Showing 297001 words to 300000 words out of 328222 words
Chapter 100 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
Haba dai kai babbane hakkuri za kayi bata da wani gatan daya wuce ku a yanzu ai
ko yanzu kuma ta fahinci kai ba irin mutanen nan bane tunda kai mata komai a
rayuwa.
Ke kika fahinci hakan ita ai fushi takeyi dani daga ita har mama na kuma rantse
a yanzu dai ban kara mata komai saita gane kurenta .
Gara dai dakace sai gaba don duk yadda akayi saika saka hannu a wani abin shi
dan uwa ai MURFIN JALLO NE don ko wakake a duniya wata rana sai dan uwa ya taimake
ka.
Rahama mu bar zancen nan idan munci gaba kina tuna min abubuwa akan yarinyar nan
yarinyar data dafa min mugun ciwon da kowa yake gudu a duniya wani murfi take
gareni a rayuwa ?
Shiru nayi ban kara cewa komai ba washe gari tunda safe yasa kai ya fita gidan
nasan hakan nada nasaban kiran da mama din take ta mashi tunda dare yaki daga
wayan.
Wani abu sai mahaifa don kuwa ko yaya ranka ya baci da hukuncinsu dole kai
hakkuri idan kana neman rahaman ubangiji.
Saratu dai tun bata yarda da zancen da ake fadi ba har ta soma yarda gashi washe
gari daurin aure saida maza suka nuna ikonsu akan mama ta yarda ta amince aka daura
aure a washegari.
Duk cikin sarakan mama mu biyar ni kadaice na bada gudun mawa a harkan bukin
aiko yaya barakha tana ta yabawa tana fadin kin gani ko ita da nasu baizo daya ba
da saratun itace ma ta bada abin arziki.
Aini tuni na gano yarinyar arzikine na daina biyewa zugin mutane akan zancen
duniya ba dole ki daina ba tunda tana ma danki rikon munafunci a yanzu ?
Komai zaki fada kan wanan yarinyar wajen malam da mukaje dazun cewa yayi hannu
akasa aka dambala mijin don ba haka yayi niya ba da farko ?
Haba mama don malam yace ansa hannu sai ace kuma Rahamace tasa mata hannu yanzu
don Allah me ta tsare mata inma hannune ai saidai tayi wanda zata tafi ta zauna
dakinta har abada.
Don Allah mama a yanzu ya kamata ki rage irin wanan magana na malamai shekaru fa
sunja mama ke in kin fada ai ba za aga laifinki ba ni wanan halin wallahi yana
damuna sosai komai ace a je wajen malam ba a barwa Allah lamatin komai yanzu gidan
nan.
Can Saratu ta dauki mama sukaje wajen malaminsu da Nusaiba yace wai sai
Nusaiba ta dawo abubuwa zasu kamkama ga zance kasan hadin bakine amma mama ta yarda
da shirmensu.
Salima ke fadin hakan aiko mama tayo cikinta da zagi na bacin rai tana batun
tsine mata saida anty barakha ta kare tana fadin nikan mama zan kira Jafar yazo kan
zancen tunda banga abin zagi ba a nan ?
Ai gaskiya salima ta fadi ni yanzu na gane malaman nan macutane wallahi don suci
kudinta sai su kakaro karya su sharawa mutum don hankalinsa ya tashi a banza.
Haka dai akai komai har daurin aure ba tare da sun samu yadda suke so ba din
salima kuma tunda ta fita har ranan buki bata leko part din ba tana wajen iya zaune
har yan kai amarya suka wuce da amarya bata fito ba.
Anje dasu yaya barakha da maman tudu sai mama hafsatu matar kawu wace zuwanta din
yaso ya jawo matsala tunda taje wajen jere don kawu yace amayarsane zata kai
amarya.
Su yaya suka tsaya sukace da inna hafsatu za a dole ya kyale ya bari ta tafi
mutum biyar dai suka je raka amarya dakinta a ranan.
Duk daba gida daya muke ba saida baji shakat da tafiyan nata don nasa an rage
wani annoba a yanzu matar yazid ce ta fara magana ta soma fadin.
Wai an rage wani kaya a nan wanan matar batayi min ita sam kamar ba ciki daya
suka fito da yan uwanta ba ta fita daban a cikinsu komai nata baida kyau wallahi.
Muna wajen iya har yamma nidai koda aka fito wai aje a sallami mama kin zuwa nayi
na zauna nan a barandan iya har suka fito muka fice daga gidan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[6/4, 07:42] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
9️⃣2️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Ba cewan da akayi kauyen sokoto za akaita bane abin mamaki sai irin gidan da mota
ya tsaya dasu a garin tambuwal.
Daga wajen gidan kawai zaka fahinci inda sukazo gidane na gandu irin gidan yawa
din nan mai dauke da tun kaka har jikoki a cikinsa in akwai.
Haka aka fito da ita zuwa cikin gidan wanda ko gidan gadonsu dasu mama ke zaune
a cikinsa yafi don a can family house dinsu shimfide yake da siminti lungu da sako
na gidan ga baki daya har bayi a shimfide yake da siminti.
Sun samu dakin nata saboda kayanta tsohuwan gidan ta tashi daga dakinta an
gyara dakin an hade mata shi da nata ya koma ciki da falo mai kama da babba da
jakka dakin nan da tsawo can ta kuryan uwar dakan da akaiwa kwaskwarima yana kasa.
Maman tudu dake rike da ita tun tana fadi a ciki har zancen ya fito fili tana
fadin ikon Allah aure shiya gaji haka yau Saratu Allah ya nufa aure ya kawota nan
kasan kuma ina ji sunan garin nan a redio amma ban taba tunanen zuwanshi ba.
Sai faman gaidasu da zuwa yan gidan keyi har suka kai dakin nata suka zauna
kallon juna kawai suke a tsakaninsu sai yaya barakhace ta iya fadin .
Shiko dai wanan mutumin a gidan yawa haka gidan kowa da kowa zai kawo saratu ina
laifin ya kama mata haya a wajen gidan don Allah dai.
Ke dai bari ai wanan dalilin yasa muka koma muka fadawa Dubu abinda idon mu ya
ganan muna ai baki san abin takaici bama barakha ni hada ban dakin nan shine ya
tayar min da hankali fiye da komai.
Ga matansa kauyawa gidadawa dasu ke bari kawai abin bai faduwa dai wallahi daki
ai kun samu an gyara komai dafa ciki gudane iya falon nan.
Gaskiya mutumin nan bai kyauta ba wallahi haba dai a,a barakha idan baku sawa
auren nan albarka kuyi shiru don Allah tana fa son abinta ita don haka ku daina
wanan magana.
Idan matansa kauyawane ita yar birni saita koya masu komai a sannu harsu gane ai
dama shine amfanin surka auren da maza keyi yanzu.
Nusaiba ce ta fito daga kuryan da suke tana fadin nikan zafi kamar zan suke
wallahi dakin nan idan na kwana a cikinsa haka ai ina sankarewa kafin safe ?
Meyasa wa yanda ke gidan basu sankare ba sai ke ku dai iya bakin ku a rabu lafiya
don Allah irin maganganun nan babu dadi gaskiya.
Mama tudu ta tarewa Nusaiban numfashi abinda take fada a lokacin yasa taja
bakinta tayi shiru ta tafi tana guna guni nan mata suka fara shigo masu da kulan
abinci dama a gajiye suke don nisan tafiyan da sukayo.
Wasu sallah suka farayi wasu kuma neman abinci irinsu Saiba ke nan tun wajen
bude abincin sukai arba da bakin miyan dake cikin katon kula girke a gabansu miyan
dai ga abin miya amma gaskiya yana da wuya yakai bakin mutum ko don bakinshi.
Inda Allah ya taimakesu kunun daka da aka kawo masu hade da abincin wanda yaji
kayan kamshi ga suga zaikai mudu biyu da robobin sha shi suka dinga afkawa cikinsu
don yunwa abinci kan abin miya suka tsame sukaci.
Akwai gaji don haka suka fara shirin barci tun a can amarya saratu ta fada masu
idan anzo za ayi dinner don haka kawarta da akazo da ita take tambaya zancen dinner
din ?
Take fadin itama har yanzu angon bai kirata ba kota kira wayanshi yana kashe
bata samunshi har barci ya dauketa ba zancen dinner din.
Washegari hayaniyar mutanen gidan ya tayar dasu wajen kewayawama fitina ne haka
suke bin lafiya har amaryan suka dai samu sukai alwala sukai sallah.
Su mama suna falo suna dan gaisawa a daidai lokacin sukaji amarya ta fasa kuka
daga kuryan daki hankali tashe suka isa gareta banda mama tana zaune tana azzakar
din ta na safe.
Sai dai ta jefa masu baki daga inda suke saida ta idar ta mike ta samesu tana
fadin shifa aure mukaddarine duk inda Allah ya nufa zakayi aure saika taka wajen.
Abu guda ya rage maki a yanzu shine hakkuri wata nacen tana neman hakan bata
samu ba ke kuma gaki kina son butulcewa Allah yanzu da baiwan da yayi maki.
Kinsan alheri dake cikin aurenki da bawan Allah nan da Allah ya hadaku tare
shine mijinki aure ba kyalkyalin duniya akajawa cikinsa ba zama na amana matukar
akwai so a tsakanin ka miji.
Ki bar komai ga Allah kisa hakan shine alherinki a yanzu kinsan tanadin da yake
maki ai yasan gidan daya dauko ki da inda ya daukoki don haka halinki yanzu shine
jarinki saratu ki natsu kibar wanan shirmen da kikeyi.
Kowa nan da kalan zabin da Allah yai mashi duk abinda kika gani ya faru da bawa
rubuttace tun asali gareka.
Ni banga wani abin damuwa ko shiga tashin hankali ba saratu kinafa son mijinki
so ba inda baikai mace a duniyan nan .
Da kalaman mama ta samu natsuwa suma din su saiba dake sakin magana duk mama
tayiwa kowa gugan zana a wajen kowa ya kama bakinsa.
Don cewa da mama tayi da wani zaman burni ko cikin daula ai gara kauye din inda
hankalinka yake kwance a san kana kauyene ba sunan kana cikin daula ba wanan zance
ya tabawa Saiba rai inda tace da ita mama keyi a zuciyarta.
Kamar ana koransu kafin takwasa na safe duk sun shirya tafiyan komawa zaria a
gagauce ga matan gidan duk da safiyane sai dake dake sukeyi suna wakokinsu a cikin
raha na nuna murnan auren daya daga cikin ahalin gidan ana fadin su jira a gama
furan barna sukace akwai nisa tsakanin zaria da nan gara subi hanya da wuri.
Sai wajen shiga mota suka samu ganin ango yazo sallamansu nan mama tayi mai dan
nasiha yana ta godiya suka tafi suka barta a nan din cikin mutanen da bata taba
sanin kalan rayuwansu ba haka ya mace ta gada dama a kaika inda baka zata ba a
rayuwa Allah yasa mu dace amin.
Ranan yan uwan Aminu mata da yaya barakha tazo dasu wajen bukin suka zo gidan
mu dama ranan zai koma can gidanshi ya gama kwanakinsa a nan.
Abinci lafiyayye na shirya masu ba wani daure fuska koma ba sakewa sosai kada
raini ya biyo baya na barsu sunyi yadda suke so tunda gidan kanin uwarsune suma
kuma basu wuce gona da iri ba yadda nayi zato.
A can gida kuma mama hankalinta a tashe yake har saida yan kai amarya suka iso a
wahale kowa na neman abinda zaici a cikinsa maman tudu bata tsaya ba ta wuce gida
da ita da yaya Rukaiyya.
Sai mama hafsatu da yaya barakha da Saiba data nufi part dinsu suka rage a gidan
yadda suke neman abinda zasucine ya tayarwa mama da hankalinta sai dai batayi
magana koma meye ai zataji su kuma basu cewa kowa komai ba kar yadda maman tudu ta
kwabe bakinsu tun can din.
A nan gida kan wajen mama ba wanda yai magana sun daici abinci sun kuma ce sun
barta lafiya tana can sun barota ita kadai.
kamar yadda ake barin ko wata diya idan an kaita gidan miji nan mama tayi shiru
na dan lokaci ai kuwa can part din yaya jafar kuma gajiya bai hanasu fada ba.
Don saiba na shigowa ta kula da kayan da yaci abincin rana ta soma fadin halan
gidan nan sweet J ya kwana ?
Asmau tace ehh cikin ko in kula daki ta nufa har ta tube tufafin jikinta kamar
an tsikarota sai gata ta fito tana fadin .
Asmau ya kwana a nan kuma kinsan nice da girki kika yarda ya kwana a nan ban
gari ke dai yar cin amanace ta gaske wallahi ?
Cikin mamaki Asmau ta dago tana fadin tau fa kaji manya don baki gari sai kada
ya kwana a nan ko ai bansan haka kika kafa doka a gidan nan ba ?
Aida zaki tafi saiki fada min kada na kuskura in karbeshi idan ya dawo tunda
kinsan jiyan zai dawo gidan nan kuma kikayi tafiya ?
Fada sosai sukayi tsakaninsu wanan kawai ya isa ya tuna maka saratu don da tana
gidan da tun a lokacin ta iso part din ko kuma ta bugawa saiba din waya tun tana
can ta fada mata abinda ke faruwa a gidan.
Har suka gaji suka kyale juna akan a bari maigidan ya dawo tunda shine
munafukin da yayi hakan saiban ta shiga tayi wanka ta fito don tunda sukaje sun
kasa yin wanka a bayin gidan.
Abincima da Asmau ta bata kin karba tayi tabar matashi a falo ta fito zuwa part
din mama ta duba ko akwai abinci a can taci .
Ta samu don mama tayi girki don isowansu din ta zauna taci tana cicika a
lokacin mama ke fadin mutumiyar ki dai tana can ta zama mutanen sokoto ?
Mama aida sokoto din take da sauki wani shegen gidan yawa ya kaita fa gina kamar
na mutanen dauri abinda babu dadin fada gaskiya.
Kai Nusaiba bakiji me maman tudu ta fada ba albarkan aure yafi riyan dake
cikinsa kayi abu daidai karfinka ba karya yafi kayi karya girman ka ya zube.
Meye laifin gidan tunda yana da gidansu aurene fa ba inda bakai diya mace ta mike
tana fadin yaya ai gaskiya na fada .
Ita mama da take fadin hakan ai ta fadane kawai tunda bata yarda akai yarta wanan
wajen gaskiya kam abu daine bai faduwa kawai sai ayi shiru hafsatu ta fada daga
gefe.
Wai ku tsaya me ake kokarin boye min ne mama din ta fada tana duban saiba din ta
mike tana fadin mama ni me zance yanzu ace kuma ina kushe aure sunana yakai tasa
kai ta fita.
Munafuka dadai ki fada din mana tunda gulma na ciki ai gara dashi yana da gidan
ke ko gida iyayyenki nada shine balle nina dawo rakiyan yarinyar nan na kula ba
mutumiyar arziki bace ita .
Barakha meye laita yanzu har kina kokarin zaginta ai gara da ita ta fada min
halinda yata take ciki kuda kuka boye min fa don yaya tace kada a fada ?
Laifine mama don mama tace kada muyi surutu mu tayata da addu,a sai hakan yazama
laifi ni naga ai abinda yakamata muyi ke nan mama ta fada.
Lalai Barakha dole kishiya ta dinga cin galabanki indai wanan halin naki na
saurin yarda da mutanen yanzu kikeyi a can ?
Yayace zatace kada ku fada min abu ke har ki yarda kiki fada min don kina bi can
sun san halinki ke sokuwace da sauri ta dubi uwar tana fadin ni mama me kuma nayi
na sokonci a nan don na fadi gaskiya ?
Damu fada maki abinda zai tayar maki da hankali a banza ita saratu na can zaune
dakinta ai gara muja bakin mu muyi shiru tunda nan Allah ya nufeta da aure.
Wani malolon bakin ciki ya tokare mata makoshi ta kasa ba yar nata amsa don
bakin ciki ta mike zuwa dakinta barakha ta dubi mama hafsatu tace wallahi mama kada
ki yarda kice komai kada tashiga wani hali su jafar su sakaki gaba a gidan nan.
Jin hakan yaba hafsatun tsoro tace ni kingama bari bazo nabar gidan nan yanzu da
nace sai yamma zan karasa gida amma yanzu zan wuce.
Dubu na shiga daki waya ta jawo ta dannawa saratu kira gidan cike yake don a
ranan suke wunin buki tunda amarya ba a gari take ba.
Hayaniyane dakin nata sai cewa take bata jin abinda mama din take fada don idon
mutane dake kanta a lokacin dakin tap yake da yan uwa da abokan arzikin gidan yan
zuwa gani amarya.
Gashi duk sun isheta amma ba daman magana yarasu sai hawa saman kujera sukeyi
suna takawa iyayyeb da diyan anci shimkafa an wawatsar mata a dakin nata.
Dole ta koma kuryan dakinta ta kwanta tana kukan zuci Allah ya gani tana son
habibinta don irin mazan nan ne da mata basu dauke ido akansu don kyau.
Wanan yasa duk inda yaje ya taya mace yake samu da sauri gashi iri mutanen nan
ne manema mata ko yaushe tsab yake komai nashi neat tun daga kanshi har takalma
zaki gashi neat dashi clean .
Saidai shi dan karyane na gaake kuma manemin mata dama idan kaga na mijin kauye
ya faye wayewa hakane dabiansa neman mata.
Ko ita saratun da karya yaje mata saita lake mai har abin ya zama masu aure bai
boye mata ba da abin yayi nisa ya fada mata shifa dan kauyen sokoto ne haka kuma
bawai wani mai kudi bane shi.
Ta dauka yana zolayantane kawai don ya barta sai gashi tace zata daiyi din ko
yaya yake don ita a zatonta kawai yana fadane don ya gwadata ashe haka abin yake.
Allah ya dora mata son habibi a zuciyarta