Showing 15001 words to 18000 words out of 328222 words

Chapter 6 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

dare sosai na shigo ba mama wajajen shigowa kaduna dare yayi min na
shigo nan wurin sha daya saura na darene ai.
Allah ya kyauta nan ya fara gaida ita cikin ladabi kafin muryan iya ya ratso tana
fadin wai Jafar ne da safen nan haka ?
A nan ya kwana Iya mama ta fada ahawaraki shine baka tayar dani na karbi jakkar
tsaraban taka ba ka mikawa marasa hankalin matanka ?
Iya ko allura ban shiga dashi ba gida sai makullin motata kawai ko yanzu kina
iya karban jakkar kafinsu ya fada yana nufar iya din itama juyawa tayi zuwa wajen
kujerun falon ta zauna shima haka ya zauna yana fadin.
Habu bai shigo bane ko har ya fitane zuwa wajen aiki mama ta karaso tana fadin
anya yau zai shiga kaduna kuwa yadda suka kwaso gajiyan nan suma.
Gama tsaraban da yayo muna nan ko kwancewa ban samuyi ba har yanzu Iyace tace
badai abinda zai lalace a ciki ko ?
To ina na sani iya ai kinga baiko tsaya muna bayani ba yafita da sunan zaije ya
dawo har yanzu bai shigo ba kuma karna taba ya kasance ba nasa bane duka naga
abinda yawa hakane ?
Ba zai shigo dasu nan ba ai idan ba nasa bane kinsan halin Habu ai mama Jafar ya
fada shi nake nema ya kamin mu fito da kayan danazo dasu ashe ba tashi ba har
yanzu.
Kuna da kokarin yaran nan saidai kai Jafar matsalan matan da Allah ya bakane sai
addu,a mata ba sanin ciwon kai ace har yakai don rashin hankalin kishi irin nasu
yar nan ta watsawa uwarku abinci a jikinta abinci mai yawa don wullankaci su
wullakantashi haka wuein bakin kishin su na tsiya ?
Abinci kuma suka watsamawa Iya kardai zancen da Nusaiba ta kirani ke nan
shekaran jiya take son min ban saurara ba don dama shiya kawoni garin nan jiya
tunda naji ta ambaci sunan mama a cikin zancen ta hankalina bai kwanta ba na taso.
Kaiko dai akan wanan zaka taso haka zuwa nan iya shegen yaran nan ne kawai don
batama san da ina tafe ba ai kodata jefowa yar uwa abincin sai saman jikina ya dira
ya zube banso iya ki fada mashi ba ai tunda anyi ya wuce ko tun a wanan ranan indai
zasu gyara su gyara don ba,a wasa da abinci.
Mama indan iya bata fada min ba waye zai fada min bayan don haka take zaune
damu gidan idan suna abu ba a tsawata masu watarana ai za a samu sun illanta
kawunansu a dawo ana ganin laifin ku daga baya.
Zasu aika tundai wanan mai zubin yan ruwa da take daukan kanta wata tsiya banda
karyan banza da ci mutunci babu abindata koya a duniya na kwarai Iya ke fadan
wanan magana a cikin hasala.
Sallaman Abubakar falon yasa suka sake zancen ya shigo suka shiga gaisawa da
juna kafin ya sanu wuri ya zauna mama dubu ta jefo mai tambaya tana fadin kayan can
dakazo dasu fa Habu ?
Juyawa tayi ya kalli wajen da mama din ke kallo kafin ya dan bata fuska yace
daga can nazo dasu meye a ciki Jafar ya tambaya ?
Mikewa mama tayi ta isa wajen jarkan da akaiwa nadi cikin buhun irin na da da
ake amfani dashi sai wasu kwanduna da aka rufe da ganye zakice gorone a cikinsa aka
rufe ta shiga budewa .
Yayin da iya da su Habu din suke hiran yanayin kasan Cameron da irin mutanen dake
rayuwa a cikinsa muyan mama dubu sukaji tana cewa Habu wanan ai ba karamin kaya
bane ka dauko ?
Meye a ciki mama Jafar ya tambaya yana mikewa mama ta juyo tana fadin wallahi
nono ne da danyan madara wanan kuma kindarmo wanan wara da ake kirada (wagashi )
warar fulanice ta ainihi da aka sani da ainihin nonon kindarmo za,aita dafashi har
ya cure a waje daya kana a dauko buhu ko abin tsama a matseshi yadda akeson
girmansa saidai nasan akwai sauran fasahan wanan abin da ban fada ba a bayani amma
dai nonoce zalla ta kindarmo sabon tatsowa ake wanan wari din dashi wanda akecinsa
danyensa ko kuma a yanyankashi kamar nama a sayo da mangyada ko manja.
Shi wanan abin yanzu soyashi za ayi Jafar ya tambaya mama Dubu tace kwarai kuwa
sai kace a karo maka idan an soya din ai ana amfani dashine kamar nama zaka iya
zubawa a cikin miya a dafa miyar dashi ko kuma ka watsa saman shimkafa kamar nama.
Ban taba ganinsa ba Jafar din ya fada nima dai gaskiya bansanshi ba Yaya J ,
kawai dai naga ana sayane nace nima aban na sayo wasu mama mashi nazo dashi.
Mama Dubu dince ta katse su da fadin wanan kuma chikwi nefa Habu sai ta mike
tsaye tana fadin amma kasha kudi a wajen nan bari nazo na dibawa yan gida akai
masushi a mutuncinsa tun bai tabu ba don in suka kai kwanakin da zanyi a nan suna
iya lalacewa.
Kallon juna diyan nata sukayi wanda ta fahinci nufinsu tace meye duniya Malam
idan kaba wani ya kare idan baka bayar bama karewa zaiyi gara ka bayar din kaci
moriyansa can inda bakai tsamani.
Ai bamuce komai ba mama zuwa anji zan shiga na gaidasu da yamma sai a zuba na
fita masu dashi don naga shi Habu kamar da sauran gajiya a tare dashi.
Duk wanan nono shanune a cikinsa ya nuna sauran jarkan dake rufe mama din tace
ina gani tana kallon danta habu ko zai masu bayani maimako ya bada amsa sai ya juya
ya koma saman kujera a daidai lokacin mama ke fadin ikon Allah man,shanune haka
cike har jarka.
Kai habu wanan lissafin dariruwan kudi akeyi fa ina kasamo wanan kaya haka kamar
na gara Iya ta fada tana mikewa zuwa wajen taga man shanun da aka fada din.
Sai fadi take saidai wani lokacin suyan manshanun fulani kamae harace don basu
irin suyan mu na mutane gari a saka albasa da gishiri don yayi kamshi haka suke
soya abinsu ba komai a cikinsa.
Kada kisha idan bai hadu ba Habu kai kaji iya tun bataci ba fara kushe abin
murmushi yayi kafin can yace ba manshanu ba ai har mai man shanun zan dauko maki
gidan idan ta girka ta baki kada kici tunda basu iya suya ba.
Au to kinji abinda ya fada shidai ke nan bafulatanan kasan can da sukaje zai
auro sai ki shirya Iya kishi da balatana kuma yanzu.
Barni a Iyata da nake yayan hauawan ma gasu gaban mu na kasa gane kansu yara
kamar kansu aka fara kishi yara kanana da bakin kishin tsiya irin ta hauka.
Ai ba dukansu bane basu da hali iya habu ya fada don gara Asmau ita tasan
darajan kowa batawa mutane rashin mutunci ita.
Babu gara kana ina suka watsawa uwarku abinci saman jiki ga hijjabin can ta jika
yaki fita har yau don iya shige irin nasu .
Abinci kuma suka watsawa mama a jikin garin ya haka ya faru mama kai ya jafar
wani mataki ka dauka akai yanzu ?
Shine nan ka ganni zaune ina son iya tayi min bayanin abindake faruwane sai gaka
ka shigo aka kawar da zancen da muka soma.
Ai bada sani hakan ya faru ba nan dai mama ta kwashe yadda abin ya faru wanda ta
sani ta mayar masu ran yayan nata ya baci sosai da hakan tunda Abubakar yafi daukan
zafi akan zancen.
Ya dago kai yace mama shine kuma kike cewa a kyalesu har su iya wanan abin kuma a
saka masu ido gobe su kara wanda yafi wanan ke nan ko idan an kyalesu.
Kaiya ita wanan mai shigar cikin bafa laifinta bane na fada maku yadda zancen
yake ya juya wajen dan uwan nasa yace kai kaji bros ya lumshe idanunsa don baida
abinda zaice kuma tunda mama ta hanashi daukan mataki akai tace rashin sanine ya
jawo hakan yayi hakkuri da matanshi ya dai tsawata masu kan hakan.
Gaba daya falon yai shiru saiga Asmau tashigo da sallamanta ganisu haka a zaune
yasata dan tsarguwa tana kuma mamakin ganin har Habu da bai faye zama dasu ba yau
duk suna tare hat dashi.
Sun dai amsa mata gaisuwan saidai ta tsargu duk da wancan kaifin ita bata sashi
a zuciyarta ya tsaya mata tunda ba itace tayi laifin take gani.
Sai bayan ta gama gaidsune ta dubi mijin nasu tana fadin yaya J an gama
breakfast don haka ta taso ana ce masa a cikin unguwa kaf manya suce dashi malam
din gidan Sanda .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f


MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,



Lokacin da Ya J ya fitar da nasa tsaraban kai tsaye part din Iya yace Abubakar ya
kai mashi a can wanan yana daga cikin sallon horon da yake son yi masu a mumuke .
Bai tsaya ya karya kamar yadda Asmau ta bukataba gareshi wanka yashiga har
yafito duk a cikin kyankyami yake haka ya shirya a cikin wani yadi fari na maza
dayasha dinki kayan sun matukar karban jikinshi sosai ga ogogonsa daka kalla kasan
bana ranke ranke bane.
Haka takalman kafansa baki masu dan igiya daga baya amma ya taushe igiyan da
dudugenshi ma,ana bai kaunan saka belt din takalman ke nan a lokacin.
Turarensa ya dauko ya fesa a jiki abinka ga farin mutum nan kyauwonsa na asali
dake rudin jama,a ga kuma jin dadin da jikin nasa ya nuna tare da wayewa sai hakan
ya taru ya karawa jikin nasa ma,ana sosai.
Duk cikin yaran mama Dubu ya jafar yafisu haske sosai duk da kaf diyanta
fararene masu matukar kyau sosai sun biyo sashen mahaifinsu da yake shima farin
bufulatanine daya bar gida tunda karanta don mutumin yolane zama ya kawosu Zaria
shida iyayyensa amma komai nasu yanzu a cikin zaria suke rayuwansu da komai don yan
bayama basu san gida ba.
Part din Iya ya nufa inda ya samu mama tana kwashe dan abincin ranan data dafa
masu yayi sallama ya shigo yana gaidasu da aiki nan yake fada mata zai fita yakai
wankin mota ya kuma leka kawu dauda don sun shaku sosai da kawun nasa.
Kusan duk wani motsin Jafar kawu dauda yasanshi shiya rike a matsayin mahaifi tun
ma mahaifinsu yana raye kafin ya rasu.
Cikin jin dadi mama take fadin ashe bari a bada tsarabansu saika mika masu daga
can yace yayi mama yana zama yake fadin akawo nasu umma na mika masu don har can
nake son shiga in gaidasu.
Ka kyauta malam abinda zance ke nan ka rigani Allah yai maku albarka ta juya don
taje dauko mashi sakon kafin ta juyo tana fadin ina ai matan naka sun gama abinci
wajensu ko ?
Sam baiji dadin zancen ba amma haka ya daure yace cikin bata fuska mama su ai
basu gaj gama abinci da wuri ba banma jin sun dora yanzu gaskiya.
Ikon Allah wanan waani irin sakacine da yaran nan miji da ake murnan zuwanshi
amma su sam ba hankalin gane haka ai wanan shine kishi na asali ba wanan haukan da
sukeyi ba.
Yanzu sai ka dawo kaci ke nan yace ko karyawa banyi ba mama saidai idan na fita
zan tsaya wani shago nan gaba kadan in karya.
Sam malam ba mutuncika bane kana da mata biyu ka koma cin abincin layi wanan
zubar da kimar namijine da matansa bari dai inzaka iya cin namu na zubo ma ka dan
hada da ruwa.
Murmushi ya sake a fuskansa daidai lokacin Habu zai shigo part din don shima
fita zaiyi to ga sadauki nan sai in diba maku kuci gaba dayan ku ta wuce zuwa
kitchen din kai tsaye.
Abunci ta zubo masu plate biyu shimkafa da miya da ganyen kabeji yaji hadi sosai
sai nama yanka bibiyu a cikin ko wani plate ta direwa kowa a gabansa.
Yaso ya basar amma aiya muda ya busar da iska yana fadin yaya naga plate biyu
mama matansa fa basu ciyar dashi bane halan ?
Yayi kamar baiji mai dan uwan nasa ke fadi ba sai wayan shi dayake faman dakila
cikin basarwa kafin ya aje yana jawo plate din abincin zuwa gabanshi.
Mama Dubu data dawo dauke da goran kunun ayya sai ledan pure water ta aje Habu
ya dago yana fadin is not right mama yana da mata a cikin gidan nan yazo nan kuma
yana ci muna abincin mu.
Murmushi mama din tayi kafin takai zaune tana fadin Habu dole ya kama in bashi
son da yafita yana tonawa kansa asiri yaje saye shago gara kawai in diba mashi yaci
a nan din.
Duk zancen da sukeyi Jafar sai aika abincinsa yake a cikinsa Abubakar din ya
dan kalleshi ya jawo plate dinsa shima ya soma ci kafin can ya dago yace.
Cikin gari kayi ina son nima zan fita ka saukeni saiga iya ta fito daga daki
tayi wanka ta sauya tufafi yadda takeyi idan mama tana gidan tare dasu ka,idace
wanka a rana gareta .
Habu ai gara ka bari yaci abincinsa a nan kada yunwa ya illantashi nima tsohuwa
ba iya cin abincin yaran nan nakeyi ba balleshi matashi haka da harshensa yake da
kaifi a yanzu.
Amma iya gaskiya ba zasuji dadi hakan ba idan sungani shiya kamata ya tsawata
masu koma meye su gyara amma haka gaskiya bai dace ba karshema zasu iya dora
laifinne ga mama.
Kamar yadda kace din ya kara tsawata masu dai hakan yana da kyau amma wa yan nan
shedanun ba kan gadone dasu ba balle su gyara din.
Tsuki Abubakar da takaici ya kumshi yaja goran kunnun ayya Jafar ya mika
hannunsa ya dauko ya kafa baki ya korawa cikinsa kaf ya aje yana gyara zama yace.
Ita Asmau ki barta da kazanta da saurin fushi yanzu haka dakinta wallahi iya
baya shakuwa don kazanta kayane ako ina watse a dakin kamar wata wace ta tara yara
goma.
Itako Nusaiba aikinma bata san kansa ba barta kawai da in za a fita sai kice
zakizo gidanta ki samu abin kwarai duk babu mai tsaba a cikinsu ga rashin kunya
kamar tashin tasha bakinta ko yaushe baya gajiya.
Nayi mamakin hada kawancesu da Asmau don ita ba yawan son maganane da ita ba
amma ta iya zama da ita haka da wanan rayuwan na banza.
Sam ban taba zaton haka rayuwanta yake ba harna yarda na fada tarkonta dariya
sosai Abubakar ya kwashe dashi jin abinda dan uwan nasa ya fada inda sabo ya saba
da halin Abubukar na kyata don a haka suka taso dashi.
Daga can kusurwan kitchen mama ke fadin ina aika diban ma matanka nasu tsaraban
ko kada azo a kwshe a nan ?
Kafin yai magana Iya tace zai shigo dashi baikai masu nasu bane ai baya kawo nan
baki daya yakan fitar masu da nasu tuncan hakan yasa taci gaba da fitarwa kawu
dauda da abokan zamanta indai ankai can su raba a tsakaninsu .
Saida ya mike yake fadin gari iya na sawowa shi don kune masu son jan garin kwaki
da manja aina gani malam saida nayi tunanen hakan Allah yayi albarka amma wanan ai
yayiwa Iya yawa bari a dibawa mutane suma susa albarka.
Baiyi magana ba don ko yayi tunda mama tayi niyar hakan saita diba din donshine
basu tsaya bata bakinsu ba ta fitar da wanda zaikai gidansu dana gidan kawu din
Abubakar ya tayashi kwasa zuwa cikon mota saida suka cika mota fam suka tafi.
Gidansu ya fara tsayawa aka sauke kayan zuwa cikin gida kafin su shiga don gaida
mutanen gidan shigansu Abubakar ya kalli part din mahaifiyarsu dan kwana biyun da
tayi wajen yai kura an rasa wanda zai share mata shi don mugun hali irin na dan
Adam.
Da ace mama mutuwa tayi ashe gidan ma ba zai basu sha,awan shigowa bake nan
kilama wanine zai gaje wajen ya zauna aci albarkacinsu.
A gurguje aka gaisa suna masu sannu da hanya tare da godiya kan tsaraban da aka
kawo din agaida mama da dai sauransu.
Basu tsaya ba sukai sallama suka fice daga gidan kai tsaye suna fita inna ta
kalli yar uwar zamanta tace mena fada maku yaya indai yayan Jushuce sai ta aiko
muna dako kwarane a gidan nan yanzu ji wanan kaya don Allah haka.
Tsuki mama taja tana fadin meye a cikin ledojin nan sabira bude muga abinda ke
ciki inda kowa na gidan ya fito ya tsaya ganin abin arzikin da aka shigo dashi din
don basu yarda a shiga ciki dashi don gudun rage masu kwantiti dinsa da suka san za
a iya hakan don an sabayi masu hakan kuma ba daman suyi magana a kai.
Mama duba wanan abin ta fada bayan ta bude ledan inna takai ido ta kalla tace
nasan wanan sai yayan jushu ita kadai takai can a gidan nan.
Kaico waike karima baki kishin kankine wanan katobara haka da nuna zalama a filin
Allah kamar wata mayunwaciya dake ?
Nidana nuna a fili za,acewa hakan ba amma kowa anan ai yana so don ban taba
ganin wanda akabawa ya marya ba a cikin mu.
Nidai don Allah ku bari sabira ta fada cikin dan hasala ga iyayyen nata dake son
nuna halinsu fadane akulum sai anyisa kuma a shirya haka ake zaune a gidan
tsakaninsu.
Mama Dubuce yana da wuya kaji harshenta a cikinsu tunko mijin nasu yana a raye
kafin ya kwanta dama haka halinta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login