Showing 108001 words to 111000 words out of 328222 words
Chapter 37 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
masu ido a tsakan
kai ba fasa halinsu zasuyi ba yaran da suka bushe fitilansu suka iya dawowa nan
idonawansu a bushe haka ?
Kayi hakkuri ka shirya da matanka ku zauna lafiya tunda ita wanan mai idanu
kwashi kwashin ido a kafe mata na rashin kunya kowa ka auro a gidan nan ba zata
taba barin ku zauna lafiya ba.
Iya komai kayi a duniyan nan saika samu wanda ya fika iyasa ai nata kuka gani
bata san wace zan auro mata ba a yanzu ki saurara zaki sha kallo ne a gidan nan ai
kwanan nan.
Allah ya zaba maka mafi alheri a rayuwanka jafaru yace amin iya yama zaba har ya
ban ki dai tayani da addua kawai iya shi nafi bukata a wajen ku yanzu.
Jafaru uwarku ba zata yarda ka kara aure a yanzu ba yadda naga ta daukaka zancen
yarinyar nan tun dawowanta gidan nan ni har tsoro abin yake ban.
Wai mama ya tambaya yana mikewa yace mama kan ki tayani bata hakkuri don aikin
gama ya gama a yanzu saidai adfu,a a tsakanin mu kuma.
Ka daiyi niya baka jin kwabo nake gani Allah ya zaba muna abinda yafi zama alheri
a rayuwan mu amma daka shirya da matan naka har dai wanan mai tsohon cikin.
Aida cikin ta biyewa sherin yar uwarta a kaina iya ni sam ban ni tausaya mata
don itama bata tausaya min ba lokacin da nafi bukatansu a kusa dani ai.
Yasa kai ya fita iyan ta bishi da kallo ita kadai a falin take magana tana fadin
tsiyan kakai namiji a bango ke nan ai shimai hakkuri bai iya bultsewa ba dama yaron
nan yayi hakkuri a rayuwansa kusan dai ace a tauye yake.
Salima dake jinsu taki fitowa su gaisa don gudunsa da takeyi kan kada su hadu
don zancen saurayinta data turo mashi washegari daya dawo garin .
Kuma ya tabbatar mata da cewa yaga J din sunyi magana amma kuma baice mata komai
ba har yanzu game da zancen.
Au damake idon ki biyu kina jin shigowan yayanki kikaki fitowa take cewa salima
din saida ta zauna take fadin ina jin ku iya tsoronsa nake ji kada yayi min fada
akan Yusuf.
Haukar banza shi zai zauna maki dashi da zai maki fada tunda kin dage saishi shi
meye nasa naki kece zaki zauna da abinki ai ba wani ba ?
Iya nifa zancen yaya kamar aure yake bida har zance yayi nisa don irin amsan da
naji yana baki a yanzu har cewa yayi ai Allah ya zaba mashi ko saidai addua.
Yo saidai adduan mana tunda nasan uwarku wanan karon ba zata yarda ba ko wanan
sakaran daya aure daga baya ai saida aka inmata.
To ita mama meye nata a ciki tunda shi zai zauna da abinsa kya fada kema yar nan
nidai banga abin sakawa yaro ido ba yana cikin lokacinshi.
Kuma ko banza tara mata ai gada yayi tunda ubanku ras mata hudu ya jera a gidansa
ya zauna dasu ashe ko aure gadonsa yayi.
Habu ya dauka suka fita don suje wajen mama suna daukan hanya daga gefe inda
yake zaune yake fadin muje samaru sai habun ya dan kalloshi.
Amma baiyi magana ba ya dauki hanyar Samaru din kamar yadda dan uwan nasa ya fada
da kwanta ya kawosu kofan wani gida mai dogon gina horn sukayi aka bude gidan daga
ciki habu yasa kai da mota ya shiga.
Bin gidan yake da kallo kafin ya dubi dan uwansa yana fadin wanan gidan fa J
gidan waye haka baiyiwa habun magana don maigadi daya iso yana gaidasu lokacin.
Hakan yasa ya bude motan tare da amsawa maigadin yace baba mun sameku lafiya habu
din shima ya fito yana kara bin gidan da kallo .
Ya juyo ya kurawa dan uwan nasa ido daga inda yake tsaye saida ya gama maganan
da zaiyi da maigadi yace to yaya kaga Surprise din ?
Kallon ban gane ba habu yayi masa yace ehh nina gina abina da kaina Habu da
gurin in mama ta yarda na baro can na dawo nan.
Yau shekara kusan biyar kenan ina wanan ginan ba tare da kowa yasan da hakan ba
sai yau nake fada maka don na fahinci mama ba zata bari na baro can ba a yanzu.
Wancan dayan ginan kuma na gaban wanan din kai da yazid na dorawa saidai rashin
lafiyana yasa komai ya tsaya min a lokacin .
A yanzu sam ba zan iya dauko saiba ko Asmau na kawosu gidan nan ba don na fahinci
basu taba canza halinsu na kazanta din nan.
Sai gashi faduwa yazo daidai da zama yanzu Rahama zan aje a nan ta zauna su kuma
su zauna can din har abinda hali zaiyi muje mana ka ga cikin gidan sosai habu.
Sai lokacin habu ya nisa yana fadin ninaso na riga wanan Surprise din ashe ka
rigani saidai ni tawa gaskiya ko rabin wanan baiyi ba J.
Tau ashe kaima kana da wanan dabaran ya ciro dan makuli daga aljihunshi yana
bude falon suka shiga ido waje Habu ke bin ko ina da kallon mamaki a gidan.
Don bai taba tunanen dan uwan nasa yana da irin arzikin da zai gina wanan mamaken
gida haka ba a ransa muryan Jafar din ne ke kara fadin.
Idan Allah ya nufa ina kuma rokonsa da yaban rayuwa na kammala gidajen nan Habu
don na dankawa kowa dukiyansa a hannunsa in huta.
Kaga wanan da kace ka fara ginawa sai na saye shi da sunan mama ta fito wancan
gidan ta dawo nan gaba daya ta zauna.
Wanan wacan kuma din sai mu barwa Saare da anty baraka da Salima a matsayin nasu
rabon da suka samu ka tayani addua habu in sauke wanan nauyin dake kaina ba tare da
an samu matsala ba .
In sha Allahu habu ya fada a sanyaye kafin shima yakai zaune cikin sanyin jiki
yake fadin kayi hikima da dabara sosai J .
Could you believe not morethan one year saida kawu yayi min zancen kudin mu dake
hanku inda na nuna mashi banda matsala da hakan ai.
Yace ni yarone ya kamata yanzu nima na fara tawa plan din don haka zaiyi magana
da mama a raba kudin nan abawa kowa nasa ya rike.
Kawu kawu na dade a raina ina zargin mutumin nan ba tsakani da Allah yake muna
wasu abubuwan ba dama ?
Habu yace nina dade da fahintar hakan tun rasuwan baba ai na fahinci waye kawu
don ba karamin abu yayi a lokacin ba da sunan karfin mu bai kawo ba.
Quet sure yayi wanan maganan iyace nasan ta taushesu da zancen amma ina da
tabbacin ya zauna da mama akan hakan lokacin.
Ohh my god meyasa mutane suke kasancewa hakane a yanzu habu duk wanda ka yarda
dashi sai ya ha,ince ka ni kawu zai zarga akan na taushe kudin magada a karkashina.
Bayan yafi kowa sanin cewa ban wasa da wanan abin koshi wani lokaci daya bukaci
da in bashi aron wasu abu daga ciki na fada mai cewa koni ban taba taba kwandala da
dukiyan nan ba Habu.
Nawa business dina na gashin kaina nakeyi habu shine kuma na dora ka kaima akai
ka samu rabonka ban amfani da wa yan kudin don in kara kaina Habu a harkan
business na shigo da kayan masarufi din dai na barsu a juya .
Sun dan jima suna magana kan kawu nasu kafin su bar gidan bayan sun leka ko ina
na gidan habu sai yaba kyawon gidan yakeyi yana ajiyan zuciya.
Suka dauki hanya zuwa babban gidan nasu a can ma basu samu shiga maza ba don
rikicin da suka samu anayi tsakanin dan umma da dan wanjen gwaggo kan gina sock
away na masai daya dan shiga gefen umma din.
Ita da diyanta suke fadin basu yarda ba tunda gidan dama rababene ai don me zasu
shiga wajensu suyi gina.
Sun dai tsaya an sulhuta inda shi Jafar ya roka da cewa suyi shawara sai a sayi
wajen a gina ma gwaggo din tunda bayi za a yi mata zama ba bayi kuma baiyi a
gareta.
Daga gefe Habu ke fadin wai tsaya Isah yaushe aka raba gidan nan bamu da labari
sai wanda aka kira da isah din yace ba dole sai kayi labari ba ai tunda ita mama
dubu tasan kowa akan bangaresa yake ai gidan nan tun baba na da rai kuwa.
To ban yarda ba yasa kai ya shiga yabarsu ana wani hayaniyan a wajen kuma iya
gaskiyarsa ke nan akan bai yarda ba din a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
3️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Zaune suka samu mama Dubu da Saare a kasan kafet din falon suna cin shikafa da miya
da aka zuba salad a gefe daya sai goran zobo a gefen kowansu da ruwa na leda.
Mama ruwan ya kare ke nan ko kun koma shan na gora kuma Habu ya fada yana zama
mama dake kokarin kawar da goran gabansa don ya zauna da kyau tace.
To Habu a zauna ba abinyi sai shan ruwa a gora wanan ma ai samunsa gatane wasu na
can suna neman irinsa basu samu ba ba kuma lafiya muka fisu dashi ba.
Sanabene kawai irin na zamani da wani ruwa iyayyen mu samu kanmu muka sha muka
rayuwa cikin sallaman ubangiji kuma.
To ai yanayi yana saka ayi taka tsantsan mama Jafar ya fada daga gefe daya sun
zauna aka gaisa take fadin saiga Rakiya hankali tashe wai kawunku yai tafiya bataji
duriyansa ba ?
Ai har nan tazo ashe Habu ya tambaya mama take fadin har nan take ai hankali
tashe bataga mijinta ba ni abin na Rakiya har yana ban kunya kuma wallahi ?.
Koda yake shiya saba mata ai dole ta damu don daya dawo baya numfasawa sai ya
zube mata kaf abinda ya nemo ta lissafe itace mai tsara yadda za a kashe a tsakanin
su.
Ita har yanzu tana wanan halin natane wai Jafar ya tambaya tome zata fasa haline
fa kuma ya daukar mata hakan ai kaga bata da laifi ke nan.
Wayan mama din dake saman kujera a gefenta yayi kara ta dauka tana fadin kaga
yar halak itace ma ke kirana ashe yanzu kuma .
Habu ya dubi dan uwansa yana fadin Isah bai san halina amma zamu hadu wanan
karon dashi rainin wayyon da sukeyi a gidan nan yayi yawa sai kace su kadaine yaya
baba ?
No saka masu ido duk abinda zasuyi suyi gida dai a yanzu kafi karfin tsayawa
kana fada a kansa Habu suda suka tsaya jiran gado sai suyi ta zaman cinsa mu dai
mun gode Allah munfi karfin hakan a yanzu.
Lokacin mama ke fadin ai gasu gabana yanzun nan suka shigo amma basu fada min har
can suke ba ai sai kuma tayi shiru tana sauraren bayanin da Rakiya keyi kafinta
tace wai wani Jafar kike nufi dai ?
Jafar yayi aure haka kowa bai sanda zancen ba jin hakan yasa su zubawa mama din
ido lokaci guda suna saurarensu .
Don Allah Rakiya ki bar zancen nan mana Jafar fa yai aure har yaushe ya taso
daga ciwo da za a kakaba mashi aure a yanzu haba dai don Allah nawa Jafar yake da
zai zauna da mata ukku biyun nan ma yaushe ya iya dasu balle yaje karo wani auren
kuma ?
Saare ta kafe mama da ido don bata fahinci takamaiman zancen mama din ba akwai
mamaki ace yayanta J yayi aure haka basu da masaniya a kai.
Mama wani masaniya zakiyi a zancen banda ki saka masu Albarka tunda Allah ya
nufa dai matarsace daga zuwa nema aka sauwaka muna komai don nisa aka daura auren
lokaci guda ai kinga anyi muna halarci a nan.
Kai dakata min da wanan zancen banza don Allah ban haifi dana don wasu ba don
haka babu wata gaiyan tsiya da za,a sake kwaso min kuma wanan aure bai dauru ba a
wajena.
Haba mama wani irin zance kikeyi hakane aure kan an riga da an daura yarinya na
zamasa a yanzu saidai kiyi hakkuri da fatan alheri a garesu kuma.
Habu wai meya hau kankane haka ina fada kana fada zan gani idan kaine ka haifa
min jafar din waima wayaje har wanan gari ya auro banda labarin komai ?
Shiru sukayi gaba dayansu sun kasa bata amsa don yadda ta birkice a lokaci daya
a hankali habu dake mikewa yake fadin you have to be strong for dis issue if
not ,,,,,
Ai da ka zageni da hausa habu abin zaifi maka sauki da wanan yaren nasaran da
kakeyi a yanzu ko bamu son jafar zamu so lafiyanshi ba tashin hankali a kansa ba.
Tsam ta mike zata shige daki cikin wani tsaya yayi magana yana fadin ke dawo
munafuka kawai ina zaki ana magana zaki daukan rahoto ki samu na yadawa ko ?
Ai ka barta ta yada din duk uban da zata kira ta fadawa taje ta kira idan wani
ya aura min matar mama ba kowa na aura ba sai Rahama dai da kika sani kanwar marian
habu itace na aura zargi ya kare.
Anty Nafisa dake shigowa don ta gaidasu taja ta tsaya a cikin mamaki tana bin
yan uwan nata da kallo tace yaya J ka auri Rahama ?
Tabbas Rahama ce na aura don wanke zargin da aka soma min iya matakin da zan
dauka ke nan tunda ance dama farkatace ita dole in mata gatan hakan a idon kowa.
Yanzu na gaskanta zancen da ake fadin fillo kakan sheri yau sherin nasu a kaina
kuma ya dawo ke nan an fada masu ni na haifa masu diyana donsu ne ?
Haba mama bai kamata aji hakan daga bakinki ba ai na dauka wanan abin da nayi
albarka zaki saka min kan yadda nayi din ba irin maganganun nan ba ?
Rahama dai kowa yasanta yasan halinta balle ta zama bakuwa a cikin mu ni kuma na
ganta nace ina so ba wanda ya tilasta min yin hakan.
Ni dai naga dacewan hakan da nayi duk da yarinyar bata sona ga hakan asalima
daga ita har maria har kawo yanzu basu sanda zancen auren ba.
Don bata ban hadin kai yadda naso ba hakama wa yanda take wajensu can basu bani
goyon baya akan nufina ba yasa na dauki kawu da Habu da Nasir muka tafi tare dasu
aka kumayi mai gaba daya.
Kiran wayansa da akayi ya katse masu zancen ya mike yana fadin yana zuwa ya
barsu a zaune zugun zugun kafin yasawa Habu kira ya mike shima ya fito daga dakin.
Fada mama dubu ta soma tana fadin yau za ayita ta kare ba sai gobe ba wanan ai
tada zaune tsayene yaushe aka taba yin hakan kagani.
Kanin ka yana auren ya kai kuma kaje ka daura aure da kanwa don shashanci kana
babba a garesa ka koma ka auri kanwa kuma ? wanan wani irin komawa bayane wai ?
Ba kowa bane maria ce keda kisisinan nan mama tunda tana ganin ta samu waje
bari ta cusa yar uwarta itama da hadin bakinta hakan ya faru .
A,a Saratu ki kama bakinki wanan zancen manyace bata yara bace kin dai san halin
yaya habu yanzune yaji abinda kike fada akan matarshi zai latsa ki wajen nan.
Ai sai yazo gata tunda hauka yayi ya kara dukan mi ya kan matarshi wanan karon
ba zan raga mashi ba .
Mama ta daiyi shiru shine alheri ta kama bakinta tunda ba zancen ta bane gashi
kuma sun fada daga maria har Rahaman basu sanda zancen ba ?
Dazun nan muka gama waya da Rahama da safe a dakin nan mamakinji metace ai
danace hutunsu ya kare tace saita kara lokaci zata dawo .
Nafisa rabu da yaudara inda kika gansu sunsan komai maganan saratuce da gamin
bakin maria akai hakan don haka ko ita ba zan kyaleta ba gidan nan yanzu.
Ya jima a unguwar saidai bai yadda ya kara shiga cikin gidan nasu ba don habu ya
fita tun bayan fitowansu ya nufi kaduna.
A lokacin ya kira anty Salma yayi mata bayanin komai tare da rokonta zai turo
mata kudi ta hado mashi laife.
Hakan akayi ina daki kwance duk da ba barci nakeyi balokacin don haka kawai nake
jin raina ba dadi aranan.
Kafana taja tana fadin lazy tashi ki rakani outing wani ya ban aiki daga
maiduguri haka na tashi na shiri muka fito ganin harda Samuel driver da yunusa zamu
fita yasa nasan babban abu zamu fitayi kfaruwa lokacin.
Bayanin da takewa yunusa yasa na fahinci meke faruwa a takaice dai wani ya sakata
hada lefe na gagawa wanan sana,an mamace mahaifiyarsu anty salma.
Donshi banyi mamaki ko kawo wani abu kasan zuciyata ba nakance alfahari da neman
suna yake sa wasu fita waje don banjinta da daukakansuna.
Amma komai da zaka sayo waje akwaishi a nan gida Nageria dan bambanci kudi kuma
kadanne a tsakani don muda kan mu muke raina arzikin kasan mu da kan mu amma
gaskiya matasan