Showing 315001 words to 318000 words out of 328222 words

Chapter 106 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

gaskiya.
Ya shigo ke nan mama zata fita suka hadu a get Aminu zai rakata sarakuwarta ta
haihu zata ganin jariri yace barin kaiki mama tace a,a malam kaje ku gaisa da
iyalinka tun jiya ta damu bata jika ba jeka na yafe maka harga Allah ga Aminu nan
zai rakani in samu mota.
Hakan yasa basuje tare ba lokacin ya shigo ina falo don ban koma ciki ba yake
sallama na amsa tare da gaidashi yake fadin kun jini shiru ko jiya?
A kasalance na juyo ina fadin nina dauka baka garine ai don baka hakan ya kai
zaune bayan yagamawa yaron dake bayan biba yana barci wasa ya juyo yana fadin.
Ina nan ina jigilan wacan gidan jiya dai su Asmau sun tare a sabon gida ita da
yara saura wanan idan na samu kudi ko a gyara maki ko kuma a gina wani don nasan ba
zakisu zama a cikinsu ba ?
Murmushi nayi na mamaki nace gida ka gina masu ashe yace an dade da ginasa ai
gyarashine ban gama ba dama yanzu kuma an gyara din.
Wanan kudin dana aje wanan gidan kwanaki aikin gidan nayi dashi kada kudin su
salwance min ban more masu ba shiyasa ban fadawa kowa ba .
Sallaman Aminu da Salima ya hanashi cigaba da magana inda ya juya yana fasin au
salima kin karaso kinga na manta munyi waya dake fa yanzun nan kince kina tafe.
Suka gaisa ta juyo ta gaisa dani nake mata takoma lafiya jiya tace lafiya kalau
kedai na koma na iske rigima yaya ashe zaka kwashe baka fadawa kowa ba.
Na koma na samu saiba na fada da mama tana fadawa mama maganganu muna tsaye
saiga kawu kuma ya shigo duk basu ganmu ba dani da Hauwan ya yazid a duhu.
Nace barin shiga shine fa na samu wani zance da kawu ke fada na ban mamaki amma
sam mama bata damu da kalamansa ba balle ta tambayeshi me yake nufi da shiri ya
baci wai ?
Shirin me ya baci shima dan uwan ya tambayeta tace waya sanar mai yaya akwai dai
abinda haka ke nufi ina fadawa iya ta mike ta sameshi cikin fada tadai kwashe duk
yadda akayi ta fadawa dan uwan nata.
Ina zaune ina sauraren ikon Allah ya nunani yace kin ganta nan itace mafarin
lalacewan komai garesu yanzu idan kin kula tun shigowan Rahama rayuwana abubuwa
suka canza a gidan nan.
Dago kai nayi da dauri ina kallonshi yacigaba da fadin shiyasa kike ganin basu
shiri da ita yana zuga mama akan Rahama tana hawa tana zaunawa tare da wanan
shashashab Saratu.
Ya san komai a yanzu matukar Rahama tana tare dani ba zai taba cinma manufarsa a
kaina ba yasa kikaga ya koma kamar mahaukacin zaki yanzu.
Nasani Salima nasan komai har abunda shi kansa bai sani ba duk an fada min duk
ciwon nan da kikaga inayi Allah ya nufa sai nayi amma da hannun kawu a cikinsa.
Ta kwalo ido waje cikin tsoro tace mayene ke nan ko yace ba maye bane amma yana
kama dashi don mugun mutumne sosai wanan matar nasa ta halakashi da yawa.
Ba zan boye maki mamace basu so da karuwa sun kulle bakinta ba zata iya magana
ba akansu koda ta gane abu saidai ta bisu kawai ba zata iya fada akanshi ba.
Salima abu tun muna kanana akeyinsa har yanzun kuma basu daina ba ki rabu da
wanan matar na kawu kawai ba mutumiyar arziki bace duk ita ta jawo wanan abin sam
da ba haka kawu yake ba ai daga bayane ya koma hakan.
Zan fada maki wani magana yau don irin hakan nake son na kakkabe Nusaiba tun
yanzu a rayuwana.
Sam ban ra,ayin maiyin shirka mai hada wanin Allah da Allah yana ganin shine
daidai na tsani wanan rayuwan tun ina karami salima na tsani masu irin halin bin
boka da malami sai gashi na tsunci Nusaiba dumu dumu da wanan rayuwan.
Zan iya hakkuri da halinsu in zauna dasu hakana amma banda zuwa wurun boka ko
malam gashi har takai ga koyawa Saratu wanan rayuwan .
Yana da wuya idan ka fara ka bari donshi kikaga gaba daya a yanzu dana samu kaina
ban iya taimakawa kawu ko kadan .
Wayan da aka kirashi yasa ya fita daga falon ta nisa tana kallona tana fadin
Rahama na suma a zaune ashe yaya yasan komai da sukeyi saiya nuna kamar bai sani ba
?
Tun dai gabanin auren nan da saratu zatayi sune har zuwa katsina wurin malamai
subbahanallahi na fada tace wallahi.
Gashi sunje din kuma abubuwa sunki dadi ga auren kullum cikin bugo waya take tana
kuka ashe gidan yawane matan shi hudu kuma dukka zube suke a gidan gado tare da
iyayyenshi da kowa nasa duk a babban gida kamar ace ku matan yaya dasu marian ki da
hauwan yaya yazid da matan su yaya Auwal duka gaba daya.
Kirji na buga irin na bam mamaki din nan tace ai bashi ba duk kinga yawansu
girkinsu to a hade wai yake waje daya ake girki gaba daya har kowa gidan.
Ance yara cakwal ba iyaka kowa kuma a wanan tukunyar zaici nace innalillahi ai
zaka halaka ato ai tagani nan da aka auroki aiba abinda bata fada ba akanki
lokacin.
Yanzu ita gashi ta fada ga wanda yafi naki sau dubu hankali ya tashi saiban da
take tayawa kuma yanzu itace ke gulmanta ranan ina jin tana fadawa wata kawarta
tana dariya .
Shigowan yayan nata baisa ta fasa maganan da takeyi din ba har saida ta kare yace
dama idan kace hassada ka iya sai Allah ya barka da dabaranka.
Ni tacewa Rahama da kurciyarta kwadayi yasa ta aureni tsoho ita tana kamar
Rahama bata ga kwadayin da zai kaita auren mai mata ba.
Duk ta dauka duk abinda da take fada banji irin abinda take fada ba ai shiyasa
yanzu na sakawa yar iska ido ai .
Allah bai hana min abinda zan kama mata haya ba a garin sokoto yanzu amma na
kyale yar iska ta dandana barnanta taji.
Haka mama nason muyi zancen da ita amma sai in zame mata sam ban yarda an zauna
dani ayi wani magana ba game da ita.
Ko shekaran jiya tunda safe ta kira mama tana kuka injinsu nayi kamar banji ba
lokacin dana fada mata gaskiya ai wucewa tayi tana fushi dani wai kazafi ake mashi
ba gaskiya suka fada ba.
Su yaya Ai ne zasuyi mata kazafi ko mama hafsatu mama ta goyi bayanta sukaci min
mutunci a lokacin.
Ni zancesu ma ya hana in tambayi yan sabon gida wai wayaga Asmau cikin sabon
gida Allah yasa dai ta daina kazantar nan nata .
Yanzu fa kika gama maganar wata na munafuncin halin ya bita ke kuma gashi zaki
dora na anty Asmau tun ba a daga ba ?
Ta kwashe da dariya tana fadin bari Rahama abinsune sai addu,a don ban taba
ganin kazaman mata irin Asmau da Nusaiba ba.
Lokacin mama da dan sauranta ai ko sunyi abinci bata iyaci saboda kazantarsu amma
yanzu ni banma ko kula ko tana ci tunda ko yaushe Nusaiba suna tare tunda Saratu ta
tafi.
Ke dai bari ana abu a duniyan nan wallahi yanzu ai zan je naga gidan da yaya
barmu da mamakinshi ace har an gina gida kowa bai sani ba ?.
Habu ya sani don tare na fara ginawa da nashi dana yazid lokacin daya samu
matsalan nan yasa ya karasa nashi da kanshi amma tare aka soma aikin gaba daya.
Dama yaya kai ka ginawa yaya habu gida ashe amma ban taba jin wani na wanan
maganan ba sai yau daka fada to kibarshi nan inda kikaji.
Shima yazid insha Allahu zasu koma a nasu kwanan nan kafin yacigana tace to yaya
gidan mu fa yace nakune mana salima dake da mama da barakha da saratu ku hudu za a
barma shi.
Binshi tayi da kallo ba ita kadai ba harni dake tunane da fulanin mu ke fadin
dan uwa MURFIN JALLONE daya baiyi saida dayan komai bacin zumunci kuwa ga mutum
wani abin don dole saida dan uwanka na jini.
Wanan kalman tun bayan komawan mu wajen baffan mu nake jinsa idan gorinsa ya
tashi a kanmu zaice shi dan uwan mahaufinmune na jini don haka mun zamo mashi
marfin jallo a yanzu don ba yadda zaiyi damu .
Tare suka fita don kiran da akayi mashi yace gashi tafe suka tafi suka barni da
mamaki da yawa a zuciyana har na rasa wani zan kama a ciki don abubuwan mamaki naji
a dan zaman nan da mukayi lokacin.
Daki nashigo tun bayan fitansu muka kwanta da Amir nake wanan tunanen ranan da
yake nasan mama bata gida barcina nayi sai bibane tayi muna dahuwan da zamuci.
Ban fito ba sai wajajen biyu da rabi ukku saura nafito daga daki koshi kukan Amir
ne ya tayar dani sam ban iya kiran sunan gatsau don sunane mai tsada a ga kowa yasa
na laoerl
akawa yaron Amir.
Koda suka bar gidan can suka nufa su yaya Auwalne sukazo dukkamsu ganin sabon
gidan don kowa bai san da zancen ginan nasa ba bayan habu shi kuma ba magana yakeyi
ba haka yake dunkum a cikin yan uwa ba wani sakewa sosai dashi.
Sun zagaya ko ina sun duba suka dawo falo suka zauna duk da gidan bai gama jin
kayan alatu ba amma ya hadu sosai yayi kyau ga abinda aka saka a lokacin don ginan
kawai abin kallone .
Yaya Auwal ya dubi salima yana fadin ke kira min Asmau ta mike zuwa kiranta din
bara jima ba sai gata ta sake gaidasu a matsayinsu na yannin miji da kuma yanninta
na cikin unguwa da aka taso a waje daya.
Ya nuna mata waje yana fadin zauna magana zanyi dake a gaban kowa yaji ta samu
wuri ta zauna a tsarge ya soma fadin to Asmau nasa a kirakine a matsayina na
yayanki tako wani bangare.
Munzo munga waje masha Allah abu yayi kyau sosai Allah yasa afi haka a rayuwa
muna fatan hakan akoda yaushe don Jafar mutumne da kowani mahuluki dake tare dashi
zai mashi wanan fatan.
To amma ke kuma ina rokonki da ki natsu ki gyara halin nan naki da kowa ya
ahedeki dashi na kazanta da son jikin banza.
Duk da Jafar yayi hakkuri yana kuma kanyi kuma bai taba kawo karanki kan ya gaza
dake ba kema haka to ina son ki sani ba zamu saka ido kina cutar da dan uwan mu ba
don son jikinki.
Jafar namune kema tamuce a yanzu don koba aure akwai hakkin makwabtaka daya zama
zumunci tsakanin gidan mu da gidanku a yanzu donshi nake gargadin ki wallahi in har
baki canza halinki ba Asmau zan shayar dake mamaki sosai wallahi.
Ganin kallon da yan uwan ke mashi yace wallahi kwarai da gaske don sai tabar
gidan nan wallahi kuma in saka Jafar auro mata biyu a lokaci daya su maye ko ina
yadda ba zata dawo gidan nan ba.
Meye ranan kazanta don Allah kun tauye yaro ba dama ya dawo gidansa ya huta wari
da ganin takaici ya hanashi zama don tsaban sakarcin tsiya kawai yayi mata tas a
gaban kowa tana hawayen munafunci.
Bashi ba duk wanda yazo gidan korafin da yake mata ke nan ko a gabanshine kuwa za
aja mata kunne akan kazantansu.
Ni dau bance zanje ba tunda batazo nawa gidan ba idan ita watace mai lissafi ya
kamata ace da muka dawo asibiti ko daga gidansu tazo ta duba jikina ai ?
Amma sai ta share wanan yasa nima na sharesu ban kula da inje in gano ba ga kuma
kummalon mata da yake cina a zuciya duk da gidana baida wurin da ya kasa amma wanan
halin matane ko yayane sai naji wanan abin koda kadan ne kuwa.
Ita kuma saiba da tambaya da yake mutane da munafunci saida ta samu wanda ya nuna
mata gidan ta tafi ya riga dayayiwa maigadinshi magana don yasan zata aikata hakan
yace koda wata tazo ya nuna mashi photonta yace kada a bari tashiga.
Donshi washegari ta juya ya koma son zai fitane lokacin sunan Amir kawai ya
tsayar dashi sai zancen tarewansu wanan gidan kuma yazo.
Tana zuwa maigadi ya shedata yako hanata shiga gidan ashe harda shirginta ta
kwaso nan ko maigadin nan ya rufe get ba ita ba duk wanda yazo a ranan sanadinta ya
hanashi shiga gidan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA


[6/12, 05:57] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

9️⃣8️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Karfe biyar na yamma ta shigo garin zaria a by pass ta sauka ta nemi shatan mashin
zuwa gida kai tsaye tana bin ko ina da kallo.
Kofan gida ta sauka bayan ta gyara mayafin kanta da kyau don kada a shedata don
ita kanta tasan ba daidai take ba balle wani ya ganta a hakan .
Dakatar da mai mashin din tace tana zuwa bayan ta dan shiga da kayanta ciki
kadan tafiya take tana bin gidan ko ina da kallo indai ba idonta ke mata karya ba a
yanzu sai tace gidan nasu a yakuce yake kamar babu kowa dake zama a cikinsa yanzu.
Daba don sautin karan tv dake aiki shiyan Yazid da shine fara isa ba da taja da
baya ta koma waje don sai tace gidan kaf babu mai zama cikinsa yanzu.
Cikin sanyi jiki ta karasa kofansu ta dan buga tanayi tana waigen kayanta data
baro a kofa don kada mai mashin din ya gudu dashi a tunanen ta uwar zargi.
Bugun kofan da mama dubu taje ga kuma muryan saratu dake kiran sunanta da mama
yasata mikewa da sauri zuwa kofan ta bude.
Itace dai saratu din ce a tsaye tana ganin uwar take fadin mama akwai dubu biyu
in biya dan mashin kudinsa bata samu magana ba illa juyawa da tayi ciki don dauko
kudin ta mika mata.
Jun maganan su yasa salima bude kofan part dinsu ta leko tana fadin umm,ummm
saratu dama zaki zone bamu sani ba tana magana ta karaso wajen ta kama mata kayan
data jawo niki niki zuwa ciki.
Ban karya ba tun safe wallahi ta fada ta nufi kitchen din mama da salima suka
dubi juna suna mamaki akwai abinci shi ta debo tare da ruwa ta nufo falon.
Ta zauna ta fara ci duk sun kafeta da ido yadda take aika cibi a bakinta kamar
mayunwaciya sai lokacin mama ta nisa ta soma fadin wai sararu lafiya kuwa ta dauki
kofin ruwan data zuba tana fadin ba dai kun gani ba mama ku godewa Allah dana samu
kaina gida a yau.
Ta duka taci gaba da cin abincinta can kuma saiji duka ta fashe da kuka mai
karfi irin na tashin hankali din nan da sauri salima ke fadi ke kuma daga magana
sai kuka ai saiki dagawa mutane hankalisu kuma ?
Ni take son ta dagawa hankali bayan wanan da nike ciki yanzu ace mutum baida
kwanciyan hankali akan yayansa duk kokarin da nakeyi kanku karshe irin abinda zan
gani ke nan kuma ?
Da wani zanji da zancen yan uwanki da suka juya min baya suka bi matayesu koda
naki dana yar uwarki barakha ko salima dake gabana ba aure ?
Mama ai gara salima da bata da auren hankalinta da nake a kwance yake nida suna
nayi aurene fa tunda naje ba kwanciyan hankali kullum cikin tashin hankali da
fargaba nike wallahi .
Tana kuka ta shiga labarta masu irin abindake faruwa ta basu labari kaf na irin
zaman da takeyi gidan aurenta da abubuwan daya faru da ita a can din.
Salima ta nisa tana fadin wai wanan lamari dame yayi kama don Allah sai kace wa
yanda akaiwa baki kamar mu kadaine a duniya yau a tashi da wanan gobe wancan za a
tashi dashi kuma ?
Ga wanan sakaran taki barin gida sai fitina takeyiwa mutane kuma yaya yace bai
mayar da itakuma ta zauna tana hauka akan sai ta koma sabon gida itama.
Ta saci kallon uwar tana fadin kici abinci kije kinyi wanka ki kwanta ki huta in
kinyi sallah har su yaya su dawo dan basu garin nan gaba dayansu ba kowa garin nan
suna wajen tafiya.
Salima kona kwanta ban iya barci yanzu sai inga kamar za a zo min da sabon
fitina kuma wallahi na gaji niba zan koma gidan nan ba kuma .
Ki daiyi hakkuri yanzu ki huta kafin su dawo asan abinyi akai amma don Allah ki
daina wanan kuka haka kina daga muna hankali in kina wanan kukan ?.
Kallon salima din mama tayi don tafita karfin hali a lokacin don ita jikinta ya
gama mutuwa da zancen tana zaune tana ganin kamar a mafalki take gani saratu di a
hakan.
Hankalin salima duk ya tashi auren har yaushe akayishi da yar uwarta zata koma
haka ba dadin gani da badon tasan waye saratu ba da sai tace gaskiya hakan ba zai
faru da ita ba.
Sun zauna shiru falon kafin saratu ta kawar da shirun da tambayan naga part din
su yaya kamar ba kowa mana ?
Sun kwashe sun bar gidan nan ai suna sabon gidansu daya gina sabon gida yaushe
ya gina gida kuma bayan tafiyana ?
Waya sanar mashi ance gidan ya jima ashe yana aikinsa bai fadawa kowa ba sai
yanzu da zasu tare shida iyalinsa shidasu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login