Showing 267001 words to 270000 words out of 328222 words
Chapter 90 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
dauka hakan gwanintane a wajenta
ai.
Abinda nake son mata su kulla a nan shine matukar kina shuka gaskiya cikin
lamarin ki ubangij Allah yana tare dake a ko wani hali saidai idan kece kika raina
abinda kika gani din a kanki.
Ban taba zato ko tsamanin cewa zasu shigo haka kamar yadda daddy ya bukaci
ganinsu ba amma sai gashi Allah yayi ikonshi dole sunzo din har gaban su ummah suna
bada hakkuri.
Washegari anty Nuratu tazo gidan ta daukeni farko wajen wata mata muka tafi yar
maiduguri ina dai kallonta a raina nace nu dake da mummy a abuja ana gwada min
wanan abin ?
Saidai lokacin da matar ta fara fitar da kayanta na fahinci kowa da nasa sabin
ashe ita anty Nuratu din ta biya da kudinta muka fito daga gida.
Muna mota take fadin ni naga no need asai maki wasu sutura a yanzu haka zaifi
kyau bayan kin haihu muyi wanan shirin .
Nima ban ra,ayin wasu sutura wanda aka dinka a baya suna nan cushe ta juyo tana
fadin wallahi ki dingawa mijinki kwaliya kanwata.
Kada ki yarda ki saje da wa yan nan matar nasa marasa kan gado ga miji tsab
tsab aje aga matansa kamar rainon kauye ba kyau gani .
Ni tun a nan na raina masu wayau wallahi suna ganin don yana kwance yana jinya ba
zaiji dadi bane idan sun gyara jikinsu ?
Krdai abinda nake so dake ysnzu Rahama shine kada ki yarda ku zama daya dasu don
Allah ki bambanta kanki dasu ta wajen kwalliya abinci da gyaran gida.
You are lucky ma ba a gida daya kuke rayuwa da kazantannan ba don wallahi dazaki
sha wuya ga hakan don haka ya kasance ya zamo yana mararin dawowa gareki ko yaushe
wanan ne kishin zamani ai ba zama ana hauka ba.
Haka kuma zancen yan uwansa daddy ya fada min komai kada ki kara damuwa da
lamarin su don Allah shi dan uwa marfin jallone basuyi saida shi haka kuma shi
bayayi saida yan uwansa.
Ki dai dauki matakin zama da kowa don Allah kada ki kara bada daman da zasu
rainaki kuma ki daina cacan baki dasu haka ko yaushe.
Sufa yanzu takaicinki sukeyi sister suna ganin kece star din gidan duk wani
shawaransa dake yakeyi so kinga dole suyi bakin ciki dake haka ?
Yaushe zaki wuce servuce dinki jn haka yasa na gyara zama ina nsawa nace zuwa
next month ne in sha Allahu.
To ki mayar da hankali don Allah Rahama ki dage sosai ki zamo wata a cikin
family dinku don Allah kece Allah ya zabo kila da zaki tallafi kowa.
Ki daina yawan shiga cikinsu sai un wani abu mai muhinmanci ya faru ke leka
kada ki jima ki fito sosai zaki dauki girmanki fa Rahama .
Ita wanan kanwar tashi ba komai bane illa zallan hassadanki da takeyi tunda taga
kin tsaya kinyi karatunki tasan zaki zama wata abu nan gaba a cikinsu.
So ina son ko baki dauki shawarana dukka ba Rahama kiyi amfani da wasu don Allah
a karshe takaini wajen gyaran jiki aka lugudeni tas na fito kamar bani ba .
Anan take fadin ki kula ki dinga shigowa kina gyara jikinki ko nan ko kano din
duk da nasan zarian ma ba za a rasa ba amma ba zaikai nan dinba ai.
Kamar yadda ummah ta sheda min wanan sister din daddy da muke kira da gwaggo
Laraba itace dasu anty Nuratu suka mai dani gidana na kaduna ranan jumma,a .
Nayi mamaki kwarai yadda naga yan sauye sauye a gidan anyi min hakama wajen
gidam anyi sabbin abubuwa na zamani a haraban wajen gidan.
Saida aka fito daga jumma,a sukai shirin komawa kaduna a lokacin kuma ya bugo min
waya yana min barka da jummah yake fadin sun fito daga sallah yanzu ya dora da
fadin.
Watau har satin nan ya shige Rahama bakiji tausayina kin dawo ba ke nan Allah ina
wahala rashinki a kusa dani sosai Rahama goben nan zaki ganni a kaduna ai.
Idan kaje ka gaidasu nikan ina zaria yanzu haka tun karfe shadayan rana muka
shigo garin nan nidasu anty Nuraru.
Kina ina yanzu na sameku nace gidana a takaice sai naji yace wasa kike min dai
ki dawo garin nan ace ban sani ba Rahama ?
Duk da ina daurewa a yanzu don fada da nasihan danasha a kanshi na dan daina jin
haushinsa da nake ji kamar farko amma hakan bai hana na dankara mashi magana ba.
Don Allah wai da gaske kin dawone ya sake tambaya nace kazo ka gani mana yanzun
nan ma su anty ke shirin komawa kaduna su.
Ina jin yana fadin kai mu gani koda gaske takeyi ya kashe wayan tashi da sauri
muna falo suna batun fita suka shigo shida Yazid.
Har yanzu dai saida dabara tafiyan nasa haka kuma kallon daya zakiyi mai ki
fahinci yana sauran jin jikin nasa karfin haline kawai yakeyi irin na dan adam.
Fuskamshi kyam a nawa yake fadin wallahi na dauka wasane kike min baki dawo ba
suka shiga gaisawa dashi gwaggo tayi mai nasiha sosai kafin ta mike tana fadin
Allah ya bamu alheri.
Sun tafi Yazid ya rakasu har gidan mai ya kara cika masu tanki da mai ya kuma
basu tukwaicin kamar yadda dan uwan nasa ya umurceshi dayi garesu.
Muna falo zaune dashi mama ta kira wayansa tana fadin wai ina kuka tsayane baku
dawo kunci ahinci ba kasha magani ga wanan mutumin yazo fa ?
Ina nan gidana mama gidanka naji ta tambaya da mamaki yace eeh wajen Rahama
data dawo yau nazo daga masallacin inyiwa wa yanda suka rakota godiya.
Ta dawo fa shine zata wuce can gidan don ta raina mutane muryan Saratu ce
karara a wayan take fadan wanan magana ga uwar.
Kallon juna mukayi dashi kafin muryan mahaifiyar tasu race dashi ke nan basu
kawota nan ba sai can gidan suka ajeta wai ko sun manta kana da uwane wai ?
Kit naji ya kashe wayan ya kalleni yi nayi kamar ban fahinci me hakan ke nufi ba
yana nan zaune muna dan hira jefi jefi har yazid ya dawo ya daukeshi nake fadin.
Ya kira yaya Ai ya sheda masu na dawo a turo min Biba yace nayi tunanen hakan
nima anji zan zo da ita insha Allahu suka fice a gidan sai annashuwa yakeyi da
kaninsa yazid.
Bandai nuna a gabanshi zancen saratu yaci min rai ba da alama kuma har mama ta
hau zancen saidai na share kawai na nuna ba komai a fili kamar ma banji ba.
Ya zama dole a matsayina na diya mace in kara hakkuri in daure in dinga shanye
duk wani bacin rai da iskamcinsu yanzu tunda nasan manufarsu a kaina yanzu matukar
ina son zama da mijina lafiya.
Wanda su basu ko iya boyon hakan har salima din da muke dan shiri wani lokacin
bata iya boye hassadanta a kaina saita fada a cikin wasa.
To tunda na fahinci Basu da wani guri saidai suga an samu matsala a tsakanina
dashi ke nan tunda na fahinta zanko tura masu haushinsu akai a yanzu zan nuna masu
kan mage ya waye ashe ?
Duk da bansa a raina zai dawo gidan ba a ranan don yadda naji kalamin mama da
nayi sallah la,asar na fito na gyara gidan tsab duk da ba wani datti na feshe ko
ina na rufe window da kofa tunda sanyi akeyi tuwo kawai na dora don ummah tasa
saudi tayi min miya mai yawa nazo dashi .
Ga kuma soyayyen nama da sauran abin bukata don haka aikin ya rage min a lokacin
ina kwance falo muna waya naji horn din motarshi gidan yazid ya kawoshi.
Bibace ta fara shigowa sai su a baya da gudu tazo gareni tana rugumana nayi
murmushi don naji kewam yarinyar sosai dan rabuwan da mukayi din.
Nan yazid ya zauna yake muna sheri donshi akwai son barkwanci damu haka don
koda su Asmau nakanga yana dan taba hakan saidai ba kamarni ba da sosai yake wasa
din dani.
To ni zan tafi yau akwai sanyi wallahi ga sahiba na barta ba lafiya na fito yau
dai za a barni na huta tunda madam ta dawo yaya .
Zaka koma ka samu jidalin mama kuwa don dai nasan yau kokai ba za a barka ba
wajen fada haba dai ina jira ai sai kaji na balla yarinyar nan saratu zuwa gobe
idan tayi wani rubishi akaina zanci kaniyarta sosai wallahi.
Biba je kitchen ki debi abinci kici nace don basar da zancensu nan yazid din ke
fadin what dama iya ta fada ai ko jiki ka mayar a yanzu.
Don Allah Yazid idan ka koma iya ta shiga cikin gida ta kwanta don kada a barta
a nan ita kadai kwanan nan duk bata kwana da dadi wallahi zazzabi yake damunta a
cikin dare haka muke kwana da ita.
Abinci fa na fada ga yazid din yake fasin naso in zauna naci abincin nan amma
kuma ina gudun makara me kika dafa mai nasan yau ai sai didima a gidan nan.
Murmushi nayi ina fadin tuwone kawai donshi nake so shi kuma nayi yace a zubo mai
yaje dashi hakan yasa na mike na hado mashi tuwon ya tafi.
Saida na zauna nake fadin iya ba lafiyane kuma yace wallahi takai kwana biyar a
hakan kafin yaci gaba wayanshi ya dauki ringing lokaci guda ya dauka yana dubawa.
Mamace take fadin Jafar ina ka fita da sanyin nan kuma nazo baka shiyanka mana
ya bata amsa da fasin gani nan yazid ya kawoni gidam Rahama.
Sai naji tace dashi gidan Rahama kuma da daren nan wai kanka daya kuwa daka je
can din maganin kafa da sanyin nan ka kwashi kafa zuwa gidanta don kawai ta dawo a
yau kome ?
Mama wanan ba abinda ya shafeki bane fa ni hakan ya shafa Rahama matatace kuma
dole inzo gidanta tunda Allah ya ban lafiya a yanzu.
Anzo inda ba a son azo din ranan da zai fara ba mama amsa irin haka dama daddy
ya fada a karshe zata gusar da wanan biyayyan da yake mata ita da kanta lokacun
daya fara hakan kuma ba zataji dadin shi ba kuma.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/23, 14:10] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
8️⃣4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
A cikin zancensu da mama a wayan na fahinvci baida niyar komawa gidansu a ranan
yana nufin a nan wajena zai kwana ke nan.
Banyi magana ba a lolacin saida yayi sallah duk a nan falo na bashi abinci yaci
an dan jima nake fadin Yazid din bai dawo ba har yanzu ga dare nayi kuma baka sha
maganin ka ba kuma !?
Kin ce ya dawone ya kawo mj magani ya tambayeni cikin tsureni da idanuwanshi da
sukayi mugun fadawa a yanzu saboda raman daya karayi kuma yana son jin amsan
tambayansa a gareni.
Saida na sada kaina kasa nake fadin ni bamuyi hakan dashi ba naga dai kana shan
maganine bai kamata a kyatare ba kuma ?
Rahama ko kema gudana kika farayi yanzune kamar wa yan can dama da wanan maganan
yakanci galabata idan irin haka ya taso a tsakanin mu.
Gudunka kuma ban guje ka ba a baya sai yanzu na fada ina daure fuskata to ba
inda zan tafi yau nazo ke nan dama ai kece mai jinyata din suka koreki ko ?
Ka daiyi kwanakinka ka koma ni kada ka jawo min wata magana kuma a sakani a
faufai ana tallah na bayan wannan da nake cikinsa.
Suyi tayi mana waya damu da zancen mutu ni yanzu ban kara jin nauyi ko idon
mutane a irin haka abinda zai fitar dani zanyi idan sun damu dani su biyoni nan su
dubani ai.
Wani kallon mamaki na sake mashi amma ban furta komai ba saboda gudun rashin
fahinta amma nasan hakan ba abu bane da zai yuyu a garemu a yanzu.
Bayan hakan nima ai ina bukatan hutu don haka ba zan sake wahal da kaina ba irin
danayi a baya koma yace din zai zauna a nan nasan mama ba zata taba barinshi ya
zauna din ba.
Mikewa nayi na shiga bedroom dinsa har lokacin banyi magana ba ya bini da kallo
na jima a ciki na gyaro mai ko ina na sauya zanin gadon nasa mai duhu saboda
maganin da ake bursune masa jiki dashi .
Ruwan wanka na hada mai na fito na samu yana waya na wuce zuwa kitchen na dan
kawar da kaya na fito na samu ya gama wayan nake fadin ga ruwan wanka can na hada
ma saidai ban sani ba ko saida magani kakeyi har yanzu.
Yanzu da ba maganin a kusafa ba sai in watsa hakana ba yaushema rabona da wankan
dare tun tafiyanki ai sai inkai kwana uku ma yanzu ko wankan maganin banyi ba.
Da sauri nace saboda kaji sauki ko ka daina magani bayan ciwon bai gama fita a
jikinka ba har yanzu ?
Saida ya langabe kai yake fadin bari kawai Rahama shiyasa manya ke fadin Allah ya
kawar da ranan yabo ga mutum aini naga abu dan tafiyan nan naki saidai kawai a
kyale kawai ba a cewa komai.
Amma ai yanzu na fahinci kowa a duniyan nan ki bari kawai Rahama sosai zakiga
halai yana ya canza a yanzu don darasin dana samu a kwanciyar nan da nayi.
Zance da bansan dawa yakeyi ba don haka ban yarda na zake sosai ba illama cewa
da nayi ka tashi ka watsa ruwan kada dare yayi.
Yai shiru kamar yana tunane kafin naga yana kokarin mikewa tsayen daga inda
nake nake fadin kona taimaka makane ka mike ?
Yace bari na dafa kujeran ai yanzu dole na koyi hakan tunda ba mai zama dani sai
iya, iya kuma aiba zan bata karfina ba tunda itama ta kanta takeyi yanzu.
Haka dai ya samu ya mike ina bashin a baya a dakin daya kai saida ya zauna yana
ajiyan zuciya nice na taimaka mashi ya mike tsaye zuwa ban dakin nayi set up din
komai don har kujara da zai zauna saida na cudashi na fito na barshi ya kara din.
Daki na koma na jawo goran ruwan zam zam din da anty Nuratu ta bani na diba na
fito zuwa dakin shi na samu har lokacin bai fito ba nayi magana ina fadin har yanzu
baka fito ba ashe ?
Sai naji ya amsa da fadin ina kara zubawa jikina ruwan zafinne don sunyi min
dadi sosai a jikin zama nayi na fara jero adduan data koya min .
Wanda kowa ya sani ga sauki ga falala ga musulmi shine suratul fatiha da ikilas
sai la,ilaha illah anta subba hannaka innin kummtu minal zallimin kafa 41 da daya
data kira shi da raina kama kaga gyaya .
Koda ya fito ya samu ina sauke falaki da nas da kulluhullahu kafa uku uku ina
tofawa yana zuwa ya zauna na mika mashi ya sha .
Saukin abin sam baida gardama shi kam ya karba daga hannuna yana bissimillah ya
kafa kai ya fara zuka nace ka dan rage in shafama ya amsa da kai ba tare da yayi
magana ba.
Saida ya shaye ya miko min na karba na fara shafa mai a jikinsa ko ina sai faman
ajiyan zuciya da yake saukewa ana son ya bushe a jikin mutu don haka na barshi nace
kada ya rufa sai ya sha iska.
Na leka dakin Biba na samu tayi barci nayi mataa addua na fito a yanzu in shha
Allah ban sakaci da addu,a abakina tunda aka tunatar dani hakan..
Na kashe mata wuuta na fito daga dakin nawa dakin na koma na kimtsa kaina tsab
na rufo kofan zuwa dakonshi na saami ya kwanta shima a bakon gadon na zauna ina
karanto addu,oin dake bakina na neman tsari daga Allah.
Shina fara tofawa kafin ni nabi bayanshi na kwanta a hankali ina jin yadda
yake sauke ajiyan zuciya jefi jefi zakice yayi zuciya akan wani abune ?
Shigowan mijin nata ta gaidashi ya amsa yana tambayan yaranshi ta bashi amsa da
sunyi barci abinci ta mike ta kawo mashi saida ta hada mai komai ta samu waje ta
zauna tana fadin.
Dazun su anty Nuratu sunzo daga kadun wai sun dawo da Rahamane yau har ya dauki
kofin ruwa zai kai a baki ya dakata yana kallonta kafin yace.
Dama yau zata dawo ashe ta bashi amsa da ban sani ba nima saida suka biyo nan ni
suna min fada wai ina nuna ban damu da Rahama ba yanzu?
Ni yaya suke son nayi don Allah kowa yana ta ganin laifina akan Rahama yanzu
shiyasa wallahi ban so auren nam nata da yaya ba tun fatko don gudun irin haka.
Kai baka gama daukan naka laluran ba ace sai ka dauki laluran wani ita Rahama ai
tunkan ta auri yaya tasan abinda dake cikin gidansa.
Kuma ta yarda ta zauna dashi shiya tare ta da fadin kanki daya kuwa kalau kike
kike fadan wanan maganan ko so kike ta bijirewa iyayyen ku da suka bada