Showing 141001 words to 144000 words out of 328222 words
Chapter 48 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
zauna din ba na mike nazo na karba ina gasheshi da dawowa jikinsa ya
hada da nawa ya matse waje daya yana fadin yaya jikin naki yanzu ?
Naji sauki na fada a cikin kunya dajin nauyinsa don irin yadda ya hade jikin mu a
waje daya din kamar yana neman wani abu a jikin nawa.
Kin tabbatar ya kara fada nayi dan murmushi kawai ban bashi amsa ba yake fadin
hankalina ya tashi sosai dazun Rahama iam sorry banyi hakan don kaina ba so sorry
kiyi hakkuri da hakan don Allah ?
Na boye kaina a cikin jikinshi yacigaba da fadin Allah yayi maki albarka naji
dadi sosai jiyan kamar nayi kuwa ban sani ba koma nayi din ai ?
Dariya yaso subbuce min na kara noke kaina saman jikinshi yace wallahi Rahama
komai naki yai min a rayuwata ina sonki sosai mu sanman kamshin nan naki don Allah
ki bani hadin kai mu zauna lafiya.
Kaina gyada kana na furta a hankali da in sha Allahu yace ba zan manta da
rayuwan daren jiya ba da komai na cikinsa har wanan cizon da aka gyatsira min a
wuya .
Ina son wanan daren har kullum ina son abinda ya faru a daren abinda ya faru a
cikinsa wani irin nauyi da kunyane suka rufeni nasa.
Yace Allah kuwa gaskiya nake fada Rahama na rasa inda zan saka kaina a jiyan
kamar in bude cikina ki shiga naji lokacin don tsaban sonki dan Allah kici gaba da
inganta min sauran dararen da zamuyi tare dake a rayuwan mu.
Ya dagoni yana kokarin mu hada ido dashi yake fadan hakan na kasa yadda yake so
din na daiyi kokarin daga mashi kai alaman in sha Allahu.
Naji yakai min kiss a goshi yana fadin bari naje na rage kayan nan a jikina in
dan watsa ruwa in dawo in baki abinci ya fada tare da sakeni ya juya ya fita daga
dakin.
Zaune nakai a hankali bakin gado ina sakin ajiyan zuciya wai yau ni Rahama mutum
kamar yaya Jafar yake fadawa irin wanan maganan a kaina.
Dama ace ni kadaine fa in more miji har miji a nan saidai kash kadara ta riga
fata nidin a haka ragowa na samu ragowan wasu ma bako mutum daya ba.
Take naji wani irin kishin matan nasa ya tokare min zuciya a karo na farko tun
faruwan alakan hada aurena dashi sai wanan karon naji zafin matan nasa.
Zafi na daban ba irin wanda nake ji nasu ba a baya akan matsin da suke min kan
yar uwata wanan wani na dabanne ya ziyarci zuciyana.
Kwance nake rigingine a yadda ya sameni da farko na soma tunanen ko yaya zamana
dasu yanzu a matsayin kishiyarsu zai kaya oho ?
Na sandai wata rana dole a hadu an kuma ce mai hali baya fasa halinsa sai yayi
koda kadan ne ashe zan iya kyalewa in shanye duk wani cin fuskan da zasu iya min
kuwa ?
Kai ina dole in rama a yanzu ga duk wace taso barazana a kaina basu ba koma
wacece indai akan yaya jafar ne ba zan taba kyale mashi ba kuwa.
Haka ya dawo ya sameni Tsarki da aminci su tabata ga Allah na furta a raina
lokacin dana kyala ido nagashi tsaye a kofana cikin kananun kaya wando da riga iri
daya saidai wandon iya gwiwa ya tsaya mashi haka kuma rigan ya dan sauka ya dan
rufe zuwa cinyarsa masu ruwan kalan dorawa da akaiwa rubutu a gaban rigan da gefen
wando cikin manyan haruffa da FREE MAN.
Na nanata kalman a bakina har lokacin yana tsaye yana waya yana fadin gaba daya
za a kwarai massallacin na fada masu sai a kara mashi girman tako goma ako wani
bangare tunda akwai sauran fili wadattace da za ai hakan.
Duk wani kayan da za a kawata massalacin dashi na riga da naba garba kwangilansa
shi zai sayo ya kawo banson aikin nan ya wuce nan da wata biyu insha Allahu tunda
akwai komai a kasa.
Aina fada mai Habu zai kawo mai kudin komai da mukai killisafi dana zirga
zirgansa duka gaba daya ya dan jima yana saurareb bayanin abokin maganan nasa kafin
yace hakan ba matsala bane ai ayi komai yadda ya dace kawai.
Ya kashe wayan yana kallona ban farga daya gama wayan nasa ba saida ya ware
hannayesa alaman inzo garesa niko na shagala da kallonsa ban farga ba lokacin na
sauke wani irin ajiyan zuciya ina mikewa.
Na tako zuwa wajenshi hannuna ya rike a cikin nasa yana rada min tafiyan nan
naki ba daidai bane har yanzu Allah ya taimakeni ba kowa a gidan nan danaji kunyar
hakan a idon mashi.
Ledan daya shigo dashi din ya dauka nidai har mamaki yake ban yadda shi bai
kunyata ko nauyina zakice mun dade da shakuwa dashine lokacin.
Falo mukayiwa tsinke saida yaga na zauna ya nufi gaban tv ya kunna ya dawo ya
zauna lokacin nake fadin a dauko abincine nan ?
Abinci kuma ya dago da sauri yana tambayana nace na girka abinci dazun danaji
sauki Ohho no no a hakan kika wahalal da kanki Rahama ?
Baki da lafiya fa kin sani da badon karna shafa maki bakin jini ba daga zuwan ki
Allah ba inda zan fita yau ina gidan nan ina jinyar abina nida nayi barnana da
kaina.
To amma rashin fitana din zai iya shafa maki laifi ga mutane da yawa musan man
mutanen gidan mu sai a dauka kece kika hanani fita.
Da ina nan ba zakiyi wanan wahalan ba haka na dan kalleshi cikin marairaicewa
nake fadin don nayiwa yayana girki kuma shine wahala ?
Haba dai ai naji saukina kuma ban iya badin ka da yunwa tunda nasan kai kafi son
cin abincin gida ko yaushe meye a cikin dan girkin iya bakinka kadai ?
Na mike zuwa dinning na dauko abincin zuwa inda yake zaune na aje a gabanshi ya
kalli kayan yana fadin kinsha fama wallahi.
Allah yai maki albarka Rahama sunan ki yaci ke din mai tausayice da imani da har
kika iya fahintana wallahi kamar kin shiga raina kin gani ina tunanen abinda zanci
mai dan nauyi da daren nan kafin in kwanta.
Kinsan ni din rainon iyace ai ban wanka in bushe a gidan mu ina dakin iya duk da
mahaifin mu bai yarda na zauna a wajenta dindindinba saidai in tafi in dawo gidan
mu in kwana.
Ya bude abincin daidai ina aje mashi ruwan sha dana wanke hannuwa ido ya lumshe
ganin yadda semon yabada ma,ana a cikin ledan dana daresu a ciki kulli biyune na
saka mai ya bude miyan yana furta masha Allah.
Zaman dirsha yayi a kasa da alaman haka zaici abincin a lokacin ina kokarin
kaiwa zaune kujeran dake kusa dashi naji yana fadin zo nan ki zauna yana nuna min
wajen zama a gefensa kasa haka yasa na sauka na zauna kusa dashi din kamar yadda ya
bukata.
Naji yace waima in tambayeki don Allah Rahama kudin da gaskiyane kun taba zaman
daji kuwa ni sam banga alamun hakan ba gareku amma ance a rugga habu ya gano muna
ku ?
Murmushi nayi ina fadin a can ya ganmu mana zama na shekara biyar mukayi a rugga
tare da baffab mu na fada ina zuba mashi abincin a plate yana bin zanen hannuna da
kallo cikin mamakin abindana fada.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
4️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Washegari shi ya shiga kitchen da safe ya hada muna breakfast ruwan zafin shayi sai
dankali da kwai suyan damke don duk ya wargaje kwan a wajen juyi saidai yayi dadin
ci gaskiya a baki.
Ina daki ya shigo ya sameni duk dana falka daga barcin safen dana dan samu amma
na kasa dagawa daga kwancen ina kwance ina faman tunane ya shigo har dakin da abin
kari.
Da sauri na tashi cikin mamaki ina gaidashi kin tashi ke nan ya fada yana aje
kayan hannunsa din na amsa da eh yaya ina kwana lafiya ya fada yana zama yake
fadin dama nayi zaton baki tashi ba ai ?
Yau muna da baki gidan nan duk da ba wajen mu sukazo ba zasu dauki kayane su tafi
wanan kayan dake dakina kayan fadan kishiyace dana hadawa yan uwanki a a kai masu.
Saidai ita Asmau don haihuwan da zatayi nasa an hada mata har da kayan baby na
kuma dan kara mata ya dara na Saiba din.
Kallonshi na danyi yace ehh ai kinga in Allah ya raba lafiya ba sai na koma
sayan komai ba kuma shike nan na gama a yanzu.
Allah ya sauketa lafiya na fada ya amsa a cikin dadin rai da amin ai watan
haihuwan nata ya kusa kamawa Allah yasa lokacin kun samu hutu sai kawai in daukeki
mubar garin nan na dan wani lokaci.
Ita kuma dayan antyn fa yaya yace wai Saiba kike nufi idan na dauketa yanzu
wazai kula da ita Asmau din, da hidima zaimata yawa ai ?
Maza ke nan na fada ni zainab makawa sai kiga namiji ya koma yaro karamin a gaban
mace yana sakin magana kamar bashi ba.
Balle J da yanzu yana da madafa dan magana zai tunar dasu cewa sun nuna suna
kyamarshi a baya don haka yanzu baida lokacin tsayawa dasu ai nasan dai abinda zai
fada ke nan a karshen zancensa.
Tare muka karya dashi bayab mun gama nakwashe kayan zuwa kitchen na tsaya
wankewa na gyara kitchen din dana fito nima wanka nashiga na zauna bayan na fito na
shirya tsab a cikin wani atamfa dinkin zamani don dogon rigace amma tellan ya tsaya
ya tsara dinkin kamar ba hannune ya dinkashi ba.
Dinkin akwai na ciki wanda zaki fara sakawa mai dan hannu saina sama mai adon da
stely din dayasha duwatsu har kasa saiki rantse daga egypt aka shigo dashi haka.
Hullane mahadinsa don dan kwali bai haduwa da kaya haka sai gyalena ainihin da
akai amfani dashi a matsayin gyalen yafawa da kayan .
A kyalen yadin kayan da akayi cin bakin gyalen dashi da duwatsu sai hakan yaba da
mana,ana ga gayan sosai zai fito da duk macen data sa a jikinta abuja ke nan.
Sallaman su yaya Ai yasa na fito don sunki zama sunata gwara sallama shima
lokacin yana ciki dakinsa kuma kofa a rufe.
Nice na fito ina amsa masu sallamansu suka juyo kofana muka fara gaisuwa nake ce
dasu su zauna sai bayan sun zauna din na gurfana ina gaidasu da zuwa.
Masha Allah anty Rukkaiya ta fada tana bina da kallo tace a,a lalai ba laifi
gaskiya Allah ya baku zaman lafiya amarya.
Na mike naje kitchen na dauko masu abinsha da snack gami da ruwa saida na ciko
tire na kawo masu na aje na juya ina fadin barina sanar dashi isowan su na nufi
hanyar dakinshi din duk suka bini da kallo anty Rukkaiya ke fadin.
Akace yayan fulanin ruggane gasu kamar ya Niger mana sun waye sosai ba zakice
asalinsu rugga bane tun wanan madin har tafi ta wajen habu wayewa ai.
Itace daidai da matanshi ai don yaran basu da mutunci baka zuwa gidansu kasha
ruwa balle abinci ni yaya Ai ko sun ban abincin su ai ban iya cima .
Yana zaune saman hasonsa ya dora kafa daya a sama dayan na kasa yana latsan
laptop nayi sallama nashigo dakin.
Kai ya dago ya dan dubeni kamar zai maida hankali ga abinda yakeyi bayan ya amsa
sallaman tasa sai kuma yayi saurin dagowa ya zuba min idonsa.
A dan maraice nake fadin su yayane sukazo suna falo zaune hannu ya miko min
bakinsa na fadin har sun iso ashe ?
Na tako zuwa gareshi ina fadin yanzun suka shigo hannuna ya kama ya jawoni na
fada jikinshi ya rugumini tsam yana fadin duk kayan da kika saka Rahama sai naga
sunfi maki kyau ga wanda kika cire.
Wai meye sirin hakanne Rahama jin hannusa ya fara yawo a jikina yasa nace dashi
cikin wani sallon fitar da magana su yaya fa suna falo suna jiranka kada suga an
barsu su kaidai zaune.
Yaja numfashi yana dagani yace kece ai kika kashe min jiki yasa na kasa tashi na
manta da zancen su .
Cikin kissa na dan kalleshi ina fadin ni kuma yaya yanzu dana shigo don Allah me
nace dakai da zakace laifinane kuma ?
Au baki san abinda kikai min ba to ki duba nan da sauri na mike daga jikin nasa
ina fadin nidai muje don Allah kada suga mun jima haka ?
Kamahin nan naki Rahama ba karamin illanta min zuciya yakeyi ba har na fara
tunanen yadda zan koma maraya ranan da bani kusa dake wallahi.
Suma da kalan nasu a can da zaka shaka dama mata suna mukatara ai amma ba kalan
mu daya ba a wajen abubuwa kowa da irin nasa fasahan ai.
Wai ashe kina magana haka dama ya fada yana gyara saita jikinsa daya mike tsaye
ni dai nayi gaba ina dariya ya biyoni da yaya Rukkaiya data dauki cup tana shan
lemo muka fara arba tayi saurin ajewa yake fadi daga bayana ashe kun iso yaya.
Mun iso Jafaru kasan halin yaya Ai ai da nabita nata aitin bakwai muna gidan
nan ita bataki hakan ba a wajenta yayi dariya yana zama yace.
Haka ake son mutum ai da cika alkawari jin suna gaisawa yasa na koma dakin nasa
ana basu waje bandakin na gyaro kafin na fara gyaran gadon dakin nasa lokacin ya
shigo dakin .
Baki dai gajiya da aiki ke nafi son ki huta yadda nima zanbi jikin ki in huta
da dare in sauke gajiyana yadda nake so amma sai ki wuni a tsaye kina aiki waike
mai wayau don mutum ya tausaya maki ko ?
Dariya ya ban sosai saidai ba halin hakan shi yana mamakin sakewana nima haka
mamakinsa nake ji yadda yake abinsa da iyalinsa cikin sakewa haka ?
Dama haka yake amma matansa suke kullum cikin fada ko dashi ko kuma a tsakaninsu
kullum ba zaman lafiya a part dinsu can gida.
Ganin ya gara akwatunan biyu yasa na garo masa sauran muka fito dasu falo zuwa
gaban su yaya din ina ajewa na juya na bar wajen naje na karasa aikin da nakeyi na
gyaran dakin.
Shine ya shigo yake fadin su yaya suna tambayan ki don ba lalai bane su dawo ta
nan din kije kuyi sallama dasu na fita na barshi a dakin.
Kudi ya dauka ya fito ya samemu yana fadin suje ko suka fice tare dasu bayan ya
gama kwashe akwatinan zuwa motanshi.
Nan kofan gidan na dan rakasu suka shiga mota suka tafi ajiyan zuciya na sauke
bayan tafiyansu din Allah yaso na hada masu leda su rike don basuci wani abin kirki
ba ga abinda na aje masu a falon na motsa baki.
Na tattara kayan na koma daki na kwanta tunda yace min sai yamma zai dawo gida
don haka ba sai nayi abinci ba ke nan.
Akwatuna shiddane suka fita dasu zuwa can gidan sai wasu jakkuna ban kuma
tambaya ba tunda ya fada min kanun zancen cewa zasuje dasu yaya can gidan kai masu
kayansu na tausan gaba irin da wasu mazan arewa keyi idan sun karawa matansu abokan
zama.
GIDAN IYA
Gidan iya kamar yadda na samu suna kiran gidan da haka suna isa da mota Saiba da
Saare suka hango tsaye saareb na magana kamar cikin fada.
Ita kuma Saiban tana gyada kai ya kallesu yana fadin kingan suko yaya yarinyar
nan Saratu na rasa meke damunta sam bata da tunane wallahi.
Saratu ai kowa yasani ita da wana matar taka kansu a hade yake ranan da aka
kawo yarinyar nan saida Iya ta shiga rigan arzikin ta a cikin mutane tayi mata kaca
kaca ta shiga hankalinta.
Suma a bangarensu ido suka zubo masu saidai basu daina maganan da sukeyi a
lokacin ba har su yaya suka fito daga motan suka nufi hanyar part din iya suna
wajen tsaye.
Shiya fito a karshe daga motan bai ko kallo inda suke ba shima part din na iyan
ya nufa ya shiga suna wajen suna shirya abinda suke gani shine daidai gulmata dana
yar uwata sukeyi ba wani abuba.
Inda Saare ke kara ingiza Saiban akan kada ta yarda ta ban daman da zan samu
wurin shiga ga miji don nufin mu mugaje gida ko ?
Tunda mu mama ta haifawa yayanta inda saiban ke jin tankar taje gidan ta sameni
tayi min tsinanen dukan tsiya don a ganin ta tana iya murzata idan ta samu gamina.
Sai saratun ta hana tace wanan su bari idan yaya ya bar garin ko ita zata rakata
ayi hakan illa dai ya zageta dama an saba hakan ai kanta.
Tasan kuma mama ba zata kyaleshi ya sakata a gaba ba zata tsawata mashi sun dai
dauki mataki a kaina lokacin.
Saiban ke fadin ita ta rasa me J ya gani a jikina da har yaje ya aureni ba tare
da ya tsaya tunane ba ?
Keko aiba kai sake bane wanan abin da gani ai aikin asirine asiri mukai mashi
muka sameshi ai daba haka ba ai ina ni inashi da za ace wai nice yake aure.
Gaisawa aka fara yi a tsakaninsu da iya mama dake daki taji muryansu ta fito
suna