Showing 186001 words to 189000 words out of 328222 words

Chapter 63 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

ai ba wasu ba ?
Ko har kin manta da cin mutuncin da kukai mai keda diyan ki da dan uwanki gashi ?
Nace kin mantane in tuna maki yanzu yadda suka zugaki idonki ya rufe akan danki
dake tausayin ki kan dukiyan da yake kula maku dashi yanzu ina dukiya nan ku yake
ina tambayanki dubu ?
Iya meya kawo wanan zancen ai taimakonshi akayi don an karbi dukiya a hannunsa
haka kuma shi bai nuna komai don an karba ai kawu dauda yake fadan hakan ga iyan.
Haka zakace tunda ka damka kana bushashanka dasu ai dole kace bai nuna bacin
ransa ba ko tunda shi ba mutum bane ko ?
To in baku sani ba ku sani duk da kuna ganin bai sauya ba dole abinda akai mashi
ya bata mashi rai don haka kuyi kuka da kanku kada ku dora laifin ga yayan mutane
da basuji ba basu gani ba .
Aure kuma mukaddarine ko a ina matanka take sai kaje ka aurota don haka ina son
ku fitar da idon ku akan yaran nan daga yau jafar dai yana zaune da matanshi lafiya
inma wani abune kece dai dashi dauda gashi kune matsalan yaranku nan ba wasu ba.
Kuka mama din ta kara dorawa sosai tana fadin meye zaisa aga laifinta shi kuma
kawu yana yan kame kame nan dai basuji din zuwan ba don tsohuwar bata yarda da
zancen da suka zo dashi ba din.
Tace kowa ya fitar da idonsa kan yaran nan da matansu inba rashin hankali ba
yaran nan meye matsalansu da auren yayan ku da kuke son sakasu gaba hakane ?
Ke in kina da hankali yadda yaran nan keda tarbiya ai abin farinciki ne ya
sameki ba wanan hakan da kikeyi a yanzu ba haka akan matan yayan ki.
Sai yanzu na kara tabbatar da kinfi bukatan ganinsu cikin tashin hankali da
matayen nasu sama da zaman lafiyan da sukeyi ashe ?
Ga dan uwankinan inba ya zama munafuki ba da bai iya fada maki gaskiya sai akasin
hakan ko yaushe shi yanzu daya samu wata da take dadada masa ai gashi da tsufansa
yana sabari a kanta da yayan angolan datazo mashi dasu gidansa.
Kiyiwa kanki karatun ta natsu tun kafin yaran na su gane nufinki a kansu dubu
su fara mayar maki da martani don dai yayanki ba rabuwa zasuyi dasu ba kin sani.
Ba kansu ai aka fara irin wanan hadin ba tunda Allah bai hana ba har uba yakan
auri kanwa da ya auri ya duk bai zama illa ba sai a gidan ki dubu kina kokari kija
da ayar Allah da Annabinsa a nan kinki kwantar da hankalinki kiki bari na yaro ya
kwanta kuma ?
Yazidu kuma kinsanshi kinsan halinsa to ki matsa dubu kikai ga abinda ba aso
akai din har yan uwanki su samu shiga kina kallo ke kikajawa kanki hakan kuma ba
wani ba ?
Nina rasa gane matsalan ki idan na tariyo sai inga duk laifin na daudane don ke
kamar kanki a burge yake yanzu tun mutuwan mijiku kuwa nake hango hakan dama shine
katangan daya tare duk wasu matsalolin da za a fahinci hakan a gareki.
Yanzu dai shawaran da zan bayar a nan shine ita mama tayi hakkuri har yazid
din yazo da matar nasa aga mata wace irin rayuwa ke gareta don Allah a fanci juna
shine zaifi tunda ya riga yayi wanan kuskuren ko ?
Banso dubu ta matsa akan zancen nan ba amma tace sai mu taso a san yadda za ayi
ya baro matarsa ya dawo nan shi kadai kawu ke fadan hakan .
Iya tace kaji shirme ko na fada maku dubu ta canza a yanzu ina kuka kwana da
zancen da nayi maku zuwa biyan bashin dake kankune dauda ?
Wanan ya kamata ace kunyi ba wanan shirme ba dakukeyi a yanzu auren da aka samu
zuria a tsakani ina ke ina shiga tsakaninsa kuma yanzu ?
Zamuje iya wajen ne yake da wahalan zuwa amma za aje din tace sai yaushe zaku
tafi ko sai kunga sun fara zaran yaran daya bayan daya zaku maida hankali ga
tafiyan ?
Goben nan ko jibi nake son duk abinda kukeyi ku maida hankali a tafi wajen nan
don naji jafaru yana zancen komawa wajen sana,anshi cikin kwanakin nan.
Zubur kawu yayi yana fadin gobe iya iya tace kwarai kai harni zamu tafi ba wai ku
kadai ba idan baku shirya ba kuyi kwatance mu tafi nida yaran nan .
Ku diba yaron nan ko bai fada ba ansan da abinda ke damunsa don yana namijin
tsayene baku gane hakan sai ya fadi kasa kuji dadin hakan ?

sorry for missing me wlh iam surfering for tooth pain all dis days yasa kukajini
shiru.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/C8kkr4INYY7FydHKKKRVhL{2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

6️⃣1️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Motsin kwarai na kasayi a lokacin gashi dai naji fitansu amma jikina ya mutu jikina
ya mutu na kasa motsin kwarai sai dubawa nakeyi ina aunawa me nayiwa mama dani da
yar uwata a zaman mu da ita ?
Saidai na kasa hango inda laifin namu yake gareta matsala dai daya shine zance
ko yar uwata data dade a tare dasu bata taba kai korafin mijinta gun mama ba yadda
sauran surukanta keyi .
Haka kuma bata taba fadawa mama wani matsala daya shafi aurensu har asani manya
su zauna dasu ayi sulhun hakan .
To balleni da ko shekara banyi a cikin su ba ince mata me akan zama da danta me
zan fada ya hadani dashi ko abokan zama da ba waje daya muke rayuwa ba balle kuma
ai bai mun wani abinda zankai karanshi wajenta ba yadda take so.
Ni dai a ganina wanan ne kawai matsalan amma bansan abinda ke boye ba a zuciyarta
amma tsanan yayi yawa a zuciyar mama kan mu.
Ban san hawaye na zuba min ba a idanu ina dai kwancene kawai naji muryanshi a
kaina yana fadin kuka kuma Rahama meya sameki kike kuka haka kuma ?
Dan yunkurawa nayi ina kokarn mikewa zaune saidai kukan yaki tsaya min naga
yakai zaune gefena ya sake fadi cikin kallona meya sameki Rahama ?
Cikin muryan kuka na daure na iya furta ba komai ina sheshekan kuka tare da
kokarin kauda kaina a gefen da yake zaunen.
Umm,humm Rahama idan kince kuka zaki dingayi kan mama zaki sha wahala sosai a
rayuwan ki don inkin duba bake taiwa hakan ba ni tayiwa don nine zaune dake.
Duk abinda takeyi bake takewa ba don nine take hakan kuma zata bari in sha
Allahu ki dai kara hakkuri nasan kinayi baga mama ba harda kannena musanman Saratu
nasan duk abinda ke gudana a tsakanin ku.
Yanzu haka ina shirin zancen auren sune da zaran Allah ya dawo dani lafiya shine
abinda nake son aiwatarwa ke nan a kansu.
Ki tashi ki shirya zamu fitane yanzu dani dake jin hakan yasa na dan kalleshi ya
gyada kai yace ehh akwai inda nake son mujena kafin na tafi tare dake.
Naji hannusa cikin nawa yana dan murzawa alaman bani hakkuri yakeyi a
zuciyarshi hakan da yai min sai nake jin sanyi a raina har ya mike yana kara fadin
in tashi in shirya kafin ya fito ya fice daga dakin.
Can falo nake jin muryanshi da iya suna hira ban tsaya saurarensu ba na shiga
shiri simple makeup nayiwa fuskana na fito na samu bai falon saidai ban jima da
fitowa ba sai gashi ya fito yake fadin kin fito ?
Iya zamu dan fita yau har gidan malam Bala nake son mu leka nida amaryata don
yayi min korafi ban kaita sun ganta ba sai labari yaji cewa na kara aure.
Yakamata kam ku dinga zumunci don zumunci a kafa yake kuko yaran yanzu kun dauka
wanan tangarahon ya wadatar maku kuma ba haka abin yake ba.
Don baku da kamar malam bala a fadin garin nan kaf shi zaku diba ku tuna da
mahaifin ki nakan so nayi wanan zancen sai in mata gashi yau Allah ya tunar dakai
hakan Allah yayi albarka kaji ya kare tsare muna ku.
Nuna mata tasan darajanka wajenshi don dama mu mata aka sani da zumunci ke kuma
don Allah ki rike ki dinga tunatar dashi tunda shi din ba mai zama bane sosai garin
kamar uba yake a wajensu bama kama ba ubanne ai.
Tunda mahaifinsu dashi Allah kadai yasan tsakaninsu har mahaifinsu ya kwanta dama
suna tare abinsu suna zumuncinsu.
Sai mun dawo mukai masu har lokacin zuciyana bai sake ba muka shiga mota ya
tayar nan yake fadin na rasa kalman da zanyi amfani dashi na baki hakkuri Rahama ?
Naga har yanzu zuciyarki yana da kunci akan zancen nan mama fa matukar tana tare
da kawu bamu taba gane kanta yadda ake so don kota dauko hanyar daidai kawu
dulmiyan da ita zaiyi so banga abin tsayawa bata rai haka cikin zancen nan ba ?
Na dan kalloshi ina sauke ajiyan zuciya da kyat bakina ya budu na iya fadin for
god sake me nayiwa mama kome yar uwata tayi mata data tsane mu haka ?
Naji yayi murmushi yana kallon hanya na sake fadin nasan tun zamana a gidan ban
taba samun matsala da ita ba why a yanzu take nuna min hakan ?
Saboda kin auri danta take ganin kunci amananta keda yan uwanki don kuci
dukiyata shine kawai kada ki kara haka mama take tun muna yara bata son muyi abokin
da zai dauke muna hankali da ita.
Ko yaushe mama tafi son ta bude ido ta ganmu a gabanta baki ganin yadda take da
yaran nan wanda bai san halinta ba sai yace ta shagwabasune amma halinta ke nan ita
taji komai namu tasan duk wani motsin mu kuko ba hakan kuke ba keda Maria.
Kawai dai tana ganin a yanzu kune kuke kokarin shiga tsakaninta damu yasa take
son sakata a gaba a fahintar ta dai kamar kuna muna wayau ne ko wani abu maka
mancin haka dai.
Wani kwana naga yabi kafin ya sauka daga titi ya juya zancenshi da fadin kinga
tsohon gidan mu da muka taso inda aka haifemu daga baya da mahaifinmu zai auri inna
shine muka koma wancan unguwar da muke yanzu don nan din yayi mashi kadan da zama
da mata hudu lokacin.
Suwa ke gidan yanzu na tsunci bakina da tambaya yace su isa da lawal ke zaune
ciki da iyalinsu su suka gaji gidan da akai rabon gadon mu.
Suna ganin a lokacin sun kware mu sun samu gida ba irin rigimar da ba ayi ba
karshe da muka hakkura sai gashi Allah yai muna sakaiya da mafificin hakan.
Dama ance mai hakkuri yana cin riba a rayuwa hakkurinkune yaja maku hakan a
yanzu ganin kofan gidab daya tsaya yasa nayi shiru ina bin gidan da kallo.
Wani tsoho mai farin gemene zaune saman wani babban tarba da shimfida yana
fitara da faifain kaba a hannunsa ya cire babban rigan dake jikinsa saboda zafi .
Gashi ya kurawa motar mu idanu nasan yana son sheda mai fitowane yake fadin ga
baba Bala can zafin nan ya dameshi sai fifita yakeyi ya samu sa,ida.
Nakanso taimaka mashi wallahi sai kuma kamar abinda aka mantar dani sai in manta
dashi gaba daya .
Fita mukayi daga motan dagani har shi muka nufi wajen tsohon da saida muka matso
kusa dashi sosai ya gane dan nasa.
Murmushi yayi yana fadin yaro mai sunan manya ashe har yanzu dai halin naka yana
nan kamar yadda nasanka a baya.
Shima jafar murmushi yayi yana fadin baba anyi mun afuwa dan Allah bawai haka
bane abubuwane suke shige mingaba yanzu.
Tsohon da duk farin gemune a fuskanshi yake gyara zama yace nasani jafaru ina
da labarin komai game daku duka ina tambayan lafiyan ku aiko yaushe gun yan uwanku.
Tare muka zube kasa gabanshi muna gaidashi ya amsa yana fadin wanan ce amaryan
taka ko don dai ba yargidan registara bace wanan ?
Kuma ba wace mukaje kaduna daurin aurenta bace yace baba wanan yar Gembuce can
yolan cameroon na aurota.
Masha Allah ya fada yana kafeni da ido nayi kasa da kaina a cikin nauyinsa kafin
naji yana fadin maddala abu yayi kyau sosai Allah ya bada zaman lafiya.
Amarya sai hakkuri kin shigo gidan yawa don haka sai kin hada da hakkuri a zauna
lafiya da kowa don Allah bisa ga amana sai kiga Allah na tare maki duk wani
farmakin da magauta zasu kai maki a boye.
Nagode baba na fada daga inda nake zaune ya maida kallonshi kan Jafar yana
fadin man Jafar ya al,amura kuma naji duk abinda ke faruwa game da yan uwanka.
Ina son ka kara zama namiji haka kuma lamarin iyayye musanman uwa gashi kuma ita
ta rage maku a yanzu da kuke tare da ita don itace zaku kalla kuyi bugun gaba da
ita koda bata raye balle tana raye to a kara da hakkuri a samu a rabu lafiya damu
dai din don wani lokacin sai an hada dole da hakkuri ake cinma manufa irin yadda
kakeyi a yanzu din.
Duk daba wai naji taka maimain zancen bane saidai ina son jan hankalinka a nan
daka kara daurewa dai ayi biyayyan nan dai da aka saba yi ko yaushe.
Haka kema amarya don Allah ki bashi hadin kai ya samu ya aiwatar da manufansa na
alheri da yakewa yan uwa da abokan arziki naji komaine a bakin Rukkaiya da Ai don
su har gobe basu yadani ba suna min bayayya kamar yadda aka taso a cikinsa.
Kwanaki sunzo gaidanine suke ban labarin abinda ke faru shine na nemi ganawa din
dakai don in kara ja maka kunne akan hakan nasa kuma kazo min da ita wanan yarinyar
na kara tausanta taci gaba da hakkurin da takeyi dai.
Nan dai ya danyi nasihanshi muna mashi godiya kafin mu muke zuwa cikin gidan
inda naga gidan babban gidane shima kamar na mahaifin su Jafar din don da gani anyi
zamani a baya tsufa da karayan arzkine ya taso yanzu.
Matan nasa duk sun tsufa ba kamar su inna da su mama dake da dan sauransu ba don
basu cikin wahalane nasan irin nasu yasa hakan.
Dakin uwargidan nasa mukayi masauki anan muka gaisa da kowa wanda Allah yaba ikon
zuwa mu gaisa a gidan don wasu kan basu zo ba suna tsabgansu a lokacin.
Wata dattijuwa mai dan tsayi take fadin Jafaru an kun manta damu yanzu koda yake
Alh yace baka zama garin ashe har aure ka kara kuma duk bamu da labari sai daga
baya.
Naji yana fadin iya ayi hakkuri auren ne yazo a haka ba kowane yasan da zancen
karin auren nawa ba don daga nemane don nisa iyayyenta sukai muna sauki aka daura
auren daga nan.
Kai masha Allah kaji mutanen arziki ba masu tunane ai nima nace dai akwai dalili
da har Alh baiji ba ashe haka abin ya kasance.
Ina kallon ikon Allah don yasan duk wani babba na gidan duk wanda yazo zasu
tsaya su gaisa sosai dashi yayi masu alheti ashe dama da shirinsa ya fito ke nan ?
Sai biyu saura muka bar gidan bayan ya cikasu da alheri muka dauki hanyar gidan
wani wajen gida ukku muka je a ranan sai bayan karfe hudu muka dawo gida.
A hanya yake cewa dani bayan ya sauke ajiyan zuciya sai naji yace wallahi sai
naji kamar an cire min kaya da naje gidajen nan.
Nan ya fara min bayanin yadda alakansu yake nagane zumuncine ya koma kamar yan
uwantaka wanda a yanzu mafiyawan sun yarda wanan akidan ta zumuncin haduwa da
mutanen da keyi a baya.
Bai kai ga ida tunane ba naji yana fadin yanzu sauran mu kaduna kuma in sha
Allahu idan na dawo zamuje muyiwa ummah nata wunin acan mu zaga wasu yan uwa a can
din don yan uwan mama akasarinsu suna zaune ne a kaduna su.
Murmushi nayi don nima hakan yana cikin raina ga mijinta da kokarin kirana mu
gaisa kwana bibiyu zai kira waya ya tambayeni muna dai lafiya ko idan mun gama
gaisawa kuma yaba umma waya itama mu gaisa.
Ganin haka yasa nima yanzu nake kokarin kiransu akai akai tunkan su kirani din mu
gaisa don kada ya fahinci ban ra,ayin shi da mahaifiyar mu.
Shiko gashi yana kamanta muna din har yaransa mata ya tayar da aka kwana biyu
akan suzo su dubani suga yaya zaman mu yake ?
Inda wata daga cikinsu take fada min ai tasan Saiba da Asmau a school daya
sukayi nan Queen Amina zaria.
Take fada min cewa abokaine fa sosai don har provition dinsu a lokacin tare yake
saidai kazamaine na gaske kowa yasan su da kazanta ko yanzu sun barine take
tambayana hakan ?
Nayi murmushi ina fadin wallahi ban sani ba don ba shiga wajensu nakeyi bani
koda na zauna gidan kowa da part dinsa saitace ki daiyi hankali dasu don ba karamar
yar shige shige bace Nusaiban nan.
Don abinda tayi ke nan ta kwacewa kawarta miji ance kuma zaman nasu ba dadi a
tsakaninsu itace ke juya kan gidan sun mayar da Asmaun kamar shasha ita da mijin
ku.
Nan ma dai dariya nayi ina fadin ba gaskiya bane anty kowa dai da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login