Showing 51001 words to 54000 words out of 328222 words

Chapter 18 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

alale da mama
ta hada.
Nikan tun da aka soma kiran sallah nashige ban fito ba sai suke kai da komo akan
abokan yayan nasu abincin asibiti da za a kaiwa ummah na buda baki na fito dashi
don dama na damu banji ana zancen kaiwa uwata abinci ba gashi lokaci ya shige wanda
aka dauka don hakan yanzo lokacin dauka.
Sai lokacin naga motoci zasu kai biyar a wajen nasan ashe yawa garesu don
abokanshi na kurciyane dama haka suka taso sunayi a tsakaninsu.
Ummah dataga har lokacin shan ruwa yayi ba a kawo masu abinci ba ranan yadda aka
saba saita dan fita don tasayo dabino da ruwan sanyi a wajen asibiti.
Ganinta yasa wata mace da suka saba take fadin hafsatu yanzu nake zancen yau
banga an shigo maki da abinci ba kizo mu zauna mu buda baki kafin a kawo maki.
Da kunya ummah tace da matar a,a ki barshi zasu kawo akwai abinda ya tsayar dasu
ai kila amma suna tafe nasani haba hafsatu .
Aiko ba sabo haka tsakanin mu akwai na musulunci don Allah zo ko dabino da lemu
kisha ga ruwan sanyi kada kice a,a ki hana min ladan hakan ?
Dole ta zauna suka sha ruwan tare saidai dabinon nan da lemon da ruwa kawai taci
daga garesu suka mike don yin alwala.
Nan suka zauna bayan sun idar suna dan hira matar tana buda bakinta tunda tasan
baci ummah zatayi ba kota matsa mata.
Ruwan sanyi ma gashi ranan tana ganinsu dashi amma haka taje gurin sayarwa ta
sayo saida matar tagani take maganan bata kyauta mata ba meye amfanin zama taren da
sukeyi kuma ?
Irin halaiyan ummah na kama kai yasa matar sha,awan ummah din sosai gashi ita
kome aka kawo mata saita nemi matar ta bata koda abin dan kadan ne amma ita bata
saka ido ga kowa sai abinda ya kawota.
Har mu dake zuwa mun san da shakuwar ummah da matar don bamu shiga mu fita sai
muje mun gaida mara lafiyan su da matar a duk inda take.
Ainihi matar daga kaduna sukazo ba a cikin garin zaria suke ba saidai suna da
yan uwa sosai a garin don haka gidane masu zaria din.
Tana zaune ta hango yaron yana nemanta ta kirashi yazo da basket da ledan poly
bag yana gaisheta bai bata kayan a nan ba saida suka shiga ciki ya aje.
Ya gaida yanda da ba,a bari su fita ko ina sai idan su suka bada umurnin mutum ya
fita daga dakin zai dan fita yasha iska ya dawo ciki.
Kai bawa ya godewa Allah aduk halin daya samu kansa a ciki rahamace hakan garesa
daga Allah wata zatayi cikinta lafiya har ta dauka ta haife bata taka asibiti ba .
Saiga wasu kuma don son haihuwan za a rikesu gun likita harsai sun haife cikin
saboda tsaro irin hakane sa,an jahiliya mace tayi ta daukan ciki tana samun mata
har mahaifa yazo a karshe ya kasa daukan cikin don wahala.
Ita kuma yanda abinda Allah ya jerabeta ke nan dashi a rayuwanta har wasu naganin
hakan samun wajena kawai da jin dadi irin na wasu matan da sukeyi da gangan.
Bayan na idar da sallolina na shiga wanka na fito na zauna na gyara jikina ina
dakin nake jin muryan Saiba a falo wai tazo idan masa da miyar sun rage a zuba masu
su kara wanda aka kai masu sun cinyeshi gaba daya.
Naji muryan mama tana fadin ba za a rasa masa da miya ba ai fruits salad din
daine ban zata yaran nan sun rage ba ?
Muryan Salimace ke fadin mama kinsan fa nida Ramaah bamuci komai ba sai anjima
kada ki kwashe ki basu duka bamuci ba.
Salima meyasa kike hakane masan nan mai yawa ina zaki kaishi don Allah azumi
akeyi balle kice da safe zaki shi .
Mama meyasa basu fito anyi aikin dasu ba aimu ba bayinsu bane da mukayi tunda
aikin mijinsune ?
Sai abin yaso ya zamo kamar fada a tsakaninsu da anty Salima din har Saiba na
fadin ai dai mijin su ya kawo ai masu dole kuma suci ko bata so ai itama zata gidan
wasu za a rama masu abinda take masu can.
Muryan ya Habu naji sai lokacin nasan ya shigo gari ashe shima yana garin tunda
yamma tare dashi akasha ruwa.
Shigowanshi gaida su mama shine kashe fitinan da saboda sanyin hali irin na mama
ta kasa kashewa a lokacin.
Saida naji fitan ta na fito ina gaidashi da dawowa ya amsa min kamar kullum ba
yabo ba fallasa a fuskanshi yana tambayan ya gida ?
Na amsa da lafiya kalau nan dai muka zauna suna hira dasu mama wanda hiran akan
saiba ce data fadi maganan banza.
Naji ya habu din yace da mama daga yau duk abinda ya kawo ki barshi yakai masu
can kome za ayi suyi masa da kansu sune dolensa ai tunda shiya ajesu.
Nima dai a raina haka nagani mutum mai mata biyu kamar yaya jafar sai ya tsaya
yana wahal da mahaifiyarsa da kannesa kuma ko kuma ya dauko yar aikin da yace zai
dauka mana a baya ya dinga biyanta duk wata.
Ina zama na debo masa kwara biyu da miya sai gashi ya shigo part din daga
rakiyan abokan nasa ya ajewa mama leda yana fadin.
Kai mama yau kun fitar dani kunya da bakin yan sherin nan kinji yadda Anwar yake
santi kuwa ?
Gata nan dai itace zaka godewa yanzu haka zancen ka samu munayi a nan matar ka
tazo nan kan wanan abin tana fadan abinda bai dace ba.
J don Allah daga yau din nan duk abinda ka samu na laluranka ka dinga bar masu
can suyi ai suma matane kamar kowa ?
Me zai gagaresu iyawa da har zata shigo nan gaban mama tana fadin magana haka
komai na gidan nan suna zaton nakane don haka yaran nan basu da daman magana a
kai ?
Me tazo tayi nan Habu ba naga Saratu ta shiga masu da nasu ba dazun kafin a sha
ruwa ?
Koma dai meye sun din suke da alhakin irin wanan aikin gareka basu mama ba da
yaran nan don a kaucewa fitina irin haka.
Kuma ka kyaleta tunda nayi mata magana ba sai kaje kayi fada da ita ba ita wanan
halintane gori da rashin kunya So ka barta don Allah.
Ranshi dai ya baci amma ya kasa magana don yasan halin matan nasa sarai kome
akace tazo tayi zata iya don yar rainin hankalice ita.
Bai jima ba ya fice daga falon zuwa part dinshi shima ya Habu din ya fita saida
mama ta tambayeshi koya leka asibiti ?
Naji yace ai can ya jima daya shigo gari can ya fara zuwa ya dubasu kafin yanzo
gida nan yake fada mata cewa likitocin sunce jibi zasu shiga da ita suyi mata
scaning a duba lafiyan cikin ta din.
Washegari kamar kullum ban fito da wuri ba kamar jiya daine kodana fito a falo
na samesu ana ta kasafin kayan shayi da abubuwan more rayuwa na dan adam a falon .
Nagaidasu nashiga kitchen har lokacin kayan da akaci ya rage suna wajen ba a
samu wace ta saka a cikin fridge ba dole na tsaya tunda miyar baiyi komai ba na
adanasu a cikon fridge din.
Rahama ku karbi key kukai min kayan nan a part dina ya habu ya fada nida salima
muka kwashe kayan a hanya take fada min wai ashe ?
Jiya ya J sunyi fitana sosai da Saiba har ya mamareta yana fadin sai ya sake ta
don ta isheshi tana son jawo mai matsala da yan uwansa.
Ina gyaran falon take fadin ai har Saare yau mama taci mata mutunci sosai da
safe tace ta daina shiga part din ya J din tunda duk tsegumi ya taso da sunanta a
ciki.
Wayanta da mama ta kira tana tambayanta ina muka tsaya gashi tana jiran mu mu
mikawa makwabta munje can mun zauna take fada mata Ramaah ke gyarawa yaya part din.
Bayan mun dawo muka dauki kayan da aka warewa makwabtansu niki niki muka shiga
gidajen muka bayar ba hutu kuma muka dauki na tudun wanda wanan ya habune ya kai mu
da motarshi muka ba kowa nasa ana saka albarka muka fito daga unguwar.
Ranan kan bamu iya komai ba sai mace tayi muna abincin buda baki ita da Saare
saboda mun gaji sosai a ranan wajen raba abin buda bakin da ya J ya rabawa yan uwa
da abokan arzkin su tunda mune kamar yara a gidan.
Sai bayan shan ruwa a buda baki iya ta soma magana tana fadin gidan nan kan
ranan da yarinyar nan ta barmu zamuji daban .
Yau kadai har munyi kewan girkin yar nan to iya kina nufin ni bam iya girki ba ke
nan shiyasa bakici ba saiga mama kuma na fadin ke salima jeki kitchen ki dumama
muna miyar jiya wanan kan ina zai ciyo ga yaji ga gishirin tsiya miya kamar an
wanke kan mahaukaciya haka ?
Fushi anty Saare din tayi tana fadin ita shiya bata zama duk abinda tayi yanzu
sai ace bai yi ba Ramaah ta fisu iya komai.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC


MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,1

1️⃣9️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Idan suna gida bamu da hutu sai sun bar garin zamu dan dafa abu mai sauki da zamu
bude baki dashi a irin hakan na fahinci abubuwa da dama a rayuwa.
Na farko komai arzikin ka a waje idan akwai wanda ya daraka naka sai ya zamo
babu mai ganinsa saidai wa yanda suka zama dolen ka su gane maka hakan.
Don yanzu da mai lokaci ake zamani harda wasu uwayen suna nuna irin wanan
bambanci a cikjn iyalansu da suka duka suka haifa.
Zakiga uwa kamar tana shakkar danta don kawai yana da hali shike daukan
dawainiyar ahalinsu sai a koma jin tsoronsa shiya zama kamar bakece kika haifishi
ba.
Da yawa a yanzu ana samun hakan ga iyayye saidai akwai jijirtattun iyayye da har
gobe suna a maysayinsu na iyayye din komai mutum ya zama kuwa.
Zaki suma sauran diya suna nasu kokarin amma ba a ganin hakan da sukeyi hankali
sai ya koma a waje daya anfi ba bangaren dake da maiko muhinmancin.
Saidai gaskiya a nan din ina kallon abin kamar da dama sosai don dukka yaran
nata biyu tana basu kulawa irin yadda ya dace uwata gari tayi din.
Don ko shima ya Habu yana tsaye da dawainiya dasu sosai duk da kamar karfinsa
baikai na jafar ba da akewa kallon maikudi a cikin dangi .
Dan kowa ya tashi dai jafaru dai jafaru dai nazo a roka min jafaru abu kaza da
yawa haka suke zuwa a cikin dangi wajen mahaifiyar nasa tunda Jafar din baida
tsayayyar matar da yan uwa zasu buga gaba da ita.
Zakiga abin mamaki a babban gida da abin haushi har dana takaici shi jafar dai
ya kasance mutum mai ujula yanzune zaizo kuna magana sai kuma wani uzuri ya kamashi
ya barka wajen.
Ya Habu kuma akwai tsare gida gashi shiru shiru bai faye magana ba amma akwai
tsayawa ya fadi gaskiya don hakane ma kowa yake shakunsa a gidan haka kuma na kula
Mama Dubu tafi ba Habu din lokacin ta da daukan sha,aninsa da muhinmanci.
Rayuwa tana ta tafiya a hakan dai inda azumin wanan shekaran ke muna bankwana
akwai dadi kuma akwai wahala wajen aikin abin buda baki ga mata.
Sallah saura sati daya suna zaine ranan dai duk iyalan mama dubu suna zaune a
falo misalin karfe hudu bayan sunyi sallah azahar ina kitchen ina ta hada abin buda
baki don yanzu ban tsayawa jira tunda jiran baida amfani karshe a kaina aikin yake
karewa kowa dayasha ruwa zai nemi waje ya labe.
Ka zamo mai zafin nama wani lokacin akan kwari mutum ga hakan kowa saiya sakama
ido don amsan zaka iya din .
Saida hakan bai damuna don da zuciya daya nake hakan, suma kuma sun sani, haka
kuma wanan aikin yafi min aikin gidan baffan mu sauki sau dubu.
Gidan baffa karfe hudu dole mu tashi mu fara surfe idan mun gama gari ya fara
haske mu dauki jarkan diban ruwa muna gamawa da mun dawo zamu cika jallon mu da dan
gudun kokon da zamusha wurin kiwo mu zamu daka amma kuma a hana muna.
Shiyasa nake kallon wanan nagatane tunda ni zan dibarwa kaina iya cina don haka
ai wanan ya zamo gata kuma ga hutun da nake samu nayi na tsawon lokacin.
Rabon kayan sallah Jafar din da Abubakar sukeyi sai mama da iya da kannensu mata
dake ta rubutu a takarda suna mannawa su kuma matan shi suma suna nade kayan.
Mama nifa har yau banji ance ga kayan sallah Ramaah ba salimace ke fadin hakan
wa mahaifiyarsu ta kureta da idanu ?
Kamar ya ba,ace Ramaah ba ba yaya Habu zai mata ba ita da matarshi Saare ta riga
uwar bada amsa .
Habu kuma Saare don tana kanwar matar Habu za,ace shi jafar ba zai mata sutura
ba kome ?
Cak suka tsaya ga abinda sukeyi gaba dayansu suna kallon mama din da saratu au
kece zaki tsara yadda abin zai kasance ashe ?
Wai akan wa ake magana Jafar ya tambaya da sauri salima tace Rahama ranan full
name dina ta fada kai tsaye.
Ramaah ya juyo ya dan kalli dan uwan nasa yana fadin Rahaam bata da kayan
sallah dama kuma baki fada min ba salima ?.
Yaya na dauka ka sani ai shiyasa ban fada ba da wuri naga kowa kuma baiyi
magana a kanta a yanzu ba yasa nayi magananta ai.
Wai wa kuke zancene bai samu kayan sallah ba cikin mutuwam jiki da jin nauyi
mama din tace wanan yarinyar wallahi .
Ni abin gidan nan yana ban mamaki ta ya yarinyar dake dawainiya daku haka zaku
dinga cewa kun manta da ita don Allah zama baice haka ba wallahi.
Iya ta fadi hakan cikin hasala tana juyawa kafin mama din tace a,a Iya munyi da
Jafar tun a waye yace kayan sallah nace na yaran nan su uku zai sayowa kinji yadda
mukayi na dauka harda nata aka hado ai ?
Wai dai wace yarinya ke Asmau dana kawo kaya mena fada maku da aka fitar dasu ?
Nikan kace nasu Saare ko kace mu zaba mu basu saura kuma muka zabi namu muka
basu nasu ta karasa a sanyayye tana dukar da kai.
Toke salima waya baki kayan ki ta amsa da fadin Saarece tashigo min dasu takai
dakin mu ko wani bibiyu ta zaba ta ban nawa shike nan.
A,a ni ban gane ba Saratu ina na wanan yarinyar ya shiga don Allah J is enough
idon kayane a barshi kawai ke salima kuje a sama mata kaya gobe shike nan .
Ya zakace dani shike nan wancan karon ma haka sukayi aka raba abu a gidan nan
suka hana mata har mama taga laifina gashi kuma again ankara yi don haka ina son
ina kayan nan suka shiga ?
Suna tsakanin makiran matarka mana ai kaji sunyi shiru ga baki dayan su sunsan
yadda sukayi da kayan ke nan a tsakaninsu tunda suna bakin ciki da zaman boyar
Allah nan gidan nan.
Itako bata ko san sunayi ba don basu gabanta sun dauki kiyayyan duniya da kyashi
sun dora akan matar kani banda tsiya harda kanwata zaku saka a kishi.
Ita kanta matar Habu bata san kunayin haukan ku ba hakama yar uwar nata gashi
dukkan mu nan gidan muna moran wanan yarinyar.
Ko wanan aikin da take ga sharan nan ga girki yaci ace yarinyar nan ko albshi
ake mata tayi kissa amma ina tunda suna da wankakken zuciya ba hakan a gareta duk
iyace take fadin hakan garesu.
No ba zancen da za ace a kyale bane wanan duk da ba zama nake a garin nan ba
nasan irin kokarin da yarinyar nan takeyi gidan nan kullum.
Ko a fito min da kayan ta inda suka shiga ko kowan ku ya kawo nasa nan yanzu ku
har saratu din ban cireta ba ?
Dama ai tunda koma meye da ita aka hada baki aka kulla hakan tasan komai tunda
hanyar data zaba ke nan bakiji kunyan hakan da kukayi ba don Allah ?
Ina yarinyar nan kamar yadda Iya ta fada duk gidan nan kowa yana cin moriyanta a
yanzu ku duba zuwansu yadda yanzu gidan nan ya koma fes dashi don Allah ?
To mama akan me zai sayo muna kaya iri daya da ita idan su Saare yan uwansane
ita kuma meye nasa don kawai tana kanwar matan Habu ?
A zabure ya tasowa Saiba din dake magana a lokacin, tayi saurin fita don ganin an
taresa daga zuwa gareta ta fita tana maganganu masu zafi game dani.
Hawaye naji sun zubo min don a yanzu kan ba fahinci zancen da sukeyi a kaina sai
hukuncin ya Habu ya burgeni da yace to ai gaskiya ta fada kada kuga laifinta don
Allah.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login