Showing 111001 words to 114000 words out of 328222 words
Chapter 38 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
masu kudin Nageria suna iya kokarinsu wajen cigaban kasan nan
saidai mu yan kasan ne bamu bada goyon bayan cigabansu.
Don munfi ganewa alfahari da bajinta a koda yaushe wanan na kara durkusar damu a
cigaban kasa da zamu samu.
Tayani zaba Ramaah kada ki damu da kudin kayan ki duba qualities dinsu kawai ki
dauka duk abinda yai maki kyau a zuciya.
Nasan wanan akidar tasu tun muna kananuwa mama kanzo damu mu tayata zaben kayan
da take hadawa din da gyaran wajen event dinsu da suke bada haya.
Jin hakan yasa na zage na tayata zaben abinda nake ganin na fita kunya saboda
furcinta sosai muka hada kusan akwati ukku da kaya na gani na fada a ko ina a
fadin kasan nan a wanan shagon na el,samad kafin mu fito zuwa Sahad.
Bamu shigo gida ba sai bayan ish,i akan washe gari za a koma a karasa sayan
kayan tunda na shige nayiwa wanka da alwala nayi sallah na kwanta.
Bandamu da neman abinci ba a ranan saboda gajiya dana debo har nake dariyan kaina
ashe ko wani jiki yana son hutu a duniya ?
Dan kwana biyun da nayi ina samun hutu a yanzu dan abu kadan yake wahal dani da
gajiya kamar bani bace nake yawan aiyuka a yan watanin baya ba.
Zaune suke dukansu a falin iya din da mama ta daga masu hankali saidai shi
Jafar bai wajen don ya wuce a ranan ya bar gari zuwa kano zaibi jirgi da zai kaishi
lagos .
Sai habu da ya tsaya shima yace da safe zaibar gari zai tafi maiduguri mama ta
nisa tana fadin na dai gane kuna son mayar dani mutumiyar banza habu ?
Na fada maku hakan ba zai yuyu ba dole Jafaru yasan yadda ya walwale auren nan
dayaje aka daura masa da yarinyar nan.
Ko kuma har naka auren shima ya samu matsala akan wanan zancen da kukeson jawo
min a yanzu ?
Saida ya dan gyara zama ya shafo kansa ya sauke wani shu,umin murmushi a
fuskanshi kafin habun ya kallo iya yana fadin a dai tsaya gana J shida yasawa kansa
son yarinyar nan da karfi da yaji.
Don dai Rahama Allah ya gani bata bada son ranta ko ra,ayin yar uwarta aka daura
auren nan da Jafar ba tunda baiyi soyayya da ita ko ya nemeta wajen wani ba.
Allah ne kadai ya nufa akwai hakan a tsakaninsu shawaran na zuwa mashi muka
yanke shawaran daukan kawu muje wajen yan uwansu ko hakan yana yuyuwa sai gashi
munyi sa,a muna zuwa har auren aka dauro lokaci guda saboda nisan waje.
Asalin zancema wallahi duk kansu har yanzu basu sanda zancen auren nan ba don
banji ita maria tayi min magana a kan zance ba kunga ke nan bata sanda labadin
auren ba itama ?
Ikon Allah abin farin ciki ashe yana zama na tsiya Dubu ?
Na dauka wanan zance ke zakifi kowa farin ciki da alfaharin faruwan hakan a
cikin mu ai don kece kika san halinda danki yake ciki na bukatan abokiyar zama
tagari da zata bashi kulawa da kwanciyar hankali?
Amma kaiyya dai abin takaici sai gashi kece tafarko da kike nuna halin uwayen
zamani akan danki don kawai ya zabawa kansa farin cikin rayuwansa .
Iya ba wai naki zancen nan bane sai duban irin yadda za a fassara wanan zancen a
waje yar uwarta fa tana gidan nan tana aure iya yanzu kuma ace shi jafar ya auri
kanwarta ?
Zargin matansa saiya tabbata tunda dama sunce yana kula yarinyar har a gabansu
bai son ranta kona yar uwata ya baci inaga yanzu ace ya aurota ?
Dubu ban soki da wanan rayuwan ba a cikin yayanki kada ki manta ke dai ba ayi
maki irin haka ba dagani har mahaifinku bamu takurawa rayuwan ku ba a baya.
Yanzu ki duba bayanin yaron nan Habu yaran nan basu san da zancen nan ba daga
tambaya akai masu halarci aka dauro auren nan ko wanan abin bai isa ki gane Allah
dayane ba dubu ?
Iya ina son ki tuna Jafaru hakkin yan uwansane a hannunshi yake juyawa suma
yaran nan suna da bukata akan dukiyan su .
Nina tauyesu na bashi dukiyan nan ya juya yau iya yana ta faman aure aure yaran nan
bai aurar da kowa a cikinsu ba banda shi habu su sauran basu bukatan dukiyansune
iya ?
Kina kallo ko abu zaiyiwa yaran nan daidai dana matansa zai basu hakan fa ina
kyaleshine kawai iya amma a gaskiya raina yana sosuwa da hakan wani lokaci.
Au tanan kuma zaki fitowa dan naki kice min tun farko bakin ciki dashi kikeyi ko
kuma yar kice ta zugaki akan hakan yanzu ?
Wanan ma mai saukine ai mama in dai dukiyansu suke so nasan ko yau din nan aka
bukata Jafar zaiba kowa kasonshi in sha Allahu iya ta amsawa habu da kwarai kuwa
dan nan.
Iya rabu da wanan tunda an kashe masa baki a yanzu komai zai fadi game da dan
uwan nasa don bakinsu daya akan zancen.
Amma gaskiya mama duk wanda ya canza maki ra,ayi akan yaya jafar zai iya cutan
mu da dukiyan mu yayi maki mumunan hudu ba arayuwa.
Ni sam ban taba wanan zargin akanshi ba mutumin da yake tsaye a kan mu da komai
namu gidan nan shine za ace yana facaka da dukiya yanzu ?
Rufe min baki salima tun ranki bai baciba wajen nan idan an tashi zance ki hana
mutum yai magana don wani ra,ayi naki na daban.
Gaskiya take fada maki mama don kuskuren da kike nema ki tabka a yanzu babbane da
nan gaba zai dame mu bake bama don duk ranan da Jafar yaji zancen nan ba za asha da
dadi ba.
Kai dukiyan nan dai ina nina danka masa da hannuna ko nayi shawara dakai da zan
bashi don haka ka kyaleni ba zan yarda Allah ya tambayeni kan hakan ba.
To shike nan mama a samu lokaci a zauna dashi kan hakan amma ina bukatan ku
cireni cikin zancen nan don Allah .
Daga hakan ya mike ya fita daga dakin cike da bacin rai part dinsa ya koma cike
da tunanen yadda zai tafi yabar yanda a cikin wanan cakwakiyar hakan yasa ya daga
tafiyansa a ranan.
Zama yayi da matanshi ya fara fada mata abinda ke faruwa tiryan tiryan inda ta
kasa fahintar abin don a zatonta yana nufin yaya J yana son ya nemi Rahama da aure
yake nufi.
Inda ta fara fadin haba dai yaya habu ina hakan zai yuyu don Allah kabar zancen
nan kafin ya kai ga zancen har an daura aure don haka Rahama a yanzu tana matsayin
zaman matar J ce a gidan nan.
Cikin tashin hankali ta fashe da wani irin kuka tana fadin amma bakuyi muna
adalci ba yaya habu haba dai Rahama fa ?
Rahama za,ace ta auri yaya Jafar don Allah ku daina wanan zancen saboda Allah
don ba abu bane da zai yuyu garesu shima ya sani.
Duk yadda yaso ta fahinci zancen ta kasa sai kukan tashin hankali da takeyi tana
neman layin Rahaman data kasa samun layin.
A lokacin wayan na wajen anty na barshi don haka bansan duk wainar da ake toyawa
ba a kaina lokacin.
Bai san ya akayi ba ya daifi zargin Saarece ta fada har matan J sukaji sai ashar
yaji yana tashi muryan Saiba na zunduma zagi daga wajen part din tana kiran su da
munafukai.
Abinda yake gudu ke nan har ya hanashi tafiya a ranan dama yasan sai hakan ya
faru a gidan idan labari yaje garesu duk da mama ta bar gidan a ranan da yarta
saare .
Sai iyace tayi karfin halin fitowa tana tambayan meke faruwane haka suke daga
murya ?
Kaji tsohuwar nan zakice baki san makircin da aka kulla bane gidan nan don kawai
aga an tozarta mu ?
To ai gamu gani idan gidan nan na shiguwa ga Rahama tazo gamu wanan kuma yanzu
meye idan ance zarginsu mukeyi a baya ?.
Jin yadda take fadawa Iya magana yasa ya bude kofa ya fito ya tsaya yana fadin
iya ki koma daga ciki ki zauna.
Suje suyi abinda zasu iya anyi aure da Rahama in ma baki sani bane ki sani an
daura aure a shekaran jiyan nan kuma aure ya tabbata mai zama ta zauna .
Wallahi baka isa ba idan ma nufinka kenan dama ka aurawa kanwar matarkashi kayi
kuskure yin hakan habu gara tun wuri ku rufawa kanku asiri kawai zaifi sauki.
Koki rufawa kanki asiriba a yanzu mijin dake da cuta kike gudun ya kamaki
Nusaiba don yanzu ya samu wace bata gudunsa kome ke gareshi har zaki tsaya kina
kumfar baki akansa yanzu.
Sai hakkuri don aikin gama ya gama faruwa saidai ina son ki sani duk kika sake
kika zageni ko matata a cikin zancen nan sai kin kwana a gadon asibiti ranan .
Idan kuma kin dauka karyane ko wasa ki gwada ko a yanzu kigani abinda zai faru
dake a wajen nan .
Yaja wani guntun tsaki tare da jefa mata wani kallo ya juya zuwa ciki baiko
tsaya ya fahinci tashin hankalin data shiga ba a lokacin.
Don da farko ba aure suke zargi ba kamar nemanta sukaji ance yanayi shine ta kasa
hakkura don ranta daya gama baci a lokacin.
Sai gashi zance ya banbanta Habu ya fito yana fadin wani magana na daban da
bata taba tunanen faruwan hakan ba wai jafar ne yayi aure ?
Auren ma auren yarinyar data gama sanin sirinsu gaba da bayansu waiko da gaske
habu ke wanan zance ko kunuwantane basuji meyace kan zancen ba ?
Ta juya a fusace zuwa cikin part dinsu hankali tashe Asmau dake tsaye tana mata
magana akan su tsaya su bincika gyale ta dauko da waya ta nufi hanyar fita daga
part din.
Wai ina zaki don Allah nusaiba ki natsu mana abi komai a sannu habu yana iya
fada maki hakan don ranki ya baci kawai tunda ba shiri tsakanin mu dashi.
Ko juyowa ta kalli Asmaun dake magana batayi ba ta fice gidan kai tsaye ta hau
abin hawa sai tudun wanda family house ta samu mama da abin duniya ya isa lokacin.
Da kyat ta daure suka gaisa da wasu daga gidan ta fada dakin mama Saare ce a
waje tana wanke kwanaku tana ganinta ta mike tana fadin daga ina haka saiba ?
Mama na ciki ta iya fada tana nan Saare din ta fada ta fada dakin ba gaisuwa sai
kukan data fashewa mama dashi wanda ya jawo hankalin mutanen gidan.
Suka nufo part din mama din mama dai tana zaune ta zuba mata ido gashi sai
tambaya meya faru akeyi duk sunyi shiru sai Saarece ta iya fadin.
Yaya jafar ne yayi aure ya auri Rahama kanwar matar yaya habu lokaci guda suke
fadin Rahama dai Rahama aure yaushe hakan ya faru ?
Haba yar nan akan wanan kika shigo da kuka haka me yaya zata iya yi akan hakan
tunda anriga da an daura aure yanzu meya rage kuma bayan hakkuri inna ke fadin
hakan.
To ba a aure ita tayi ina mijin kawarta ta aura amma ai ita wacan batayi tashin
hankalin nan ba da tayi hakkuri gashi an zauna lafiya .
Duk wanda zaizo sai yayi kwatance a kanta da cewa hakkuri akeyi ai itama ai wata
ta sama kuma tayi hakkuri haka ta mike bata iya fadan komai ba ta fice kuma direct
ta nufi wajen shiga motan zuwa kaduna.
Baifi yan mintuna da hakan ba yaya Habu ya dora yadda akai daurin auren a rugga
ya rubuta Jafar and Rahama Allah ya bada zaman lafiya abin median nan danan aka san
da zancen auren aka fara yadawa masu dorawa suna dorawa a saman wayansu.
Ganin hakan Jafar ya kira habu yake tambaya yake cewa dashi yanzu kan ai kowa
ya gama sanin abinda ke nan ya kwashe komai ya fada mai saidai ya boye mashi zancen
da mama tayi game dashi don gudun bacin ransa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
3️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Kwance nake har lokacin cikin gajiyan da ba zance ga dalilinsa ba ina dai dangata
hakan da fitan da mukayi da anty salma yasa jikina weak a lokacin.
Nayi mamaki yadda wanan ya narka kudi aka hada mashi wanan lefen a cikin kwana
biyu rak kayane dai aka zuba wanda zaki dauka cewa macen ba zata taba neman wani
abu mai suna sutura ba ko kayan kwaliya.
Gaskiya maishi ba karamin kokari yayi ba hakan ko banjitane ko kuma so an dai
narka nairori a wajen nan gaskiya irin tunanen da nakeyi ke nan a zuciyana naji an
turo kofan dakina.
Muryan anty salma danafi zaton itace don ba kasafai yan aikinta ke shiga dakunan
kwanan mu ba saida wani dalili mai karfi.
Wai kwance kike har yanzu na yunkura ina mika nake fadin haka kawai naji duk
jikina ya mutu nasan gajiyace na mike ina gaida ita.
Mama ta bugo waya muje yanzun nan tana neman mu dani dake jin abinda ta fada
yasa na kallota da sauri ina fasin mama kuma ?
Lafiya dai ko anty Salma tace ai kinsan halin mama kilama ba wani zance bane tana
dai son ta gamune kawai tace mu taso.
Murmushi nayi don ko yana yuyuwa haka din ne sai muje tace ayya yaran nan ban
ganku ba kwana biyu kuna cikin gaein nan kun shareni ko ku nemeni ?
Hakan yasa na tashi na shirya da sauri don na fahinci a shirye anty Salman ita
take a lokacin ba wani dogon shiri nayi ba wasu dogon riga da ya tsaya iya gwiwa
tare da wandonshi sai gyalen dana rufa iya wuyana tunda daga mota sai mu shige
cikin gidan mama din don haka ba saina tsaya wani bata lokaci ba.
Karshema zata iya sakani wani aiki a hakan yasa ban tsaya wani dogon gyara ba
kodana fito anty na zaune tana waya tana ganina ta mike tana fadin muje ko tana
mike yaranta.
Na dan marairai ina fafin kin rufo dakinkine anty wayata naso dauka a nan na
barta tun jiya sai naji tace gashi na saka maki a jakata muje saina baki a can din.
Ba wani dogon tafiya bane don basu da nisa sosai da juna sai gamu gidan daddy din
tun a waje na fahinci daddy yana gidan a lokacin.
Yan aiki keta kara kaina a tsakar gudan duk da yanzu gidan ba yawa sosai ko
masu aikin su ukune yanzu ba kamar lokacin da mukai tamu rayuwan dasu ba da muka
cika masu gida.
Mama fa ta tambaya tsohuwar tace tana gun Alh suna nan falonsa zaune hakan yasa
muka nufi can naso togewa iya ita ta shiga sai ta juyo tana fadin muje mana kin
tsaya kuma kai wanan bakar bafulatanan dai ?
Murmushi nayi don sanin sun rike wanan wasan ta fulani da barebari a tsakanin mu
ko yaushe kuma har daddy suna tsokalan mu dashi.
Daga mama har daddy din suna waya a lokacin muka shigo abinda kunnena yaji mama
na fadi shine ai gasu mun kirasu daddy zaiyi magana dasu daga baya sai inkirani
kiji meke nan.
Ta kashe wayan ta dago kai muka fara gaisawa ranan fuskansu ba wasa a cikinsa
don ko dan zolayan nan babu sai daddy daya mikawa dan salma hannu da yazo yaron ya
leke a jikina.
Mama ke fadin karka kama gaye ka sake reshe kwana biyu ba zaka ganta gidan kuba
dan nema kawai salma ta shafo kan yaron tana fadin ai tare zasu tafi zaria da anty
salma ko ?
Akayi dariya muka zauna dai a cikin harshensu suke magana wanda duk zaman mu
banda gaisuwa da dan wasu abu da muka rike har yanzu bamu jin yaren nasu sosai amma
muna fahintar me suke fada da kanuri din.
Don naji mama na fadin ban sani ba tace a,a har yanzu dai bansan komai ba amma
sai ban kawo a kaina suke magana ba.
Daddy ne ya ambaci sunana da Rahama hutu ya kare ko sai shirin komawa makaranta
na dan dukar da kai ina murmushi yace to Allah ya taimaka na amsa da amin kawai .
To Rahama nace yar uwarki tazo dakene nan don muyi maki magana irin ta iyayye
yau a duniya dai kin sani ko Abdullahi mahaifinku yana raye ni Adamu ina iya yanke
hukunci a kan ku ?
Zama na gyara don nasan maganar kila a kainane zancen komawata gidan su Yanda da
anty salma tace ba zan koma ba ke nan ta kawo gaban daddu din hakan yasa na amsa da
baki da kai da alaman hakane.
Yace madallah ina son kiyi amfani da tarbiyanki da natsuwanki da iliminki haka
kuma ki zamo musulma mai ruguman kaddaran da duk ta samu bawa ta rayuwa walau mai
kyau ko akasin hakan ?
Na sake jin kaina ya kulle min lokaci guda har na fara tunanen ko nayi rashin
wanine a lokacin falon yai shiru babu mai magana na dan lokaci.
Mama ta zuba min idanu daga inda take zaune hakama anty salma ke kallona cikin
wani yanayi na tausayi sai duk na kara tsunkewa lokaci guda.
Yayin da suka fahinci tun bansan meke faruwa ba yanayina ya sauya tun soma
maganan