Showing 222001 words to 225000 words out of 328222 words

Chapter 75 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

a cikin lokaci dole ta tashi ta dafa masu din kamar yadda yace din.
Ta kuma kawo bai kyaleta ba nan ya hau fada yana fadin zaman me sukeyi a gida
haka tsawon lokacin basuyi aure ba sai shiga maganan manya da takeyi tana hada
mutane fada.
Hakan yasa zuwansa yai min dadi don kwana biyu bakijin motsin yar iska don kamar
bata gidan ma zakice saboda ta natsu sosai a yanzu saina gane ba shiri a tsakaninsu
kenan ashe ?
Ranan dayayi wani shigo ya samu ina gyaran part din nagaidashi da wuni nacigaba
da aikina ina jin yana tambayan mama wai ni kadaice ke jinyar dan uwansu.
Mama ta nisa tana fadin kaidai fadi dan nan aini abin yafi karfin ganina yanzu
nan dai ta zauna tana koro mashi labarin abubuwa da suka faru da farko.
Sai kada kai yake faman yi yana acting a cikin mama kafin ya dan gyara zama yana
fadi yanzu da wanan halin yake zaune dasu mama ?
Tayi dan murmushi tana fadin to yaya zaiyi Yazid tunda mamanku tana hanashi
daukan mataki yayi wani shu,umin murmushi ya gyara zamanshi yana fadin.
Wanan Asmau tafi ban mamaki har da ita cikin wanan shirmen waiko tsoron kawar
nata take ji da har ta yarda ta aure mata miji ?
To za,ace dama dai ita din za ace tunda yanzu bata yarda da iskancin wanan dayan
da suka hada kai da saratu suke iskanci ni in anbarni sai ince duk asiri tayi masu
da basu ganin laifinta.
Na rasa me Jafar ya gani a jikin yarinyar nan tun farko daya leke mata a lokacin
sam zuciyana bai yarda da wanan yarinyar ba dama.
Shigowan iya tare da matan kawu part din ya katse masu hiransu dashi sun gaisa
da mama yana zaune ko kallonsu baiyi ba sai mama hafsatuce cikin karfin hali take
fadin sannu yazidu anzo lafiya kwanaki munzo gaisheku da zuwa bamu sameku ba ance
kunje bauchi kaida habu ?
Ehh ai gara da baku sameni ba ko yanzun ma ba zaki taba samuna ba kiyo sabon
shirinkine kikazo kaina kuma ?
Basu mama ba harni dake shirin shigewa daki saidana juyo ina dubansa cikin
dakewa ya mike tsaye yana fadin banga dalilin da zaku bar mai mugun nufi tana
shigowa nan ba asalima gidan nan gaba daya ya kamata matar nan ta daina shigowa.
Wani tsawa mama dubu tayi mai tare da ambatab sunab shi tana fadin kai Yazid
kanka daya kuwa matar kawun naka kake fadawa wanan magana haka ?
Mama don tana matar kawuna ba zan fadi gaskiya a kanta ba matar dake da mugun
nufi akan mu kun sani kuma kuka barta tana shigo maku gida haka ?
Ko Allah yace mu nisanci makiyan mu idan mun gansu yasa kai ya fita sai hafsatun
ta fara salati tana kuka tana fadin .
Ni wanan yaron ya kira da muguwa me yake nufi nice na dorawa jafar wanan laluran
kome ?
Iya ta amsa da fadin ,Yanzu ai gashi can baiyi nisa ba sai kije ki tambayesa ai
hansatu mukan ina muka sani tunda bamu shiga zuciyarki mun gani ba ?
Ba a gane mugu a goshi amma ana gane gaskiyan kowa a fuska don kowa na nuna shi
nagarine ako wani lokaci kuka ta dan fara tana fadin .
Zargina akeyi kan Jafaru kome iya haba shiyasa ashe duk nazo gaidashi sai a nuna
min ba zan samu ganinsa ba ko ace min yana barci ko kuma ana mashi wani abu ashe
ana zarginane da maita ?
A,a haaa mukan bamu kiraki da manya ba amma koma meye kin sani ai koda yake shi
maita bawai saika kama kurwa bane kake maye ko mugunta ai maitane shima.
Da kyat mama ta samu hafsatun ta fita daga part din banyan mama tayi ta bata
baki tana tausanta akan koma meye ba yadda take nufi suke nufi da itaba dole
akwaidai abinda.
Mama dubu dai tana zaune ta kasa cewa komai akan hakan nima ina tsaye daga kofa
nakasa shiga dakin da zanyi a lokacin sai bayan fitansune mama din ta mike ta bisu.
Iya ke fadin haka kawai yaron nan yayi min daidai daya fito mata fili da mugun
nufinta ta dauka ba asan me take ciki bane ta kwaso kafa don bata da kunya zuwa
munafunci.
Wai iya hafsatun ta hurhurane yanzu maman tudu ke tambayan iya din cikin bacin
rai iyan ke fadi ko maita take ai ba a mussu tunda kwadayi kekai mutane ga halaka
yanzu.
Hakanane fa idan kafaye saka abin duniya a rai sai ka tsunci kanka ga mahalaka
yanzu mutane da yawa haka ke faruwa dasu ai mama ta fada ta kare da Allah ya kyauta
.
Ni dama naso nace bafa kowa ya kamata yana shigowa part din nan ban ganin yaron
nan tunda muna ganin sauki a cikin lamarin nan.
Yakama ace saina gida sosai zai dinga ganinsa a yanzu mutane basu da kyau kana
tufkane ana maka walwala don haka kada kuga laifina a yanzu matakin da zan dauka
don shigowa wajensa inma son samune zan daukeshi zuwa wanan dakin da matarshi ke
kwana ya koma can din sai wanda aka yarda dashine kadai zai shiga wajensa.
Barin shi falon nan hankalina ya daga sosai ina take tazo ta gyara dakin a mayar
dashi cikibinyaso mu muyi amfani da dayan dakin shike nan aga abinda Allah zaiyi
kuma.
Tun wanan ranan aka dauke yaya a falon zuwa dakin wanda hakan yayi min dadi
sosai don Allah ya gani zamanshi a falo sam bai min ba dama don ba dama nayi masa
wani abin idon tsofin yana kanmu saidai yayi ta faman bin na da kallo duk inda na
gilma da idanu.
Haka kuma duk wanda yazo iyakansa falo yanzu ba kowane suke yarda ya shiga
wajensa ba sai su shakikyansa kadai sukan shiga su jima a ciki wani lokacin tare
dashi ni kuma in samu barci koyin wani abin.
Na samu daman zama dashi a yanzu nayi maganan da zan mai duk daba amsa min yake
iya yiba haka dai zai kafeni da idanuwansa .
Bani kadai ba dukkan mu matanshi muna shiga gunshi mu kebe dashi na dan wani
lokaci za,a zauna nan tare dashi koda barci yakeyi saina fahinci wanan tsarin na
mama bani kadai yaiwa dadi ba ashe yanzu.
Abin dana fara kula wata rana ina zaune da dare bayan nagama shafa mashi magani
zamu kwanta sai kawai tunane ya dibeni sai kuka na fada jikinsa in kuka a hankali
kamar a mafalki naji hannunsa na kadawa a hankali yana dagasu zuwa kaina.
Innalillahi na samu ambata tare da katse kukan da nakeyi ina binsa da kallo amma
ya kasa abinda yake son yi din don hannun nasa ya kasa daguwa yadda yaso din.
Naja bakina nayi shiru daidai a yanzu nakan kama yatsunsa din ina masa massage
dinsa har dana kafafu da duk inda jijiyansa suke kafin mu kwanta .
Cikin irin haka ranan banyi aune ba su mama tare dasu yaya Habu da sukai tafiya
suka shigo suka sameni ina masa hakan.
Muryan Yazid ne ke fadin gaskiya wanan kina da fasaha sosai nayi wanan tunanen
ince ko za a dinga dan masa hakan sai gashi ashe kina masa hakan zai taimaka sosai
wajen karfin jikin insha Allah.
Ni dai ganin sun shigo yasa na daina na sakeshi na koma gefe na rakube can dai
na mike na dawo falo na samu iya zaune ta idar da sallah muka dan fara hira jefi
jefi.
Hiran dai bai wuce akan jikan nata ba take tambayana ko biba ta kara shigowa nan
nace ninace ta daina zuwa don ranan da sukazo kuka tayi sosai har saida ta kwanta
ciwo hakama yar uwarta da sukazo tare wai iskanta ya tashi itama da suka koma
gidana a ranan .
Ba kaji ba iya ta fada ai duk wanda keda iska yaga jafaru yasan da iska aka
hadashi bashi kadai bane don irin yanayin da yake ciki duk mai hankali zai gane
hakan.
So sukayi suyi mai farat daya Allah bai yarda ba shine suke wahalal dashi haka
insha Allahu Allah yafisu yafi sherinsu ai kinga har yau kawun ku ya kasa zuwa
gidan nan .
Da yasan ba komai aida tuni yazo gidan nan da fada tun ranan yace anwa yar gwal
dinsa kazafi yaciwa mutane mutunci haka itama kinga ba wani mataki aida ta dauka ga
abinda yaron nan Yazidu yai mata.
Nan suka fito suka samemu muna maganan mun dan jima suna zancen kafin su fita
muka rufe part din namu yaya ibrahim shike kwana a falo yanzu.
Mu kuma muna daga ciki sai daga baya bayan yan gidan su Saiba sun kara zuwa
dubanshi sai ga zance ya tashi saiba din taje wajen mama wai suna son a basu
hakkinsu suma su dinga kwana dashi kamar yadda nakeyi.
Mama dubu din tazowa su mama da iya da zancen iya ranan tayi fada sosai take
fadin na kula dubu kema ba lafiyan yaron nan kike soba ?
To anki a raba kwanan su mayar muna da jinya baya muna ganin sauki suja muna
hasara ba za a yi hakan ba data zauna dashi a baya wata uwar take tsinana masa a
lokacin banda sharan barcin ta da takeyi a nan saman dogon kujera.
Dole dai akaci gaba da hakan don dai kada tsegumin yayi yawa na fara komawa
gida ko gidan yar uwata in zauna sai dare zan dawo gidan.
Ma,ana dai su, su wuni dashi da rana ni kuma in kwana dashi da dare saiya
kasance wahala da dawainiya ya fara komawa kan tsofin don su zasuyi ta fama dashi
hakana har zuwa lokacin dana dawo.
Suko matansa excuse din girki ko kula da yara suke bayarwa abindai ba dadi
wallahi don gaskiya bai cancanci haka a garesu ba za ace dai ina fadane kawai don
in yaba kaina in bata su gaskiyan zancen ke nan nake fada a yanzu.
Burin su a fili yake shine yaya zai mutu su kuma suci gadonshi don takan ce kura
da shan bugu gardi da kwatan,kudi.
Gara dasu dai kome za ace ace su dai keda riba tunda su suka haifa sune kuma
keda Jafar aje ayi ta aikin wahala din don neman yabo .
Alkawari nayi insha Allahu ba zan kara biyewa shirmensu ba idan sunayi ko da
dangwarana mace zatayi matukar muna cikin wanan halin na rashin lafiyan mijin mu.
Gata da wani hali kamar tashin kauye da yawan habaici da sake magana kowa tana
iya yiwa hakan abindana fahinta ke nan yasa naba banza ajiyanta yanzu.
Ni kadai zan iya cewa ga cigaban da aka samu yanzu kan matsalan nashi saidai ban
fadawa kowa hakan ba har maman tudu dake kula dashi din.
Don ita mama dubu iyakarta ta shigo ta dubashi inda wani shawaran da zasuyi kuma
zasu zauna suyi a kan matsalan iyakartavke nan tunda mama ta nuna ita din uwace
gareshi.
Ankai yanzu yana dan iya daga hannu tun iya iya motsawa har yakai ya fara dagasu
yana dan juyawa saidai ba bakin magana gareshi har lokacin.
Anty Salima ko nafisa sai idan sunzo gidan zakiji bakina ko in muna tare da iya
wani lokacin tare da salima din mukan fita muje can gidan mu wuni.
Ranan ma mun shirya din zamu fita don na kwana biyu ban leka gidan ba yasa
nacewa mama din zanje in gyara gidan tace ya kamata shine muka shirya zamu tafi
din.
Suna falo zaune a lokacin dana fito duk daba wani shigar azo a ganine a jikina
ba amma ta dago kai ta kalleni ta kawar da kan nata gefe daya.
Tsanar da tayi min take jin yana karuwa a zuciyarta duk zata kalleni takan ji
kamar ta daina ganina har abada a duniyan nan don bata kaunan ta bude ido dai ta
ganni saboda haushin da takeji nawa din kishi ke nan.
Nima dai din ina jin haushin ta saidai baikai nata ba don ma taki zaman lafiya
danine ya kawo hakan da zan iya rufe ido in kawar da duk wani kishinta da nake ji a
raina.
Kishi mukayi da itakata kwashe ranan ta zauna ta kwashe min kaina da tsiya da
komai haka na zauna tayi min kitson a kaina sai kusan goma muka dawo gida.
Tunda muka shigo da sallama naga irin kallon da mama tayi min nasha jinin jikina
tana zaune tana cin abinci muka gaidasu nake tambayan iya tace tana ciki.
Na mike zan shiga naji ta kirani tana fadin Rahama ina kuka shiga haka dan Allah
keda kike da mara lafiya ki bar gida don gudun bacin ran wasu ba zaki dawo gida da
wuri kiga halin da mijinki yake ciki ba ?
Yau jikin nasa da zazzabi ya wuni saida likitanshi yazo yai mashi allura ya samu
dan barci yayi amai yakai sau uku gashi kin barmu da tabararrun nan a gida sai
shirme suke muna sin kasa anyana komai akansa.
Da sauri na fada dakin ban tsaya jin karasan zancen ta ba yana kwance yana barci
nagaida iya ina karasawa wajensa na dan dafa wuyanshi da hannuna.
Zubur ya bude idonsa ya sauke min yana kallona sai kuma ya mayar da idanun nasa
ya lumshe a hankali sannu nayi mai na zauna a kusa dashi hakan baisa ya bude idon
ba.
Sai lokacin muka gaisa da iya dake zaune a kasa tana lazumi take fadin yau
jikin nasa ya tabu bayan fitan ki masassara ya kamashi.
A hankali nace haka mama ta fada min yanzu amma da sauki ki daina wanan fitan
don kawai kina gudun zargi ko wani abu yau ai uwarsa taga amfanin ki don kwasan
amaima jidali ya zamawa wavyancan balle kula dashi din kinga ai tun kafin magariba
da suka gudu basu leko ba .
Duk yadda kikayifa sai an zageki wasu kuma su yabaki ki daure kici jerabawan duk
nan mun san dalilin dake saka kina wanan fita din hakan kuma ba wankeki zaiyi daga
zargin kishiya ba tunda anki mata yadda take so.
Na dan waigeshi yaban tausayi matuka na mike na kwabe kayan jikina dakin da
akace yayi ta aman nashiga gyara na tsabtace shi na saka kamshi.
Har ban dakin saidana gyaro na koma dayan dakin da suke amfani shima na gyaro
masushi likitan ya dawo tare da Yazid sun kara dubashi sai lokacin nasan ya daao
garin .
Sun dan jima suka fito na samu nashiga wanka na fito na zauna na dan gyara
jikina na saka rigan barcina falo na fito na hada mai shayi mai kauri koma dakin.
Cikin dabara na samu na tayar dashi na bashi yasha saidai na kula kamar yana
fushi ko kuma yanayin ciwone hakana yake damunsa oho ?
Saida kafa ya dauke na rufe part din don mama ta fada min ya Ibrahim bai nan
yaje Abuja da safe cab zai kwana kuma.
Na jima zaune bayan na fafa mashi magani ina mashi addua nakan koma saman
kujera in kwanta amma haka kawai nace na kwanta a kusa dashi ranan don yanayin da
yake ciki din.
Nakai kamar minti goma da kwanciya a gefesa kamar a mafalki naji saukan
hannunsa saman jikina saida na dan zabura nayi mamakin jin ya rikeni a ranan.
Cikin fargaba nake fadin yaya kaine kuwa ba bakin magana kai kawai ya daga min
bai iya ban amsa ba hamdala nayi a zuciyana jin yadda hannunsa ke motsi a jikina
din.
Sannu a hankali naji abin yana rikida zuwa wani yanayi don ya wuce tsamanina a
hankali na runtse idanuwana acikin fargaban abinda zai iya faruwa a lokacin.
Ba lakka bane a jikinsa ko wani kuzari don haka na kyashi yana abinda yake
tsamani zai iya a lokacin amma ya kasa sai ajiyan zuciya zuwa can kuma bayan mun
rugume junane naji saukan hawayenshi a saman jikina.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

7️⃣1️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Kusan hakan yake faruwa a tsakanin mu tsawon wata daya saidai na kasa fadawa kowa
wanan maganan.
Wa zan tunkara da wanan zancen nace ga abindake wakana a tsakanina da mijina
alhalin yana kwance haka sharkaf dashi bai ko wani dogon motsi balle magana.
Har abin yakai ya fara damuna da zaran dare yayi banda katabus dashi ya dinga
bina da ido kenan harsai yaji mun hada jiki dashi a sannan zai dinga jero ajiyan
zuciya yana saukewa a fili.
Dole zan biye mashi da abinda yake so na fannin wasannin aurataiya a tsakanin mu
har zuwa lokacin da naga ya samu gamsuwa na jaye jikina daga nasa in koma gefe ina
hawaye a cikin kunci.
Ganin dai a kwai sauki sosai dake shigansa na gane hakan kuma nadaga cikin
karuwan samun kuzarinsa a lokacin don yakanyi barci a daren da duk hakan ya kasance
a tsakanin mu sosai.
Washe gari nakan kula da fara,a a fuskanshi da walwala idan anyi magana zakiga
yana dan murmushi a gefen fuskanshi sai gashi kwatsam naji suna zancen cewa zasu
fita dashi kasan wajen.
Nafi kowa sani a yanzu ciwon yaya bana asibiti bane ciwone dake da alaka da
jinnu ko sihiri da akewa mutum wani lokaci.
Ranan babu kowa nake fadin mama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login