ENGLISH DESCRIPTION
FATTANAH – A Story of Destiny, Secrets, Faith, and the Unknown
Everything in life happens only by the will of Allah.
In the stillness of the night, during a moment of devotion, an old woman witnesses something terrifying. A powerful light fills the sky, stars move as if they are about to fall, fear grips the heart, and faith is tested. This is not a dream. This is a warning.
Elsewhere, a young man named Aliyu Modibbo lives a calm and faithful life, yet he carries a mystery even he cannot understand. What he sees in his sleep is neither dream nor reality. So what is it?
In the royal palace, a bold and restless girl named Fattanah, known for her sharp tongue and fearless nature, is about to face a destiny that will change everything.
As events begin to connect, the secrets of the night, divine power, and destiny collide.
Love, fear, faith, power, and survival will intertwine.
One question remains:
Is the light a blessing or a coming disaster?
If you love stories filled with:
- Deep emotional romance
- Spiritual lessons and faith
- Mystery and supernatural events
- Royal life and human struggles
- Destiny and hidden truths
Then FATTANAH is a story you cannot put down.
HAUSA DESCRIPTION
FATTANAH – Labari mai cike da sirri, al’ajabi, soyayya, kaddara da rikicin rayuwa
Komai na rayuwa sai Allah ya nufa.
A cikin dare mai cike da nitsuwa da ibada, wata tsohuwa ta fuskanci wani abu da bai taba faruwa ba. Wani haske mai firgitarwa ya mamaye duniya, taurari suna motsi kamar zasu fado, zuciya na rawa, imani na gwaji. Wannan ba mafarki ba ne. Wannan gargadi ne.
A gefe guda, wani matashi mai suna Aliyu Modibbo yana rayuwa cikin nutsuwa da tsoron Allah, amma yana dauke da wani sirri mai zurfi wanda har shi kansa bai fahimta ba. Abubuwan da yake gani a cikin bacci ba mafarki bane kuma ba zahiri bane. Shin meye gaskiyar wannan hali?
A cikin masarauta kuwa, wata yarinya mai suna Fattanah, mai cike da rudani, son fada, da halin da ya ja hankalin kowa, zata shiga cikin wani lamari da zai sauya rayuwarta gaba daya.
Lokacin da abubuwa suka fara hade wa, sirrin dare, ikon Allah, da kaddara zasu hade su zama abu guda.
Soyayya, tsoro, ibada, iko, da gwagwarmayar rayuwa zasu hadu a wuri guda.
Tambaya daya ce zata dame ka:
Shin wannan haske alheri ne ko kuma bala’i da ke tafe?
Idan kana neman labari mai dauke da:
- Labarin soyayya mai zurfi
- Sirrin rayuwa da boyayyun abubuwa
- Labarin addini da darasi
- Al’ajabi da abubuwan ban tsoro
- Rayuwar masarauta da talakawa
- Kaddara da gwajin imani
To FATTANAH shine littafin da zai dauke hankalinka daga farko har karshe.