Showing 174001 words to 177000 words out of 328222 words
Chapter 59 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
daga ita har yaran nata.
Taji dadi sosai da ganinsu tayi kuka tana masu bayani inda suka bata hakkuri kan
ta daure namiji yafi danan idan ya tashi kumsawa mace bakin ciki ai.
Ta shareshi ta nuna ba komai tunda Jafar ya nuna zai dauki mataki akan kudin
nata miliyan biyar da dan kai dayayi mata dadin baki ya karbe.
Ai kafin wani lokaci labari ya karade unguwa na zuwan yan uwan Barakha din
kinsan halin mutane nan makwabta suka fara shigowa suna fadin albarkacin bakinsu.
Yaya Ai tace ba komai ai tsakanin miji da matane ai aure karuwane idan akwai
fahinta don haka fatan zaman lafiya suke masu yanzu.
Wanan zancen sai a kunnen Iliyasu ya shigo yana fadin kwarai yaya abinda naso
barakha ta fahita ke nan taki fahintana aure mukkadarine banyi auren nan don in
tozarta taba wallahi.
Ba wani kadai bata kudinta aiba auren akace kar kayi ba kudinta dai take bukata
kawai a hannunta saratu ta fada don tana kule dashi tun shigowanshi gidan.
Haba saratu ke da na dauka zaki goyi bayana kuma har dake cikin wanan tunanen
yanzu dai ayi min hakkuri nasan nayi laifi don Allah.
Ai haka zakace dama yanzu kai don Allah dama haka amaryan zatazo ta samu yaya
daki kamar zauren malam ?
Daki ba komai alhalin tana da kudin ta ka rike kana kumsa mata bakin ciki haba
saratu yayanki fa taki kwantar da hankalinta muyi magana.
Yanzu dai kawo wani abu a shiga kasuwa ko kayan amfanin daki a saya mata sai ya
kwashe da dariya yana fadin saratu hoo ?
Ya shura takalmanshi ya fita matar zata fara fada yaya Ai dai ta tausheta tayi
shiru sukayi sallah sukaci abinci sai suka dan fita.
Kudin da Jafar din ya turo masu da suka sanar dashi abinda suka sameta ciki
suka dauki babban yarta tare suka fita basu dawo gidan ba sai yamma lis.
Sun sayo gado har da sabon katifa dasu zanin gado kula haka dai suka hado mata
kaya kamcankam kamar amarya.
Allah sarki tana ganin hakan kuka ta saka don murna dama wanan ne burin mace da
za aiwa kishiya kada kishiya tazo ta sameta hondadakwai daki kamar zaure.
Basu zauna ba suka shiga gyaran dakin nata hakana ko fenti babu amma ba laifi
kayan saiya haska dakin ya fito neat dashi nan aka zaune hira saratu ta samu bakin
fadawa yar uwar sakon mama din tana fadin ai kingani yanzu dai sai ki san zamanki
da mijin nan naki.
Yau badon ya J ba da kunyan duniya yaciki kan mijinki donshi ko a jikinsa bai
damu da halin da kike ciki ba balle yayi tunanen hakkinki yana hannunsa ba ya
fidsake kunyan hakan.
Bari saratu har kunyan jafar nake ji idan na tuna da abinda ya faru yadda mukai
ta sakin magana a lokacin kan kudin nan amma hakan baisa yayi fushi dani ba sai ga
hawaye na zubo mata.
Tana kuka saratun tace ai mama zaki godewa tunda ita ta tsaya yai hakan don
badon mama ba wallahi Ya Habu ba zai bari ya kalleki ba mamace ta datse shi yai
hakan .
Muryan inna da basu san da zuwanta wajen bace tace ko yaya ta saka yayi in baiyi
niya ba aiba zaiyi ba.
Ji inna don Allah saratun ta fada tace kwarai ku dai godewa Allah daya bamu
Jafar a cikin mu wallahi ya kamata a dubawa bawan Allah nan irin kokarin da yakeyi
din kan yan uwa.
Bawai dakinku ba kawai duk wani abu na gidan nan yanzu Jafar ne jigo ko wani daki
kuma ko haihuwan matan isah shine ya aiko da komai da akayi ga hadin kan yan uwa da
yake kokari yi a yanzu.
Barakha a cikin kuka take fadin ai gaskiya inna ta fadi saratu ko mama ta saka
yayi inbaiyi niya ba aiba zai min ba ko ?
Ni sai ince auren nan na jafar alheri ya zamo muna yanzu wallahi tunda kan gida
ya haduwa ta dalilinshi ba kamar baya ba da kowa yake a watse gidan.
Wanan zancen da inna tayi bai kwana ba saida saratu ta faki ido taje tayi waya da
mama tana zuzuta maganan ga abinda ya dace ta fada ta tsaya tana haddasana a
tsakaninsu kuma.
Washegari dasu da yaran anty baraka din suka taru suka kara gyara gidan tsab da
wasu makwabta aka dora girki ta saka les din da mama ta aiko mata dashi ta hanyar
saratu.
Wanan yasa duk wani iya shegen da aka dau damaran yi ba samu yiwa barakha din
ba don dan uwanta da yafitar da ita kunyan duniya lokaci guda.
Sai ga kayan kallo da frdge sabo ibrahim ya shigo dashi haba anty Barakha a
gaban yan unguwa tasa sabon kuka tana fadin Jafar jafar yau ka zamo min uwa da uba
a cikin duniya na gane ba abinda yakai dan uwa dadi a duniya.
Dan Uwa Murfin Jallo
Ya J ya dinke wanan wanjen sai kuma wani.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
5️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
A cikin kwana biyu yaya Jafar yayi wani irin rama lokaci guda na kula da hakanne da
safe dana sameshi a dakinsa zaune yana shafa mai zaisa kaya.
Bandai yi magana ba inda na karbi man ina fadin ya kawo na cika ladana bai kiba
ya mika min na shiga shafa mai a cikin sallo da hilla irin ta zolaya yana lumshe
idona na gama na zabo mai kayan da zaisa naji yace dani .
Rahama da kin bani kaya mara nauyi in saka zaifi don ba ko ina zani ba yau zan
daije gida in dubosu don Asmau ta bugo min waya jiya wai idon jaririn yana ciwo
kuma.
Amma iya tace normal ciwone da akasarin yara keyinsa lokacin haihuwa zan dai je
nagani idan zamuje asibiti dashine a dubashi yau.
Allah sarki yaro ke nan ya shigo duniya ya fara karo da matsalolin rayuwa ke nan
yanzu Allah ya bashi lafiya ai iya zata san hakan tunda sun saba da ganin hakan su.
Na taimaka mashi ya zura rigan a jikinshi ya tashi muka fito falo ya zauna muka
karya dashi din yau ba zaki fita ba ke nan nace sai zuwa shabiyu zan leka don banda
lecture da safe.
Zan dawo in kaiki ya fada nace zanbi motan kasuwa ai ka huta da sauri naji yace
no don Allah kada ki soma banson hakan ba mutuncina bane aga matata a cikin motar
haya.
Ya mike tsaye yana fadin dolema in koya maki mota ai don gudun haka koda ibrahim
bai gari zaki iya fita ke kadai ina ganin hakan zaifi sauki amma banson zancen
shiga motar haya din nan tunda Allah ya hore min abinda zan iya saiwa kowan ku mota
a yanzu.
Nidai yadda naga ya dauki zancen da zafi yasa bance kalla ba koya min mota kuma
na yaushe nidana koya a abuja kuma saidai naja bakina nayi shiru bance komai ba.
Yaje can gida din dubasu nan suke magana kan yaron dasu iya yace a dai bari ya
kaishi asibiti a dubashi inda abinda zasu bashi.
Saidai yadda ya samu maijegon a jagalce ana mata kumshi da kitso yasa rai bace
yace da kanwarta ta dauko yaron suje asibitin dashi da salima.
An duba yaron an bashi magani suka dawo ya ajesu ya juya ya koma gida lokacin
harna shirya ina jiran dawowanshi don har lokaci yaso ya kure min.
Gaskiya da ba don irin hakan ana ganin tauyewa bane da sai ince nikan gaskiya
haka yayi min daidai a gidan miji don irin zaman nan bakama tuna kana da kishiya
sai idan kasawa ranka damuwa da hakan.
Hausawa sunce kazantar da baka gani ba sunan shi tsabta to ban gani ba ban kuma
damu da in sani ba tsakanin rayuwan can gidan da iyalinshi don haka nake jin kaina
kamar banda kishiya duk da ba,a cika baki da zancen namiji da sai ince nidai a
yanzu na cika ban sanarwa gaba dai idan zama yai zama a tsakanin mu abinda zai biyo
bayan zaman namu nan gaba.
Duk haukan saiba hankalina sam bai daga ba da rigimar ta don hakane ma na yanke
shawaran ko ranan sunan ba zanje gidan ba duk da naga alaman hakan shima agareshi.
Yadda yar uwata take tayar da hankalinta kan aurena da ya J ni a wajena sam
abin ba haka bane kila dai don tana cikinsu tana gani kuma tana jin irin barazanan
da sukeyi a kaina ne hakan ke daga mata hankali nikan a waje a yanzu da saiba ta
gwada min hakan muka zoje da ita ko darrr kuma banji yanzu a kansu kamar farko da
nake da tsoron a zuciyana.
Dama ance da ka bari a raina ka kayi taba kishiya tsoro da mataki yafi ka fito
kana sa,insa da ita a gaban miji irin hakan raini saiya shiga tsakaninku da ita
gashi kuma yanzu na gani a kaina hakan gaskiyane.
Haka kuma na yarda samun waje ga mace yana fitowa daga matsayin da miji ya
daukeka dashine tun farko.
Don sai ince yaya J bai bada daman da wani nashi zai kawo raininsa wajena ba don
nasan da zuwa yanzu tuni mun gwada hakan da anty Saratunsu din tsakani da Allah dai
ita bata kaunanane a zuciyarta don sai ince tafima kishiyoyin nawa daukan zafi
dani.
Nata sam bai damuna don bankula ta ba balle wani abu ya shiga tsakanina da ita
don koda naje gidan banda gaisuwa ba abinda ya hadani da ita ranan .
Ina kallonta yadda take bina da kallo mai kama da harara wanda ko wace take
tayawan saiba batayi min irinsa ba a fuskanta don ita saiban banda shigan da nayi
na samu suna fada a kaina bata yarda mun hadu ba a ranan don haka bancewa tayi min
don da mijinta ta tsaya fadan da takeyi din.
Karfe hudu ya daukoni zuwa gida inda na koma na samu tarin sayayyan da yayo na
abinci nasan don in hakkura da school a ranan.
Daki nashiga dan sallah inda na samu period dina yazo min don haka na watsa
ruwa na fito na shirya kaina saiga kiran anty salima take fada min gobe zasu shigo
nan zasu kwana don aikin da zamuyi din mun dan kai wani lokaci muna waya don ita
idan tana waya bata gajiya da surutu koda baka bata amsa kuwa.
Haka nake ganin ta daukeni kamar aminiyarta a rayuwa don tun ba zancen auren dan
uwanta akaina ni kadai take fadawa damuwata in kuma bata shawara yadda ya dace da
zancen.
Saidai sam duk da ta girme min a shekaru ban yarda zancen mijina yana hadani da
ita ba ko taso bugun cikina akanshi nakanyi dariya kawai in basar da zancen a
wajenta.
Mun gama na fito falo zaune na sameshi yayi shiru kamar me tunane har saida ya
ban tausayi a raina ba karya koda na zargi hakan akwai damuwan yan uwa dana iyali a
zuciyar bawan Allah nan saidai baida wanda zai fadawa danuwan nasa yaji sanyine
kawai yake bari a zuciyarshi.
Har na tako zuwa inda yake na shafa kanshi kamar yadda anty salma take min hira
idan D dinta yana cikin damuwa itace takan zauna ta kwantar mai da hankali har ya
gamsu ranan kuma biba bata nan don tace zataje gidansu kitso da kumshi daga school
don haka ban sa rai da dawowanta ba don haka mu biyune kawai a gidan lokacin dagani
saishi a lokacin.
Ajiyan zuciya naji ya sauke yana kamo hannuna zuwa jikinshi na biye mashi na
zauna saman cinyarshi ina fadin .
Tunane yaya na kula tun shekaran jiya baka cikin dadin rai ina fatan dai bani
bace nayi ma laifi haka don Allah ?
Murmushi yayi yana gyara zamanshi ya dora kanshi a saman jikina yana fadin me
zakiyi min Rahama da zai bata min rai kawai dai akan matsalan mu dasu mama kika
ganni haka a kwanakin nan.
Subbahanallahi na fada na zare jikina daga nashi nakai zaune saman kujera ina
fadin har me yayi zafi haka yaya kaida nasan kana kokari akan kowa naka ?
Kema da kika shigo rayuwata a yanzu kin fahinci haka tun yanzu balle su da aka
haifemu a tare yanzu fissabillah za ace mama kawai yayanta mata ta damu dasu muko
mazan ko oho ?.
Duk da wani lokaci nakanyi tunanen kamar hakan ba laifinta bane laifin kawune
yake kokarin shiga tsakanin ya rabamu da mahaifiyar mu a fakaice amma mama din bata
gane hakab ba.
Kawu kuma amma gaskiya da bai kyauta mata ba tunda shima aiya haifa kuma shima
naga kuna girmama lamarinsa gwargwado.
Yanzu ki duba akan yaya barakha ta sani a gaba dazun nan saida na nuna mata
raina ya baci duk abinda nayi Rahama wai ace mama bata gansu da hakan ya ake son
inyi don Allah ?
Matar nan tazo garin nan da cin mutuncu na cinye masu kudin gadonsu dake
hannuna ita da saratu suka tada hasumin sai in fito masu da kudinsu in basu suma
suna bukata.
Na basu kudinsu cikin salama ta dauki kudi takaiwa mijinta ya cinye ya kuma dauki
mata kishiya Rahama banyi fushi ba tunda naga ran mama din ya baci na tayar dasu
yaya Ai suje suga halinda take ciki ko zataji sanyi da zuwan su din.
Bayan sunje din suka bugo suna fada min labari ba dadi na bayar da kudi asaya
mata duk abinda ya dace anyi din tun jiyan wai amma kuma mama saita nuna yanzu
meyasa na tura su yaya Ai da inna ?
Don Allah hakan kuma laifine wai suwa zan tura idan basu ba amma sai mama ta nuna
wai nayi hakan don in fallasa asirin sakintane kawai ?
Umm,umm gaskiya akwai dai kila wani ya fadi wani abu kan zuwan nasu har bataji
dadi ba ta nuna hakan na fada ina kallonshi.
Naji tace wa zai fada banda yar banzan nan saratu data bisu nima hankali akanta
yaje direct don nasan itacema zata fadawa mama wani abinda ranta zai baci don ban
yarda na tura mata kudin sayayyan ta account dinta kona barakha din ba.
Amma ba komai idan bakin cikinsu ya kasheni ai kowa zai huta sai su nemi wani
kuma su kadarmashi zancena da Saiba nace ta tafi gidansu amma mama tace bata zuwa
ko ina Rahama ?
Haka zan zauna da mace a kullum ba ranan shiryuwa a gareta sai cin mutunci da
tonon asiri ina duban saboda iyayyenta nayi hakkuri na kai wanan lokacin da ita
hakana yanzu kuma matakin da nake son dauka mama ta hanani daukanshi akanta ya
akeson inyi don Allah ?
Nikan gabanane ya fadi da jin furcin mutuwan daya kirawa kansa nasan abu yakai
mai ko ina a rayuwansa tunda har ya furta hakan .
Cikin dan marairaicewa nake fadin don Allah yaya kabar ambato mutuwa akanka
yanzu in ka mutu yanzu nima ai zan mutu ne nasani .
Murmushi yayi yana shafo fuskana yace Rahama baki son in mutu ne mutuwa ai dole
ayishi tunda munzo duniya ko ?
Shiru nayi ina tunane tare da jin wani zafi yana fita min a jikina lokaci guda
ni kadai nasan irin tunanen da nayi cikin dan lokacin kafin muryanshi ya dawo dani
da yake fadin.
Ba lafiya ke jikin nan nawa ba amma mama ta kasa gane hakan karfin hali kawai
nakeyi Rahama kike ganina a tsayen nan amma nina san abinda nakeji.
Naje asibiti har nagaji amma likitoci sai suce dani banda matsalan komai a jikina
donshi na fawalawa Allah lamarin a yanzu amma idan ka ganni haka sai ki dauka mai
lafiyaneni a tsaye.
Har lokacin na kasa magana sai wayan da nake latsawa ina neman lamban Dage daya
fado min a rai lokaci guda nayi sa,a ya daga na fara magana a cikin yaren mu dashi.
Da farko fada muka soma yana fadin naje birnin zaria na mamta dashi cikin wahala
bai dauka rashin mutuncina yakai haka ba ai ?
Ace har aure hardo ya daura min amma ban nemesa ba ga baffa yanzu ba lafiya ke
gareshi ba shima dai a tsaye yake dai.
Nan dai na bashi hakkuri na nuna mashi nima bansan da zancen auren ba yadda yaji
haka najishi ban sani ba shine ma yanzu na kirashi akan mijin nawa ai don baida
lafiya a jikinshi.
Yace Jam jam Anini kada ki auri gawan fari fa nace ba akai can ba yayana Dage
tunda ina da Allah dasu ai hakan ba zai faru ba in sha Allahu.
Sai ya dirka min zagi yana fadin ohho yar damcen uwa taga kudi taga wajen ci ku
kadai kecin kudin ku sai mahaifiyar ku da yan uwanku duk da nasan ba karya ya fada
ba amma nace wani kudi dage in akwaisu ai kasan tare dakai zamuci.
Ni dai yanzu kiranka nayi daka taimaka min ko da wani abu da zaka bamu ko nawane
zamu turo maka dashi yanzun nan yace koda Fam dari nace Anini ?
Wucema hakan ai Dage kai din ai dan uwanane banda wanda ya wuceka dage
donshinema na nemaka yanzu ai ?
To ki kwantar da hankalinki ina kuna da dawakai a garin ku nace kwarai kuwa ba
za a rasasu ba in sha Allahu tunda akwai sarakai a garin .
Dadina dake akwai kiran Allah to ku nemo ruwan da doki yasha ya rage