Showing 126001 words to 129000 words out of 328222 words
Chapter 43 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
a cikin tumbula da zaki iya ganin ruwan karara kwance a cikin
madaukin sai cup din glass irinsa dana hado dashi na kawo gabansa na dan rage tsawo
ina tsiyayya masa lokacin ya sauke hannunsa dake saman goshi ya bini da kallo tare
da ajiyan zuciya da shi kadai yasan dalilinsa.
Ya miko hannu ya karbi ruwan tare da fadin thanks ya kai bakinsa saida ya shanye
ruwan tas ya aje kofin yana fadin Salima yasu iya dai ?
Au bakaje can ba ke nan yace direct nan na nufo ai nagaji sosai yau salima da
safen nan fa na dawo Nageria na kuma hau jirgi zuwa Abuja daga lagos yanzu kuma
gani gida aikinga akwai gajiya.
Kayan na kwashe zuwa kitchen na barshi dasu nan suna dan hiran zumuci can na
gama yan dabaruna sai gashi na kata fitowa da da try din dana hada na sake direwa a
gabanshi.
Kazace data sha gyara wace taji albasa da kabeji su tattasai da kayan kamshi nayi
warming dinta a ovorn ga kuma lemun kwakwa da madara na kwali na aje na kallosa.
Naga duk hankalinsa yana kaina nace bissimillah yaya dare yayi kada ka kwana da
yunwa suma nayi masu tayi.
Ai kema ko dazun da mukaci bakici komai bs ki zauna kici Nafisa ta fada nace aiko
naci mana anty Nafisa mamaki kamar zai kasheshi a lokacin haka ya daure ya jawo
zuwa gabanshi yana cire foilpepper din dana rufa ya kai idonsa sama.
Ya kara lumshe idanunsa tare da hamdallah ga ubangiji yake fadin duk tare za aci
ai ki zauna muci ya fada yana masu bissimillah.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
4️⃣3️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Wani yanayi na wasan yar tsamane ke gudana a tsakanina dashi agaban yan uwansa a
lokacin don saiki rantse da Allah dama akwai shakuwa ko soyayya sosai tsakanina
dashi lokacin a haka muka nunke zuciyarsu da kasa fahintar mu.
Suma din sai faman mamaki hakan kowansu keyi a zuciyanshi don yadda komai
nakeyinsa a natse cikin wayewan kai nafisace ta fara mikewa wanan lokacin.
Don barin falon wanan dakin da sukaiwa kansu masauki a cikinsa ta shiga da
sunan kewayawa bandaki daga nan bata fito ba kuma.
Kafin Salima itama tabi bayanta zuwa dakin suka barshi shi kadai a falon zaune
yana waya.
Don lokacin na mike ina kwashe komai da akai amfani dashi zuwa kitchen na dawo
na gyara wajen nan na samu su dukkansu sun bar wajen a lokacin.
Zuwa lokacin barcine duk a idona don nima hidimar bukin da jewadi ya kashe min
jiki don sai a lokacin nake jin tsamin jikina na gama na nufi dakina na barshi nan
a zaune falon kofan na rufo na fara zuge zip din rigan jikina na fada bandaki.
Ina shiga na fara cude jikina da wani ruwan turarensu na madara irin tasu ta
mutanem maiduguri wanda mama tabani tace dinga hakan dashi da dare kafin na kwanta.
Bayan na gama na fito na dauki Rigan barcina dana dauko na dauka saman gado ina
zurawa a jikina ji don barcine sosai ne a idanuwana nake jiba a lokacin .
Ina kokarin zura rigarne naji anrugumeni ta baya ana sakar min nauyi da sauri na
iya furta subbahanallahi na ambata a fili duk jikina yana rawa lokaci guda don
tsoron hakan da naji .
Danshina nayi kokarin juyowa cikin faduwan gaba don ganin ko waye haka ya
razanani lokaci guda duk da ban faye tsoro ba amma hakan dai ya firgitani.
Saidai haka din bai samu ba a gareni don irin rikon da akai min sam na kasa
jiyowa din inga waye a lokacin.
Amma saboda sautin numfashinsa dake shiga kunnena a lokacin naji a cikin wani
yanayi wanan yasa lokaci guda jikina ya dauki rawa tsoro yana dada shigata.
Wani abu naji yana min yawo tundaga tsakar kaina har zuwa yatsun kafana jikina
sai kyarma yakeyi don ban tsamaci hakan a lokacin ba.
Nauyin Kanshi da naji ya kwantar a kafadana yana fadin relex baby Rahama ba komai
zan maki ba just live me to hug you.
Na samu natsuwa kawai nake son samu a wanan lokacin yanzu gareki ya fada kamar
mai yin rada a lokacin cikin kunnuwata.
Kalman na natsuwa na sake maimaitawa a ciyana kamar wanda ya karanto zuciyana
din naji yace please Rahama don't judge me accondin to my sin ina kaunarki har
cikin raina ke din kamar zabinace Allah ya kawo min a sauwake har gida don Allah
kada kice zaki hukuntani bisa kuskuren fahinta .
Hawayen da nake kokarin tarewa kada su zubo daga idona sune suka dinga diga
saman hannunshi haka ya sanar dashi kukan da nakeyi a lokacin mara sauti.
Subbahanallahi are you crying Rahama sabodani No no no no don Allah ki daina
nasan ni mai laifine a wajen na shiga maki rayuwa bada sanarwan ki ba.
Amma ina son ki dauki hakan a matsayin kaddaran mu gabaki dayan mu Allah yayi
sai munyi rayuwa irin hakan a tare dake koda iya hakane kuwa a rayuwan mu.
So ki bari na gama dan abindake gabana kafin mukai ga matsaya a tsakanin mu ba
zan maki dole a kaina ba Rahama ko haka Allah ya barmu nasan kinyiwa iyayye biyayya
dani.
Naji dadin natsuwan da kika nuna a gaban sisters dina ko iya wanan kika barni
dashi nagode Rahama don kinyi min abinda ban taba zato ba a wajen ki.
Na dauka sam ba zan samu kallon arziki ba ko tarbo sannu da zuwa sai gashi kin
fitar dani kunya a lokaci guda wanda ni ban taba kawo hakan agareki ba.
Yana maganan yana kokarin dago habana dake dage yayin dana gane nufisa na cije
cikina a waje daya naki yarda hakan ya faru.
Sai naji yayi murmushi ya dan rage rikon da yai min din da farko wanan karon
hannuna ya kama zuwa bakin gado ya zaunar dani shima ya samu waje ya zauna a kusa
dani.
Dan shiru ya biyo baya a dakin kafin yace wallahi Rahama banyi haka don in tauye
maki rayuwa ba nayi don ni a wajena komai naki wallahi yai min ina sonki sosai
Rahama saboda halaiyan ki don haka ki ban hadin kai mu zauna lafiya.
A raina nace bakai bane yanzu fa ya gama cewa jn bashi time in rufa mai asiri ya
fara fuskantar abindake gabanshi yanzu.
Yanzu kuma ya dawo yana rokona da mu zauna lafiya bisa amana kada dai ya zamo
munafukin namiji mai baki biyu ?
Wa yan can suma Allah kadai yasan irin dadin bakin da yaje yayi masu a kaina duk
da ban tabbatar ba amma akasarin maza haka suke da baki biyu ga matansu.
Me aka fada maki Rahama akan zargi wata zuciya ta tuna min da hakan daga
bangaren zuciya tiryan tiryan nake tuno zancen su hjy yabi da sukai min a karshe
don haka dole inyi taka tsantsan da rudin zuciya mai kai mutum ga halaka .
Wanan aure dai matukar bashi yace ya fasa ba dole in hakkura da komai in zauna da
yaya saboda biyayya kamar yadda su daddy suka rokeni dayi don haka alkawari na
dauka in sha Allahu zanyi biyayya ga zaman aurena a gidan ya Jafar har inda rabon
zaman a tare dasu.
A zatona zai koma dayan dakin daba kowane kamar yadda anty salma take sheda min
wancan dakin yurakanshine nan kuma nawa sauran dakunan biyu kuma na aje don baki
daya kuma na dinga amfani dashi ni kaina daki biyu ke nan suka ware min ni daya ko
ina zan kaishi oho ?
Hannuna ya sake rikowa yana dan murza yatsuna a hankali kamar dai wanda ke wasa
da hannun yaro yayin da wani boyayyen sakon da ban,saba dashi ba ke bin ilahirin
jikina yana sakar min da kasala.
Kan na tantance sai ji nayi ya sumbaci gefen wuyana nan da nan jikina ya fara
rawa tsoron hakan karara ya baiyana a gareni lokaci guda.
No kwanta ki huta akwai gajiya a tare dake ya fada yana kokarin kwantar dani
saman gadon kamar karamar yarinya banki ba nayi yadda yacen na dunkule a waje daya
ina mai kame jikina.
Wani ajiyan zuciya ya sauke yana kaiwa kwance daga gefena nima din na sakankace
da zancenshi hakan yasa na lumshe idona ina sauke ajiyan zuciya.
Ido a rufe zuciya tab da fargaba da zullumin hakan dana tsunci kaina a cikinsa
lokaci daya naji saukan hannunsa saman jikina a daidai wajen da nayi shekara da
shekaru ina boyon abina da hijjabi ko gyale yau sai gashi a saukake hannun wani ya
kai ga wanan abin.
Bai dai min komai ba a ranan kamar yadda yace saidai nasha luguda kamar mangoron
da akeson ya nuna a lokaci daya.
Da misalin karfe hudun asuba naji tashinsa already na falka a lokacin don sabo
da hakan danayi a rayuwata ban daki ya shiga ya dan jima kafin ya fito yana dan
kiran sunna da intashi kada in nakara ganin na falka ya bude dakin ya fita hakan ya
ban daman samu na mike na shiga bandakin.
Wanka nayi ina hawaye har nagama na fito na dauko kayan sallah acikin wardrobe
dina na tayar da sallah ina idarwa na koma barcin don idona cike yake da barci a
lokacin.
Alhamdullahi don ko na samu barcin nayi ban falka ba sai wajajen takwas na safe
na tashi dakin na fara gyarawa duk da a gyarensa yake amma haka bai hana na kara
tsayawa na gyara ba na sauya zanin gadon na sharo na kawo kamshi na feshe dakin
dashi na shiga wanka.
Bayan na fito na saka kaya wasu light green lace mara nauyi da akai masu dinkin
riga da skirt na saka sunji duwatsu anyi kwaliya a gaban rigan da bakin lace din
saina zauna gyaran fuskana a gaban mirro.
Lokacin ya shigo dakin a cikin shirinsa na wasu fararen shadda da akaiwa dinkin
gajeren hunnu sai bakaken takalma a kafasa kansa babu hula.
Da sallama na amsa ina dukar da kaina kasa ya karaso yazo daidai bayana ya tsaya
muna kallon juna a morron nayi kasa da kaina na zame kasan kujeran na duka ina
gaidashi da kwana.
Wani irin mamakine da yarinyar nan take kasheshi dashi yaushe rabon daya tunama
ana gaida miji da kwana a addinance ko al,ada ?
Wani irin son ta yaji yana kara shiga zuciyarshi don tunda yake koda tuntuben
harshe matansa basu gaidashi da kwana wani lokacin ma da fada suke tashi tsakaninsu
tun asuba.
Hannuna ya kamo muka koma bakin gado muka zauna naji ya ambaci sunana yana fadin
Rahama jiya kin shayar dani farin ciki a rayuwata kin tabbatar min ke din yar
mutuncine data gaji hakan.
Kin tsare mutuncinki dana iyayyenki ko a hakan da kikai min nagode sosai Allah
yayi maki albarka nayi kasa da kaina a cikin nauyi da kunyarshi.
Wallahi Rahama komai naki kara burgeni yakeyi ina son ki sosai wallahi don Allah ki
ban hadin kai mu zauna lafiya Rahama".
Abune a baiyane da kika sani tun bayan wata ukku da aurena da Asmau farin ciki
ya gushe min ba zance banjin dadin zama dasu ba don su din matanane amanatace kuma
su din.
Amma sun kasa ban irin farin cikin dana taso ina mafalkin kansancewa a cikinsa
sun hana min kwanciyan hankali sun kasa gyara kansu wanan duk ba bakon abu bane a
wajen ki don kinsan komai.
Wayanshi dake ringing bai kula dashi ba nakai ido na kalla sunan ya Habu na gani
a wayan ganin ina kallon waya yasa ya dauka yana fadin.
Hello Habu ganina shirya yanzu zan karya in fito kana gida ko ban daiji amsan da
habu din ya bashi na daiji yace hakan yayi daidai zanzo da salima din.
Mike tsaye yana fadin tashi muje ki karya yaran nan sun hada muna abin kari yana
falo ina son in mugama zan shiga gida mu gaisa dasu don ban samu zuwa jiya ba na
gaji da yawa.
A raina nace ka daizo hanawa rayuwata shakat malam banki ba din na mike na yafo
gyale a kafadata muka fito falon a tare dashi.
Salimace a falon tana jera kayan breakfast din data shigo dana karshe jin
motsin nu ta juyo tare ta ganmu munfito daga dakin ta fara gaida yayab nata kafin
ta juyo kai muka gaisa a yar kunya da ita.
Ina Nafiss ya tambaya take fadin tana kitchen ku zo ku karya zamuje gida dani
dake mu dubo su mama ba zamu jima ba so Nafiss ta jiramu mu dawo.
A gurguje naga ya karya da ruwan shayi sai dsnkali da kwai ds suka soya shi
naga ya tutura ya juyo yana fadin ina salima din ta fito mu tafi kada mu kara,
Barin lekasu indawo don Allah ya juyo yana fadan haka gareni a cikin kullawa
nayi masa Allah ya tsare ya kare ya amsa da amin ya fita.
A waje ta sameshi har ya shiga mota saboda kawu da yaya Habu yayo masa da text
yazo ya gashi a falonsu mama suna magana daya shiga gaisheta.
Koda suka kama hanya da salima ya kalleta yace salima kunsha fama ban nan ashe
abinda kawu ke kulla min ke nan jiya ban fito da maganan bane don Nafisa dake
zaune.
Ai kawu gaskiya mugun mutum ne yaya makin ya taushe mama ya bata hakkuri wai
amma shi da matarshi sune suke zuga mama a kanka ni shine ya bani haushi wallahi.
Yadda kake kokari dasu din nan amma suka iya haka basu nuna mata gaskiya ba wai
ace mama ta zauna tana shirin ci maka mutumci akan inda zaka aje matarka ?
Me Rahama tayiwa mama don Allah tunda ba itace ta tillasta maka dole ka aureta
ba kai kayi ra,ayin haka kuma iyayyenka suka bata duk fa yaya Habu ya fada mata
komai amma mama ta yarda ta dauki zugi a kanta game dakai.
Bakomai salima dukiyane yau zan mayar ma kowa da abinsa inyaso suyi abinda suke
gurin yi dashi nadai godewa Allah da ban taba dukiyan nan ba.
Yanzu yaya mayar masu zakayi wallahi yadda naga su kawu sun damu kamar suna da
wani manufane akan kudin nan in bashi ba meue nasa a ciki don Allah ?
Maigadi na bude masu get kawu din suka fara hangowa tsaye kofan part din Iya
yana waya ya zubawa motansu ido har suka karaso.
Da farko bai sheda waye ba saida J din ya bude motar ya fito tare da salima ya
gane shine lokacin kuma waya yakeyi game da J din yana tambayan lamban a wajen
abokin J din daya sani.
A,a Jafar dama kana kusa ashe to sannu da zuwa ashe kana hanya dama ?
Eh kawu ya fada yana hawo step din da zai sadashi da kofan iya bai tsaya ya
gaidashi yadda ya saba bakawai yasa kai ya shiga wajen iya da sallaman shi.
A,a a lale marhabin dan halas kaki ambato ashe ana nan ana faman cigiyan ka
kamar wanda ya bata sai gaka kwatsam ka fado ?
Ashe dama kana kusa ba nisa kaje ba to sannu da zuwa yaya hanya iyace ke wanan
magana tana taba hannayenta daga inda take zaune.
Iya wake cigiyata haka kedai ko don kada amarya ta daukeni ya fada yana zama
gefenta sai wani annuri yakeyi da ganinsa kasan abubuwa sun zauna ana cikin lokaci.
Iya tace ba dole ba Jafaru tunda ance ka gudu ba a san inda kashiga ba anyi
kiran wayanka baya shiga kowa ya kira baya samun ka ka dauki dukiyan mutane ka
salwantar ka kama gabanka ka bace wa mutane.
Iya wani dukiya na salwantar tace to danga dukiyan magada dake hannunka mana
masushi suna bukatan abinsu yanzu tunda ance sune kake,,,,,,,
Haba iya wacce ya gudu da dukiya nai cikin mu waga dabi,a batayi ba iya mi da
zaki hwada mai haka don Allah ?
Anty barka dake fitowa daga dakice ta tare iya dake fadin zancen da dan fada
fada iya tace yanzu kuma zakuce baku fadi hakan bane a gabansa ?
Nan fa kuke keda yar nan saratu kuna fadin magana tundai saratun nan bakinta
baya fadan alheri game da kowa saidai sheri.
Anty Baraka ashe kinzone ya fada yana kallon anty baraka din da ta bata rai
don abinda iya ta fada a gabanshi yaiwa kowansu zafi.
Nazo tun karshen satin can jafaru an dawo lafiya ya hanya wai tace ance ka gudu
to wayace banda abin iya da shirme baki san me ake fada ba kije gulma ?
Murmushi yayi yana fadin da hankalinta ba shirme bane iya bata son wani ya
sokeni kila inke baki fada ba taji wani ya fadi hakan ta rike a ranta.
Inke baki fada ba ai uwarku sun fada ko zaki toge yanzu don kun gasa ya dawo a
yadda baku zata ba ,,,,,,,,
Iya koma me aka fada aishi yaja a fada mai hakan don babu yadda za ayi dukiyan
mutane yana hannunka ka zauna baka kara maishi sai kanka kana ta faman auren daba
riba don me ba za ayi magana ba ?
Mama dake fitowa daki take fadin hakan ta murde fuska ga dan nata a karo na
farko haka ya tabbatar mashi cewa kome akace mama din ta fada akanshi lokacin zata
iya fada.
Mama na gudu kuma ban kara kowa ba kamar yaya nabar