nan hjy ba sai ta zauna a hostel bama tunda ga gida nan dole dai matakin
da zan dauka yasa kowansu natsuwa a yanzu.
A yanzu a son samuna don Allah ba wani boye boye ko kwanaye kwanaye don so nake
ta ban baki daga nan in wuce can wajen hardo mu gana dashi.
Zubur na mike tsaye don jin maganan da nayi kamar saukan aradu a kaina na fara
tafiya a baya baya ina kada kai na juya zuwa ciki da sauri na barsu a nan din.
ZARIA
Ringing din wayantane ya tayar da ita daga barcin data samu tun bayan fitan Saare
a dakin da suka gama dariyan plan dinsu na jiya yadda yayi daidai da abinda suka
hada din.
Dauka tayi a cikin magagin barci tana amsawa wayan mamansu shiyasa tace hlo mama
ke ba mama bace nice Rashida naga kiran kine ai dazun ban kusa da wayan.
Jin hakan yasa ta watsake daga barcin tana fadin wallahi anty Rashida na kira in
fada maki komai ya tafi daidai yanzu haka tabar gidan nan tun jiya ta tafi abuja
wai hutu.
Nasan ko ba hutu bane tagudune don kunya na dasawa shegu bakin ciki daga ita har
yarta din yan iska .
Ke kice min kinyi maganin shishigi ke nan gobe ta kara rawan kai ga mijin wata
mugani ita gata sarki iyawa ko bari a koreku a yabeta ?
Ta dauka zataci bulus ne ta tafi a banza rabuda yar iskan yarinya tana wani
daukan kai kamar diyan wani da wata ?
Yanzu ina mijin naku yake shi kuma wani dan iska guda haka kawai uwarka ta kore
matanka kayi zaune a kwaso maka wasu yan iska suna maka karairaya kana binsu da
kallo ?
Haba dai dayan fa kanwarsace ya Raahida mahaifisu daya sai ita dayan mara kunyar
su a dole ga jikan munafukai don ta gyarawa yarta hanya a yabeta mu kuma a kushe
muna.
Ni yanzu ko Asmau takai min ko ina wallahi yaya ina bakin ciki in bude ido inganta
a cikin gidan nan a matsayin matar sweety.
Ke na fada maki bar wanan shasha,shan makarine a wajen ki bar banza a haka ki
fita zancen ta don yanzu kina kawar da ita gidan nan wallahi wata zai jajibo maki
tunda ya saba zama da mata biyu a yanzu.
Shima anyi rigimame dan wahala kamarshi zaije rigimar aje mata har biyu don
Allah nifa idan ya jero daku nakan ga kamar ma kun girme mashi ga shekaru ?
Haba dai yaya Rashida wallahi ya girmemu kawai dai rigimace irin ta maza dashi
kawai ni dama nafi son hakan mu tsufa tare da abin mu.
Wai yana inane yana nan yana fushin har yanzu ko ?
Yanayi wai yayi tafiya dazun shine bai sanar da kowan mu ba sai a bakin sakaran
nan saratu nake ji wai ya zo nan kadu daga can kila zai wuce katsina.
What baki tunanen hakan plan ne dama ko tare suke da yarinyar nan tunda jiya ta
wuce itama wallahi ba abinda namiji ba zai iya yiba Saiba.
Kai haba yaya Rashida Allah ba zaiyi hakan ba kawai dai tafiyan yaje dama tun
ranan ya fada zaiyi tafiya a yau din kafin zancen nan.
To shike nan nidai kibi sannu kinsan dai kece mai dan maski maski a cikin mu
kada kije ki jawo wani sabon wahala kuma abubuwa suzo su tsayawa mutane.
Haba dai aiba zan yarda akai hakan ba kawai nima ido na zuba mashi ya kare
fushinsa nasan ina nan zaizo aiya sameni dama mun saba .
Ni wallahi tausayi ya ban sosai da ake maganan amma haka na badawa idona toka
naci masa mutunci ga kowa nasa a zaune ya kasa daukan wani mataki tana fada ta
kwashe da dariya.
Ni dai shirun nasa ne nakewa tsoro wallahi kinsan halin Jafar fa Saiba dan
duniyane na karshe wallahi saita tare yar uwar da fadin barshi ba abinda zaiyi
wallahi haka yafi shegu su daina dagawa mutane kai ai yanzu gidan.
In kinga yadda Habu din nan yake ririta wanan yarinyar da yar uwata zakice wani
romiyone da juliya suke soyayya duk da sun haihu ba abinda suka rage ga komai
wallahi.
Ai shiyasa naji tsoro kada shima jafar yaje ya jajibo maku yar bafulatana boni
ya cimu ina mu ina kishi da mugun iri ina ganin yadda yaya larai take fama da nata
bafulatanan.
Barshi ai kafin ya gama fushinsa ya dawo hanya nagama duk wani shirina da zanyi
a kansa wanan karon zaisan ko wa nake kudina ba zasu tafi a banza ba.
Sun gama hiransu yunwa ya fito da ita falon ta duba ko Asmau dake da girki ta
karasa saidai ba motsin Asmau din kitchen ta leka nan ma wayau babu wani alaman
girki a kitchen din.
Ta fito ta nufi dakin Asmau din dake da tsohon ciki kwance ta sameta tana barci
cikin daga murya take magana da nifa ban gane ba Asmau ba za ayi muna abinci bane
yau ?
Hakan yasa ta bude idanu tana kallon abokiyar zaman nata tace banji dadine akwai
miyar jiya na nan a fridge idan na tashi zan dafa muna shimkafa ko taliya.
Kinsan kuwa karfe nawa yanzun Asmau yanzu fa karfe biyu ake nema nifa wanan
halin idan shi za ayi wallahi saidai kowa ta dinga girka abinda zataci yafi min
sauki gaskiya da wanan halin .
Kina iya zuwa aiki dafa ko yanzu ina jin jikina sai ibtashi in shiga kitchen
dafa maki abinci to naki ki dinga dafa naki abinci mana sai me ?
Haka kikace ce tace eeh na fada haka kawai ina barcina zakizo ki tayar dani daga
barci ?
Zakiga abunda zanyi din ta juya ta fita tsuki Asmau taja tana fadin haka kawai
zakiyi kokarin yi min turaja.
Cikin bacin ran da take ta kira wayan mijin nasu duk da tasan yana da wuya ya
daga yadda yake fushin nan.
Tayi sa,a kiran nata ya shiga yana tsaye bakin mota Isah na kwashe kayan dayazo
muna dashi kiranta ya shigo wayanshi.
Duba wayan yayi yaja tsuki har wayan ya katse bai dauka ba bai kuma dagawa din
ko kira nawa zatayi ya fada a zuyarshi da tasan abinda yake ji game da ita da bata
kirashi wanan lokacin ba.
Yaja motansa ya fita a cikin sanyi sam bai tsanmaci hakan ba daga yarinyar nan
ya dauka ba zai samu wani matsala sosai wajen shawo kanta ta amince dashi ba sai
gashi gaba daya ta nuna bata yarda da tsarin nasa.
Wanda yasan badon komai ta nuna hakan ba sai saboda wa yan nan baka more din
matanshi daya tsani duk wani halinsu na banza yanzu.
Amma zaiyi kokarin duk yadda zaiyi wajen ganin bata subuce masa ba a yadda ya
hango hakan ayanzu gareta.
Meye laifin da wanan hjyr zatace haka bai yuyuwa tunda ga yar uwarta a gidan itama
tana fama da kanta balle ita kuma tashiga ciki.
Ke nan saboda matanshi ke nan suke ganin hakan ba mai yuyu bane kome yarasa mesa
mutane ke daukan al,ada fiye da addininsu.
Hotel din daya saba sauka idan ya shigo Abuja ya nufa ya kama daki yayi
kwanciyarsa saidai duk yadda yaso ya huta hakan ya gagareshi a ranan.
Don ransa da yake bace da wani zaiji a zuciyarsa bacin ran saiba da yake ciki ko
wanan abinda yake ganin yana nema ya zamo mashi matsala ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,

3️⃣3️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Gado na fada ina sakin kuka ba zance ban fahinci inda ya J ya dosa da zanceshi ba
maganan gaskiya shine ya J yana nufin yana sona idan bani bace ban fahinci zancensa
ba ?


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login