Showing 36001 words to 39000 words out of 328222 words

Chapter 13 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

danyi gaisuwa sama sama
da yar uwar tawa da sai bin wajenta takeyi da kallon mamaki don ko kai waye shiyan
yar uwata dole ya baka sha,awa kome tsab yake ga kamshi.
Ita Saiba zance baifi sau nawa ba duk dan zaman mu gidan data shigo part din sai
wanan dalilin daya kawota yanzu din.
Kodana fito wanka ta fice antyna ke nuna min nake fadin kici donni ya hau min
kai tun a wajen suyan da mukayi din na koma nayi sallah.
Saida na fito take fadin ina ganin Habu yana hanya Ramaah kallon ta nayi ina
fadin ya bugo ke nan tayi dan luuuu da ido tana fadin haka dai naji a jikina kawai
kamar shima zai zo dai yau.
Hira muke jefi jefi da ita wanda hiran zaman mu na Abujane wanan abin da mukayi
ya tuna muna idan wani zai dawo gidan yadda akan wuni ana gyaran waje da aiyuka
saidai su banga hakan garesu ba ko kadan.
Karan wagale get din gidan da akayi ya katse muna hiran mu wanda mazan gidan ne
suka iso lokacin ashe zancen antyna gaskiyane ya Habu shine yaje ya dauko dan
uwansa da yai wajen wata uku bai kasan .
Ta window part din anty na muka leka mukaga tare suke ashe dukka su ukku har da
wasu mutum biyu a lokacin.
Ya Abubakar ya jima bai shigo part dinsa ba don sun tsaya a na sauke kayan yayan
nasu zuwa part dinshi na tsaya jiransa mu gaisa sai gashi ya shigo mukai mai sannu
da zuwa.
Shi mutum ne wanda baida sakewa da kowa haka yake dunkunkun dashi ni ina mamaki
ma yadda suka hadu da yar uwar tawa haka.
In har kinji muryan yaya Habu yana tare da iya ne ko mahaifiyarsu saiko idan
ransa ya baci zai tsaya yayi fada akan abin ko kuma ya barka a cikin zullumin abin.
Bayan na gaidashine na shige na dauko abinda zan dauko nafice na koma wajensu
iya a zaune na samesu ga kayan tsaraban da aka shigo dashi part din tsofin a gefe
daya an tara.
Ban zauna falo hira ba saboda gajiyan dake jikina na shige dakin kwanan mu nan
ma ba kwanciya nayi ba saida na dan tsabatace dakin har ban dakin kafin na kwanta.
Can cikin barci nake jin maganan su Saare dake fadin dama nasan wanan abin sai
yaya yayi fada wallahi idan ya iso ya samu waje haka.
Warin ne yayi yawa Salima ta fada tana hawowa saman gadon da muke kwana tare da
ita tace na bude fridge din aina duba naman kaine yake wanan wari haka.
Makin su zubar amma wai sun aje basu fitar dashi ba duk part din ya dume da
warinsa ga kuma kazantan dake falon koshi ai takaicine.
Banfa sa sunda yau zai shigo garin nan ba Saare ta fada nan nasa masu baki nace
kuma gashi munyi aiki ba a gyara falon ba saukin abin ita Saiba ta dan gyaro
wajenta dazun din don kodana shiga na samu tana gyaran dakinta ai.
To ai a banza Ramaah duk fa cikinsu babu mai tsabta a raina nace kamu na zagin
koko ke nan kuma ai halin kuka dauka na fada kasan zuciyana.
Sai gashi Salima na bata amsa da fadin abinda iya ke fada muna ke nan kullum
wallahi nima dai zagewa zanyi da koyon irin na Ramaah ina dan aiyuka a gidan nan
don in saba.
Tabe baki Saare tayi tana fadin ko ita dake hakan ai halittance hakan bawai yin
kanta bane muryan ya J ya dakatar damu don tabbas a falon iya yake wanan tsawan.
Tsit mukayi a dakin muna saurarenshi yana fada ina zan iya kwana cikin wanan
kazantar haka iya sai doyi da bashi wajen keyi a nan dakin yusuf zan kwana yau.
Muryan mama naji tana mashi fada akan ya koma ya kwana wajen matanshi ai dole
su gyara tunda ya nuna masu bacin ransa a fili.
Can dai muka daina jin muryanshi a haka barci ya daukeni sai washe gari na falka
don akwai gajiya sosai a jikina na mulkan fulawan da mukayi jiyan.
Hakan bai hanani fitowa nayi aiyukan dana saba yi ba anan suka dawo suka sameni
part din iya suka nufo gaba dayansu shida ya Abubakar din.
Wanan ya hanani komawa part din na nufi wajen yar uwata bayan mun gaisa na karbi
aikin da takeyi din nacigaba ita kuma ta koma dakin kwanansu tana gyara.
Har inda na gama bai shigo ba dakina na koma nayi wanka na gyara jikina lokacin
naji muryan shi ya shigo yana fadin .
Bansan ya matan can suke son mayar da kansu ba gidan nan miji ya dawo tun jiya
yake bala,i dasu akan kazanta ki shiga ki saka hijab dinki kije wajen iya zamu
zauna a nan.
Ma,ana dai a fahintana zasu dan yi magana da dan uwan nasa nan part din antyna
ke nan hakan yasa nayi sauri karasa shirina a gurguje na fito daga dakin kusan
lokaci daya muka fito a dakin da ita.
Muna gaisawa dashi take fadin naje kitchen na fito mashi da kayan karyawa ita
kuma naga ta koma dakinta na dauko muka aje muka fito tare da ita daga part din.
A wajen muka samesu shida kawu suna magana muka gaidasu tayi mai sannu da dawowa
muka shiga ciki wajen su mama din dake falo suna duba tsaraba.
Shi tsaraba ga iyali wani abune mai daraja dana sanshi tun ina kankanuwa a gidan
hjy Fannah Abuja idan wani daga cikin iyalinta yaje tafiya ya dawo haka zai bimu da
tsaraba gaba daya gidan ba wani raba kai ko nuna muba yan gida bane a wajensu haka
zasu kawo muna tsaraba mai yawa da sunan mu.
Haka kuma zamu dunguma anawa wanda yakawo din godiya group group yadda muke
gidan tana saka muna albarka gaskiya don in tuna da wa yan nan mutanen arzikin a
rayuwana.
Naso antyna ta barni naje ko nidaya na ganosu tace min sai idan mijinta ya yarda
da hakan dana kara tuna mata kuma sai cewa tayi dani wai yace tare zamu gaba daya
da ita tun lokacin ban kara magana ba kuma.
A wajen su mama din gefe muka koma sai can mama din ke fadin idan kin tashi
maria ga taku tsaraban nan ta nuna mata wasu kaya harda na abinci shi yaya Habu din
yazo ya kira mama din da kansa .
Sun jima a can har iya yayin da antyna ta kwanta a nan falon tana barci don
maganin da take sha a yanzu barci yake sata da zaran tasha maganin da safe.
Lokacin da suka shiga falon Habu din Jafar ya shakin kamshin da falon keyi ya
dan lumshe ido yana sauke ajiyan zuciya bin ko ina ya farayi da kallo komai gwanin
ban sha,awa awajen, irin falon da yake muradin samu duk da part dinsa ya kusan ukun
wanan din amma kazantar matansa ya hanasu tsayawa su gyara din.
Duk da komai na zamani na more rayuwa ya zuba a falon gwaunin ban shawa amma
komai yazo ya koma masu shara a yanzu don rashin kulawansu.
Yana mamakin irin halin da matan nasa suka dauko yi mashi a gidan gaba dayansu ba
wace zai buga gaba da ita a wajen tsabtan muhalinsu wanan abin yana matukar kona
mashi rai.
Nan ya Habu din yake gabatar masu da abin karyawan da aka aje mashi din a tare
su ukkun suka karya a nan mama tazo ta samesu a part din don zancen dasuka zauna
suke son magana da yaran nasu baki daya.
Zama sukauyi na fahinta yadda ya dace din a tsakaninsu kan matsalolin da malami ya
fada a zancenshi .
Wanda kusan abin duk kamar akan shi yaya jafar zancen ke nufi da magauta suna
binsa sosai bayansa.
Sam bai dauki zancen da wani ma,anaba a wajensa don bai faye yarda da irin
zancen malaman nan bashi kawune ma ke kokari ko yaushe akansa baiki yake karba.
Yanzunma bai ki ta bakinsu ba don yasan dolene irin wanan harkan nasa ya samu
irin hakan bayan sun gama kuma sukayi zance akan matsalolinsu inda harda zancen
yayata ya fito cikin zancen.
Don asibiti suna son su riketa a can wajensu sai zuwa lokacin data haihu sin
yanke shawara kan mahaifiyar mu zatazo ta zauna da ita wanda already sunyi maganan
hakan da hardo shine ya yanke shawara kan mahaifiyar mu zatazo ta zauna da ita din
a asibitin.
Azuciyarshi shi kadai yasan yadda yake ji a ransa a yadda yaga part din yar
uwata din data gyara shi fes wanda shi a rayuwansa bai samu hakan ba duk da uban
daulan da yake labta masu agidan.
Haka yasa ya kara jin bacin rai a zuciyarshi yana tuno irin zancen da suke fada
akan auren bafulatana da Habu din yayi saida wata rana ya fito ya tsawata masu akan
irin maganan da suke yawan fada a lokacin kafin a auro yanda din a gidan.
Yau sai gashi bafulatanan da sukewa dariya tazo da tsarin da su suka kasayiwa
kansu suna tauye kansu da nasa hakan yasa a yanzu yakan sharesu na tsawon lokaci ya
zauna a can abinshi yana harkokin gabanshi.
Hakan kuma bai hana idan ya tashi zuwa gida zai tsaya ya sayo masu kaya na
alfarma na kyace raini da za,a gani a fada a wajensu.
Sai kamar bayan kwana biyune da faruwan haka ranan jumma,a kowa yaci kwaliya da
dogayen rigunan daya sayo masu inda na dauki wani kampalana dinkin dogon riga na
saka a jikina .
Zaune muke muna kallon film tare dasu mama dubu suka shigo part din gaidasu muka
farayi ban faye zama a falon ba idan suna falon nakan daga in koma ciki ko in fice
zuwa wajen anty na muyi hira.
Sai bayan sun gama gaisawa na mike na nufi cikin dakin kwanan mu lokacin mama
dubu ke fadin niko Jafar ina ta son in maka magana akan wani abinda kayi da ban
samuyi ba sai yanzu.
Ya kamata ace kayan nan daka sayo ka hada da wanan yarinyar da zamanta yanzu ya
dawo a nan bai kamata ace idan zaka sayowa matanka da yan uwanka abu kana debeta a
ciki ba.
Naji nauyi sosai da kunya tunda yau da kowa ya saka tsarabansa yai adon jumma,a
dashi a gidan nan sam banji dadin hakan ba wallahi.
Mama wace yarinya kike nufi tace kanwar matar habu din nan mana da take tare da
yar uwarta gidan nan .
Yarinyar da kwazonta wallahi ko wanan abin da kake ta yabon matanka sun hada
itace yarinyar nan ta hada masushi .
Hakan ma ba girma bane duk zancen da suke kanyi baice uffan ba don a saninsa ya
fada masu cewa da matar Habu da yar uwar nan nata a cikin tsarabansu sai Habu din
yake fadin .
No ki barshi mana mama aiba sai ya basu abinda duk ya kawowa matanshi ba hakan
wani sabon fitina zai iya kawowa kuma a tsakaninsu ai.
Ke nan itama matarka ba a bata ba ke nan kake nufi ba,a bata ba gaskiya yaya
Saare ta fada daga gefensu tana kallon yayyun nata.
Nasan udan kince sai anyi hakan zai iya kawo matsala a gidan nan don Allah a
barshi kada a kafa wanan hujjar don ni kaina ba zan iya hakan ba ko wani lokaci.
Amma Habu kai kace kai ai karami sama dashi ba dole bane sai yabawa matarka amma
yar nan dake tare da yaran nan hakan da nauyi gaskiya ace komai ba a bata ba cikin
abindaya sayo a gidan nan .
Mama ta dauki takakmana idan zai mata ban faye son takalma irin wanan ba dama
Salima ta fadawa uwar nasu dake magana cikin damuwa.



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC


MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

1️⃣4️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Ranan monday da safe na samu labarin abinda ke faruwa a gidan koshi abakin anty
Salima da yanzu muke dan shiri sosai da ita.
A wajenta nake tsuntar labaran abindake gudana gidan nasu don ni ban damu da
nasan komai ba abu daya zuwa biyu nafi rikewa a raina shine nidai yar tafiyace
ma,ana yar rakiyar aure.
Nazo gidansu a sanadin rako yar uwata aurene saboda debe kewa a gareta nasan
kuma rashin gata yasa aka hadomu tare ba wani abu ba don a ragewa mahaifiyar mu
nauyi a gabanta.
Idan bashi ba a shekatuna goma sha nayi girman da zan zama yar tafiya na koma
Murfin Jallo ga yar uwata da yanzu auren nan kamar ta danballene ma nake gani don
da da dan kuzarin ta amma a yanzu ta koma wata sau da ita bata da lakka ko wayau.
Don haka tuna sanadin zuwana gidan bai bari na wuce iyakata ba iyaka dasu halin
zama tare sun bani mafaka ni kuma in basu karfina wajen abinda ya dace.
Zance bai tasowa tun zuwan mu gidan kaji sunan yar uwata a ciki balleni musan
yadda muke takon mu dasu bakaji zance a bakin mu saidai a kiramu don shedan muna
wajen abin ya faru.
Koshj wanan zancen a zaton salima nasan da zancen take fadin gobene za a kai
Maria asibiti ko ?
Azotana irin zuwan da sukeyi suje awone take tambayana sai nake cewa eh gobene
sai naji tace dani Allah sarki ni tausayi mariya ke ban wallahi a daidai lokacin da
mutum yake son zama da mijinshi ace za a rikeshi asibiti ya zauna har sai ya haihu
wanan abin akwai takura ai a cikinsa wallahi ?
Anty Maria din zata zauna cikin asibiti har sai ta haihu anty Salima tace ba
haka akace ba Ramaah koke baki fahinci zancen bane wai Ramaah ?
Kodana dago kai hawayene ya bata min fuska ban iya magana ba ta juya ta shiga
bandaki don dama wanka zata shiga muke hiran .
Mikewa nayi na fito daga dakin zuwa wajen yar uwata da akwanakin nake ganinta
cikin damuwa zaune na sameta a falonta ta kifa kai a saman hannun kujera.
Nayi sallama na shigo fuskanta kawai na kalla nasan itama tayi kukan a lokacin
nafara fadin meyasa baki fada min abindake faruwa dake bane Yanda ?
Duk da sunan yanda din da suka san ma,ananshi a yanzu sun mayar da sunan akaina
a gidan ni kaina a yanzu ina kokarin karbe mata sunan nata da mahaifanmu ke kiranta
dashi na yan mata.
Mezan fada maki Ramaah tashin hankalin da nake ciki kema ki shiga amma ai ba
yau muka fara fadawa junan mu tashin hankali ba yanda nakirata da sunan da muka
saba kiranta dashi din.
Nacigaba da fadin ko a yanzu ban cancanci naji damuwanki bane kamar baya yadda
muka taso daga mu sai Allah sai mahaifanmu a tare damu.
Ramaah me kikeso na fada maki nace dake likita yace ba zan iya renon ciki ba
sai da kulawansu duk na tayar maki da hankali kamar yadda nawa yake a tashe ?
Kallon kofan dakin su da takeyi yasa na juya mijintane a tsaye yanayinshi kadai
zaka kalla kasan yana cikin matukar damuwa shima din a lokacin.
Hakan baisa nayi shiru ba don da yare muke maganan nace kinsan matsalan ki yanda
bata asibiti bace dole sai mun koma wajen baffa an suhunta dashi zaki zauna ki
tauye kanki a nan kuma ?
Ba wai hakana bane Ramaah abinda likita ya fada suke bi duk da nasan abin nada
alaka da baffa amma su nan birnine ai ba zasu yarda da hakan ba su.
Gyaran murya yayi na sake juyawa gareshi karasa fitowa yake zuwa falon ya samu
waje ya zauna yana fadin lafiya dai ko ?
Kalloshi nayi cikin yanayin damuwa ina fadin ina kwana ya amsa sai naji tace
zance take akan tafiyana asibiti wai lalurana bana asibiti bane sai naga ya tsuke
fuskanshi lokaci guda.
Yana fadin idan bana asibiti bane na meye ke likitace Ramaah da zaki fadi taki
hasashen abinda likita ya hasaso gareta ke nan ba zatayi wani dogon motsi ko daukan
abu mai nauyi ko wani abu da zai iya taba lafiyan mahaifan dake dauke da jinjirinta
ba a yanzu ?
Don haka dole sai sun riketa a wajensu suna bata kulawansu su saka ido ga duk
wani motsi nata a yanzu shine kawai dalilin da zata zauna a wajensu din ai.
Ummah zatazo daga Jimeta a gobe insha Allahu itace zata zauna da ita asibiti don
haka wanan ba wani abin damuwa bane insha Allah.
Duk da naji ummah mu zatazo zama da ita hakan baisa naji dadin zuwan nata ba
don nasan wahala kadai zatayi a can din tuno da lamarin baffa da zuciyana ke min.
Akan bakin halin baffa a lokacin a gaban idona naga yadda yake tauye Hanne data
shiga huruminsa abinda bai kai ya kawo ba amma haka baffa ranan don fada kawai akan
yara da suka kora shanunsu zuwa kiwo suka samu hanne ta riga su zuwa da nasu shanun
a inda zasu sake shanun mu.
Sukai magana ta kwashe taki kwashe shanayen nasu tace aita rigasu zuwa dole suka
juya da nasu shanun zuwa wani waje suka sakesu kiwo.
Bayan an dawo gidane baffa ya taresu yana fadin yau shanu basu koshi ba yasan
kuma komai shi Hanne zatayiwa tsageranci zai nuna mata ko ubanta bai isa ja


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login