Showing 327001 words to 328222 words out of 328222 words

Chapter 110 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

Duka duka cikin kwana ukku ya daga yabi bayansu duk wanda aka fadawa ya tafi
makka sai yayi namaki tunda yace sai wani shekara zai tafi.
Ashe gara da Allah ya kaishi don kuwa mama tun zuwansu ta fadi ciwo yau ciwo
gobe lafiya har suka bar madina zuwa makka ana fama da ita hankalinsu yaya duk ya
tashi sai ganinsa sukayi kwatsam yace hankalinshine bai kwanta ba.
Zuwan shi ne dan dama dama don dole aka samu keke yana garata ta samu tayi aiki
a lokacin ganin ta dan samu sauki ya koma da ita madina sukai ziyara ya rigasu
dawowa Nageria tunda shi jirgin yawone.
Saida ya dawo muke jin cewa ga abinda ya faru a can din da mama ai taji jiki
sosai badon zuwanshi ba zata samu aiki ba sosai amma bai dawo ba saida ta tabbatar
da tayi ibadan daya dace tayi.
Yaji dadin yadda ya samemu da yaran don gaskiya ba yabo ba yaran sunyi kyau
sosai duk da ba komai nake masu ba amma tarbiya ba guda ba kowa na fadi.
Dan matsalan da aka samu shine fadan da akayi da Saratu yaya Habu kuma yaci
mata mutuncu tun ranan akan naman laiyane datace wai naman da aka bata bai mata ba
tazo har gida taci min mutunci ina fada mata ni banda labarin komai akai su yaya
suka raba aka aiko min tace attabau laifinane tunda yaya ya bar muna shanu da
raguna shine don an raunata za a kawo mata nama kadan.
Karshe dai na biye mata mukayi cacan baki da ita Aminu ya kira yaya Habu yazo
gidan ya sameta yaci mata mutunci sosai tabi hanya tana kuka.
Da yaya ya dawo yaji abinda ya faru yaje nemanta ashe tana jin ya dawo ta gudu
ta boye bata yarda sun hadu ba dashi.
Labarin abinda ya faru da mama suna dawowa yabi gari nasan kuwa yan gidane ke
fada akaji aka sauya zancen kawu yazo taron ta don anyi belinshi shi yake tambaya
ashe haka tasha matsala a can tace eeh nasan ba komai bane Allah yati min haka in
gane gaskiya.
Yaron nan Jafaru Allah ya kara mashi albarka dashi da zurianshi jafar yayi min
komai duk da Jafaru danane dole in nemi gafaranshi ko alhakinsa da ake sa inci yana
hanani ganin rahama a rayuwana.
Baidai ji dadinta ba ranan har ya tafi zance zuwa makkan nan ya kawowa mama sauyi
sosai a rayuwanta dkn naga zuwata biyu gidan mu ko tsaraba ita da kanta ta kawo
muna har gida ta kuma wuni a nan ita da anty barakha sai dare suka koma gida.
Asmau ta dawo makka ta samu nasa yara makaranta inda na koya masu abubuwa da dama
dole tasan yaran sun samu natsuwa a yanzu abinda banji dadi ba shine da taso ta
nuna min wai tafi a yanzu.
Ko don tana ganin taje makka ni bai kaini bane oho sai taso idan an hadu tayi
min irin sakin maganan nan na gugar zana na daiyi gaba na baya sai hange a raina
nace taji dashi nasan abin da nakeyi ni.
Mama bata ragawa sararu ba kan abinda tayi min gashi taji ga Aminu mijinta tazo
kwanashi ukku a gidan lokacin da basu nan hakan ya batawa mama rai tace sai ta koma
dakinta.
Ta kira kawo tace ta gaji yaba yara kudinsu ita ta gaji da abin kunyar dake
faruwa hakana yayi mamaki sosai da mama ta iya budan baki ta tambayeshi kudin .
Gaba daya yasan komai ya lalace mashi a yanzu gareshi wai ashe dama akwai
kaddara da mutymin nan ya boye yana jiran abu ya lafa ya fito dasu yaci bulus duk
da dai ba duka aka samu kudin ba sun dai samu abinda suka samu a wurunshi yazid
yace ya hada da gidan iya ta mara mashi baya ya karbe gidan.
Ashe ya biya muna makka ni da salima nafisa lawisa kanwarsu yar wajen ummah sai
matar yazid da maria sai kannisa maza su ukku da zamu dasu dashi kanshi.
Kiri kiri yaki biyawa saratu makka kamar zatayi hauka yace bai biya tunda bai
isa da ita ba ga auren yayan yaya barakha da za ayi kafin tafiyan mu makka din
Ni ba abinda yai min dadi sai yan uwana maza da karatun su yanzu yaci gaba a nan
da dawowansu a kusa dani yayi muna dadi sosai yaso ya hada da ummah muje mijinta
yace shi zai biya mata ta bangareshi tunda yana dashi.
Anyu buki da sati ukku muka fara shirin tafiya mama taso Amir ya zauna hannuta
amma yaya yaya yace mama zata zo ta zauna dasu a gida da yar wajen yaya Ai babba.
Haka Asmau tace akawoshi gidansu yace a,a shine hakam ya dan hadasu hatsaniya
tace yaki ya kawo mata dana amma ita ya kwashi nata takai min na zauna dasu.
Yace yakai daya kai din bashi ba har ita taji dadin ganin yaran yadda suka dawo
suka samesu ai don haka ba zai kawo Amir ba ta kashemashi shida yunwa nata ma ya
kwashesu yakai ma mama dubu yace har ya dawo.
Dole ta kyale muka tafi muka sauke farali munyi aiki sosai muna can labari yazo
muna dan wajen Asmau ya fada tankin ruwa ya mutu.
Hankalinmu ya tashi sosai da jin hakan shiya fara tambaya ai gidan ba tankin
ruwa wai ashe bayan rafiyan mu uwar tazo ta kwashesu taje dasu gidanta wai zasuyi
sallah a can shine wanan abun ya faru dashi.
Haka muka dawo cikin bacin rai saidai nikuma muna dawowa ciki ya baiya a gareni
ciki na biyu ke nan haka nayi ta fama lauyi ga tajiigindin duniya wanda ba a rasawa
a kullum dake faruwa na haihu lafiya na kara samun namiji again nan kishin Asmau
ya tashi saida yaya yayi mata iyaka dani ta shiga hankalinta.
Na kusa haihuwa kuma ciwon yar wajen Saiba ya tashi itama ta rasu nan
hankalina ya tashi sosai Allah dai ya taimakeni na haihu a lokacin.
Na dan huta da haihuwa don tazaran shekara ukku ban haihu ba nasake samun wani
cikin na haifi wani dan yanzu haihuwana biyar da nake maki labarin nan shagunana
biyu manyan store daya a nan zaria daya a kaduna.
Sau daya muka hadu da saiba ba don farin sani ba ba zan shedata ba muna dakin
yaya kubura wajen buki suka shigo wai suna tallan kayan mata tunda tayi arba ta gan
mu nuda Yanda da matar yazid da yanzu muke aminai ta saka kafa ta fita falin bamu
kara ganinta ba.
Sai dai ince Alhamdullahi don muna zaune lafiya da Asamau Allah kuma yana ta
budawa mazajen mu Saratu daice a gida itama auren yaki ta koma tafito har sau ukku
a karshe dai auren ya mutu iya kuma ta amsa kiran mahalincin mu muna da shekara
biyu da dawowa makka lokacin.
Alhamdullahi da fatan an dauki wani darasi a cikin dan takaitattacen labarina na
fahinci rayuwa bai tafiya ga mutum daidai sai tare da dan uwansa da duk maison ya
ga haske a rayuwa ya rike zumunci in mace ko namiji don naga hakan a rayuwan gidan
mazajen Alhamdullahi muna cikin rufin Asirin Allah sosai a yanzu fiye da lissafinki
mai karatu da fatan zaki yafeni inda nayi kuskure Allah ya bamu ikon cikawa da
imani amin ya Allahu.




ZAINAB IDRIS MAKAWA.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login