Showing 177001 words to 180000 words out of 328222 words
Chapter 60 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
sai ki
kirani zan fada maki yadda zakuyi dashi godiya sosai nayi mai nace ga fam darin ka
da kace din zan turo mashi hardana goro dubu goma na tura mai a layinshi take a
wajen .
Don nasan komai zaiyi zaiji karfin gwiwan bani har abinda baiyi niya ba saboda
kudin donshi ne banji komai ba na tura mashi kudin haka.
Na dago kai ni ya J ya zubawa ido kafin naji yace dawa kike wayane haka na
lumshe ido nace Dage ne dan wajen baffan mu wanda ya taba ban maganin dana baka
kwanaki.
Sai naga yayi murmushi ya gyara kwanciya kanshi na saman cinyana har lokacin
yace ai matsalan nawane Rahama yana da daure kai.
Idan mutum baiyi hankali ba sai yayi shirka gara ka dogara da Allah duk abinda
ubangiji yayi ga bawa daidaine dashi Rahama.
Amma kinki duk inda naje sai ace matsalata na gidane kuma mamace kadai mafitan
matsalan nawa amma ta kasa kwantar da hankali ta gane hakan.
Wanan yasa kikaga zuwan ilimi a yanzu ba karamin amfanan al,umma yayi ba sosai a
yanzu don malumanmu suna kokari wajen wayar da kan mutane sosai a yanzu na su daina
irin shirkan da akeyi a da can baya a cikin duhun kai.
Don gashi abin baibi kowa a cikin muba saini yake bibiya haka kuma mun kasa
tsayawa mu fahintar da mama inda matsalan namu yake .
Hardo ya fada min komai lokacin danaje zancen auren ki mutum dayane zai iya shawo
kan mama a yanzu itace iya.
Don da zan zauna in fadawa iya abinda ke nan daga kawu har mama din zata zaunan
dasu ta bincika maganan .
Katseshi nayi da fadin wanan mai saukine ai yaya idan har baka iya zama da iya
kafada mata a can gida sai mu daukota nan ta kwana biyu daga hakan sai ka samu
daman fahintar da ita komai dake damun ka din.
Shiru naga yayi na dan lokaci kafin yace hakane gaskiya don zance ne dake son
natsuwa da fahinta nakanyi tunanen zancen hardo da yake fadin duk matsalan yana ga
kawun mu dauda.
Kawu dauda kuma na fada cikin mamaki ina kallonsa yace hakane kawu yasan komai
amma yake boye hakan don wani nufinsa akan mu da bamu san na meye ba ?
Munyi magana sosai a lokacin inda na fahinci yana cikin damuwa akan matsalan
lafiyanshi dana iyali dana sauran yan uwa dake cinsa a zuciyarshi.
Nake fada mai dage yace ya nemo ruwan da ake ba doki wanda yasha ya rage idan an
samu mukirashi zai fada muna yadda zakayi dashi.
Naji yace sai yanzu na yarda ba banza fulani suke zaune a dokan daji ba ashe da
shirinsu suka zabi zaman dajin da sukeyi ana masu kallon basu san me sukeyi ba ?
Waya fadama basu san komai ba su suna ganin ku dake cikin gari a zaune kune
suka kwara ai yace naga alama ai.
Wani abokin mahaifin mu bafulatanin nan dajin zaria ne kwanaki da nazo har
wajensa muke da yan uwana yake fadin nayi dace tunda na auro bafulatana a gidana.
Murmushi nayi nace baka sanin hakan ai shi daya san irin wahalan da bafulatani
yakeyi kafin ya mallaki mace ai dole ya fadi hakan.
Kiran sallah da aka fara a wayanshi yasa ya mike ya shiga yin alwala yayin da
nake zaune a wajen ina charting da anty salma.
Har ya fito ya sameni a zaunea inda ya barni yake fadin amma kinji lokacin
sallah yayi nace yanzu zan tashi ban fada mai ina fashin sallah ba kai tsaye.
Kodaya fita munci gaba da hiran mune da ita har ya dawo ya kara samuna wajen zai
dauka na dawone na zaune a wajen kuma.
Tun bai zauna ba dana gaidashi nake fadin a binci na saman dinning na hada yace
ok barin gama waya da Meabei tana kirana ina masjid dazun ban daga kiran nata ba
lokacin.
Na saba jin wayarsu don haka na mike na shiga kitchen na dauraye yan kayan da
mukayi amfani dasu da rana koda na fito wanan karon yana waya da matarsa Saiba.
Naji yana fadin ok sai gobe idan nashigo zamu gaisa a raina nace miji da mata ke
nan sai Allah dama idan kace zaka shiga tsakani kai za a bari a cikin zancen.
Da mama ta sani tasa masu ido ba zata san lokacin da suka shirya ba a tsakaninsu
dazun nan yagama min korafi kanta yanzu gashi suna waya kamar ba komai a
tsakaninsu.
Tsawan daya daka mata yana fadin nace maki ba zan shigo ba sai safe ko bakiji
mena fada bane ban dai tsaya jin abinda ta fada a bangarenta ba na nufi wajen
abinci na zauna ina jiransa don ko abincin kwana biyun nan ya rage zama yaci soai
don haka nayi hikimar yin wanan dabaran don nasan dole ya taso yadan tsankwara koda
kadan ne.
Naji yana waya da yan gusau suna fada mai washegari zasu taso yayi masu ban
gajiya lokacin ya mike ya sameni mukaci abincin a tare.
Bayan ya gama na mike na hada kwanonin zuwa kitchen don ya shiga dakilan
wayarshinema lokacin hakan ya ban daman tsayawa in wanke kayan na kife ina gyara
wajen najishi a baya.
Ya rike min kwankwaso yana fadin sarkin aiki ke baki gajiya da aikine wai ko
yaushe kina sa kanki busy na kula ko yaran nan ke ke faman dawainiya dasu a gidan
nan idan ban nan ko ?
Nace a,a nida su duka munayi bani kadai suke bari da aiki ba ai ga kuma habiba
tana taimaka min sosai itama.
Tsoman hannuna ya karba yana fadin gashi bata dawo ba nace ta kira da wayar
yayanta dazun wai kumshine basu fara da wuri ba nace tabari sai gobe ta dawo ba
matsala.
Jana yayi muka koma falo bayan na rufo kitchen din muna zama kuma ya shiga waya
hakan ya ban daman samu na sulale zuwa daki don lokacin a tsawale nake jin kaina
wanka nayi na shirya sosai na lakace jikina ko ina da humran mama na maiduguri a
jikina.
Yana falo kishigide yana waya a cikin natsuwa idonsa yana kaina harna karaso ina
fadi a hankali na kawoma ruwan shayine yanzu ?
Kai ya gurgizamin yace ki bar shayin nan a koshe nake yau Rahamce ashe da yaya
Habu yake waya na dai ga yayi murmushi yana miko min wayan na karba.
Naji muryanshi yana fadin Rahama kina son J yafini kiba ke nan kike faman dura
mai abinci haka ?
Murmushi nayi don ban iya wasa haka dashi ba da yake jana dashi a yanzu tunda na
zamo matar dan uwanshi din.
Munkai wani dan lokaci a falo kafin mu koma daki da sai lokacin ya gane fashin
sallah da nakeyi tunda ya fahinci hakan naga mood dinsa ya canza .
Ya lafe yai shiru sai can naji yana ajiyan zuciya yace na dauka cikine dake ai
Rahama da sauri na jiyo ina fadin ciki kuma yaya ?
Kamar ba zai ban amsa ba sai kuma can yace baki son haihuwa yanzu ke nan nayi
kasa da kaina ina fadin ba wai banso bane yaya in Allah ya ban ina so mana .
To Allah ya bamu ni ina son haihuwa sosai wallahi ina son ganin kema kin samu
rabonki dani tun ina raye da raina.
Yaya kana kashe min jiki idan kana wanan maganan dazun ka fada yanzu kuma kana
fadan hakan sai naji yace ana son bawa ya dinga tuna duniya ba matabbata bace a
gurinsa ai.
A raina nace lalai akwai abindake damun mutumin nan abin kuma babbane daga Allah
saishi saiko kila yaya habu suka san komeye matsalan don bai fada min ba.
Haka na kwana da damu akanshi washegari zuwan su Salima yasa na dan sake shi
kuma ya fita ya barmu a gidan bai dawo ba ashe yana can gidan da yan uwan saiba
suna fafatawa dashi kanta.
Da yamma kuma yan gusau suka dawo zuwan Ibrahim daya dawo da mota yasa muka
fahinci hakan sai gashi shima ya dawo suka zauna tare sukaci abuncin rana dana aje
mashi.
Aiki mukayi sosai har dare ba hutawa duk mun hada komai don washegari suna sai
dare na samu na kwanta da asuba kuma muka dora abincine don yan zanen suna da za a
fita dashi da safe.
Na aikawa makwabta dashi duk daba shiga gidajensu nakeyi ba kuma sunji dadin
hakan da mota su ibrahim suka jida zuwa family house dinsu.
Muka dora wani kuma da za akai part din mama duk da suna abinci suma a gidan
sai wajajen two na rana suka kwasa suka tafi nace dasu in ya dawo zan samesu daga
baya duk da nasan yana da wuya inje.
Koda ya dawo din bai nuna alaman zuwana ba sainice nace dama kai nake jira
zancen zuwa can gidan ?
No ba sai kinje ba tunda kinyi aiki a nan kowa yasan kin gaji ai ban kara
maganan ba sai darene mama takira waya tana tambayan dalilina kin shigowa suna ?
Naji yace shine ya hana don munyi aiki mungaji donshi yace in zauna ba sai naje
ba din ni dai nasha jinin jikina ina mamakin mama da halinta a kaina yanzu ?
Don nice dai bata so da danta har bata iya boye hakan acikin ranta na kula duk
abinda zanyi laifi mama zata kirkiroshi a kaina.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
5️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Barci nasamu nayi sosai washegari don babu kowa gidan har biba a can ta kwana wajen
su anty Salima dagani sai shine a gidan shi kuma ya fita tunda safe .
Ina kyautata zaton yan uwan saiba ce zasu koma gida a washegarin suna din don
haka na samu nayi barcin gajiya mai isata da yake ina fashin sallah donshi na samu
har karfe hudu ina kwance saidai fitsari ya tayar dani kawai.
Karfe hudu na samu na mike na shiga wanka na fito na shirya na fada kitchen don
girka muna abinci ina gab da kammalawane naji tsayawan motanshi alaman ya dawo ke
nan lokacin.
Ko ina na gidan fes yake sai kamshi ke tashi ga kuma na girki dayake dan
shigowa ciki lokacin muryanshi naji yana shigowa a zatona na dauka waya yakeyi
ashe shida iyace da habiba suka shigo.
Ina tsaye daga kofan kitchen da niyar gaidashi da dawowa sai ganin iya a
bayanshi nayi habiba na biye da ita da dan jakar kayanta .
Cikin murna na hada ina masu sannu da zuwa na dauka ganin idon iya din zai
hanashi yadda yake min idan ya dawo saidai hakan bai hanashi ba don saida yazo ya
rugumeni yana fadin how are you ?
Fine na fada ina dan nokewa ya gane me nake nokemawa din don iyace sai naji yace
wai iya ai zataji dadin ganin yadda kike ban kulawa don itama hakan take son na
kasance.
Ni dai na wuceshi ina murmushi zuwa wajen iya din ina kara mata sannu da zuwa na
nuna mata kujera ta zauna a sama tana fadin masha Allah abu yayi kyau sosai wallahi
haka ake so a rayuwa dama cigaba aiba wanda yakishi.
Zonan mu gaisa da kyau tana nuna min gefen da take zaune na zauna kamar yadda ta
bukata din ina fadin iya yaya gida ya taro kuma ?
Taro Alhamdullahi ke dai anyi lafiya an kuma watse lafiya sai abinda ba a rasa ba
dai wanan kuma ai an saba dashi kuma ko ?
Habibace ke gaidani na juya ina fadin biba yan suna nayi ta zuba ido jiya inga
dawowanki shiru ta danyi murmushi tana fadin ban samu wanda zai dawo dani bane har
dare yayi na kwanta a can.
To bagashi yau kin dawo ba bata da sabo kin ganta nan taki sakin jiki da kowa
amma yanzu kinga tana zuba kamar ruwan sama.
Mukai dariya na mike kayan da Biba ta aje gefe na dauka zuwa dakin da iya zata
zauna wanda a nan Biba take gyara dakin nayi sosai tare da Biba din na shimfida
sabin zanin gado dana dauko daga dakina na wanke bayin tas duk da dama baida datti
sosai amma na kara gyarawa nasa kamshi.
Falo na dawo na sameshi tare da iya yake fadin ina kika shigane haka nace ina
gyarawa iya dakine sai naji tace kaji arziki ba a inda aka santa Allah dai yayi
maki albarka kinji.
Kitchen nakoma na kwashe abinci na hada miya ina tsaye biba ta shigo ta sameni
zata kama nace jeki huta aina kammala tun dazun kafin ku iso.
Ke kuma ai da gajiya a jikin ki tace banyi komai ba a can wai anty ai gara da
bakije ba wallahi ana ta fada dasu anty salima da matan uncle wai ta aiko a dibi
abinci mummy salima ta hana shine tashigo tana ta zaginsu harda ke da bakije ba
din.
Maman tudun wada kuma ta farwa mummy salima din da fada har ta kira uncle shima
tace wai an kawo abincin mai kyau gidanki andafa ba akai can ba gashi kuma yanzu
abincin ya hada fada.
Ikon Allah nafada cikin mama sai tace ai uncle yace duk abinda ya sawo nan gidan
shiya saya a can kuma na can din yafi yawa tace dai ya dinga adalci.
Bayan haka kuma aka zauna da yan uwanta akaita fada da uncle din tana ta kuka
shine mama tudun wada tace wai in tashi in fita na koma part dinsu Abba na zauna.
Biba irin hakan dama dole zaki gani tunda kina tare dani ko kingani kibar damuwa
saivyarinyar tace Allah mama tudun wanda bata sonkine anty haka shima uncle ya fada
yace me kikai masu meye matsalansu dake ne wai ?
Muryanshi naji yana kirana nazo yake fadin to bakuwanki zaki kai daki zatayi
alwala na amsa da to iya muje dakin kiyi ko ?
Tafiyan nata daine yasa dole nima na taka a hankali muka shiga har dakin sai
fadi take masha Allah kinga arziki dole ai yarinyar nan tayi hauka sunzo jiya da
yan uwanta sai koke koke suke muna wai Jafaru ya fita batunta ya maida ita bora a
gida.
Uwarku kuma kamar sun gama da ita sai wani noke noke takeyi makin ta fada masu
gaskiya ta tsaya marawa karya gindi ita da yar nan saratu mara hankali.
Duk abinda dubu keyi da zugin saratu takeyinsa ni yaushe zan zauna yaro karami
yana min wanan shegantaka in dauka yarinyar dako auren fari batayi ba.
Kinga ki daure kibi mijinki yadda yake yabon nan naki karki yarda ki canza
halinki ko gaba haka nake fadawa yar uwarki wanan zancen don yadda suke hattaranta
a yanzu gidan.
Dan dama wanan Asmau din naga kamar ta fita wanan shirmen nasu tunda tasan Allah
dayane taba da kai bori ya hau har abin suna naga ta hado akawo maki amma uwarku ta
rabewa mutane duka.
Naman daine na suna nayiwa Jafar magana tasa a debo maku har muka fito bata bayar
ba nace iya nagode ba komai wallahi Allah dai yabashi lafiya tace amin kafin kuma
tace dani.
Wai har yanzu dai jikin nasane kome ni naga yana rama a tsaye nake tambayanshi
yace min damuwane kawai da abubuwa da sukai mai yawa kuma.
Haka yake fada iya idan anyi magana baidai fada maki gaskiya bane amma da abinda
ke damunsa gaskiya sai kin zauna dashi kila zai sanar dake damuwansa din .
Jam jam Allah kaza gata a garemu shiko abu na cinsa bai fada tun abu bai baci ba
ni yaron nan tausayi yake ban don da kurciyarsa nauyi ya hau kansa haka ?
Na dai nuna mata ban daki ta shiga tana mita na fito na samu biba ta kammala
komai a kitchen din dakina nanufa na zauna ina azzakar na yamma.
Ban fito ba saida akai isha,i na fito na dauki abincin nakaiwa iya din har ruwan
sha dana wanke hannu duk na aje mata a nan inda take sallah din.
Na koma gefe muka zauna da biba muna hira ta gama addu,a ta shafa ta juyo tana
fadin shi dai mutunci gadarsa akeyi haka yar uwarki take faman dawainiya dani
kullum gashi na fito ban samu sallama da ita ba.
Ayya bari na kira maki ita kuyi sallama din tace hakan shiyafi kada taga rashin
hankalina nasan yanzu ta shigo bata sameni ba.
Itama uwar naku naji tana fadin gobe zata gida ai saigashi Jafar yazo yace dani
ai in shirya muzo nan in kwana biyu daku in huta hakan yai min dadi sosai wallahi.
Kwana biyu kuma iya nida nasha kinzo ke nan baki komawa a nan zamu zauna dake
tace haba ina haka zai yuyu ai sai a zageni nazo nan na tare don kwadayi kamar
yadda ake zagin yar nan salima tunda na saratun nan ba mai ido a tsakar kai.
Na fadawa dubu ai tayi mata aure ta huta da ita yafi zaman ta sai gulma tsakanin
yayyun ta da hadin hasumi da takeyi a gida.
Aure lokacine iya idan yazo koba shiri sai anyi nata harda ruwan ido kinji aiba
maneman ne ta rasa ba ruwan idone kawai ta dafewa yaron nan da akace baida kirki
sai karya yake masi ko yaushe gashi turo magabatanshi ayi zancen aure.
Ina ji masu tsoron irin na