Showing 249001 words to 252000 words out of 328222 words
Chapter 84 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
mike zuwa part dinsa ya
dan jima sai gashi da furan gora mai sanyi ya kawo min yana fadib ko zata sha wanan
din a gwada a gani ko zai tsaya mata.
Shina karba nasha na gama na koma daki na kwanta ina lumshe idanuwana rayuwa ke
nan rayuwan yanzu sai a hankali yau wai ummah ce zatace ta manta da wasu halaiyan
mu na baya data san mu dashi.
Ina jin muryansu a falon da alama waya takeyi don naji shima tsohon ya karbi
wayan yana fadin haba dai ta dai fadane ai akan me zata zubar da cikin dake da
ubansa ?
Bacin raine kawai yasa ta furta hakan amma ai Rahama yarinya ce mai hankali
kawai dai sun tabatane take son ta rama abinda sukai mata din.
Can naji ya koma fadin haba dai ba inda zamu barta ta tafi tunda tazo nan ai
shike nan ku barta din ta huta hankalinta ya dawo daidai kawai ?
Hawayene suka gangaro min a idanuwana naji wani bakin ciki ya tokare min zuciya
da niyata shine in samu da safe in karasa inda na nufa don banda niyar zama wanan
gidan gaskiya.
Saidai nasan wa yan nan kattan sojojin dake gadin get din gidan yana dawuya in
fice wani baiga fitana ba a cikinsu don haka na fara lalubo hanyar da zan gudu nan
din don bansan illan daya kaini tsayawa a nan din bama da har na tsaya.
Wana furan dana nasha ya rike min cikina bayan nayi sallah magaribane ummah ta
shigo tana fadin kada inyi barci fa in tashi inci abinci nakoshi nace daga kwancen
da sauri ta kalloni tana fadin me kikaci bayan furan dazun ?
Shiru nayi ta koma fadin ki tashi ga Saudi nan tayi maki miyarki daban na nama
kici abincin dole na tashi zuwa falon nata.
Tuwon shimkafane miyar kuku yaji daddawa da kayan yaji kamshi shi kawai zai
sanarma da hakan tsaye tayi a kaina tana fadin ko bai maki bane miyar ?
Na dago a hankali ina kallonta a sanyayye na bata ama da yayi min ina lasan miyan
tace to kici don Allah kada ki zauna da yunwa don Allah kinsan yanzu bake kadai
bane.
Ki kula sosai ko baki son abinci ki daure kici don Allah kada lafiyan ku ya
tabu daga ke har abin cikin cikin naki kai kawai na iya gyada mata ban iya amsawa .
Har zata fita sai kuma ta dawo ta zauna tana fadin ke banda abinki Rahama me
zaisa ki bar gidan mijin ki saboda wasu yan uwansa can ke baki ga yadda yar uwarki
ta koma masu kurma bane tunda ta fahincesu.
Nasan ba haliku daya da ita ba duk da hakan ya kamata ace kin koyi hakkuri hawaye
suka soma zubo min ga loman tuwo a hannuna.
Falon yayi shiru zuwa can ta mike ta fita tana kiran saudi mai aikinta wai tazo
ta zauna dani zata duba tsohon mijinta abinsu a yanzu ya daina ban mamaki.
Nasan sauyi rayuwane Allah ya kawowa ummah a yanzu yadda tasha wahala rayuwa a
baya saudi din tazo ta zauna dani a falon tana dan jana da fira sai dai ban saki
jiki ba.
Ta soma fadin wa yan zaria ai ai kasan halinsu kake iya zama dasu kina ganinsu
kamar gidadawa sai kin zauna dasu zaki fahinci bakin kishi dasuke dashi ga sakar da
haibaici ga mutum Allah ma yayi maku gyadan dogo mazan naku suna son ku ai da baku
kai labari ba.
Haka suke da sa ido ga abinda yayansu keyi da matayensu su koma kamar kishiyo
dasu saidai ba a taru an zama daya ba don wayayyun basa haka gaskiya.
Banda murmushi ba abinda nakeyi kawai na gama na wanke hannuna ta koma fadin kai
gaskiya mijinku dai yaji jiki wallahi wasa wasa fa yakai shekara da rabi yanzu ai
nace za a kai gaskiya ciwon ya dade a jikinsane .
Tace balle abu ya kasance na jifa ai sai yawancin rai irin hakan son ma dai suna
tsayene suma ba a samu yadda ake so ba dashi.
Hamma na soma yi hakan yasa take fadin tashi kije ki kwanta ki samu hutu yar nan
nima bari na kwashe kayan nan zuwa kitchen hakan ya rabamu da ita ranan na fahinci
tana da son surutu gaskiya.
Washegari kodana tashi nayi sallah na koma na kwanta abinda ban sababa nayi
barcin safe mafarkin da nayine ma ya tayat dani misalin tara da rabi na safe sai
nake ganin ai rana yayi sosai lokacin.
Mikewa nayi zuwa bandaki ban fito ba saida nayi wanka na tsabatace jikina nafito
na shirya zuwa falo ina neman abin karyawa.
A falon na samu ummah zaune tana karyawa itama tana waya tun kan na karaso na
fahinci wayar dai a kainane har lokacin gaida ita nayi da kwana ta amsa tana fadin.
Yanzu nake zancen na tayar dake ashe ki dade da falkawa ga abin karyawa nan ki
zauna kici ta fada tana nuna min abincin a bakin table nakai zaune kamar zan bude
sai kuma nace daddy fa ya fitane ?
A,a manjo ai bai fita ko ina shi indai baya kama ba ko ina bai zuwa shi ko
yaushe yana gidan nan dan dama da yamma yana zama ta wajen gidan nan da mutanen
unguwa.
Balle yau da yasan yana da baki koda fitan ya kamashi ai bai zuwa ko ina sai
sunzo sun wuce ban tambaya suwaye bakin ba tunda ba abinda ya shafeni bane.
Sai misalin karfe sha biyun rana saiga sallaman mama da iya tare da yazid maria
da habu suna bayansu suka shigo gabana ya fadi daki na tashi na koma da sauri don a
falo nake kwance ina kallo abinda na dade banyi ba ke nan a rayuwata.
Ummah ta kunna min wai in rage rana a nan din tunda ni kadaine bata san hakan
baya damuna ba don na saba ko a gidana wani lokacin ni kadai ke zama ai.
Sun shigo naji ana gaisawa dasu suna tambayan ina inane tace ina ciki maria ta
mike zuwa uwar dakin ta sameni ko kallonta banyi ba a wajen .
Take fadin yanzu ke haka yayi maki ai gashi saratu taji dadin hakan can yazid ya
kamata tana waya tana fadawa Nusaiba yai mata dan kareb duka jiya ya hade mata
haushi biyun ta da yake ji.
Dama nayine taji dadin ai abinda bakina ya fada ke nan nace kinga saita dawo da
nusaiba din tazo tayi ta haifa masu yayan halas a gidan.
Ki bar wanan zancen don Allah jiya aita kwammace da bata fada ba din don yadda
akai mata dukka yan uwa kuma sunce wata daya suka bata ta fito da mijin ko suyi
sadaka sa ita.
Ke jiyafa da yaya J ya mutu wallahi don faduwa yayi harda jin ciwo wai abarshi
ya biyo ki ko yanzu ma dakyat aka samu ya zauna don mama tayi mai alkawarin dawowa
dake yau din.
Cab aiko tayi kaffara don wallahi ba inda zani barin fada maki wanan gidan har
shi sun fita raina wallahi suyi da wata kuma badai Rahama ba kuma ?
Wasa dai kikeyi kina son bawan Allah nan ya shudene Rahama baki ganshi bafa
mama tayi fada duk da bata so laifin Saratu amma tun jiya take kan zaginta gidan
nan akace.
Su wanan ya shafa ko ince ku amma ni na fada maki ba zan koma ba gaskiya nagaji
wallahi neman sanadin abinda zai zubar da cikin nan nasa nakeyi yanzu a jikina na
daina tuna komai nasa ga baki daya.
Wai kanki daya kuwa Rahama kodai kema din Nusaiban ta hada da kene wajen mallaka
ta yamutsa maki hankali baki komawa kamar yaya ?
Nusaiba fa kikace Yanda in an fada maki nusaiba zata iya min wani abu ya kamani
a duniyan nan baki mussawa ko kin manta dani yar baffa ne ?
Saidai ta Allah bata mutum ba kin sani amma mutum ya gwada idan yana ganin haka
sai kace ba diyar fulanin asali nake ba muryan ummah ne dake kirana tana fada akan
banji zuwansu bane naki fitowa mu gaisa dasu.
A daidai lokacin kuma mijinta ya shigo falon suke gaisawa dashi na fito na
gaidasu duk sun kura min ido suna bina da kallo ?
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:44] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
7️⃣8️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Ya kasance mun shigo falon a tare da daddy muka gaisa nan mama ta soma fadin haba
diyata don me zakiyi min haka duk hakkurin da nake baki ?
Dukar da kai nayi kasa a cikin jin nauyinta ina wasa da yatsuna ta cigaba da
fadin kin kamo hanya kibar min dana a cikin tashin hankali jiya ?
Gaba daya jiya sam bamu gane kansa a gidan nan don ya rikice muna ciwo yana
kokarin ya dawo saba a jiyan Allah dai ya gyara.
Alh ayi hakkuri a bamu yar mu mu yafi da ita don Allah ko zamu samu ya kara
kwantar da hankalinsa don in ba komawa tayi ya ganta ba gaskiya yana iya samun
matsala.
Murmushi daddy yayi ya gyara zama yana fadin ai hjy banki ta takiba don babu
iyayyen dake son yarsu ta taso daga gidan aurenta ai gata nan zaune idan tace zata
biku din wa,lillahi hamdu udan kuma tace a,a to ba dole don ni banwa yaro dole akan
rayuwansa.
A,a Alh kada kace haka adaiyi hakkuri shima ya tareta da fadin yes iya gaskiyata
na fada don yarana kaf banwa kowansu dole akan matsalan aurensu.
Don bani ke zama dasu ba a can amma ba inda za ace asa ido yarinyat dako auren
farko batayi ba tana kokarin sheganta jinin dan uwanta amma ba a dauki wani
kwakwaran mataki a kanta ba.
Inaga idan dan yazo duniya sai abinda taso zatayi mai na wullakanci ke nan don
tun jiya datazo da zancen nan da ace nine na haifeta da wanan yar ta kwana a
cell .
Taje can ta koyi ladabi da kama baki na kwana biyu kafin a sakota saidai za ace
don banina haifi Rahama ba a yanzu idan nayi hakan.
Alh dan yaune kanayi kamar bakayi in bashi ina wanan zancen zai fito haka a
bakin yaro adaiyi hakkuri don Allah an tsawata mata ai.
Nan Habu ya tsoma baki yana fadin daddy yarinyar kamar wata mai motsi a kai don
tsaban iskancin da takeyiwa matan mu saida na taka mata burki a gidana.
To kagani kai kayi mata iyaka da naka gidan gidan dan uwanka ke nan ta koma ashe
gaskiya zancen yayi muni ace a bakin yara ya fito bako manya ba ban taba gani ko
jin yadda dan uwa zai batawa dan uwansa jininsa haka tun baizo duniya ba ?
Yarinyar banzace daddy ayi hakkuri don Allah hakan ba zai sake faruwa ba da
yardan Allah kwanan nan duk aure za ai masu su kama gabansu.
Kaiya ko kun masu aure ai suna tare daku kun taba ganin inda wuya yabar kai sai
gangan jiki kawai ?
Yanzu ga yarinyar nan ai a kusa muji ta bakinta na fada maku tun farko ba zan
mata dole bani don bani shiga hakkin mutum a rayuwata.
Kafin ya rufe baki na amsa da daddy ni gaskiya ba zan koma ba su aiko min da
takardana kawai in huta ina fada a cikin kuka sai salati mama da iya sukeyi .
Mama na fadin yar nan da bakinki kike fadan haka a gaban mu me mijinki yai maki
da zaki yanke danyen hukunci haka tsakanin ku ?
Iya take fadan hakan kuka sosai nasa ina fadin iya niba zan koma ba inda ba a
kaunata ba kuma ba mai daukan min mataki ga hakan saidai aga laifina idan na dauka
ni gaskiya ban komawa gidan nan kuka sosai nakeyi a lokacin.
Haba yar nan kiyi hakkuri zancen nan ya mutu a nan ki shirya mu koma gida amma
zancen ba zaki koma ba ai bai taso ba mama ta fada.
Mama nagajine nagaji nina san abinda ake min kan ya jafar ina hadewa gara kawai
in bar gidan zaifi ni dai bani bace na dafewa yaya saina aureshi shi yaje yasa
iyayyena suka aura min shi bada sanina ba kuma nayi hakkuri na zauna dashi duk da
irin barazanan da nake gani a gidan wallahi ba zan koma ba.
Cikin bacin rai don ya nuna min shi wanine a gareni lokacin ya mike tsaye yana
fadin Iya ku tashi muje tunda hakane don taji ance ba zata koma ba udan bata so
zata tsaya tana muna wanan shakiyancin haka ?
Habu ke fadan hakan cikin bacin rai ya mike yana fadin su tashi suje nan dan
uwan yace a,a bros ba za ai hakaba dole mu lalashe ta tunda laifi akai mata.
Me kake son muyi yanzu tunda an fada mata matakin da za a dauka kan abin tace ba
haka ba ba saita zauna gidan ba ban taba mashi rashin kunya ba sai a ranan .
Nima a hasale nace dashi a barini mana sai me idan na zauna gidan ai yafi min
sauki da zama inda ba asan darajata ba sai wajen amfani .
Ko an barni aiba mutuwa zanyi ba hakan ma tafi min dadi da zama inda a kullum
laifina ake nema a gorantawa iyayyena don ana daukan mu marasa gata.
Rahama ni kike fadaqa wanan maganan yau haka ya fada yana kallona da sauri mama
tace kai habu gyara mukazo yi ba barnawa ba don haka kabi abin nan sannu don Allah.
Nima shina gani tunda har yarinyar nan tayi haka an dade ana cusguna mata tana
hakkuri yanzune take ganin tagaji koma waye gaskiya haka zaiyi.
Baiyi magana ba har matanshi shiru tayi shiko ya juya ya fice falon yana fadin
ummah nina tafi ke nan sai anjiman ku ya fita.
Daddy yayi murmushi yana fadin ga alama nan ya nuna kanshi ko a yanzu yarinyar
nan an tabata a rarasheta amma yana son ai mata dole ta koma ?
Ba dole yayi min hakana ba tunda kansu hade yake da dan uwanshi amma aishi da
aka tasa matarshi gaba ya dauketa yabar gidan a lokacin duk da ban gidan ban huta
ba tunda har inda nake ake biyoni aci min mutunci akan gaskiyana.
Dashi da jafar din waya taba daukan mataki udan ba iya ke kusa ta tare min ba
bagaji wallahi ni ba zan iya ba gaskiya na fada na mike zuwa ciki ina kuka .
Ajiyan zuciya ya daddy ya sauke yana fadin wanan abin dole a tsaya a natsu abawa
yarinyar nan lokaci don Allah harta sauko don na fahinci ranta abace yake yanzu.
Idan munce zamu mayar da ita da karfi da yaji abin ba zaiyi dadi ba gara dai a
bari ta dan huce zaifi sauki saita koma din.
Abinda nakewa gudu ke nan nasha fadawa dubu hakan tana ganin bai zama komai ko
kuma ta dauka ai basu da gatan irin haka yau gashi dai din ya faru ai.
Amma na dauka akan Saaratune da abokan zamanta matsalan ai yazid ya fada yana
kallon iya iya din tace ai kaji metace ko yanzu kokai matanka ai don suna ciki
kullene ko yaushe basu kwasa da ita.
Bar dubu inda ka ganta akan yaran nan da kawun ku hardai ace maka sun hade da
shedanin nan guda dauda to ka barsu kawai na gayama .
Ni yanzu aiba mu koma babu yarinyar nan bace yaron nan Jafar ya rikece muna
yadda yayi jiya ni shine tashin hankalina a yanzu.
A to mama tunda ance a barta ai dole mu barta din har ta huce yaya zaiyi kuwa
banda hakkuri tunda ba tare aka haifesu ba dama ?
Yasan yana sonta haka yarinya tana kokari dakai baka iya kareta ga kowa anatayi
mata cin fuska yana kallo bai dauki mataki ba da nine gobe wata ba zata kara ba ai
idan anga irin matakin dana dauka.
Yaren fulancin da mariya tayi tana mikewa tsaye shine yasa suka bita da kallo
itama ummah yaren tayi mata tana bata amsa don fadi take wai akan me zanyi haka
tunda an biyoni bari ta ganni.
Shine ummah din tace gaskiya itama bata son a barni in koma kawai kowa ai hakkuri
yakeyi a gidansa shine ta nufi dakin wajena.
A kwance ta sameni na kifa cikina ina hawaye tashigo ta tsaya a kaina tana fadin
yanzu ke kinga haka yafi maki kizo ki zauna nan ?
A fusace na dago na tareta da fadin ai dole kice haka tunda bake bace akewa
abinda akemin a gidan koda yake ke naga hakan bai dameki ba ai dama toni ban daukan
hakan .
Kiri,kiri mama ta nuna bata son zaman mu da diyanta abinda take muna idan ayiwa
diyanta zata dauki hakan ta kyalene ?
Ko gaida matar nan nayi duk zuwan da nakeyi gidan nan bata amsa min sai taga
dama duk abinda sararu tayi min da sanin mama .
Tunda sunce ni ba alheri bane ga yaya Jafar sanadina abubuwa da dama suka
sameshi na barshi don abubuwan su wuce din garesu tuda nice matsalansu.
Ashe in kina bin zancensu ba zaki zauna da mijinki lafiya ba kuwa don su ko
ajikinsu kuma kina gani tun baki aureshi