Showing 27001 words to 30000 words out of 328222 words

Chapter 10 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

Abuja sai naga ya dan kalleni na second sai kuma ya juya zuwa ciki .
Komawa nayi kitchen ban fita ba na wanke kayan da nayi aiki dasu na tsabtace
kitchen din yadda ummah na koya muna tun muna kananun mu.
Dama kuma idan kinsan bafulatana badai kazanta ba don tsabta kan akwaishi wajen
fulani ko cup aka fara darazanshi wajen wankewa sai yayi fari sol za a barshi haka
kore da sauran kayan aikin mata.
Muryansu naji yasa na fito daga kitchen din dauke da kayan abincin part din
tsofin dana wa yancan mutanen kamar yadda naga anty Yanda ta zuba masu a jiyan.
Nasu na fara kaiwa suna falo dukkansu biyun nayi sallama na shigo bread ne ko
ina baja baja a falin yaransu suna wasa dashi .
Kyan kyami naji haka na ratsa ina gaidasu na aje masu abincin na juya da zumar
fita daga wajen naji muryan wata na fadin.
Ke meye wanan din kika kawo muna jin hakan yasa na juyo ina fadin abin karyawane
sai akace daku bamuyi ba anan sai an kawo muna ?
Ita kuma Asmau cewa tayi kice a daina kawowa hakana mun gode basai ta wahal da
kanta ba kinji zoki dauka ki tafi dashi ta kara fadan hakan.
Kallonsu na danyi kafin na yunkura zan dauki kulan abuncin naji muryanshi yana
fitowa wani daki yana fadin ke ajeshi nan kice an gode ni aka kawowa baku ba da
zaku yanke hukunci kuba da dokan kada a kara sako min abinci.
Lah illah amma wanan kan gaskiya baiyi ba dan abin karyawan ma sai ankawo muna
saboda me za ace a zubo muna.
Nikan tunda yace in tafi na fito part din da saurina na barsu sunayi bansan ya
suka karasa ba a wajen.
Na koma na dauki na tsohuwar na kai mata suna daki suna hira na shigo ina
gaidasu suka amsa na aje abin karyawan nasu a gefe daya.
Wuri na samu na zauna gefe daya tunda ba sabawa nayi dasu ba lokacin sai ga
mama dubu ta fito daga daki alaman wanka tayi tana fadin .
Badai wanan yar girki tayi ba yanzu nake cewa idan na fito akai mata abin
karyawa can wajen ku ai sai ga kuma wanan abin ta nuna kulan dana shigo dashi da
hannu.
Nice nayi mama anty Yanda tana daki kwance ina gani na fada yar albarka irin
yaran nan ai bakuntanku baida wahala a waje.
Meyene kuka dafane Sare data mike zuwa bude kulan abincin take fada tana bude
kulan don taga abinda ke ciki Arish ne sai kwai da suyanshi yayi kyau sosai bai
kuma yamutse ba zakice wata mace ce tayi aikin.
Ke baki da kunya ku diba kuna daki yarinyar nan duk fadin gidan nan itace ta
shareshi tas ta gyara nan ta gyara wajen yar uwata yanzu kuma ta hada masu abin
karyawa.
Kai amma kuwa dai tayi kokari Sare din ta fada nikan hankalina yana ga tv dake
aiki ina tuna wani rayuwa a baya idan an saka waka muka kama rawa muna nishadi a
falon yara gidan daddy na Abuja.
Anty Salma yar daddy din itace ke koya muna rawa da waka sai mu dinga rawa ina
yawan cin gasa idan ana competition a tsakanin mu yara.
Sweet zata sayo da cake da yought a dinga rabawa a wanda ya iya rawa wai tana da
saurayi mai rawa da waka shine take koyon waka itama.
Yadda ta fado muna dakin zaisa kaji tsoro tana haki yasa gaba daya muka mayarda
hankalin mu a kanta muna kallonta.
Mijin ne yashigo a hasale ya nufota ta boye bayan mama Jafar meya hau kanka
hakane kanka daya kuwa duk iskaci ai ba zata zo gurina kace zaka biyota ba ?
Nikan tsorone ya kamani sosai da har yasa na mike tsaye juyawa yayi ya fita sai
bayan fitanshi ta soma magana tana fadin.
Kawai don nace ba zaici abincin wacan yarinyar ba shine wai zai dakeni mama din
tace wace yarinya ke nan matar Habu dake sako muna girki idan tayi .
Shine yake ci tun jiya yau nace ba zaici ba na zubar shine ya biyoni zai dukeni
kafin takai aya mama tace kika zubar da abinci Nusaiba har kike fadi kin zubda ?
Mama akan me zai zauna yana yaba girkin yarinyan nan daga zuwanta yana fadin
haka aka san mace da iya,,,,,,,,
Shiru tayi don ganin Habu dake tsaye kofa ya harde hannayesa a waje daya yana
saurarensu don tunda suke rikicin har fitowanta yana tsaye kofan part dinshi.
Ganin mijinta ya fita hasale ya shigo ya gaida mama ya samu tana kokarin aibanta
matarshi da kwananta biyu kawai a gidan .
Zama yayi su Sare suka fara gaidashi ya amsa a dakile yace mama kiyi masu
kashedi akan maria idan suna rikicinsu da mijin su ya tsaya iyasu amma kada su kara
hadawa da matana balle mace tace zata aibanta min mata.
Sam ba zan dauki wanan ba ban shiga zancen yarinya ba mama kada wata mace ta
kawo min zancen banza za a jini da mace a cikin gidan nan.
Nasan za a rina da wanan yau alheri da kyautatawa abokin zama kuma laifine
Nusaiba ?
Shi dan arziki a duk inda yake yakan nuna halinsane da irin tarbiyan da akai
masa ai alheri kuma a cikin jinin bawa yake.
Nayi mamakin yadda yaran nan har zasi iya saka muna abinci bama mu kadai ba
harku a gidan amma ku din nan kuna bakin ciki ace yau abinku ya shigo a hannun ko
tsohuwar nan balle ni ?
Har yaushe yarinyar nan tashigo gidan nan da wani zance can zai biyu baya binsu
mukayi da kallo mijin da dayan matanne suka shigo part din zama sukayi nan mijin
nasu shima ya dora da fadin yazo dasu gaban tsofin ne ya kafa hujja akan abinda
yake son fada game da matan nasa.
Ga kaninsa nan ya soma fadin tare da iyalinsa ina son kuji ku sani kada ku dauka
ban san plan din ku bane saboda kun daukeni bansan me nakeyi ba.
To ina son ku sani duk ranan da wata daga cikinku naji kona gani tayi fada ko
tsangwama akan yarinyar nan da aka kawo gidan nan zan ba mace mamaki sosai ga
matakin da zan dauka.
Babu macen da zata hadani fada da dan uwana ko wani nawa a gidan nan mama ki
duba matan nan basuji kunya ba don Allah idan zanyi magana mama kice na barsu zasu
canza.
Yau ace matar Habu ce datazo jiya jiyan don nan tasan tayi girki ta sako maku
abinci har nima a saka min don girmamawa da halarci wai kuma don suna dolaye sun
kasa fahintar ma,anan hakan da yarinyar nan tayi.
Aiko ita bayin kanta bane mijinta ko wani ya bata dabaran ta dinga hakan Saiba
ta fada daga gefen mama wajen da take zaune din.
Ban fada maki idan kina zancen ki kibar sakani a ciki ba habu ya fada a harzuke
yana mikewa tsaye zai dosheta don abinda ta fada.
Kai Habu koma ka zauna kada ka tako wajen nan mama ta fada mama ki bari in koya
mata wayau don Allah wanan yarinyar bata da kunya wallahi.
Kinfa ji abinda ta fada waini na koyawa Maria wanan hikimar idan kuma bani bane
wani ya saka tayi hakan tana nufin ke kenan ko iya ?
Ballema nice ta tambaya jiya da zata zuba ta kirani tace mutum nawane manyan
yaya Habu a gidan nan na fada mata amma wallahi ba wanda yasa tayi hakan a gidan
nan .
Na fada mata basai ta saka ba tunda muna girki a nan muma tace a,a idan tayi
hakan rashin kunyane tayi girki iya bakinsu bata ba manyan shi ba da wani ido zata
kallesu .
Don ya habu yana mijinta ai bashi kadai zata bawa abinci ba su a wajensu hakan
rashin tarbiyane kuma bayan hakan ina zata da alhakin kamshin da mutane sukaji a
kanta.
Sare ce dake rike da labule tana kallon draman da yaninta keyi da matan nasu
take fadan hakan amma wallahi ba wanda ya saka anty maria zuba abincin nan.
Ita tasan darajan mutane tarbiyan data taso a gidansu cikine ta fara nuna muna
nan koyin da gidansu sukai matane take wanzarwa yanzu a nan.
Ai dama ko wani tsuntsu kukan gidansu yakeyi a duk inda yaje haka kuma Allah ke
nan ya nuna maku bakin cikin da kuke shukawa sarakuwarku gata zaune.
Yau ubangijo ya kawo mata yar da zata share mata hawayenta kuna kallo ban taba
gani ko ji inba gareku ba yau ace matar data haifi mijinka baka san darajanta a
idanunka ba.
Uwar mijinka tazo ko ruwa baka iya daukowa ka bata balle abincin alhalin kuma
dantane ya ya sayi wanan abincin kika zauna kikaci har kina bawa yan uwanki amma ba
zaki iya ba yan uwan mijin ki ba ?
A,a iya mu munga cewa abincin nan duk abinda ya kawo sai an kawoshi nan wajen ki
shiyasa aka daina zuba maku komai idan mun dafa.
Fau ya dauketa mari yana harzuka yace idan duk na kawowa iya ina ruwanku sai in
zauna ku kashe muna tsohuwa da yunwa kome ?
Jafarne ya dauke Asmau dake kusa dashi zaune mari ya mike yana fadin wallahi iya
ban taba sanin cewa basu dafa abinci da kuba a gidan nan sai yau din nan amma babu
komai ke kuma zaki dawo ki sameni ai bari ganin kin boye a bayan mama ya fada a
hasale ya juya zai fice daga falon.
Kada ka daki yarinyar nan bai tsaya sauraro ba ya fice fada sosai iya da mama
sukai masu Abubakar ya mike yana fadin indai abincin part din kune na soke dama
bansan ta saka maku ba da ban bari takai maku ba don ku ba mutanen arziki bane kowa
kuma ya sani.
Matan dake bakin ciki da yan uwan mijinsu kada wani yazo gidan nan ya ci wani
abu daga jikin J basu kaunar ganin J yaiwa wani alheri a rayuwansa .
Ina son ku sani ba J kadai yake da ikon gidan nan ba gaba dayan mune muke da iko
a cikin gidan nan har Ahmed da yake yaro yana da hakki a cikin gidan don naji
abinda kuka fada ranan game da zaman mu a cikin gidan nan.
Mama gata nan itace mukewa biyayya dagamu har mijinku din don ra,ayin mamane
tagan mu a waje daya haka zaune.
Ra,ayin uwarkune hadin kanku dana matan ku amma wa yan nan shedanun da Jafaru ya
tara da alaman zasu durkusar da wanan mafalkin na Dubu nason taga kun samu hadin
kai tsintsiya daya madaurinta ku daya.
Iya ta fadi hakan ga shi Habu da ya saura a falon yace basu isa ba iya kuma
sunyi kadan mu zuba da mace a gidan nan a yanzu zasu gane waye Habu ?
Duk abinda akayi ina zaune a gaban idona akayi shi har fitan matan yayan nasa
da sukaji fitan mijinsu suka koma part dinsu bayan sun gama koke kokensu don ranan
mama ta nuna masu bacin ranta sosai a gabansu.
Tunawa nayi da yar uwata da naji ana fadan wai bata da lafiya hakan yasa na mike
na nufi part dinta da sauri na sameta zaune a falo saidai yanayin ta kawai zai
sanarwa mutum bata da lafiya.
Sam ban fada mata tashin hankalin da akayi ba balle in kara mata damuwan da na
ganta a cikinsa abinci na dora muna bayan tayi min bayanin abinda zan dafa saidai
har lokacin zuciyata tana min sake,sake.
Na wani irin rayuwa akeyi a gidan nan haka kuma yaya yar uwar tawa zata kasance
cikin matan nan dana hango rashin da,a a tare dasu dolene nima in zage a yanzu in
kare yar uwata tako wani hanya .
Can wajensu kuma sai waya kowa keyi nan aka fara fadin mena fada maki saiba
tunda kikace bafulatana kanin mijinku ya dauko ?
Fulani da kika gansu mutane da akewa kallon basu san komai ba amma sunfi mutum
sanin duniya kar suke kallon mutum sun iya sace zuciyar duk wanda suke so su kuma
nunawa wanda basu kauna boni a cikin ruwan sanyi kin fara gani ke nan wanan ma ai
kadan kuka gani indai bafalatanin mutum ne.
Wallahi mama saina nuna mata ba kowa take ba a gidan nan ba zan yarda da sherin
daduk zatazo muna dashi ba yar daji da ita kawai.
A dakin Asmau kuma yar ta ke fadi a cikin waya bance kada ki yarda da hadin kan
Nusaiba ba Asmau nusaiba munafukace yar iskace ta karshe irin na bugawa a jarida
din nan amma kinki ki gane me nake nufi ?
Ki zauna tayi amfani dake ta cika burinta a kanki ta fitar dake gidan kila
lokacin zaki gane me nake nufi da kalmana inba kina shasha ba.
Ta yaya zaki zauna yarinyar data hanaki farin ciki a rayuwanki kin sani wai ki
dinga bin kaidin ta kuna musgunawa uwar mijinku da kakanshi ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC


MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

1️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Wanan case don da akayi shine mafarin komai a gidan har zuwa wani lokaci muna
rayuwa dasune kawai da sunan muna gida daya.
Amma hassada da kyashin duniya sun dauka sun dorawa anty Yanda dani kanwarta a
gidan bamu da da matsala da surukan anty Yanda ko kadan .
Don mutanene su masu mutunci daba zan iya fadan irin halarcinsu ba a garemu don
sun rikemu kamar mu din jininsune .
Haka muma bamu yarda wani rashin hankali ko sabani muyi kuskure a garesu idan
mama ta koma can tudun wada nice zanta hidima da Iya .
Wanda ban daukeshi wani hidima a wajena kafin na wuce makaranta zan tashi kiran
sallah farko in gyara part din tsohowar ko ince part din mu in dora ruwan zafi na
wanka dana flask idan akwai dumame in gyara muna don tafi son dumame ita.
Sai infito in share haraban gidan nan kaf ba zakiga wani datti ba a wajen gidan
ko kadan saidai kafin in dawo zaki matan part din yaya J sun jefo abubuwa sun bata
wajen hakan bai damuna.
Don wanan kadanne daga aikin da muka baro a gidan baffa ba yabon kai ba nafi anty
na kuzari nakan gama nawa na hada da nata sai mun gyara garken shanu munyi ma
matansa tatsin nono da surfe da acan muka koya wata rana harda fura mu wuce kiwo.
Sai yamma lis zamu dawo gida mu sakawa shanaye hayaki muna kula dasu wanan yasa
ban dauki aikin gidan nan wani aiki ba a wajena.
Idan na gama inyi shirin school in wuce kuma ban makara tunda karfe hudu nake
tashi zuwa makarantar idan na dawo nayiwa iya dan miya ko abincin da take so taci a
ranan kullum cikin saka min albarka take.
Duk da haka kuma zan shiga wajen anty na na gyara part dinta don shigan cikin
data samu mai bata wahala hakan yasa yanzu da mijinta shima dan uwansa ya kadashi
cikin business dinsa bai zama sosai a gari idan bai gari abincin da nayi wajen iya
mekeci tare da ita.
Duk ciwon da anty maria takeyi bai sa matan yaya J tausaya mata ba ba ruwansu
da ita wai bata da lafiya balle su tausaya mata.
Haka itama lamarinsu bai dameta ba idan bani gida ina school zata shigo wajen
iya su zauna tare har lokacin dana dawo.
Wani lokaci a nan zamu zauna sai dare zata koma wajenta wanan ya jawo tsegumi
saidai ba suyi a gabanta don ba ruwanta dasu ko abinda sukeyi bata kallon hakan don
ita bata da yawan magana kamata.
Don ni a cikin dan lokaci nasan mutanensu sosai har iya kan aikeni irin gidan
Kawu dauda ko can tundun wanda wajen mama .
Ko acan wajen mama da mukanje mata wuni wani lokacin nayi sabo sai da mutanen
gidan don akwai yan mata sa,anina da wa yanda suka girmemin a gidan.
Hakan ya jawo sabo sosai a tsakanin mu cikin dan kankanen lokaci wata rana na
dawo daga school da rana ina zaune muna hira da iya da antyna.
Anty Asmau ta shigo part din kallo guda zakai mata kasan bata da lafiya gaida
ita mukayi na cigaba da kankare kumbana da nakeyi .
Naji tana fadin iya don Allah nazo aron budurwan nan nakine taje ta taimaka min
tun shekaran jiya banda lafiya .
Girki nakeso dan Allah ta taimaka min har yanzu saiba taki dora girki kuma
tasan banda lafiya amma bata do,,,,,,,,
Jeki ki girka mata din saidai ki sani ba zan yarda da hakan kullum ba haba iya
iya yau din nan ne ko zuwa gobe dai haka har Allah ya ban lafiya.
Koma dai meye banson abinda zai jawo kace nace akan hakan son Allah iya ta fada
tana kara kallona tace min jekiki ki taimaka mata din kinji yar albarka.
Kallon yayata nayi tayi min alama da intafi mana tunda iya tace inje din tare
muka shiga part din nasu ga dai gida kan amma babu mata a cikinsa saboda kazanta.
Wani plate don


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login