Showing 321001 words to 324000 words out of 328222 words
Chapter 108 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
ko ?
Ina ya kamata in tafi nayi shiru tunda nasan tambaya dai kawai yakeyi saida yakai
zaune nace saura kwana ashirin da biyu muyi arba,infa yanzu.
Sai akace kada inzo sai kinyi arba,in ko banda wanan koda kikaga ban zama saboda
mamace kuma aiki akai maki kina son hutu yasa nabarki ki huta don nasan innazo zaki
wahal da kanki da aiyuka yasa na daure har wanan lokacin.
Kamar ince yanzu ko kagaji da hakkuri da zamanta ka dawo ko karanta zakayi daga
gidan iya dai tunda mukaje suna bata dawo ba tayi zamanta gida tace na samu sauki
ai saidai.
Banyi magana ba na shiga bandaki na hada mashi ruwan wanka amma saida na koma
daki na dauko ruwa a cikin flask don ba ruwan zafi gashi ana sanyi a ranan balle ya
watsa ruwan sanyi.
Ya shiga wanka na koma dakina muka kwanta da Amir ban falka ba sai Asuba na
tashi nayi sallah kitchen naje na hada muna ruwan zafi don yin wanka har lokacin ba
wuta a garin gashi engine din gidan ya baci ba a gyara ba har lokacin duk da ban
jona mashi kayan nauyi dama.
Na juye ruwan na fara hada breakfast don bakin dayazo dasu mama najin motsina ta
fito daga daki tana fada nace aina sa biba ta kwashe min ruwan takai min.
Lafiyayyen breakfast na hada nayi wanka na gyara kaina lokacin mama ta fito
tayiwa Amir wanka ta kimtsashi ta miko min shi in bashi nono Biba ta shigo tana
fadin Anty naga wasu motoci a wajen gidan nan fa ?
Da maisu a gidan ai motocin me kuma kinkan fara maganan ki ke nan mara ma,ana
nace ta ganine mama yaya ya dawo jiya da dare kuna barci.
Cikin mamaki mamake fadin lalai munyi barci jiya ban kayi dogon zance mai tsawo
da ita saidai ita ta dinga min hira ina murmushi ba ita kadai ba kusan hakan
dabi,atace rashin dogon magana mai tsayi da kowa hakan nake.
Shine ya fito yana muna sallama mama ke fadin yanzun nan take fada muna ka dawo
jiya da dare ina tunda iska ya taso aka fara hada hadari muka shige daki ai suka
gaisa dashi tayi mai yaya hanya ?
Bayan sun gama gaisawa ya juyo yana fadin mutanen nan zasu kama hanya yanzu
gashi na makara ba ayi masu abin karyawa ba kuma ?
Nayi na fada a sanyayye kinyi fa eeh na soya dankali da kwai sai dan ferfesun
dana hada da sauran kayan cikin daya rage muna a fredge amma kin kyauta wai da
nafitone in kaisu su karya su kama hanya.
Biba ta fito da kayan zuwa wajensu ya jima a can din kafin ya dawo bayan ya
saukesu inda zasu shiga mota na na hada mai ruwa yayi wanka sanan ya fito karyawa .
Bayan ya zauna yake tambayan mama nake fada mai tana daki yace nayi mashi magana
da ita nashiga na kira mama din tazo.
Mama din tafito tana fadin ka dawo ashe bakin sun tafi ko yace sun tafi mama
daga can nazo dasu sun jawo min motocine zuwa nan yan kamfanine aikinsu ke nan idan
ka sayi mota a wajensu zasu jama sukai maka duk inda kake so.
Tana mamaki tace su kuma ta haka sukeci da iyalinsu Allah ka rufawa bayin ka
asiri ya amsa da amin tafiya ai tayi kyau sosai mama addu,anku yana aiki sosai a
garemu kullum sai kara ganin haske a rayuwa mukeyi mama .
Addu,an mu da alherin ka ga mutane malam da zamu samu irinka biyu zuwa ukku a
cikin mu da yanzu an gama saninku a ko ina fadin kasan nan hannu daya akace baya
daukan jinka.
Anyi ma yawa akai malam dole jiki yayi tsami ko a hakan mama Alhamdullahi don
tafiya anyita a sa,a sosai wana karo ban taba tafiya mai sa,a kamar wanan ba a
rayuwana ba.
Mama ta gyara zama tana fadin Alhamdullahi haka muke son ji ko yaushe gareku muji
kuna samu karuwa tako ina shine addu,an mu gareku ai.
In sha Allahu mama bana ina son ku taka arfa gaba dayan ku da yardan Allah
cikin mamaki tace gaba dayan mufa kace yace insha Allahu hakan nake fata mama.
Allah yace malam Allah yace daga gefe na amsa da amin a cikin murna tace dadina
dake yar nan hankali yau da watace ya fadi hakan saita nuna bakin ciki a fili wasu
matan basu da lissafi a rayuwa ko kadan wallahi ni dai nayi murmushi ina fadin mama
aikoni keda hali haka zan iya kaiku insha Allahu.
Haka shike yata nasam zaki iya hakan idan Allah ya hore aka kwashe da dariya
suna ta hiransu yana karyawa har ta dauko mai zancen yadda saiba taje tayi hauka da
kuma zancen zuwan saratu gida.
Nan ya tsayar da cin abincin yake fadin me kuma saratu tazoyi gida yanzu ko haka
akeyi kazo gida daga kaika gidan miji wai ?
Towa zai sani malam uwarta ta boye zancen ga yan uwanku nasan kai ake jira ka
dawo yanzu daka dawo ai dole a nemesu ai yaja tsuki da alama abincin ya fita mai
rai yace Allah mama naje gida banji wani abu mai karfi ba yau din nan tana konawa
dakin mijinta.
Basu san ka dawo ba ke nan tace shigowa na gari na yo nan gidan don bakin nan
dana zo dasu nasan idan na kaisu can karsheta inji kunya don haka nayo dasu nan
gidan ai.
Bai wani jima ba dai yabar gidan muka zauna hira da mama tana kara ban tarihin
rayuwansu lokacin mijinsu yana raye kafin ya rasu.
Gidan Asmau ya fara biyawa a lokacin ya samu suna karyawa ta dan fara kame kame
tana fasin ta zubo mashine tace wani ai tun jiya na dawo garin ina gidan Rahama can
na sauka.
Tayiwa bakina abin kari sun karya har sun kama hanya sunce sun wuce kaduna tun
dazun nasan kona kasu nan takaici kawai zaki barni dashi ace yara kananu sai
wajajen sha dayan rana suke karyawa kina kwance kina barci don baki damu dasu ba ?
Yaya ban damu dasu bafa kace ko nayi abin karyawa tun dazun karshenta baci
zasuyi ba cikin tsawa ya hauta da fada yana fadin nasan maganin ki yaya Auwal zan
fadawa shi zai dauki mataki a kanki.
Da sauri tace yanzu dai ai na dinga tashi da safe ina hada masu bashike nan ba ka
kaini kara wajen yaya Auwal kasa yazo har gida taci min mutunci ga banza.
Fita yayi ya kama hanyar gidansu mama da ita ya fara cin karo zata unguwa
ganinshi yasa ta dakata tana tambayan yaushe ya dawo yace jiya da dare.
Tare suka shiga wajen iya suka gaisa da ita Salima ta fito suka gaisa har
tabada baya zata koma daki tayi brush ya dakatar da ita yana fadin yaron nan kabir
yana gari ko yayi tafiya ?
Yana nan yaya kice yazo karfe hudu ina nemanshi yakira layina yaji inda nake
lokacin ta amsa da to yaya tashige don kimtsawa ya dubi iya yace zaman salima da
Nafisa a gida yana damuna iya ?
Ina son ayi aurensu a huta aji da wa yanda ke tasowa yanzu kuma ita Nafisan tana
da mijine yarinyar da uwarta ta koya mata kitihi iri iri wa zai aureta ?
Haba dubu kikan fara maganan ki ke nan nafisa dince da kitihi har kala kala haka
ita wace ba a koyawa ba tayi auren ne ina mamaki gaka da abin zagi a gindinka kaje
zagin nawani ?
Irin abubuwan nan tambayan bawa sukeyi a rayuwa ke da girmanki meye na fadan
hakan akan dan wani don Allah kinsan nufin yaron nan akan auren nan akan yaran nan
daya fada ?
To iya nidai bada wata manufa ba fada ba din Allah dukkansu aure zasuyi kwanan
nan ita saratu bagata can gidan mijinta ba yanzu an huta da ita.
Wace saratu saratu saratu kan na dakin uwarta yanzu ka ganta tashigo gidan nan
tace zata gidan kawarta a kwashe mata kai.
Saratu fa iya garin yaya ta dawo gida kuma iyan tace ka tambayi uwarta ita tasab
dalili nayi magana tunda mijinta ya bugo ta koma ance ina nafito.
Ya kuma turo abokinshi uwarta tace bata komawa sai yazo ya juya wajen mama din
yana fadin mama yaya akai haka kuma ban sani ba ?
Ta yaya zaka sani tunda baka nan yau kwananta goma sha daya da zuwa miji ya
dauketa ya kaita kauye ya aje cikin matanshi ina saratu zata iya aikin yawa da
sukeyi ?
Mama ba aure taje yi ba su wa yanda ta sama ba haka suke zaune dashi ba tunda
suna son mijinsu ta tareshi da fadin sai ta zauna wahala ya kasheta ke nan ko ?
Mama dakata don Allah kin taba jin inda wuya ya kashe mutum don Allah ita mace
fa da hakkuri akasanta ita dabance a cikinsu daba zata iya hakkuri da mijinta ba ta
zauna yadda kowa ya zauna yana hakkuri ko tafi sauran matan nashune da suka zauna
su ?
Ina an fada mata tace tana iyawa karya ake mashi saida na zauna daku kafin duk
su yaya su saka baki cikin maganan tana iyawa tace min tana son shi san nan yanzu
zata dawowa mutane gida don tana yar iska uba me tadawo yanzu ayi mata to nan ?
Kana magana kamar baka fahinci mutane ba ina saratu zata iya girkin mutum kusan
dari don Allah ?
Amma mama ita tace tana sonshi ai yau din nan zata koma ai tasan yana da iyayye
yana da mata da yara tace ta amince ta aureshi mu zata dawo ta rainawa wayau
yanzu ?
Irin rainin wayau da na guda ke nan gun Asmau don nasan sakarauce ta mayar da
kanta sha,shasha saboda son jiki nazo da baki dole gidan Rahama naje na sauka
jiyan.
Ina zakazo da boka a barshi da yunwa yanzu dana biya gidan sai yanzu na samu wai
tayiwa yara abin kari zasu karya yaro za a bari da yunw har wanan lokacin saboda
sha,shancin banza da suka dorawa kansu.
Dama nasan za a rina wanan daban tsiyan da suke taruwa sunayi a wuni ba mai iya
yiwa kansa abin kwarai yanzu gashi duk ta dauka in anyi magana mama kice an matsa
mata ba a kaunarta ina tsiya ina girki ga mace girkifa za ace ya koro mace gidan
miji idan ba tsiya da samun waje ba.
Naki bai hadaki da mijinki ba sai zancen girki din Allah mama ta amsa da fadin ai
shima ya shafi mijin tunda yasan inda ya dauketa da zai kaita kauye yace sai tayi
kalan aiyukansu.
A ina ya dauketa gidan attajirai ko gidan sarakuna naga dai har gobe gidanku suna
aiyukan hannu na hausawa iya ta fada yanzu inane yar nan Nafisan da kike zagi ba
zata iya shiga ba ?.
To taje kauyen ita amma saratu bata komawa kauyen nan sai dai asan abin yi
gaskiya kauye kan ta fito ke nan cikinsa in sha Allahu.
To shike nan mama tunda haka kikace saidai ku sani duk wani zance na saratu daga
yau bani ba ita wallahi ta zauna gida tunda kunga hakan yafi maku.
Ya mike iya ke fadin kai Alh dawo mana ya juyo yayi dan murmushi yake yana fadin
ke kuma matar Alh ba don bana in sha Allahu ga kujeranki ga tawa iya muna gaban
jirgi da yardan Allah ni dake.
Kai kai kai kar kasa in fara shiri don Allah wanan ai ba karamun fata bane kayi
min Allah dai ya nufa yasa hakan abakin yan amin.
In sha Allahu iya haka nake da niyan dake da uwayena dukansu hudu in Allah ya
yarda zamu keta hazo muje dakin Allah mu ziyarci kabadin Annabi mu sauke nauyin da
baba yayi niya Allah bai nufa ba.
Kace in fara shiri ke nan dai Jafaru yace iya fara insha Allahu makkan bana dake
ciki da yardan ubangiji kuwa iya in ranmu yakai.
Ranmu yakai jafaru ranmu yakai Allah yasa muna da rabon ganin hakan da rayuwan
kai naji dadun wanan fatan ko ince albishir din Albishir dai iya.
Su kishiyoyinki na sayowa ko wacensu mota ita Asmau daya ita kuma Rahama daya na
tausan gaba uwargida zata makka a taushi kirjinsu ta kwashe da dariya tana fadin
aiko uwargida ta kosa tunda motace tausan gaban kishiyoyin ta.
Mama na gefe sai dan murmushin take takeyi saida raga alaman fita zaiyi daga
falon race wai da gaakiya kakeyi ne yace insha Allahu mama haka nake fata ku sauke
farali a banan nan kedasu mama da su yaya Auwal inda hali zan hadaku da barakha din
iya kuje.
Allahu Akbar lalai dan nan arzikine iliya dan mai karfi ke nan yaro ya zo da
arzikinsa da kardin Allah ,,,, ji iya kuma ana zance wani dan kike magana tace mai
babban suna mana wani dan ai haihuwansa alherine a waje dubama ga yadda aka samu
yaron nan koshi ya isa yasa mutum ya fahinci hakan .
Fita yayi ya barsu bai kara zancen saratu ba fitan da mama batayi ba ke nan a
ranan ta kira yaya barakha tana sheda mata abunda ya faru barakha din tace kai amma
jafar ba abunda za ace mashi.
A yanzu jafar din ya juye mata kamar bashi ba tana jin shakkunsa da nauyi ba
kamar jafar dun baya data sani ba da rake iya tankwasawa kota umurceshi yabi.
Tasan yasan abunda ke nan akan kawu amma ya share ya nuna bai san da hakan ba ko
zancen bai dauko mata ba amma zata kyaleshi taga gudunsa.
Tasan ba zai taba kyale kawu di yazid ya wullakantashi ba ai tunda daga yazid
har habu sam basu jin zamcenta yanzu jafar din ne mai dan dama dama a cikinsu.
Yanzu kuma shima ya juye har yana son ya fisu gashi ta kasa gane matsalan daga
wajenrta yake balle ta gyara Allah yasa mu dace amin.
Sai washe gari yabawa kowa motarta ya fadi kalan tace Asmau ta zaba tace baka
take so tabar min farar munyi mai godiya dani da ummah har da mariya ta kirashi
tayi mai godiya ya kuma ji dadin hakan sosai nagane hakane da yake cewa ke kina ta
wahal da mutane da kira halal zaki saya masu credit ne ?
Zancen makkasu ya tabbata wurin mutum goma ya biyawa makkah da zasu tafi har
labarin irin tarin dukiyan dayasamu a yanzu yakaiwa saiba sai gashi ta fara bugo
mashi waya tana ban hakkuri.
Kashedi yayi mata yace kada ta sake kiranshi idan ba haka ba zai kaita ga hukuma
ayi masu tsakani da ita amma hakan baisa ta daddara ba.
Don sai ta fito da sallon kiran wayan taba yarta idan ya dauka tace daddy yaushe
zakazo ka daukemu bata san tsiya ta kullawa kanta ba a wanan sallon .
Haka yasa ya tura su yaya Auwal su karbo yarinyar a hannunta nan kuma tace bata
isa ba shima yaya Auwal yace bata kai mashi can ba dole tabada da yarinya don bai
yarda da tarbiyanta ba.
Dole mahaifita yasata gaba ta mika masu yarsu suka dawo da ita kaduna can gidan
Asmau aka aje yar don yaso yace a wajena zata zauna mama tudu tace dashi ko kusa
zaman yar nan yana iya kawo matsala tsakaninka da yarinyar nan kaga ba shiri take
da uwarta ba.
Ka barta can ta zauna tare da yan uwanta tunda dasu ta saba dama ita yar hakan
zaifi mata dadi yace mama niba ra,ayinta naso ba don ta samu tarbiyan da nakesone
ai tace barta dai can tukun na hakan yasa dole da akazo da ita ya barta gidan Asmau
din.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/14, 22:19] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
1️⃣0️⃣0️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Zance dai tun ana ji kamar karya saiga abu ya tabbata Alhazai sunata shirin tafiya
saudiya don yin ibada wa yanda sukai nasaran zuwa sune yaya Auwal da ya Isah yaya
barakha da Asmau matarshi su mama su hudu sai iya da yaya Rukkaiya.
Kamar yadda ake samun kalubali idan haka ya faru dole sai anyi tsegumi shima ya
samu a wajen mahaifiyarshi don ta nuna rashin jin dadinta tayi fada don me zaikai
har mutum uku maka dakin mama lokaci daya ga dan uwanta da suke uwa daya uba daya
bai kaishi ba ?
Kome kawu yayi mashi dai jininsune don shiyasha nono ya sake mata baiyi magana ba
a lokacin don sai ana gab da tafiya aka san masu sauke faralin ya hana kowa ya fito
fili ya fadi donshi kowa ya kama bakinsa da zancen.
Saida ta kara tayar da zancen a gaban yan uwansa gashi ga habu ga yazid ga iya
dasu salima ta soma korafi akan ya nuna mata yanzu yakai tunda har dan uwanta badai
daraja a idonsu ya biyawa kowa nasa makka yaki biyawa dan uwanta don ya tozartasu .
Ace dakin mama harsu ukku zai biyawa makka mama tudu ta fitane gareshi ko takaita
daraja a wajenta a,a mama kada kice haka don Allah ?
J da kike gani ni yanzu ban iya cewa komai akanshi yasan dalilin da yayi hakan a
garesu ba wani magani ko munafuncinsu daya cishi.
Mutanen nan suna nunawa a gaban kowa shi dan dakinsu abinsa idan ya taso tun
baikai haka ba sai idan karfinsu ya kare akanshi da baida lafiya nan gaban kowa
yaya Ai take kuka tana fadin dama ita