Showing 33001 words to 36000 words out of 328222 words

Chapter 12 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

matukar tashi amma kawu ya kwantar mata da hankalin hakan ba
komai bane ai suka bar zancen.
Kawu bai kaunar komai za a fada kada wata mace daga cikin sarakansu taji zai
kasance abin sirine da iyasune zasu iya jin matsalan a tsakaninsu yasa ya hana
zancen gaban yar uwata.
Shima a tsorace yake da abinda malamin ya nuna don baisan abinda ke shirin
faruwa da diyan yar uwar tashi ba lokacin da sunanansu ya fito a zancen malamin .
Don shine bai tsaya yayi bin kwakwafi ba a lokacin kan zancen don Yanda dake kusa
ga yanda din bata cikin kwanciyan hankali kan matsalanta.
A gida kuma bin kwakwafin tambaya suke min don saiba taga fitan su iya gidan da
yayata saidai bata san inda suka dosa ba da ita hakan yasa tazo tana fadawa
kishiryarta .
Wace yau ayi fari gobe zama duk da shirin bai wuce na yan mintuna ayi fada a
shirya don dokan da mijin nasu ya saka akan duk wace ke ja mashi matsala zai rabu
da ita a cikinsu.
Asmau ce take bugun cikina taji inda suka tafi na nuna mata bansan fitansu ba ai
ina daki suka fita hakan yasa ta kyaleni da zancen.
Sun kai wani lokaci kafinsu dawo gidan ina part din antyna na kara gyara ko ina
dan shigowan da akayi din yasa na kara tsabtace wajen tas.
Har cikin falon iya ta rakota tana mata sannu kafin iya din dan matsa kusa ds
ita tana fadin ki kula kada kowa a gidan nan yasan halin da kike ciki ki kumayi
yadda aka ce kiyi din .
Ta amsa a galabaice ta samu waje ta kwanta abincima sai da kyat na samu taci
saboda damuwa da take ciki a lokacin hakan dana ganta cikine ya dan daga min
hankali sosai ban dai nuna a fili ba.
A cikin dare mijinta ya shigo gari daga misalin karfe tara saura muna falo zaune
ya shigo horn din motarshi taji take fadin yaya Habu.
Na dago na dan kalleta a inda take zaune naci gaba da kallo tunda batayi magana
ba nayi mamaki sosai daya tabbata shi dine ya dawo a lokacin.
Banyi shishigin tashi ba na dai gaidashi da dawowa na nufi kitchen na dauko mai
goran ruwa kodana kawo na sameshi ya rankwafo saman kanta yana magana da ita na aje
ruwan da sauri tare da nufar daki.
Don kada insha hakkinsu a yadda na gansu din ba don niba a lokacin tugimar
matarshi zaiyi a jikinshi kayana duba na dauki abinda zan dauka zuwa part din iya.
Na fito na barsu nan a falon bayan fitana kuwa abinda danake zargi ya faru don
rugumeta yayi a jikinshi yana fadin Maria hope ba abinda ya taba lafiyan ki dai
yanzu ?
Tayi na rai narai da idanu tana fadin ba komai ya Habu saidai yawan mafalkin da
nakeyi shine ke daga min hankali sosai.
Kara jawota yayi zuwa jikinsa yana shafan kanta yake fadin ba abinda zai faru
dake wanan karon da yardan ubangiji Allah ya fishi yafi mugun nufinsa akanmu insha
Allah.
Nan ya zauna tana masa bayanin irin yadda take wahala sosai a cikin mafalkin
haka kuma yayi ta kwantar mata da hankali yana karfafa mata zuciya akan ta yarda ba
wani mahaluki da ya isa yaiwa dan uwansa mutum wani abu sai Allah.
Su anty Sare na samu a falon suna kallo na shigo sai lokacin suka sanda dan
uwansu ya dawo gari ban tsaya falo kallo ba na nufi daki don in gyara inda zan
kwanta a lokacin.
Nasan ba lalai bane in samu dakin yadda nake so Allah yayimu fulani da tsanda da
tsabta don akwaimu da tsabta sosai nima din haka na kasance a cikinsu lokacin.
Banji motsin mama ba har na kammala gyaran dakin na sake fitowa falo na zauna
ina tambayan mama nan suke fada min aita koma gida tunda akai magariba.
Mun dan taba kallo muna hira jefi jefi dasu a wajen nakoma daki na kwanta tare da
tunanen halinda yar uwata take ciki a lokacin.
Don nasan baffa mugun mutumne baida imani ko kadan a rayuwansa tunda kuma tace
tana ganinsa ko wani lokaci a mafalkinta dole akwai wani mugun abinda yake
aiwatarwa akan mu lokacin.
Amma yar uwata mai tayi mashi da mahaifinmu yake fadanshi tsakaninsu don me zai
taba min yar uwa kuma a yanzu wani irin tsanar baffa naji kasan zuciyana irin da
ban taba masa ba sai a ranan duk ko da wahalan da mugasha a hannunsa ?
Haka barci ya daukeni washegari dana falka banyi sanyin jiki ba wajen gyara ko
ina dana saba gyara kafin na shiga nayi wanka na gyara jikina.
A yanzu ban damu da yin abin karyawa ba a part din iya kamar yadda nakan yiwa
iya idan muna mu kadai daga sai ita don ganin masu part din sun dawo hutu a
lokacin.
Don haka yasa na koma na kwanta bayan nayi wanka na gyara jikina tsab sai barci
ya dan daukeni ban sani ba.
A cikin dan barcin dana dan samu nayi wani irin mugun mafalki daya firgitani na
tashi ina zufa ina bin dakin da kallo.
Muryan iya na tsinkayo a falon naji tana fada da yan matanta kan basu fito
sunyi mata abin karyawa ba har rana wanan lokacin haka ?
Mikewa nayi a cikin sanyi jiki na fito falon na samesu fada tsohuwar keyi sosai
dasu suna zaune suna kallo an rasa mai motsawa a cikinsu ta shiga kitchen din a
lokacin.
Nima ban shiga ba na samu waje na zauna ina gaida ita da kwana ta amsa take
fadin .
Ke dai yar nan kedai sannu da kokari kinfi min mutanen banzan nan da basu san
ciwon kansu ba gidan nan suna koyi da halin wa yan can shashashun matan dan uwan
nasu.
Inda mace zatayi kwance cikin lalaci da kiuya ba zata zage ta tsinanawa kanta
komai a rayuwanta wai a haka kuma mace zatace aure takeyi don lalaci ?
Da kece iyanzu nakai ga abin karyawa a gidan nan amma su wai yanzune zasu dora
min abin kari da rana tsaka kiri kiri haka ?
Sallaman ya Habu ya katseta take fadin kai kuma yaushe kadawo garin tana mashi
kallon mamaki ?
Saida ya karasa shigowa falon yace tun jiya da dare mana nasan kinyi barci a
lokacin yasa ban shigo nan ba ai.
Antyna ce tashigo a bayanshi tana dauke da kayan karya kumallo data hada a
hannunta tana gaida iya da kwana sai binta takeyi da kallo cikin mamaki.
Yar nan har kinyi karfin halin tashi shiga madafi yin giki a yadda kike din nan
hankalina ya daga matuka da zancen yarinyar nan jiya .
Abin tausayi wai ace kuma yar nan mai hankali har akwai wanda ta tarewa wani
abu a duniyan nan yake binta da sheri.
Wai, nakane yau yake kokarin illanta ka haka don bakin ciki an daiyi mutum banza
a wajen nan wallahi wanan mutumin da zan gashi saina tsine masa albarka.
Kina zaginsa mugune fa iya kada yazo ya waiwaiyeki habu ya fada yana zama a
saman kujera sai naji iyan tace meye hadinshi dani kuma da zai dawo kaina ?
Wayace ki zageshi yanzu yana iya jinki ai koba haka aka fada maku ba a can inda
kuka je jiyan ba zaginsa nayi ba habu halinsa na fada ai yanzu .
Muryan Yanda cetace Iya ki kyaleshi ga abin karyawa na kawo maki ta fada tana
aje bowl din data riko a hannunta ta samu waje itama ta zauna a kusa dashi ta fara
gaida iya dake fadin Allah yai maki albarka yar nan kinji.
Yanzu nake sababi da yaran nan suna daki sun mimike kafa wai sai yanzu zasu dora
muna girki ta fada tana kiciniyar budan kwanan gabanta din.
Nan Sare ta taso tana dariya ta karbe kwanon tana budewa iya ta soma fadin
kingani ba, ki duba ba kunyane dasu ba ai, ace mace na kwance wai tana barcin safe
a daidai lokacin daya dace mace ta mike ta dorawa mijinta da yara girki safe.
Idan baku koya a yanzu ba sai yaushe zaku iya hakan don Allah, irin wanan
lalacin shike wahal da matan shiyan can da yayanku yatara.
Idan baka koya a gida sai bayan kayi aure kace zaka koyi abu yanzu don basu koya
a lokacin daya dace ace sun koyi hakan ba yaushe zasu iyashi yanzu.
Dankalin turawane da kwai shake a cikin kulan da Sare ta bude din take fadin
nasan dai wanan har damune aka zuboshi.
Nasan baza a rasa ruwan zafin da za a hada shayi a nan ba ai shiyasa ban dauko ba
maria din ta fada tana kallon Sare.
Hakan yasa na fahinci ta zubawa kowane harni mu karya a nan din mikewa nayi na
dauko plates s kitchen na fito dashi na zama nayi na fara dibarwa iya dana fahinci
tsohuwar tana jin yunwa a lokacin don fadan da takeyi.
Na zuzuba masu a cikin plate na mikawa kowa nasa lokacin naji ya Habu ya soma
magana yana fadin Iya zankai Maria asibiti a dubata ?
Wani abin kuma ya samu maria din iya ta fada tana duban yar uwar tawa yace a,a
iya zandai kaita a dubatane ko da abinda zasu iya bata asibitin ?
Wani kallo tayi mai tana hade dankalin data tura bakinta dakyat tace Habu kana
haukane da zaka dauki matarka dake fama da laluran jinnu zuwa asibiti ?
Jinnu kuma iya ya fada yana kallon tsohuwar yayinda yar,uwata ta dukar da kanta
kasa cikin sanyi jiki nabita da kallo cikin mamaki jin abinda tsohuwar ta fada.
Kaga mubar zancen nan yanzu ka bari uwarku nasan tana nan tafe gidan nan taje
ta shirya wajentane ta dawo yau din nan don ta fito jiya bada shiri ba yasa ta koma
gidan.
Sun dan jima a part din kafin su fita nabi yar uwata da kallon tausayi don na
fahinci me iya ke nufi da zancen ta saboda matar baffa dake fama da matsalan jinnu
idan tafara lalura saita ba mutum tausayi.
A yadda naji yan rugga suna fadi lokacin wai saboda matsalanta baffa ya aurota
don ta rasa manemi baffa yace shi zai iya yanzu har ta haifi yaya uku da baffa
lokacin da muke rugga din tare dasu.
Tuna hakan yasa hankalina ya daga sosai a lokacin gashi mijinta yana gari bamu
samu kebewa da ita ba tun safe saboda mijinta dake gari.
Misalin shabiyu saura mama ta iso da alama zata kwana biyu a gidan don bata saba
zuwa da kaya haka masu yawa ba idan zatazo.
Balle a yanzu din da taga inawa mahaifiyarta komai mama din ta rage zuwa sosai
kamar yadda takeyi a baya zatazo tayi sati biyu ko wata kafin ta kwasa ta koma gida
kuma a yanzu saidai tayi kwana biyu ko ukku ta koma.
Munyi mata sannu da zuwa nice na dauko ruwa na kawo mata tana zaune iya tana
bata labarin yayan matan mama din yadda suka kwasa dasu da safe.
Daki na koma tunda na fahinci kamar suna boye muna halinda ake ciki yasa na
nuna ban damu da insani ba nima saidai a zuciyana zancen jinnun da iya ta ambata
yana daga min hankali.
Yar uwata da take kamar uwa a wajena tun tasowan mu da ita na bude ido yau naga
tana son shiga halin rayuwa duk da ta girme min nisa ba kusa ba amma tare muke
komai da ita ko yaushe muna tare muna gudanar da rayuwan mu.
A bakin iya nake jin cewa wai ashe sun fita asibiti a ranan duk data gargadesu da
zuwa asibitin fadan da takeyi da yaya Habu din a lokacin ya tayar dani daga dan
barcin dana samu a lokacin.
Kiran sunana da ya habu din yayi yasani fitowa ina amsawa yake fadin naje Yanda
din tana nemana a part dinsu.
A kwance na sameta falo da alama sosai tana jin jiki don yanayinta daya nuna
hakan sosai a lokacin gaida ita nayi take fadin in gyara part din in dora masu
abinci .
Cikin dan lokaci kankani nayi duk wani abinda ta umurceni da yi a lokacin na
jera masu abincin dana samu taci sosai saida mijin ya shigo wanda kallo daya zakai
mashi kasan yana cikin wani yanayi na bacin rai.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC


MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

1️⃣3️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Sosai mama Dubu ta bada lokacinta tana kula da yayata haka kuma taja min kunne nasa
ido kan yar uwata sosai ga duk abinda zataci ko zatayi a gidan.
Hakan kuma nake wanan kokarin duk da a lokacin akwai sauran kurciya sosai a
kaina amma ban fita saina tabbatar da nayi komai daya dace a gidan.
Dana dawo kuma zan shiga in mata abinci da gyaran waje saidai indan mijinta yana
gari dan yanzu bai faye dogon tafiya ba sosai.
Koya tafi baifi yai yan kwanaki ba ya dawo saboda laluran matashi a yanzu duk da
abin baikai daga hankalin da kowa zai fahinci akwai matsala ba gareta.
Bayan kamar wasu yan satutuka ya Jafar daya je kasan waje kamar yadda nakeji a
bakin matanshi da yan uwansa ya dawo kasan.
Ranan Anty Saiba ta sauke jin kanta ta samemu a part din Iya zaune muna kallo
take fadin Sare zuwa nayi don Allah muje wajen mu ku tayamu aiki.
Anty Sare na mata ba,a da cewa lalaima ba dole ba maigida zai dawo ana mashi
soye suka dan taba ba,a zata tafi har ta juya sai kuma ta tsaya tana fadin .
Ramaah har kefa zamuje don aikin yayi muna yawa sosai gashi rana yayi komai bamu
hada ba yasa nake son don Allah kuzo ku tayamu.
Mama dubu ta kalli inda nake zaune tana fadin Ramaah ai bata da matsala ga dai
mashiririta nan su da kika fara gaiyata ba komai zasuyi ba banda surutu.
Saida naje wajen antyna na gyara don mijinta yana iya fadowa ko wani lokaci
gidan yasa koda yaushe cikin tsabtace mata wajenta nake zakice ba wani mahalukin
dake rayuwa a part din don yadda yake kal ko dayaushe.
Nayi mamakin yadda na samu wajen nasu don na kwana biyu banshiga ba saboda exam
din da mukeyi banda lokacin laka part dinsu a yanzu .
Haka kuma iya ta hana wanan aikin da Asmau ke fakewa tana sakani a baya yanzu iya
tayi mata gatse da hakan yasa na samu ta shafa min lafiya.
Don wai ashe shigan cikine da ita lokacin yasa take narkewa haka bata iya yiwa
kanta komai a rayuwanta nayi mamakin yadda mata biyu zasu kasa gyaran wanan
katafaren ginan nasu .
Su biyu sai yan yaran su amma part din har wani bashi yakeyi da tsamin dauda
tunda daminane a lokacin aka shiga.
Kitchen na samesu tsaye suna shawaran abinda zasuyi din ga dai kaya abincin nan
amma da yawa sun lalace saboda rashin amfani dasu da ba ayi sun lalace.
Wanan bashin kuma wai daga fridge dinsune wari ke fita haka da ace nice zan
kwashe kayan nan kaf in kyautar dashine in wanke fridge din insaka kamshi ko wani
yaro ba zanso yaji wanan warin da fridge din nan keyi ba balle babba.
Saidai kashh duk sherin da Sare ke zuba masu kwando kwando bai sa sun duba maike
wanan warin haka su fitar dashi ba karshe falo muka koma muka kara aikin ko a nan
ma warin bai barmu mun zauna da dadin rai ba.
A dakin Nusaiba maigidan zai sauka shine dalilin wanan shirin da mukeyi din inda
Asmau take dakinta tana shakar barcinta hankali kwance saida muka dawo falone
hayaniyar mu ya tayat da ita ta kuma dan jima bata leko falon ba a lokacin.
Saida ta bushi iskanta ta fito sabe da yarta a kafada da dan cikinta daya tasa
kadan tana fadin duk aiki ake sha hakane ?
Banza kowa yayi da ita ta samu waje ta zaune don sun fahinci kishine ya hanata
fitowa a yadda na kula su anty Sare sunfi kula Saiba bisa ga Asmau wata kila don
kyautantane data dara Asmau din dashi ko kuma wani abu can dai na tunanensu.
Dukko da cin mutunci irin na Saiba da nuna ita watace kuma matan wani saidai
zasuyi fadan kiga sun dawo sun shirya kuma dasu nidai wanan abin yana daure min kai
dasu sosai wallahi.
Munyi cake dunut milk pop wanda a karshe aikin ya dawo nawa suka koma tayani
don da ban wajen shirme zasu tabka da hasara don basu iya kwabin bama balle .
Wasa wasa saida muka kai yamma don suyan kajin da muka tsaya yi wanda yayi ja
gwanin sha,awa dashi sai bayan magariba muka samu kan mu da aikin muka kammala .
Ni dai ina mamaki rashin ganin sun gyara falon gidan tsab da sauran part din
gidan kosu Sare banji suna masu tunin hakan ba a lokacin a kasan raina nake mamakin
hakan sosai a lokacin.
Wanka na shiga antyna tana falo zaune tana azzakar Saiban ta shigo part dinta
tana fadin ina Ramaah ga dan abin da mukayi na debo mata.
Tana wanka Anty maria ta fada ta aje saman table suka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login