Showing 264001 words to 267000 words out of 328222 words

Chapter 89 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

Humm,ummm ya fito daga bakjn Saratu hakan yasa yazid fadin tayi karya ko ta juyo
tana fadin me nace yanzu don Allah kuma ?
Sai in karyaki a nan ta godewa Allah taga nata rayuwan auren ki saurara naki ke
kuma saukin abin dai auren sai bawa yayi matukar yana raye .
Zaku fara halin naku ko me kaji ta fada yanzu da kake kokarin mata baki har kana
fadin ,,,,,,
A,a dakata hjy don Allah dama yarki ce matsalan yarinyar nan kaf dinku kun sanda
hakan a wajen nan to gashi a gaban mu ta nuna maganar banza akeyi a yanzu.
Ina ganin abin nan kawai a hakkura hjy don yarinyar nan ta nuna muna bata da
tarbiya da zataji sulhun da akeyi a wajen nan balle a koma a zauna lafiya.
Wallahi bata isa ba Alh ita dinme harta isa ta hana min matana zama a gidana
saboda ita abu dayane yanzu a gaban kowa tunda tace haka zan mata iyaka da matana
dukka don ba ita kadai bace kanwata ai ?
Ina da yan uwan dake kaunan zumuci dani sai yayi kamar ya sarke don maganan da
yakeyi a cikin bacin rai hakan yasa da sauri dan uwansa mikewa zuwa gareshi tare da
goran ruwa a hannunsa.
Ya bashi suka hau lalashinsa akan yai shiru don Allah yazid sai fadin yake
wallahi kikai sanadin yaya kowaya tsaya maki sai kasheki Saratu.
Kin gani dai mama tazo ta nunawa mutane rashin tarbiyanta a nan yanzu haka kuma
tana kallon yadda dan uwan mu ke wahala amma wai yarinyar nan tana neman bata muna
tafiyan mu don tana yar iska kawai.
Kananan maganganu ta soma yi daddy sai murmushinsa yakeyi irin nasu na manya
yana kada kafanshi irin yasan za a rina ?
Saida iya ta samu sukai shiru ta hau fada yake fadin dakata tsohuwa wanan abu
ai mai saukine yanzu kai malam Jafar kaje kayi hakkuri don muna son yar mu gaskiya.
Rahamatullah ba zata koma gidan ku ba da wanan halin da kuka nuna muna a
gabanmu which means koda ta koma dai halin yana nan bai caza zani ba.
Yar mu tana fama da laulayin ciki don likitoci sun bata hutu komai batayi a yanzu
sunje asibiti da uwarta an sakata a rest don haka kuje kawai Allah ya hada kowa da
rabonsa.
Don wanan abin ba zamu mayar da yarunya wajen da babu kwanciyan hankali ba
alhalin mun sani kuma mun gani wani abu yazo ya sameta.
Saiga iya a kasa tana hada daddy da Allah yaiwa Allah yayi hakkuri ya bar Rahama
ta koma dakinta kodon mijinta tayi alkawarin ba abinda zai faru insha Allahu kuma.
Tausayin iyan yasa daddy din ya sauko yake fadin tsohuwa kuje insha Allahu zata
dawo amma ba yanzu ba saita kara samun lafiya za a dawo da ita.
Yazid da aka hana magana sai lokacin ya samu furta don Allah Alh ayi hakkuri
kodon halin da bawam Allah nan yake ciki da cewan Jafar.
Sai daddy ya gyara zama ya soma fadin ai nace zata koma amma ba yau ba sai ta
kara lafiya saidai ina son ku sani matukar uwarku gata a zaune bata daina wanan
halin ba ba macen da zatayi marmarin zama da iyalinta.
Mama din ta kallonshi yace yes ni ban tsoron kowa da kuka ganni nan ya fara
karanto masu mukaman daya rike da yake aiki inda ya dora da fadin .
Yau a duniya mutum ya fito filli kiri kiri ya nuna nasa yake so dan kowa ba da
bane a wajensa sai duniya ta barshi da dabaranshi a hakan .
Banga inda zaka dauko dan mutane ba ko danka ya dauko ka nuna naka kake kauna a
fili duk mutum mai wanan halin abin tsorone gaskiya.
Anso dai ayi ba dadi a wajen don daddy ya tsaya ya fadawa mama gaskiya shida iya
sai gata tana kuka tana fasin a gafarce ta ita ba a a fahince ta bane yakawo hakan.
An dai basu hakkuri akan su koma daddy yayi masu alkawarin shi zai kawoni har
zaria da kanshi idan na kara jin dama don kada abi hanya dani a jijigani wani abu
ya faru da cikin jikina.
Saida zasu tafine daddy yasa na fito wai inzo mu gaisa dasu din banso fitowan
ba amma don gudun bacin ran iyayyena din dole na fito muka gaisa dasu.
Najin dadin yadda daddy ya nuna masu akan mu yana iya sharia da kowa koda duk
abinda ya mallaka zasu kare saidai su kare din .
Amma matukar aka kara muzanta ni ko yar uwata a gidan yadda akayi a baya zai
dauki shari,a dakoma waye ba ruwansa da kankantan mutum ko tsufanshi.
Sukayi sallama damu haka suka tafi donni tun bayan gaisuwa ban kara kallon inda
yake ba asalima haushinsa naji ya karu min a zuciyana don yadda sukazo din sukayi.
Ban kuma rakasu ba na koma dakin ummah na kwanta ina hadiyan bakin rai daya
tokare min zuciya tare da tunanen mama ita wata irin macece wai ?
Anya kuwa ko Jafar din tana kaunarsa kuwa a zuciyarta gashi ya rame ya zama baki
sai kasumba daya tara a fuskanshi dama nice maiyi mashi aski yanzu ko nasan bai
yardane kowa yayi mashi.
Suma a mota da fada sosai aka dawo gidan inda suka taru sukaciwa saratu mutunci
don kuwa suna barin gidan mu saiga wayan Nusaiba tana tambayan ance sun shigo
kaduna din zasu karaso gidansune suga mimi yarta ?
Nam yazid dake jin abinda ya fada ya soma fada yana kantamawa saratu zagi yana
fadin idan batayi hankali ba saita rasa mijin aure tunda ta zama iblis ?
Uwar taso fada wai don me zai kirata da iblis iya ta tare ta kara fadin aita
zama iblis don inda rahama yake bata a wajen sai hadin hasumi shine nata.
Nadai gane baku kaunar yaron nan da alheri daga ke har uwarki saratu duk yadda
akayi kinkai uwarku wajen malam da kuke bi dake da yarinyat nan da har bata ganin
laifinki a yanzu ?
Nikan iya ku kasheni ku huta yafi wanan aibantanin da kukeyi haka ai bata karasa
ba shi mara lafiyan ya juyo yakai mata mari tas sai da kowa na motan ya kadu.
Cikin irin maganarsa na saurin harshe ya soma magana yana fadin kar kiga ina
kyaleki ki zata ban iya daukan matakine a kanki tausayin ku nake ji ba komai ba ?
Iskancin nan ya isheni daga yau ki kama kanki dani da duk wani abu daya shafeni
don kinga ina kyaleki zaisa har ki wuce gona da iri ?
To muzu ba dani dake a gidan nan kuma na baki nan da wata daya ki kawo miji kona
aurar dake ga duk wanda naga dama a zaria.
Haba dai kuyi mata fatan samun mijin mana sai mugun fata kukewa yar uwarku haka
ko yaya take dai ai yar uwarce sai kuyi hakkuri da halinta.
Kema bakin tsiya yayi maki yawa meya kaiki fadawa Nusaiba mun shigo tunda kinsan
ba wajenta muka zo ba don kawai ki tayar da wani hasumin wa kanki kome ?
Kaji ko J mama bata ga laifin yarinyar nan ba sai namu shike nan ai ranan da duk
kika iskancin ki a sai kin iskamci ki tsaya dashi iyasu da saba yiwa amma bani ba
don ban iya daukan wanan halin banzan naki.
Na rasa yadda akayi yarinyar nan ta koma haka jafar yake fada cikin takaici sai
iya ta amsa mashi da fadin dama hakan take ai halintane a hakan .
Wanan yasa mama tayi shiru har suka kai zaria bata kara magana ba mota na tsayawa
suka shiga ciki nan tahau fada da yar nata tana fadin .
Da wanan halin kike tunanen zakije aure Saratu na dauka abinda zaki barine ashe
abin naki bana bari bane ke a gurinki.
Bansan baki da wayau ba sai yau din nan ki rasa wanda zakiwa tsiya sai Jafar duk
irin kokarin da yaron nan yakeyi daku sakaiyar da zaki mashi ke nan ?
Kallon mamaki saratu ke mata tace kwarai indai kinayi don Nusaibace tun wuri ki
daina don bani kaunar yarinyar nan mai bakin wayau tsiya ta dawo gidan nan .
Taje abinda sukaci a gareshi ya isa hakana naji da wanan dake son tsaya min a
makoshi don na kula Jafar baisan ciwon kanshi ba.
A zatonsu naje bikone saboda Allah na daije kawai don kada ya halaka a yanzu
tunda ya kwallafa ransa ga yarinyar nan don shi kawai naje kadunan nan .
Dukkansu biyu kallon mamaki sukewa uwar har dai Salima dake kallon ikon Allah
yanzune fa suka bar kaduna tare da alkawari akan dawowan Rahama dakinta amma mama
take fadin wanan magana kuma ?
Tsam ta mike zuwa daki cike da tsoron halin mahaifiyarsu din tabbas wanan hali
na mana yasa bata shiri da saurab kishiyoyinta ashe ?
Da wanan tunanen ta wuni ta kwana sai washegari data je gaida yayan nasu da
kwana take basu labari shida iya.
Iyace ma ta hau fada yana zaune baice komai yayi shiru yana tunane a zuciyarshi
kafin ya umurci ita salima din data gyara masu part din don yasan idan ba ita ya
saka aikin ba Asmau ba zata taba tunanen zuwa ta gyara masu ba dama kuma yana jin
haushin halin ko in kula da take nunawa a kanshi.
Shidai abinda ya dauka hakan wani jerabawa a rayuwansa Allah ya kawo mai dan ya
kara imani da hukuncin ubangiji ga bawa.
A yanzu yasan masoyanshi da kuma masu nuna hassada akanshi dan zaman jinyar nan
da yayi gida bai fita ko ina.

ZAINAB IDRIS MAKAWA


[5/21, 07:47] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

8️⃣3️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Sai daga baya na fahinci daddy daya fada masu cewa banda lafiya don haka sai naji
sauki saudi ce ke fada min ai gata yayi min da fadin hakan .
Yanzu kinga ko kin koma gidansu bake ba sauran wanan aiyukan da suka bar maki
ke kadai dole za a canza tsari yadda ya dace ko kuma ya dawo naki gidan kamar yadda
akeyi a baya tunda ya samu lafiyan fita a yanzu.
Saidai wanan kaunar tashi kamar har yanzu tana da sauran ja don yanayinta ya
nuna bata saduda ba ?
Bam tsamani cewa zasuje wancan gidan dayar matarsa yada sukaiwa yarinyar nan
caaa a kai ita kuma munafukace dai ta karshe watau ?
Kinsan ya rabu da ita meye na kiranta a waya kina fada mata sirin gidanku koda
yake uwarma da alama goyon bayanta takeyi yadda takw ba diyan nata amsa.
Murmushi nayi kawai bansan me zance a zancen ba tunda gaskiyar ke nan ta fada na
rasa gane mama ko wace irin uwace ita ?
Da bata iya tsawatawa Saratu wanan halin yan wutan da takeyi na hadin hasumi
gashi ta sani ba abu mai kyau suke aikatawa ba ita da Nusaiba amma sai ta tsare
kada ayi mata fada.
Saidai wani lokacine ita kan dan tsawata mata idan ta wuce mata gona da iri a
lamarin ta koshi ba ko yaushe ba sai can ba a rasa ba zakiji tana tsawata mata din.
Nidai har barci ya daukeni tana zuba bansan tashinta a dakin ba saida na
falkone na ganni ni kadai a daki ina barci hakan yasa na tashi na kashe tv na koma
daki na kwanta duk da dare baiyi ba sosai a lokacin .
Sai bayan kamar kwana biyune da zuwansu ina zaune ina shan iska a waje da yamma
saiga ummah da kudi a hannunya ta zauna a kusa dani tana fadin.
Ungo wanan daddy yace a baki koda akwai abinda zaki saya a nan kafin ki koma
zaiwa antyku Nuratu magana tazo ku fita tare da ita .
Kudin nabi da idanu ban karba ina mamaki nace ummah me zan saya kuma komai yaya
J yana sayo muna a can ?
Kingani ai munsan da hakan shiya muketa baki hakkuri don shi bai maki komai ba
uwarsace da kanninsa sukai maki laifi bashi ba ?
Don haka ba zaki hada duk dashi kice kina fushi ba ko ranan har suka koma baki
kirashi kinji yadda suka isa baiyi fushi ba ya kira kuma kikaki dagawa ?
Da sauri na dago na dan dubeta na maida kao kasa na sada tacigaba da fadin banga
dalilin da zaki hada dashi kina fushi haka ba ?
Su dai da suka tabaki ai dasu zakiyi bashi ba ummah idan banyi hakan ba ba zai
dauki mataki ba wata rana kuma har sai kuji cewa sun kai ga taba jikina tunda suna
da niyar hakan dama a manufarsu ?
Kinga kuwa da ace sunsan bai kaunarki da yanzu sukai ga abinda suke so don ba
wanda yayi tsamanin cewa zaiki kai har wanan lokacin a gidan ?
Yau gashi har Allah ubangiji ya kawo rabo a tsakanin ku abinda basu taba zaton
zai faru ba ke nan don ance suna fadi wai saidai kiyi zaman wahala kina jinyarsa
din da kikeyi a kare ga hakan.
Kwatsam saiga shigan cikin nan na jikinki koshi bai isheki godiya ga Allah ba a
sanadin cikin ne ai ita dayar kishiyar taki ta fita tabar gidan ko ?
Don Yanda na fadin sosai suka girgiza lokacin da baiyanan wanan cikin na jikinki
don haka dole ki daure ki koma dakinki a yanzu koyi goyon cikin nan a gidan ubansa
yadda basu kaunar gani din suga Allah ya fisu.
Don Allah Rahama ki koma kiyi hakkuri a dakinki ki dubi mijinki dake fama da
kansa don Allah ko sun kiraki da yar wahala kinfisu morewa Rahama don ladanki yana
ga Allah.
Allah ya gani mu munsan da zuciya daya kike zaune da Jafar kosu sun sani abu
daine na hassada akan mutum kawai sukeyi.
Don ni uwarsu na kasa gane alkiblanta har yanzu na rashin kaunarku da yayanta da
batayi ban taba ganin uwar da bata da tunane irin wanan matar ba a rayuwana.
Tanayine don zugin da dan uwata ke mata a kanmu ummah tanayin ne kuma don kawai
an sakata tayi muna hakan kada mu mamaye masu gida kamar yadda dan uwanta ya fada.
Dan murmushin yake ummah din tayi tana fadin kaiya ta makaro wallahi ai tunda ta
haifa sai an mora din yadda bata so.
Yanzu dai ki karbi kudin nan ki shirya din gobe ku fita da antyn naki don jibi
zasu mai dake dakinki in sha Allahu.
Jibi kuma ummah na tambaya da sauri ta mike tana fadin me zaki zauna nan kiyi
Rahama ga mijinki can yana bukatanki a kusa dake.
Ta juya ta tafi nabi kudin dake hannuna da kallo zasu kai dari biyu kila da dan
kai don nauyinsu da naji a hannuna din.
Koda na shiga daki na samu wayata dake makale a caji tana ta rigin na duba
shine a kan layi yake kirana har yayi min three mis called a lokacin ina waje.
Kamar zan share sai kuma na daga da sallama ya amsa yake fadin ina ta kira baki
picking ba tun dazun dama nace in tura habibane ta gyara maki daki ?
Ai Key din suna wajena na bashi amsa da hakan yace saida nayi tunanen hakan
saidai falon da sauran dakuna ko nacewa Yazid a kawo maki kayan abinci fresh a
kwashe wa yan nan tunda sun dade .
Nagode kawai na fada a darare yake fadin please Rahama kiyi hakkuri kada kice
baki dawowa yanzu rayuwana tana bukatanki a kusa dani wallahi.
Da sauri nace dashi aiba ni kadai bane bayan haka akwai yan uwa kaida kake cikin
gatanka ga kowa naka a kusa zakace kana cikin wani hali a yanzu ?
Haka dai kikace idan kika wuce satin ban Allah saidai in dawo kaduna daddy ya
bamu daki a nan mu tare baki dayan mu.
Kit na kashe layin cikin takaicinsa don ni dai shine ya jefani a wanan halin da
ya barni yadda muke da shike nan yanzu muna zaman mu lafiya da kowa a gida yaje ya
kawo zancen aure a tsakanin mu daya jawo min bakin jini a cikinsu yanzu.
Zama nayi ina tagumi a bakin gado tunanen abinda zan koma in tarar yanzu kuma a
gidan nakeyi duk da nasha alwashin cewa ba zan kara kulasu ba duk abinda zasuyi min
nasan wanan karyane muje dai din don dole wata rana in kula.
Nusaiba kuwa daga ranan da suka shigo kaduna din zuwa wanan ranan tashiga
tashin hankalin dayafi a girka duk iya shige shigenta bukata bai biya ba yadda
malamta suke mata karyan zai faru din.
Don gashi har kaduna suka shigo amma ba wanda ya kula da lamarinta har waya da
tayi da mama ta fahinci maman batayi na,am da hakan ba.
Koda basu zo donta ba ai zasu shigo su duba yarsu dake tare da ita amma kememe
tayi ta jiransu sai sakon Saratu data samu cewa sunma kusa shiga zaria ai.
Hakan yasa ta kasa hakkuri ta dinga tura masu sakon bakar magana a cikin bacin
rai tana kara dasa kiyayarta a zuciyarsu wanda ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login