Showing 162001 words to 165000 words out of 328222 words
Chapter 55 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
fadan hakan akanta.
Ta dai fiki ko keda kika mayar da kanki banza wajenta saratun ta fada sai
salima tace kona mayar da kaina banza ba kaina bane farau ai don kafin nayi da
Rahama wasu sunyi da Saiba ai duk ko da cin mutuncinta da komai haka naga ana binta
sau da kafa gidan nan.
Balle Rahama dake ban girmana da mutuntani tasan darajana dana dan uwana da kowa
nawa kinga ko kowa na son kyautatawa a rayuwa.
Kukan dabi,anku baida kyau wallahi ku zauna kuna cin junan ku kamar kishiyoyi
kowa kamar yana jiran dan uwansa ya fincika ?
Bama shiba dai su daiyi kokari su kama nasu dakin shi yafi garesu ba shiga
tsakanin matan dan uwansu suna saka ido ba iya ta fada.
Fada masu dai iya wanan abin takaicin dame yayi kama yara basu san ciwon kansu
ba kullun jidali da juna kamar kishiyoyi ?
Wanan yasa ran mama ya kara harzuka da zancen dan nata don koda yazo yana mata
sannu da zuwa a fusace ta amsa mashi zaice a yanzu hakane tsakaninsu da ita.
Mama ance kina nemana ya fada cikin maida hankalinsa a kanta tare da natsuwa
yana saurarenta cikin ladabi.
A,a ka bari idan ka gama abinda ke gaban ka jafar sai kazo kaji me nake nemanka
dashi yanzu ai kana uzuri tunda hankalin ka yana wajen yarinyar nan ayanzu.
Kallon bangane ba yaiwa uwar tace ehh ance kace saika sauke Rahama zaka zo kiran
da nake magaka shine nace kaje idan baka gama uzurinta ba kagama ka dawo.
Mama da Rahama zanzo gidan nan koda aka kirani na daukota daga school zan kaita
gidane don da motanta nayi amfani yau na bayar da datawa a wanke min.
Allah sarki ita Rahama ashe harda mota ka saya mata su sauran ina tasu take
take ?
Baga mota a gidan nan na ajiye ba mama haka itama na aje mota ibrahim yana kaita
makaranta dashi da sauran laluran gidan.
Kadaiji tsoron Allah jafaru kasani dukkansu amana suke agareka baka nuna kana
banbanci a tsakaninsu ba haka a fili.
Kayi tafiya daga gidanta ka dawo ka kuma sauka gidan ta kayi adalci ke nan jafaru
kana son kona kankane da hakan Jafar ?
Mama kodana sauka gidanta jiya ai da hujjana na sauka a wajenta don kodana tafi
kwanakinta bakwai da Allah yace ayiwa budurwa bai kare ba na tafi wanan yasa na
sauka na karasa mata kwana dayan daya rage a can din.
Kadai ka sani tunda abin ya zamo bin bashi har kana rankon kwana a tsakaninsu
dolene akace kayi mata kwana bakwai dinta tunda uzuri ya kamaka na tafiya ?
Wanan shine adalcin Jafar kake ganin su nan zasu fahinci hakan da kayi jahilcine
ko tauye hakkinsu akan wata tunda daga gidanta kayi tafiyan?
To ita kuma saiba dakace meta dawo yi a gidanka nice nan naje na dawo da ita
don banga abinda tayi maka na wanan hukunci ba har da saki ?
To shike nan ai mama ta zauna ga gidan nan amma ni abinda ya dace nayi akanta
naga yayi don ba zan zauna da mace haka ba tana gurbata min gida.
Au ita saiba ce kadai take gurbata maka gida su sauran basu wani mugun hali da
baka dauki mataki a kansu ba jafar ?
Ikon Allah ke nan kada ya dauki mataki akan iyalinshi dubu wanan wani irin
rayuwane wai don Allah gaba daya kina neman hanawa yaron nan walwala a rayuwansa.
Shin yar nan daya aurace baki so dashi ko shine yayi maki laifin da har kika
tsaneshi hakan dubu don abin yayi yawa gaskiya shima fa yana da hakkin a kanki idan
kin tauyeshi da yawa dubu ?
Yanzu iya ni zakiwa sheri kina zargin ina zuga mama nice zan zuga mama kuma ?
Iyan tace ke ungo nan yar banzan yarinya mara mutunci duk abinda kukeyi ina
kallon ku keda uwarki .
Ki dubeni da kyau banyi tsufan da ban fahintar komai a yanzu ba nan gabana yanzu
kika gama zuga uwarki akan yaron nan har abin yaso zama fada tsakaninki da yar
uwarki don haka ki shiga taitayinki dani na fada maki niba dubu bace dake daukan
maganan ki.
Shiru tayi don tunda taga iya dinbta juye tasan yanzu idan ta matsa ranta zai
iya baci don haka tayi shiru, ya mike yana fadin yi hakkuri iya ki barta ai tayi
Allah na ganinta.
To wanan kalamin da yayine yasa saratu din kuka wai iya taja dan uwanta yana yi
mata Allah ya isa kan abinda bata aikata ba.
Bayan fitanshima iyan bata kyalesu taci gaba da fada tana fadin ta yaya zaki
zauna kina bin maganan yara dubu ?
Ko yaushe yarinyar nan ta zugaki kika aikata abinda ba daidai ba aka yaron nan
idan aka taliyo sai a iske kune baku da gaskiya.
Yaron nan yasan abinda yake yi dubu idan bai isa ba baya tara mata ukku a
karkashinsa don haka daga yau ina son ku cire masa ido akan iyalinsa don Allah ?
Ku barshi ya zauna lafiya da matansa ku barshi ya tsara irin rayuwan da yake so
dasu a gidansa don Allah .
Ke kuma duk abinda zakice kice saukin abin dai gidan wani zakije kema don ba a
nan zaki tabbata gidin uwarki ba saratu dole dai wata rana kiyi aure ki barta.
Kina wanan halin na hade haden fada saratu wa zai yarda da hakan a gidansa in
wanan dan uwankine yayi hakkuri ya zauna dake da halinsa can inda zaki fada ba
lalai bane suyi hakkuri da hakan.
Yarinya tana abu mara kyau kina mara mata baya wanan hali idan tacigaba ba zai
haifar mata da mai ido ba nan gaba.
Ranan dai bai samu dawowa gidana ba sai kirana yayi yana fadin mu rufe gida ba
zai samu dawowa gidan mu ba a ranan.
Kishi kumallon mata a take naji wani abu a raina lokaci daya kishi ya rufe min
zuciya naji wani irin ba dadi a kasan zuciyata.
Zancen anty Salmane ya fado min da take cewa Rahama ki cire ido akan duk abinda
mijinki zaiyi akan matarsa matukar kina son ki zauna lafiya ki tsira da aurenki.
To sai kin dinga kawar da kanki ga rayuwansa dana matansa kada ki zamo mai bin
kwakwafin abinda yake tsakaninsu har ki dinga tada jijiyan wuya akai don Allah.
Mace mai wanan halin itake sayawa kanta bakin ciki da kudin ta itake sawa
hankalin mijin da kishiya dana zagaye dasu su farga da halinki mara kyau a kan
kishi.
Duk abinda zakiyi Ramah kada kiyi wanda zaki yarda ki kona kanki ki kona mijin
ku don Allah tare da matansa kika sameshi bawai bai sonsu bane ya auroki ?
Suma so da kaunace ya hadashi dasu don haka kada ki yarda kuje lahira ana shari,a
dake kan namiji don Allah ?
Kiyi kokari ki yaki zuciyar ki akan zaman kishi donshi dashi aka halicce mata
kishi tun muna kanana muke da abin mu a cikin jinin ko wace mace yake don kishi
kamar hassada yake a zuciyar mace sai ka tsira daga sherinsa kake samun haske a
rayuwan zaman auren ka.
Tayi min irin huduban nan sosai taka min kwantace da kanta tace kingani nan idan
D baya gidana kwata kwata nakan cire zancensa a rainane amma da zaran ya dawo
gareni kuma ya zama miji sai ranan daya bar gidan nan .
Take naji abinda nake ji a lokacin yana ragewa a zuciya inda na fara karanta
wallahu Ghalibun har karshe ina jin wani sanyi a zuciyana.
Karshe falo na fito nasawa Biba kira ta fito muka zauna nan muna dan hira da
ita don mu rage dare karfe tara nace zan kwanta tace to bari ta je daki nace a,a ba
zan barki ba ki dawo dakina mu kwana tare tunda ba kowa a gidan.
A Gaskiya ina jin dadin zama da yarinyar sosai a rayuwata don gwargado tana da
gudun zuciya sosai tun da safe da zaran ta sallame sallah asuba zata fito tayi
shara da ta gyaro ko ina har kitchen idan na kammala abinci takaiwa su salima dake
daki kwance ta dauko namu zuwa falo muyi wanka muyi shirin fita don tare muke barin
gida da ita.
Shiyasa nake son shakuwa na tsakani da Allah ya shiga tsakanina da ita tun yanzu
kada ta koma tana shakkata har a zata ina mata wani mugun riko.
Dakin Asmau ya kwana a ranan don saiba tunda ya shigo ta shige daki a zatonta
zai biyota irin da suka saba tun tana jin motsinsu a falon har yakai ta daina ji ta
leko ta samu daga shi har Asmaun basu falon a lokacin.
Duk yadda taso ta taushi zuciyarta yadda kowa ke bata shawara ta kasa hakan a
lokacin cikin daren nan ta kira yarta tana labarta mata abindake faru.
Nan dai ta bata hakkuri akan ta bari da safe zata je gun wani malami suji yadda
za ayi inya kama tazone da kanta saita san karyan da tayi tazo kaduna din suje
tare.
Zancen yar uwar nata ta yarda dashi har taji dan sanyi a zuciyarta inda ta kwana
tana tunanen daga mijin har mu biyun don ko Asmau ba kyaleta zatayi ba tunda tagane
tana munafuntar ta ko ita fitar da ita gidan zatayi ta huta da wata kishiya.
Kaiya koda ta samu sa,an hakan ai wata zai dauko mata abinda mata basu gane ba ke
nan don Asmau dai bata tare mata komai ba a rayuwanta.
Don itace take kwarar Asmau ma idan za a fada tsakani da Allah amma tace dani
din da take ganin shigowana gidan da bakar tsafi mu na fulani na juye kan miji ya
koma gareni gaba daya yanzu da Asmaun da bata dauka bakin komai ba duk zatai muna
kan mai uwa da wabine lokaci guda ta huta.
Ita dai butinta shine ta bude ido taga ita kadaice a wajen miji sai yarta ban
mantawa da case din da sukayi lokacin akan cikin da Asmaun ta samu ita bata samu ba
kafin mijin ya kwanta ciwo.
Case sosai akayi don saida kawu dauda shiya yazo gidan da sunan sulhuntasu aka
zauna da mijin dasu akai case din.
Wai ashe ita Saiba data haihu tace zatayi planning don karta samu ciki yarta
karama mijin ya kaita sukaje sukai planning din.
Sai gashi kwatsam taga Asmau na laulayin ciki tace sun munafunceta ita dashi ta
tayar da bala,i ta hana zaman lafiya a tsakaninsu.
Inda planning din ya sako mata reaction dinsa tana jini akai akai nan kuma
hankali ya dawo ya tashi sukayi ta zuwa asibiti sai da kyat ta samu lafiya.
Bai shigo gidan mu ba don yasan mun fita school sai karfe biyar na yamma yaje ya
daukoni school muka dawo tunda na tunkaro motan naga yadda ya kura min ido nasan ya
tsargu shima.
Ina zuwa kan na bude motan nake cewa dashi ina wuni yaya ya mutanen gida kuma ?
Ya dan washe yana fadin shigo mota mana kafin mu gaisa kya tsaya waje kina
gaidani muje saimu gaisa a hanya ya bude min nashiga na zauna yaja motan muka tafi.
Saida muka hau titi da kyau yake fadin ya kuka kwana nace lafiya kalau yasu
mama dasu iya kuma suna lafiya iya ai tace dani wanan zuwan bazan koma ba saina
kawota gidanki.
Allah sarki nima haka nace ai kafin kabar gari zanje ina son zuwa na gaidasu ai
don baka nan ne banje ba amma abin na cikin raina sosai.
To dake da ita bansan wa zai fara zuwa ba sai kiyi hakkuri tazo gidan naki
inyaso daga baya sai in kaiki ki gaidasu ko ?
Abinda kace yaya shi za,ayi naga yayi murmushi ya kai hannunshi saman nawa yana
murzawa yace iya sarkin rigima na kula ita kadai ke mara min baya sai salima da
Habu game dake Rahama ?
Nace to ayi hakkuri kowama zai mara ma idan sun fahince ka daga baya rashin
fahintane a yanzu din don anyi masu ba daidai ba ?.
Haba dai ni abinda ke ban mamaki dayane shine wai yadda mama ta kasa fahintar
manufata har take zargin wai bani cikin hankalinane.
Na zata manace zata fara farin ciki da wanan abin sai gashi makiran yaran nan sun
shiga sun fita suna neman hadani da ita a yanzu kuma ?
Bandai tambayeshi suwaye ba shi kuma bai fadi sunansu ba nace anty Yanda fa da
Abba suna lafiya ko ?
Wai maria kike nufi sai naga ya bugi bakinshi yana fadin wai sorry sister nake
nufi nama rasa yaya zan kirata a yanzu sai abin ya ban dariya nace to ai
surukarkace mana ba dole bane saika saya mata suna koka kirata da maman Abba kawai
idan kana jin nauyintane a yanzu ?
Fine sunan yayi min sosai maman Abba din zaifi sauki an wuce wajen yanzu ai
maman Abba din yafi min saukin komai sosai wallahi.
Bamu je gida ba naga ya dauki hanyar cikin gari wani waje mukaje ya tsayar da
mota dan nisa da mutane ya fita ya shiga wajen .
Ya dan jima a ciki sai can na hangoshi ya fito da ledoji ga wani a bayansa sun
nufo wajen motar mu kai tsaye ya bude bayan motan aka loda mai kayan a ciki ya
sallami wanda ya rakoshi din yana mai godiya.
Yana zama yake fadin sorry na barki zaune ko na danyi murmushi na dago kai ina
fadin ai baka jima sosai ba ya tayar da motar muka bar wajen.
Mun hau titi yake fadin naso na dan tsaya in saiwa Asmau magani jiya taban
tausayi sosai da dare shine naso in biya in karba mata magani wajen abokina.
Bari dai in saukeki sai in dawo haba dai idan hakan yafi sauki muje mana Allah
dai ya sauketa lafiya naji yace amin tana wahala sosai don tace min duk kwanakin
nan haka take fama da dare.
Allah ya bata lafiya na kara fada cikin rashin wani abu a kasan raina da nake
tunane watau a dakin Asmaun ke nan ya kwana ba saiba ba yadda nake tunane da farko
na zata gun saiba ai zai sauka ashe ba haka abin yake ba.
Munje ya karbo maganin mun kamo hanya yake fadin yanzu da bakowa a gida ita
habiba fa dawa take zama ke nan ?
Na dan nisa ina fadin nima tunanen da nakeyi kenan a raina don nasan ta dawo tun
karfe biyu gashisu anty salima basu gidan yau don da kota dawo suna gida zata
samesu.
Kai gaskiya hankalina bai kwanta da hakan ba don kinga diya mace ce kuma gashi
ba wani gida kuke hurda dasu da zata zauna kafin ki dawo ba.
Bayan haka nima ba zanso tana shige shigen gidaje ba gaskiya gara dai din a samo
wata mace da idan ta dawo tana gidan tare da ita.
Saidai banson kuma ai yawa a hana min hutawa na a gidan koda yake bari zan daiyi
tunane akan hakan asan abinyi da zai dace.
Mun isa gidan ban tsaya ba son fitsarin daya cika min marata a lokacin na shiga
gidan saida na rage maratane na fito na samu ya shigo da ledojin an aje a falo.
Biba kuma ta gyara gida har ta dora girki ruwa yana batu tafasa lokacin hakan
yasa natsaya na tuka muna dan semo da zamuci.
Haka kuma na dibar mata kayan miyan da zata daka muna inyi amfani dashi kana
nafito na nufi dakinshi na sameshi yana zaune bakin gado yana waya ganin hakan na
juya zan fice dakin da hannu ya kirani na dawo ya nuna min waje in zauna.
Zaman nayi a gefenshi dan nisa kadan dashi kafanshi yasa ya tokaro kafata hakan
yasa na kalloshi yayi murmushi yake tambayata da hannu wai na kara matsowa na make
kafadata alaman a,a.
Ganin zai kamuni yasa na mike tsaye da sauri na fice ina dariya kitchen na koma
na samu biba ta hada miyan tana soya markade na tsaya na karasa na hada.
Ina gab da karasawane naji yasa min kira a falo na amsa na fito bayan na fada mata
yadda zatayi ta sauke idan yayi.
A zaune na sameshi falon naji yace dani why kike guduna tun shekaran jiya Rahama
na fahinci hakan.
A,a ba hakana bane yaya ina dai guje muna shiga hakkine shiyasa amma ai ban
gujeka ba akan me zan gujeka kuma ?
Zonan ya fada yana nuna min kusa dashi duk da akujeran dake gefenshi na zauna a
lokacin haka yasa na dan matsa kusa dashi din naji yace Allah sarki.
Kisa a ranki mijin ki Rahama ba jahili bane duk nasan wanan kada ki tunanen hakan
a kan mu don Allah baice don bake keda girki kada in tabaki ba.
Iyaka dai kada mu wuce gona da irine a halaka da har zan shagala in manta da
wata a gabana ko a da Rahama ni jafar banyi hakan a tsakanin abokan zamanki ba
balle yanzu da shekaruna suka karu.
Na san me nakeyi na kuma ji dadin hakan da kika san wanan a zuciyar ki don haka
ki saki jikinki idan zaki saka amma tabaki saina taba gaskiya don ni mutum ne mai
son hutu a jikin matana dake kusa dani lokacin.
Ban daiyi wani magana ba yake fadin ga wanan kayab mana kira habiba ta dauke
makushi zuwa ciki ki duba ki gani ban zaunu ba balle na san abinda za a karo maku
na amfani.
Mun gode na fada yayi murmushi tare da mamakin komai yayi min irin hakan na
amfanin gida zanyi mashi godiya kamar ba kanshi yaiwa ba abinda bai saba dashiba ke
nan ga matansa.
Alam din wayanshi yayi kara ya dauka yana fadin