Showing 234001 words to 237000 words out of 328222 words

Chapter 79 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

sheganta masu cikin su duk da kowa yasan abunda take zuwa
yi kaduna lokacin.
Haba haba kada ka biye masu a zama daya mana kome mutum yayi don kansa ai ba za
a biye mata a zama daya ba .
To tabari yarinyar nan dai bata shiga zancen ta don haka itama ina son tafita
zancen ta tun muna sheda juna tsakanina dasu a gidan nan .
Ranan naga haukan kannan miji a gaban kowa akai tujara har saiba na fadin ashe
su ake cuta da aka hansu kwana daki dashi ansan abinda aka kulla ayi yasa aka
kakabesu da karfi da yaji karshe dai yazid yai tsaye yace.
Wallahi bata kwana gidan idan kuma mama tace sai takwana sai ya kusa kasheta a
ranan hakan da tajine yasa ta fice daga part din.
Don daga inda yaya yake kwance shima bakinsa bai mutu ba a ranan fadi yake
matatace nayi abinda nake gani daidaine a gareni anyi din kije kiyi duk abinda
zakiyi.
Yana magana kamar zai daga daga inda yake kwancen ya karaso gareta ganin da mama
tayi auren saiba zai iya mutuwa yasa ta izata zuwa wajen.
Nan Yazid ya dage kan lalai sai tabar gidan a ranan inba haka ba sai ya halaka ta
dole da yamman nan ta nade tabar gidan don tdoron yadda taga yana kokarin cin mata
a lokacin.
Bani ba har yar uwata tayi koka sosai da tsohon cikinta don a yanzu tana cikin
watan haihuwantane ummah muka iya kira muka sanar da ita abinda ake ciki tace tana
zuwa.
Ashe daddy ta kira abuja ta fada masu saiga kiran mummy tana fadin mu shirya gobe
zasu zo su tafi damu duka idan basu son mune suda suka haifemu sun san darajan mu
ai.
Hakan ne ya faru don kamar hadin baki saiga iyayyeb Saiba sun dawo da ita suna
bada hakkuri ana cikin wanan zaman su daddy da mummy suka iso tare da anty Salma.
Sai ummah da mijinta da suka shigo suma a tasu motar suka hade duka a gidan gaba
daya iya tace yau dubu kinkai ga yadda kike so ke nan
Don ba sassauci a wajensu daddy yace dagani har Yanda tafiya zasuyi damu tunda
uwar mazanmu ta nuna bata kaunarmu to abashi diyanshi ba zai barsu inda ba a
kaunarsu ba.
Nan mama ta fara kame kame tana salati tana fadin ita itace za ace tana nuna
halin kyara da hattara a garemu don bata kaunar mu ita saidai a dauki alhakinta ga
hakan.
Daddy da mummy sun kafe akan sufa tafiya zasuyi damu don amana muke a wajensu
don haka ba zasu saka ido ana tozarta nu suna kallo ba gara kowa ya kama gabanshi.
Banda kuka ba abinda nakeyi a lokacin dole aka shiga ban hakkuri ana tausan su
daddy din da suka hakikance lalai tafiya zasuyi damu.
Iya ta soma magana da fadin to dubu yaukan sunanki ya cika dubu don dubu ya cika
dake saidai ki sani yau ana daukan yaran nan su koma hannun iyayyen su ke kuma zaki
rasa dan ki guda tunda baki yarda da kaddara ba a zuciyar ki.
Dama irin ranan nan nake maki gudu ranan da hakkurin yaran nan da iyayyensu zai
kare a kanki ranan da zasu fito fili haka su nuna maki sun fahinci me kike nufi
dasu.
Ace ka zauna baka da tunane kai maganan yara kake amfani dashi duk abinda yaran
nan suka fada akan abokan zamansu ya zaunu a wajen ji dubu baki bincike sai dai ki
goyi bayansu.
Narasa me yaran nan suka tare maki haka dubu duk wani kyautatawa da akw bukata a
wajen yaro yaran nan suna maki shi a gidan nan amma baki ganin hakan ke abinda nake
maki gudu ke nan a kullum dubu ?
Yanzu dai Alh kuyi hakkuri kubar yaran nan a daku nan su don Allah tunda kowa ya
gane kuskurenshi cikin zancen nan a taru ayi hakkuri don Allah dama haka zama ya
gada wani lokaci.
Daddy yace ai yayi hakkuri amma tafiya damu ya zama wajibi a garesa tunda har
aka nunawa yarsa haka shiba zai lamunci hakan ba gara dai ya dauke diyansa ya tafi
dasu.
Mijin ummah na fadin kwarai tunda abu yakai har ana kokarin shegantawa yarinya
cikin jikinta ai gara kawai ayi hakkuri aje a zubar da cikin kowa ya kama gabansa.
Jam jam Alh kana dattijo bai kamata ka fadi hakan a bakinka ba ai kai mai bada
hakkurine cikin nan kasai ya ishi mu nan ishara don wani hikimace ta ubangiji ga
hakan.
Ace cikin nan bai samu ba saida yaron nan ya shiga irin halin nan haka kadai ya
ishi bawa ya kara yarda da lamarin ubangiji ai don Allah Alh kuyi hakkuri da zancen
tafiyan nan ku bar yaran nan a daku nan su zaifi.
Yunkurin da yaya Jafar yayi don ya sauko zuwa wajen daddy ya bashi hakkuri sai
akai rashin sa,a ya fado saman gadon saida yan uwansa suka tare shi hakan yasa
hankalin kowa a falon ya koma kansu kuma .
Ihu mama tasa tana fadin a ceceta don Allah kada ta rasa jafar don suman da yayi
a lokacin mahaifin Saiba yace to Nusaiba kin gani kinga inda fitinan kishi ya kaiki
yau ?
Rashin hakkurin ki ya jawo mijin ju zai rasa ransa saboda bakin ciki ke yanzu
wani dadi kikaji ga hakan don Allah ?
Ki tunafa mutumin nan Allah ke talkafe damu shine tallafe damu ta sanadinsa muke
a cikin gidan da muke a yanzu shine cin mu da shan mu amma sha shancun ki ya hana
ki natsu ki kwantar mashi da hankalin gidansa.
Komai ace nusaiba ce silla ke wani riba kika samu ga hakan wai haba dai baba ai
wanan kyautatawan tsakanin miji da matanw ba kuma sai ka fada a nan ba tunda
kowansu yanayiwa ai ?
Wallahi a,a don ni baiyiwa iyayyena hakan ba Asmau take fadan hakan cikin jin
haushin abinda taji din a lokacin don ranta ya baci matuka.
Ke yi shiru nan sulhu akeyi mama tudu ta fadawa Asmau din daddy yace tana da
right din da zatayi maganan ta yadda bai maki ba haka muma sai bai muna ba a
bangaren yata kinga ashe yarsu itace da riban shiya take fadan wani yazo ya rabeshi
shima yaci arzikin nasa ..
Habu da yazid suka fito daga dakin suke fasin ya samu barci don Allah daddy kuyi
hakkuri yanzu dai ai taji abinda take son ji haka kuma kowa yasan cikin nan da
ubansa tunda ga matakin da maicikin akaga ya sauka wajen sheganta masa cikin sa
din.
Magana ta gaskiya duk ranan data kara wani magana akan acikin jikin yarinyar
nan ta kwana da sanin zamata a gidan nan yazo karshe.
Nan dai aka samu aka lakashi daddu yayi hakkuri bayan ya kafa hujja akan duk
ranan da wani dan uwansu ko wata mace ta fadi wani maganan daba daidai ba kotuce
zata rabshi da maishi a rayuwansa


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

7️⃣3️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Yadda naga dare haka naga safiya a ranan don ko ban runtsa ba har safe tunda na
idar da sallah asuba na dauko wayata ina kiran maria.
Duk da banso hakan ba nasan tana fama da kanta a wanan lokacin saidai haka ba
zaisa ta shareni da yawa ba nayi magana tace mijintane yace ta natsu a waje daya
saboda laluran cikin jikinta da take fama dashi.
Tana dauka na hau kuka ina fada mata cewa ni zan tafi abujane nagaji nagaji ba
zan iya ba hakkurina yana gab da karewa a gidan nan yanzu.
Subbahanallahi meya faru Ramaah ta fada cikin rikicewa ta dora da fadin kun
sake wani rigimane kuma yau din dasu ?
Bamuyi ba zamu daiyi nan gaba kiris don har mama wanan karon zata san halina
tunda bata kaunan mu to wai meya hadakune haka Ramaah ?
Saidai kinzo zakiji na fasa ina kashe wayata a cikin takaici hankalintane ya
tashi dan jin mena fada a lokacin don tasanni da karfin hali tasan halina idan na
rikice kuma.
Hakan yasa ta kira mijinta Habu take fada mai akwai abinda ke faruwa a can gida
don na kirata hankali tashe har ina mata ikirarin cewa zan tafi abujane ko wajen
ummah kaduna.
Cikin tashin hankali yake fadin ohh lord mekuma ya faru matan nan basu bari a
zauna lafiya baga Yazid a gida ba na kuma fada mai yasa ido a kansu.
Bari na kira yazid din naji abindake faruwa zan kiraki daga baya da hakan suka
rabu ya kashe wayan yana dannawa yazid don kira saidai bai dauka sai wajen kira na
ukku ya daga suka gaisa.
Suka gaisa sama sama ya soma fadin yazid meke faruwa a gidanne baka fada min ba
ko dazun munyi waya da kai ai ?
Wani gida ke nan yace nan mana yarinyar nan Rahama amaryan J ta kira hankali
tashe tana kuka yace gaskiya ban sani ba dan uwa .
Amma zan shiga in bincika yanzu habu yace dole akwai abinda ke faruwa gidan don
dai ta kira a cikin kuka dazun nan har sun kare wayan zai kashe yace wait dan uwa.
Kodai akan cikin jikintane suke magana dama nasan za ai hakan saboda jahilcin su
irin na mata amma bari na shiga inji dai ?
Ciki habu ya fada cikin mamaki yace eeh ciki gareta mana kuma na bincika na J
din ne so me zasu tsaya sunyiwa rigima kuma ?
Matarsa ce ba zina sukayi ba don me hakan zai zama abin tashin hankali kuma har
su sakata kuka akan hakan su barta taji da abinda ke damunta mana ?
Ciki fa kace habu a hakan har ta samu ciki dariya Yazid din ya kwashe dashi yace
miji da matane fa meye kakewa mamaki kuma sai habu din yayi murmushi mai sauti yana
fadin no banyi mamaki ba ai amma nayi kabar guy din nan inda kaganshi gaskiya J
yakai dan iska haka ashe kana kwance haka ka dirkawa diyar mutane ciki ka barta a
cikin tashin hankali da surutun mutane.
Bari dai in shiga din inji kome ke faruwa ya daga daga kwancen yana zura
jallabiyarsa a jikinsa zuwa cikin gida.
Duk da bai saba ganinsu hakan a part din da safe ba yasan dole akwai wani abinda
ke faruwa ke nan da gaske saidai ana ganinshi kowa yayi shiru sun gaisa dasu mama
ya nufi cikin dakin inda dan uwansa yake kai tsaye.
Ya jima a dakin suna tare dashi kafin ya fito ya fice daga part din don yayi
nazarinsa baiga wani abin daga hankali daga gareshi ba don haka ya kyaleshi bai
fito mai da zancen ba.
Mama tudu ta sameni a daki ina kwance take fadin wai ba zaki tashi ki fito
bane kina daki tun dazun kin dunkule ai sai hakan yasa baki gane jikin kiba ?
Tsayuwan da tayi a kaina yasa dole na tashi na fito zuwa dakin kwanan mu inda na
samu yaya J din shidaya a dakin yana kwance.
Haka kawai naji ina ganin bakinsa tare da takaicinsa lokaci guda naji gaba daya
ban kaunar ganinsa a rayuwata
Saboda yadda zuciyana yake raya min duk wani kunci da tsana da nake fuskanta a
rayuwa kusan nace saboda shine nake ganin hakan a yanzu.
Banda ganin kutse da katsaladan din shigo masu rayuwa da matansa suke ganin nayi
haka kuma a yanzu suke ganin na yaudaresu ko ina ha,intansa nakwaso ciki a waje
nace shine dashi.
Abu dai da yawa suka taru sukai min yawa a lokaci guda bake ganin gusawa daga
nan din shine kawai mafita a gareni da zaisa in samu sallama.
Ina jin muryanshi yana badaniyan magana dani dana shigo hakan baisa na juyo na
kalleshi ba lokacin na dauki abinda zan dauka zuwa ban daki na shiga.
Nayi kuka sosai a ciki kamar yadda na kwana ina sharban kukan a lokacin gab da
in gama wankan naji zuciyana tana tambayana akan yata din da yanzu shi meye nasa a
cikin zancen nan ?
Da har na hada dashi nake fushi mutumin da ko a kwancen da yake yana nuna ina da
muhinmanci a zuciyarshi aiko bai cancanci nayi mashi hakan a yanzu ba wata kilama
wani abu yake so na shareshi baki kulashi anya kuwa Allah ba zai tambayeni dalilin
hakan da nayi ba ?
Ga mama nasihanta a gareni kullum idan mun kebe shine kada in yarda a ji kaina
da mijina inyi hakkuri dashi dako wani irin hali na daure kada in taba bari a san
tsakanin mu.
Yau kuma sai taji akan abinda ba laifisa ba suji cewa ina fushi dashi har mun
samu sabani a tsakanin mu nasan ranta ba zai taba dadi dani ba.
Kodana fito abin mamaki yana kokarin dagawa daga saman gadon da kanshi da sauri
na isa gurinshi nace kai kuma meye haka idan ka fadifa kaji ciwo.
Maganan kamar an kwatoshi daga bakinsa yake fadin me akai maki meya faru naga
kinyi kuka binshi nayi da kallo nace ina turu baki gaba ni banyi kuka ba.
Ya koma ya zauna yana nishi na juya zan nufi wajen kayana haka kawai aka banko
kofan dakin kamar a cikin fushi duk muka bi kofan da kallo cikin mamakin ko waye ?
Saiba ce tana wani huci a fuskanta tana ganina taja tsuki tana fadin ai duk
abinda mutum keyi a boye Allah naganinsa kuma ba azzalumin kowa bane.
Inma wani kato yaba yarinya ciki take kokarin dafawa mutane sai Allah ya baiyana
maishi ta nufi wajensa ta aje kayan abincin data dauko na karyawa.
Ban kulata ba yi nayi kamar bansan ta shigo dakin bama a lokacin don ko
gaisawan dole da mukeyi da aka tillasta munayi a tsakanin mu bamuyi ba a lokacin.
Kokari nayi na taushi kaina ban kula mata ba na juya na fita bayan na saka
tufafi a jikina nakai kofa take fadin iskancin banza sai asirin yarinya ya tono a
gidan nan.
Azo ana daga muna kai ashe ba class ba aji nakowa clininc cema kowa ya hau ya
wuce hakan data fada yasa na tsaya na juyo ina fadin komai zaman mutum nakowa
ubanki yayi kadan ya shiga wanan clinic din.
Ke dawa kike wakike zagi nace da wanda ya amsa min da ita nakeyi kamar su mama
suna jirace sai gasu sun fado dakin ita da iya.
Kai kai lafiya wai meke faruwa hakane kuma daga shigowan ki nifa irin fadan nan
na cacan baki na kauyanci na fada maku ba a nan ba don bashine a gaban mu ba yanzu.
Har ita ta isa ta zagi ubana ita din me abin banza ke inkina da kunya har kina
da bakin magana banda abin kunyar da kikaiwa kanki din nan ?
Miji yana kwance haka sharkaf kije ki dauko mai cikin shege ki kawo mai zaki mana
mashi don an kiraki da yar iska zagi akayi ko halinki aka fada ?
Ai shine nace da ubanki mukayi iskancin ko don sune manyan gidan yan iskan da
muke zuwa,,,,,,,,
Muryan yaya jafar dake badaniya a saman gado ya dakatar damu duk daidai shigowan
mama da tawaganta yake fadi da karfi ba cikin shege tayi ba nine da kaina nayi
abina.
Yana fada yana kokarin nuna kanshi da hannunsa don a gane me yake fadi to kinji
abinda ya fada dai yace cikinsane abinda yake fada ke nan yayu wani kada kai alaman
ehh kamar wani tsohon kadangare dashi lokacin.
Yana kokarin cigaba da maganan da yake son fada kowa a dakin yai shiru yana
kallonsa yace saiba kiyi hankali idan kika kuskura kika sheganta min cikin nan zan
sakeki ya fada kamar maganar tana kwato mashi a bakinsa.
Haba dai wai meye hakane kin gani idan kika jawo muna wani matsala a cikin
zancen nan wallahi ranki zai baci sosai yaron nan tun farkon maganan nan ya nuna
cikinsane yasan da hakan ba shike nan ba ke meye naki a cikin zancen wai ?
Ciki dai Allah yayi lokacin zuwansa duniya yayi a haka ba wani mahalukin da ya
isa yace kar yazo yau ninaji karfin halin maye da hauka.
Akadara ma bash yayi cikin nan ba ke meye naki a ciki zancen nan yanzu tunda
aurene kawai ya hadaki damu yarinyar nan kina da karfin hali sosai wallahi.
Maman tudu take fadan hakan a cikin hasala iya dake salati tana fadin yanzu
yarinyar nan sheganta masu cikin nan kike kokarin yi ko me ta cabe zancen mama da
fadin.
Yarinyar nan wai hankalinta daya meye a cikin zancen nan ke kishiya tunda dubu
ta nuna kinfi kowa a wajenta har yakai zaki wuce gona da iri ?
Ke Nusaiba ku fita daga nan, na fada maki ai inma ba cikinsa bane ganewa za ayi
tunda ba a bace jinin gidan nan suke ba.
Ni dai nafice tare da nazarin lafazin kowa a wajen nayi koka sosai a ranan daga
baya naba kaina shawara akan zancen sai zuwa karfe ukku ya Habu da yanda suka shigo
gidan.
Ina jin muryansa suna gaisawa dasu mama suna tambayan yaushe ya dawo yace da
ranan nan ya wuce ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login