Showing 57001 words to 60000 words out of 328222 words

Chapter 20 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

dress nayi dogon riga sai hijab a jikina saboda sanyin safiya na fito da
yar jakkata da zanyi tafiya nan na samesu falo har da yaya Habu a cikinsu suna
magana da dan uwasa.
Na gaidasu da kwana suka amsa min mikewa Jafar din yayi yana fadin ka barni
dashi Habu nasan yadda zanyi maganinsa ai.
Ramaah kin shirya ga yaya zaije Abuja yau shi zai wuce dake don shi wancan sai
da karfe biyu wai zai tafi banyi magana ba shiru nayi.
Rahaman ta fito kuwa mama dake fitowa kitchen ta fada na amsa da eeh mama tace
toga wanan din tsarabarce da zaki dashi ki gaida muna su son Allah a kula da kai
kuma aje lafiya a dawo lafiya.
Na amsa da insha Allahu mama su har sun kai bakin mota a lokacin suna tsaye suna
cigaba da magana da gani dai magana ce mai muhinmanci a garesu.
Nida salima iya sai mama suka rakoni har bakin motan da kayana salima tayi mai
magana ya bude bayan motan muka saka kayana a ciki.
Kafin na zagaya na tsaya ina jiransa a gefe daya salima na min sheri da indai
yaya ne yanzune zaku kai Abuja don gudu yake da mota sosai wallahi.
Ai shine matsalansa ranan da ya kaimu kaduna ai fada nayi dashi sosai kamar wanda
zai tashi sama damu mama ke fadan hakan nidai ina kurum sai ya Habune ya dago yana
fadin bude mana ki shiga Ramaah .
Baya na bude da zumar shiga naji yace a,a gaba zaki bude mana ai ina ganin
kamar ba wanda zai tafi dashi ko ?
Ta shiga mana ni kadai zan tafi ya fada daga mama har iya kudi suka dunkula suka
ban suna min a dawo lafiya saiga ya Habu ya kara min kudi daya miko min wana rike a
hannuna.
Nayi masu godiya ya shiga motar suka juya don komawa cikin gida ya fara ribas da
motar sai naga yaja ya tsaya.
Ta karaso bakin motar rike da yarta a hannu tana fadin wacece kuma tare dakai
naji yace ki fadi meye don Allah kada in makara banson rana yayi min a hanya.
Lekowa tayi ta ganni kamar in shareta saidai nace da ita ina kwana anty Saiba
bata tsaya amsani ba sai cewa ita kuma ina zata ?
Tsuki yaja yana fadin gata nan ai ki tambayeta ya fisgi motar da karfi don
maigadi na tsaye yana jiransa da get a hannunsa rike.
Amma ai ka tsaya dai muyi magana sweet J bai saurareta ba ya fice yanawa
maigadi horn da mota na lumshe idanuna na hankali a yadda nasan halinta zasuyi
rikici sosai da daukata da yayi a motarshi yau.
Ban ko kai karshen zancen zuci ba wayanshi ya katseni naji ya dauka yana fafin
umm,humm ina jiki ta fara fada Jafar ina zaka da yarinyar nan baka fada muna ba ?
What ki shiga hankalinki wallahi Nusaiba kina wuce gona da iri fa a rayuwata
dolene sai na fada maki inda zani da ita ki je ki tambaya idan kin damu ?
Naji ya kashe wayan yana tsoki dama nasan za a rina yadda take da zafi akanshi
tunda Salima ta tayar dani tace dashi zamu tafi gaba saida ya fadi nayi wanan
tunanen da sai wani abu ya faru kan hakan gashi kuwa.
Tsuki ya kara ja yana lalubo wayan daga inda ya jefata da farko ya dauko yana
tuki yana neman lamban da yake nema a lokacin.
Can naji yace mama wallahi idan Nusaiba bata yi hankali ba yau din nan saina
saketa kafin ta bata min suna a banza.
Banji me uwar tace dashi ba naga ya kashe wayan nasa a hasale yana faman jan
tsuki akai kai saida muka tsaya gida mai a kaduna ya tsaya magana da wani kafin ya
dan sake.
Hanya muka kama sosai inda barcin azumi yake dan dibana a wajen lokaci lokaci
saboda sanyin AC motan nasa daya sake .
Maganan Salima ya tabbata don ganin mun shigo Abuja ga signboard din THIS
ABUJA baro baro a jikin allon shiga iyakar Niger da Abuja din.
Wani unguwa zakije ya tambayeni ba tare daya kalloni ba na amsa da maitama
kinsan gidan ke nan zaki gane na amsa da ehh .
Har yayi shiru naji ya kara fadin idan ba zaki gane ba ki kirasu a waya suyi maki
kwantace nace banda waya amma zan gane gidan.
Cikin mamaki ya juyo da kyau ya dubeni yana fadin baki da waya fa shi Habu yana
me da basu saya maki waya ba ?
Shiru nayi don ko da zan taso saida mukai zancen waya da yayata da salima kuma
har Salima tace zata ban karamin wayanta bansan meyasa kuma ta fasa ba.
Shiga wanan lungin fada wanan muka isa wani katafareb shago yaja ya tsaya ya
dauki abu naji yana fadin ina zuwa jirani kadan in dawo don Allah .
Ya fita lokacin na sauke ajiyan zuciya a hankali ina bin wajen da kallo shagone
babba don jama,a sai shiga da fita sukeyi a wajen.
Can na hangoshi da ledoji kusan ukku rike a hannunsa ya nufo inda motarsa yake
ya bude ya baya yana aje lodejin aciki kafin ya juya zuwa gaba wurin driver ya bude
ya shiga.
Sorry na dan dade a ciki na barki zaune bakomai yaya saida ya zauna da kyau ya
dauki hanya muka bar wajen hanyan maitama naga ya dauka kai tsaye.
Ajiyan zuciya na dan sauke an karaso gida ko naji ya fada na danyi murmushi ban
dauka yana da saukin kai irin haka ba.
Wancan layin na fada ya mike zuwa layin dana fada muka shiga dab tafiya kadan
nace wanan gidan mai bakin get nan din gidansu hjy mamace daga waje ya tsaya ya
juya yana dauko ledab a bayan mota naga ya fitar da waya sabo dal a kwalinsa ya
fara duba lambobi a cikin wayansa yana lodawa kafin ya miko min wayar yana fadin
layin mama dana Salima saina habu suna saka maki .
Saida na dan dubeshi nayi kasa da murya ina mika hannu nace nagode yaya Allah ya
kara arziki amin yace a uzurce da alama sauri yakeyi a lokacin.
Horn yayi sai ga wani dogon sauriya ya leko yana duban mu kafin naji yace daga
Zaria ko nace ehh sorry duk basu gida sun tafi umura last week amma anty salma tace
idan kin iso a kaiki gidansu .
Sai lokacin naji zuciyana ya dan sake da har nashiga vibration inane gidan nata
yake naji yaya ya fada tana Aso rock muje ka nuna min ya fada.
Saurin yace ga mota nan da tace in kai ta sai naji yace.
No muje dai ka kai,mu naga gidan na ajeta baiki ba naga ya juya ya fito da mota
muka bi bayanshi har gidan anty Salma din.
Duk wanda yaji ance gida a Aso yasan ba karamin gida bane ke nan za a gidan ya
hadu iya haduwa mijinta wani babban dan kwangilane mutumin maiduguri.
Gaeinsu daya asalima yan uwa suke dashi itace matarshi ta biyu yanzu anty salma
yaranta biyu dashi bayan barin mune akai aurensu dashi mun dai sanda zancen auren
kafin Allah yaiwa mahaifin mu rasuwa mu koma gida.
Ko kuma Allah na tuba ka yafe min inji mata gashi kuma zan fada ince Baffa ya
cinyeshi don shi yai sanadin barinsa duniya duk da lokaci yayi dama.
Tsayar da motar yayi yana fadin kice min gidan manya kikazo dama murmushi kawai
nayi ina mashi godiy.
Ledan ya dauko daga bayan mota ya cusa kudi a ciki ya miko min yana fadin rike
wanan inda matsala ki kira gida a zo a daukeki .
Na amsa da godiyana na fito daga motan ya fito ya bude baya aka fito min da
kayana zuwa ciki ban shiga ba saida na kara mashi godiya naga tafiyansa na sa kai
zuwa cikin gidan.
Ina shiga saiga anty salma da gudun ta muka rugume juna da ita a cikin murna
kafin ta sakeni tana fadin wai Ramaah tace nan haka ta zama yan mata ?
Nayi murmushi ina fadin nice anty muka kwasa zuwa cikin gidan nasu tana nuna min
kauna don haka muke da ita tun ina karamata .
A zaria motarmu na dagawa ta juya zuwa part din su mama a hasale take babu ko
sallama ta fado masu a falon ta samu kowa a falon zaune.
Mama tana ganinta hakan hankali tashi ta soma fadin Nusaiba lafiya kuwa na ganki
a haka hankali tashe ko wani abu ya faru ?
Babu komai mama dama karan J na kawo maki mama ta dan sake kallonta tana fadin
jafar kuma me kuma ya hadaku dashi ?
Mama din ta tambaya cikin kulawa don ta kwantar da hankalinta tayi mata bayani
yadda zasu fahinci abinda ya hadasu .
Mama don ya dauki yarinyar nan Ramaah ina tsayar dashi zanyi magana amma J ya
daka min tsawa ?
Bai saurareni ba ina ruwana da inda zai tafi da ita tunda da ai an,san ya dauke
ba a hanashi ba saboda ita zai dinga muna wullakanci haka mama ?
Haba yar nan ki saurara mana kada kiyi furci irin haka ga mijinki don Allah koda
kika ganshi da yarinyar nan Rahama hanya ya rage mata ai.
To don me ina tsayar dashi in fada mai yarinyar nan jikinta yana zafi amma yaki
tsayawa saboda Ramaah zai min wullakanci mama ?
Point of correction ki gyara zancen ki kwarai da sanin su ya dauki Ramaah zuwa
Abuja kada ki tsaya boyewa don kinj zafi ya dauki wata a tare dashi salima ta fada
a hasale.
Ki barta tayi maganan ta mana ke ina ruwan ki salima wajen mama tazo fa ba wajen
ki ba Saare ke fadin hakan .
Dole inyi magana don mu ba yan iska bane da kike son fadan hakan a gaban mama
tana fadin wai saboda Ramaah ?
Kinzo nan ne kiji dai ina zai tafi da ita to Abujan daya nufa can zai kaita
gidan yan uwanta a can zatayi sallah
In kuma ya Habu daya bashi ita yakai yaji an juya wanan zancen wallahi mama rai
zai baci sosai a gidan nan don sai yaba kowa mamaki matakin da zai dauka kowa kuma
yasan hakan .
Kada inyi magana ita din muharamince halan da zai dauketa daga shi sai ita a
mota da zakice kada inyi magana mijinane fa J dole inji dalili ?
Mijin kwace ba da kika kwace wa kawarki mijin har zakizo nan kina kokarin
karantawa mutane hauka kega mara kunya don ana kyaleki ?
Wai Salima me kike nufi da bazanyi magana ba naga kamar dama kina jirace dani
ashe ?
Jinan Nusaiba tunda kinji abinda ke nan sallah yarinyar nan zata Abuja tayi
gidan yan uwansu shine habu ya hadashi sa ita ya sauketa banga abin hayaniya ba a
nan ?
Mama niba hayaniya nazoyi ba kawai dai nazone in fada maki abinda yai min akan
Ramaah saiya dinga nunawa mutane banza muke mu ?
Wasa wasa zancen dai ya koma na Salima data gaji da halin Nusaiba fada sosai
sukayi a gaban mama tana zagin Salima din don me zata hanata magana a kan
gaskiyarta.
Hayaniyan su ya fito da ya Habu daga part dinshi yashigo yana fadin wai meke
faruwa hakane meye haka ga mama zaune ga iya kuke wanan abu haka ?
Sam bata san yana gidan ba ta dauka ya fita ko bai gari ta don basu sani idan ba
sun gashi ba tasan waye Habu din bai dariya da kowa a gidan balle aje ga wasa .
Nace meya faru duk sukai shiru ya juya wajen Saratu yana fadin ke Saare meya
hadasu fada da safen nan haka ?
Bafa fada bane ita Nusaiba tazo wajen mamane da magana shine ,,,,
Yaya zakice ba fada bane ita mama din sa,artace da zatazo tana fada akan ya J ya
dauki Ramaah a motarsa salima ta tare Saare dake kwana kwana da zancen tana kokarin
dora mata laifi.
Kai ya girgiza cikin takaici yana fadin don J ya dauki Rahama shine abin fitina
ba dan uwana bane J Rahama kuma tana zama kanwar matatace a gidan nan .
So baki da right din da zakice kada ya dauketa wai ma a gaban mama kika zo kina
wanan haukan ke yanzu bakiji kunyar wanan abinda kikeyi ba don Allah.
Assuming nine yanzu zani kaduna saiga kanwanki zata sai ince ban daukanta don ina
tsoron Maria kada ta shakeni ko ranta ya baci kome ?
Ai yau naga mamaki ga yarinyar nan gara da Allah yasa kana gida ka ganewa
idonka irin cin kashin da sukewa uwarku a gabanta ba zagin da yar nan bataiwa
Salima ba yau don ta raina arzikin uwarku balleni ?
Bazan ce komai ba sai mijinki ya dawo daga Abuja shida ya ajeki zanwa iyaka da
shigowa part din nan idan ba alheri ke kawoki ba dama ?
Fice kafin na canza zuciyana koda yake banganin laifin ku gaskiya waje kuka samu
nayin hakan ni akwai matar da ta isa tayi min haka ko yar wacece ita kuwa an dauki
wata a mota idan ya dawo yau ki kasheshi don Allah.
Amma ke kan kibar wanan halin wallahi salima ta dubi yar uwarta ta fada tana
mikewa don barin wajen.
Mama duk hakan da laifin ki wallahi idan mutum zai dauki mataki kan irin zancen
nan kice ina ruwansa ?
Saida mama ta nisa tace aini yau yariyar nan ta nuna min iyakata a gidan nan don
,,,,,,,, dakata don Allah gaskiya danki ya fada tun farko na fada maki ba aiwa
yaran yanzu haka.
Duk kama girmanki da kikeyi kina kau da kai ga rayuwansu sun dauka baki da amfani
a gidan nan yadda yar nan ta nuna ?
Yau gashi salima da abin ya isheta itace ai tayi fadan akan ki don bata da kunya
zatazo da wanan shirmen haka a gaban mu.
Wanan hali naki dubu shiyasa mutanen gidan ku duk wanda ya dauko sharansa akanki
yake juye tsiyarsa .
Wanan sanyin zuciyar taki tayi yawa Dubu kima godewa Allah daya baki yayan da
suka san zafin ki amma anyi mutum haka bai iyawa kansa katabus ?




ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

2️⃣1️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Sallah nayi na kwanta saboda gajiya a dakin da anty Salma ta kaini don bamu ko
zauna munyi wani hira da ita ba a lokacin saboda gajiya.
Sallah la,asar ya tayar dani na falka kinsan hakan baiwane ga musulmai da zaran
lokacin ibada yayi in barci kikeyi sai kin falka saidai shedan yayi kokarin
rinjayanki ki koma barcin.
Hakama idan idon ki biyu da zaran lokacin nan yayi sallah ce zata fado maki a rai
musulmi na kwarai duk abinda yakeyi a rayuwa sallah tana a zuciyarshi hakan aka san
musulmin kwarai dashi.
Nima irin hakan yake kasancewa dani komai nauyi barci zan falka a daidai lokacin
ko lokaci ya dan gwauta kadan in tashi in gaida ubangiji subbahanahu wata,alah.
Bayan na idar da sallah ina zaune na jawo wanan karamin ledan da yaya ya miko
min a hannuna lokacin da zan fita motan shi daya kawoni.
Na fara budewa kudi yan dubu daya sabbi,fill dinsu duk daba nauyi kudi na sani
ba a lokacin balle na kiyastasu nasan wanan yafi karfina a lokacin.
Sai wasu sarkoki da bangus da yan kunne guda biyu bangus biyu masu kyau ga
kudinsu nan a manne jikinsu ga yar takardan da akaiwa rubutu ja.
Mamakine fal a fuskana na dalilin sayan kayan nan duk da nasan shi mutum mai
alherine dama mutane na fadi ina ji uwarsu kuma ko yaushe tanawa abinta kirari
wajen alheri kullum ina ji.
Ban kara girgiza ba saidana mike da sauri na fara budan suran ledan gabana
nafaduwa nake zaro dogayen riguna masu kyau da daukan hankali guda ukku ko wani da
gyalensa a ledansa.
Tsorone fal ya dira min a zuciyata mu fulani mukance alherin namiji gareka nuna
alaman sone ko kauna sai wanda ka damu dashi kajin lamarinsaa zuciya kakewa alherin
bajinta irin haka ?
A take wani gefe ya gargadeni da ke wawiya wani so yaya Jafar nefa ina so zai
shigo tsakanin ku kuma yadai nuna ke kanwarsace yasa ya saya minsu.
Ko kuma don zancen da sukayi na cewa abinda matansa sukai min yake kokarin wanke
min zuciya sai gashj nafi amincewa da wanan na karshen wanda kuma haka dinne ko a
wajensa.
Don yaya Jafar nauyi da kunyana ya dinga ji na abin daya faru yana sane kuma nima
abin yayi matukar tabamin zuciya hakan yasa na tsame kaina ga lamarin kowa a gidan.
Karshema sai gashi na yanke shawaran in dawo Abuja inzo inyi sallah wanda yaga
sakacin dan uwansa Habu daya yarda nazo abuja din idan shine haka ya faru ba zai
bari naje ko ina ba zai tsaya ya tura masu haushin abinda suka aikata wanda sai
sunyi dasun sanin hakan da sukai min a lokacin.
Koda muke tafe hanya yana da takaicin Saiba amma kuma yana sake saken ta yaya zai
dan farauta min ba tare dana rikesu ba a zuciyana don cin fuska bai da dadi ga
mutum irin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login