Showing 54001 words to 57000 words out of 328222 words

Chapter 19 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

Nine ya kamata in dauki nauyin matana dana yar uwarta dake zama da ita gidan nan
ba J ba kowa yasan albatkacina sukazo gidan nan .
Kai Habu ka bari a fanci inda zancen nan ya dosa dan uwan ya taresa da fadin
hakan inda yaci gaba da fadin kowa dake wanan gidan har gidan kawu nauyin irin
hakan akaina ya rataya don hadin kan mu da kowa namu don me zasu so zarta hukuncin
dabani na tsarashi ba .
Yau yarinyar nan kamar kowa take a wajena tunda zamaka takeyi zaman mu kuma a
cikin gidan nan to ai yaya komai za a raba saidai na raba nawa biyun in bata haka
akeyi kulum a gidan nan salima ta sake fada.
Ke ina aka kai kayan yarinyar nan ya kallo Asmau yana tambayanta suna wajen mu
ta fada kai tsaye ki daukosu yanzun nan ya fada.
Kayan nan fa basu gidan nan nake gani Saare ta kara fada a bangareta sai iya
dake kallon mamaki take tambayan .
Nikan me yarinyar nan ta rageku dashine a gidan nan wai ?
Bakin ciki mana Iya amma in aikin karfine kowansu ya iya zuwa nan yace don Allah
Rahama kizo ki taimaka min da kaza amma ba a sonta da karuwa .
To wallahi kuji ni ban raba kan yayana ba a gidan nan ba macen da zata shigo
tace zata raba min kan gida haka yanzu wanan abin dame yayi kamane wai ?
Rikici sosai sukayi a kan kayan ni kan ban kulasu ba na gama miya na dora
shinkafa na shige dakin mu na kwanta don fada sosai ya J yayi ya kuma rantse idan
basu fito dashi ba duk kansu ukkun zasuji mamakin shi wallahi.
Bansan ya akayi ba sai ga kayan an fito dasu da yamma an kawo min mamace ta
kirani ta ban na karba nayi godiya saidai a kasan zuciyana na nasa cewa ko zan tafi
tsirara ba zan saka kayan ba don nima ta fulanin sun hau a lokacin.
Duk da karfi bai kai ba amma zuciyan gado yana nan a jinina aiki kuma idan ba na
cikin part din mu bane na dainashi daga wanan ranan .
Har washegarin da aka ban kayan raina ba dadi da safe na gama shiryawa nace da
salima zanje da kaina asibiti in duba yar uwata dama haka nake bayan kwana bibiyu
nake zuwa yanzu tunda aka soma azumi din nan.
Sam ban fadawa yar uwata komai ba game da abinda ya faru akaina gidan sun dai
tambayeni ba komai konace ba matsalan komai.
Na zauna a nan don na nasa irin zaman da zanyi ban bakin ciki da ko banda Saratu
da bansan abinda na tsare mata ba a rayuwata ?
Don haka nake bakin ciki da in girka taci a raina tunda nima yar adam ne kamar
kowa gara in fito masu a mutum don a zauna lafiya.
Kwatsam saiga anty salma daga Abuja ta bugo waya tana tambayan Yanda karfin
jikinta suka dan taba hira take tambayan ina gida ko tace ina kusa ta mika min
wayan .
Mun jima muna hira in tambayi wancan in tambayi wanan har take ce min nazo mata
sallah mana Abuja nace ba za a barni bane .
Tace waye zai hanaki zuwa wajen mu Ramaah ?
Nayi shiru take fadin naba Yanda waya sukai magana na daiji tana fadawa salma
din zata fadawa mijinta idan yashigo insha Allahu zanzo din .
Naji dadin hakan sosai yaushe rabona da Abuja koda Yanda taje da mijinta suka
kwana hudu acan da yai wani zuwa basuje dani ba rabona da mutunen arzikin mu nida
mahaifiyar mu tun rasuwan mahaifin mu da muka koma rugga da zama.
Saida akai Azahar na soma shirin komawa gida na tattara kayan dana kawo mata
abincin safe na fito babu abin hawa hakan yasa na soma shawaran takawa don komawa
gida.
Wani mai mota yazo ya tsaya ban kulashi ba yaja motarshi yayi gaba hakan yasa
na soma tafiya da kafa ga kuma kaya niki niki a hannuna dukka biyu.
Saida kyat na samu abin hawa nashiga ya kaini gida abin mamaki ashe mai motan nan
yana biye dani a baya zan bawa dan mashin kudinsa naji yana fadin malam ta barshi
kazo ka karba.
Na dago kai na dubeshi shine dai ya tsareni a bakin asibiti na dangwarawa
mutumin kudi na shige gida da sauri.
Gidan kaca kaca ga ganin idona kaina kawar na karasa na shiga falon da sallamata
suna zaune suka amsa min mama ke fadin yar halas yanzun nan nake zance ki fa a
raina.
Nadawo mama na tsaya rana yayi sanyi na dawo tace aikuwa yau ana kwada rana da
zafi a garin nan kayan nakai kitchen na aje kayan dana dawo dasu daga asibiti.
Kafin na juya zuwa dakin kwananu suna kwakwance suna barci adakin na tube kayan
jikina nashiga bayi na watsa ruwa na fito na samu waje nima na kwanta.
Sai barci ban tashi ba sai wajajen la,asar da karan wayan anty Salima ya tayar
dani alwala nayo na dawo nayi sallah ina idarwa na fita zuwa part din anty na na
gyaro don yaya Habu dake gari baya dawowa gida sai lokacin shan ruwa ko kuma idan
wani abin ya dawo dashi.
Kodana fito kitchen na samesu da mama din sai fada mama keyi tana fadin aiko
wani rai yana son hutu a cikinsa shike nan kun mayar da yarinya yar aikatau din ku
kowa ya mike kafa saidai ta girka kuci kuma babu kyautatawa.
Hakan da tayi yau yai min daidai wallahi aiko shige yanzu ba awa gorin uban don
da uban hanya a zamanin nan balle da gatanta mutuwa yasa kuka ganta nan tare da yar
uwanta.
Daga faloma iya na kada nata suna kurum nidai ban fito ba sai dana dan jima a
daki na fito na samesu wanke wanken kwanonin dana gani suna fara daurayewa mama din
na fadin ai in bari suyi meye amfaninsu suna mata dasu ?
Saare tayi girkin a ranan don ita salima tace a raba ai idan hakane nidai ina
wanke wanken ina jinsu har na gama na koma falo na zauna mirsisi da ido kuwa.
Duk da nasan sun fahinceni ko basu bahinta bama nima so nake su fahinceni din
zaifi sauki har aka kira sallah lokacin shan ruwa yayi bata karasa aikin ba.
Sai faman fada da ita mama keyi karshe ma tunda mukaje sallah ni dai ban fito ba
na zauna ina jiran ayi kiran isha,in inyi sallah in kwanta.
Tun a wanjen diban kunun tsamiya dana fito yi nasan akwai matsala ranan don
kawai shi nake soma sha na diba da kyat na sha rabin wanda na dibo din na mayar da
saura kitchen.
Na dawo na kwanta ke nan naji muryan su yaya sun shigo shan ruwa shi ya je duk
da maganan da akayi anan part din yake shan ruwa har yanzu.
Ita Saare din ta zubo masu abinci da kanta suna hira ya Habu ya fara kai cibi a
bakinsa ya kasa hade shinkafan.
Yayi shiru sai shi jafar dake magana da iya ya diba yakai shima a bakinsa
furzowa yayi da sauri yana fadin wayayi wanan girkin mama ?
Yana binsu da kallo suma duk kallo suka bishi dashi lokaci guda habu yace na
rigaka ji shiru nayi kawai mama ta nuna saare tana fadin gata nan ita tayisa.
To me girkin nawa yayi kuma tana turo baki zo nan kici kiji abinda yayi jafar
din ya fada a hasale yana fadin shame of you Saratu.
Badai wanan abincin aka kai masu asibiti ba ya habu tambaya yana kallon mama din
a sanyaye mama ke fadin shine mana nina san tsiyan data kwabawa mutane ke nan ?
Ba maggi ba gishiri komai babu a miyan nan fa mama da sauri mama din ta kallota
tace na matane kila ban zuba ba.
Rufe min baki sakariyan banza kamarki saratu zaki kasa dan wanan girkin da baida
yawa ina ga mai yawa ke nan ?
Ina wanan yarinyar ne yau da aka bari tayi wanan shirmen a hasale mama din ta
juyo tana fadin yarinya kan aiba boyansu bace ko ?
Da zata zaman girkawa suna ci kullum yau itama ta hutar da kantane su dandana
suji wai shine wanan sakariyar ta kwaba muna abinci haka ?
Tsam Habu ya fara mikewa yana fafin zai fita bai tsaya saurareb fadan da mama
Dubu take yi ba lokacin da Saare.
Yana fita ya tsaya ya hada wani take away da gasassun kaji biyu da drikis ya
nufi asibitin dashi don yasan ba zasu taba iya cin wanan kwaban ba na saratu ranan.
Hakanne kuwa don koya samesu a zaune sunyi zugun zugun sun gama magana kan
abinda ummah zatayi buda baki da sahur sai gashi ya kawo masu wani abinda zasuci
din.
Da bai kawo ba haka zasu zauna da yunwa don ko ba zasuyi magana ba saboda
kawaici irin na fulani da kunya suje tambayab surakansu ya hakan ya faru ?
Shima ya J din fita yayi a hasale yana fadin wanan baki da maraba da girkin wa
yancan idan zaki zage ki koyi girki ki zage har ace karamar yarinyar nan tafiki iya
girki ?
A hankali tana gunguni take fadin zaku hadani da yaran da suka bude ido da dafon
abinci tunda zaman aikatau sukayi a abuja har suka iya abubuwa haka ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

2️⃣0️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Karfe tara na falka ba wanda ya motsa kowa na kwance yana barcin azumi na kewaya
bandaki na fito na kitsa jikina na fito falo.
Ashe iya na zaune a falon ita kadai jin motsina yasa iya juyowa gaida ita na
fara yi kafin na juya zuwa kitchen don in hada kayan wanke wanke.
Yadda naga kayan a wajen bakyau gani yasa na shiga hadasu har falo duk na kwaso
cups din akai amfani dasu da asuba don ranan dai ba wanda yaci abinci zance a
gidan.
Saidana hada kayan tas na fara sharan part din nasharo ko ina har dakin Iya da
mama dubu dana samu ta falka don jin motsina da tayi ina aiki.
Falo ta fito ta zauna tare da iya na gama shara na koma kitchen din abincin na
tsaya na kalla na tsayin lokaci kafin na juya zuwa wajen su ina fadin mama ya za
ayi da abincin nan me yawa ?
Ta juyo tana fadin kedai Rahama ina nasan yadda zanyi wanan iskacin na Saare
aida yawa yake yarinya ki haramta muna cin abinci haka kiri kiri ?
Ta mike tsaye ta biyuni zuwa kitchen din ina tsaye gefe daya na kura mata idanu
ta nisa tana juyowa gareni tace ki barshi a tukunyan anjima idan Auwalu yazo
yakaiwa almajiransu.
Hakan akayi na wanke kayan tas na kara gyara kitchen din ina gab da gamawane
naji muryan ya Habu a part din suna gaisawa na fito ina gaisheshi da kwana ya amsa
min har zan wuce naji yana fadin.
Ramaah ashe Abuja zakije sallah jiya suke fada min asibiti danaje da dare
murmushi nayi kawai zan tafi kuma naji yana fadin .
Sai kuje da salima kasuwa ki sayi tsaraba anjima gobe akwai wanda zan hadaku
yakaiki Abujan nace nagode yaya.
Nashige na barsu ina jin mama din tana magana saidai banji abinda tace ba wai
ashe tace da alama yarinyar nan ta dauki zancen nan da zafi don banji tana zancen
zuwa Abuja ba ai ?
Sune suke son tazo masu sallah a can ita wace zataje gurinta ta bugo min waya
jiya tana rokona Allah ya kyauta mama din ta fada.
Murna yasa tun a lokacin na fara shirina yan kayan da zan dauka da sauran
abubuwan amfanina da nake bukata na hada saman gado.
Wanka nashiga nayi na fito nashirya zuwa lokacin sun tashi na samu salima zaune
tabini da kallo tana fadin kayan meye haka kika hada ?
Abuja zanje sallah anty Salima cikin mamaki ta maimaita da Abuja wurin wa nace
anty Salma kinsan mutumiyatace sosai yanzun nan da safe ya Habu ke fada min ta bugo
waya tana son inzo inyi sallah wajenta.
Shiru tayi na dan lokaci kafin ta tashi ta mike ta fita daga dakin nagama
shirina na fito falon na samesu suna zaune zama nayi gefe daya ba tare da magana da
kowansu ba.
Sai iyace ke fadin yar fullo ina za a hakane naga kinyi kwaliya kamar bakya jin
azumin nan ke ?
Murmushi nayi ina fadin asibiti naso inje iya inyi ,,,,,,, ina jiya kinje
Rahama ku koyayyi zuwa asibitin nan fa kuna kanana daku mama ta fada.
Naso naje kan tafiyan da yaya yace zanyi gobene kada in wuce banyi sallama dasu
ba daidai lokacin ya J ya shigo yana fadin mama kinko ga gidan nan yadda yayi kaca
kaca don Allah ?
Inda nake mama ta kallo nayi kamar ina kallon tv da wani malami ke wa,azi akan
zakkan fidda kai da za,ayi idan ansha ruwa.
Sai naji tana fadin ato ita daice me sharan gidan ai tunda tazo gidan nan take
wanan aikin bayan ita ba maiyi a cikinsu tana nuna yaranta mata.
Suma matanka ba zasu iya komai bane wai Jafaru saidai suci su sha su kwanta su a
dole ga bazan ta samu garesu yau da gobefa sai Allah jiki da jini kuma ?
Yarinyar nan ta gajine fisasbillah kunga abin nan da yar nan keyi ba a banza zai
tafi ba hakan duk gidan da tayi aure nakab fada ince sun huta wallahi.
Mijin da zai aureta ya dace mace ba son jiki ba keta ba algus gako wani aiki ta
saka kanta yi zata tsaya tayisa tsakani da Allah yarinya ce karama data san ciwon
kanta.
Haka zakuyi kuma a gidajen ku muddin baku gyara kada ku dauki hakan kamar
wayewane kanku kuke cutarwa wallahi.
Iya ta karasa fada a cikin takaici tana maida fuskanta wajen tv dake aiki balle
dan mutum rana garesa ai, .
Yau yarinyar nan bata kimu ba ta yaya zaku nuna baku kaunata kiri kiri haka ba
kunya dan zanin da duk dadewansa yan shekaru a jikinta kuce ta kasa ramawa ?
Itama fa rayuwane a jikinta kamar kowa yadda kuka rufe ido aka tozarta ta a
gidan kowaye dole yaji ba dadin hakan don sai ince duk da sanin ku aikai hakan idan
na debe shi namiji a cikin ku da bai bibiyan me ake ciki.
Wallahi iya bansan da wanan shirin ba Rahama ai diyatace a yanzu bata da
banbanci dasu Salima a wajena don itama a karkashina take rayuwa.
Munafunci daine irin ta yaran nan da suka shirya komai da sanin saare aka
hadashi a gidan nan makircin nan kuma yana gindinta.
Kuka Saare din ta fara tana fadin mama ni ya zanyi tunda sunce ba zasu bayar ba
kamar Ramaah zata saka kaya irin wanan tare dasu ?
Dama Saiba har ta raba kayan a tsakaninsu ai lace din nan ne suke rigima a kansa
jifa wai rigima don Allah akan abinda baku da hakki kansa mama ta fada.
Ban raba daya biyu don ko rantsuwa nayi ban kaffara akan wanan zancen yarinyar
nan zata tafi Abuja gobe aiba yau take gidan nan ba bataje Abuja ba saida haka ya
faru.
Wayan da yakeyi ya dakatar yana fadin Abuja kuma me zata tafiyi Abuja gab da
sallah haka kuma ?
Wai mutanen Abuja din sukace dashi ya bari tazo nan tayi sallah a wajensu niko
nasan don wanan zancen suka fadi haka.
Shi Habu kuma ya yarda da tafi din ya yarda mana tunda har yazo da safen nan
yana fada mata ta shirya gobe akwai wanda zata bi su tafi.
Ai nima goben insha Allahu zan shiga Abuja amma bai fada min ba yanzu muka gama
magana dashi na shigo nan .
Ku barta taje don Allah kada kuce zaku hana yarinyar nan tafiyanta iya ta juyo
tana fadan hakan garesu mama dubu tace ai ba zance kartaje ba iya.
Sam baiji dadin yadda abin ya kasance ba haka ya fita gidan da bacin rai wani
kauye da ake kira da kinkinau suka nufa shida kawu .
Wasu filaye ya saya a wajen sai daga baya kuma mai filin yake son ya tayar da
ciniki don wani yazo ya kara masa kudi.
Kudin da yaya ya ban ba wani sayayya nayi ba na dai sayi kayan kwaliya saura
kuma na dunkule abina a jikina don banga wani tsaraba da zan kaiwa anty Salma ba
daga bangarena.
Sai traveling bag dana saya mai kyau don shi nake kwadayi dama na dawo gida na
shirya kayana tsab ina jiran washe gari tafiya idan Allah ya kai mu.
Ina barci naji Saare na kirana da dan karfi da in tashi yaya yace in fito mu
tafi gabana ya fadi ina duban lokaci shida da wasu yan mintuna na safe.
Da sauri na mike tsaye na shiga shiri Allah ya taimaka nayi wanka da asuba hakan
dabi,atace watsa ruwa kafin na fara aiki don in samu kuzarin aiki da kyau.
Simple


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login