Showing 219001 words to 222000 words out of 328222 words

Chapter 74 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

da gani cikin wahala yake zuboshi.
Daki kamashi ya dago mama ta fada saita juyo ta dan dubi mama din tana fadin ni
yaya zanyi in kamashi haka mama ?
Ke yar nan amma baki da kunya dazun nan kike fada akan wata tazo ta taimaka
yanzu kuma kice ke baki san ya zaki kamashi ba ?
Duk yadda zaki kama ai kin sani tunda wace ke iyawan kin yakinceta da zuwa kusa
dashi din yanzu ki dagoshi kada ya sarke don Allah ?
Tayi kamar zata dagoshi din sai kuma ta fasa ta juyo gun mama din tana fadin sai
wani ya taimaka min hakan yasa mama tashi ta kamashi a hannunta ya karasa aman
saida ya gama ta wanke mashi bakinsa.
Washegari kuma dai haka mama tasata gaba akab tayi mai wankan magani din a
wahalce ta karasa kwana biyun ta sai gashi wai ta kwanta bata da lafiya tunkan
lokacin ta ya kare Asmau ta karbeta din .
Dole mama tasa na kama don Asmau ko wahalan goyo ya isheta haka dai ake rayuwan
a jigirce don kowa mama bata bari ba a cikin mu wanan zaman sai gashi an daina zuwa
kwanan da aka fara saidai wace zata karbeshi itace zata shigo koshi na dolene nikan
da rana bani wuni dasu ina wajen exam dina .
Wani lokaci kona fito da wuri zan wuce can gidana in huta sai yamma zan dawo sun
wahala lokacin don mama zaune suke suna bada command kuma dole ayi din .
A hakan na gama exam din na a wahalce abin farun ciki amma yazo min da rashin
walwala don ba wani farin cikin da nayi da hakan asalima nasan dai faduwa zanyi ga
jerabawan nan don banyi karatu ba .
Dole na mayar da hankali gun jinyar yaya don yadda ko ganina yayi na gitta ya
kafawa wurin ido ke nan bai kawarwa sai idan ya daina ganina .
Don a yanzu yana gani saidai ba magana ba kuma wani motsi jikinsa a sake yake
kamar jikin ya mutu nakan kebe in samu wuri inyi kuka mai isata in fito.
Tun dai ranan da Saare da Saiba sukai min habaici a cikin magana da Saiba ke
fadin kwadayin wasu baiyi rana ba don an kare a wahala.
A dama ai ance kuda wajen kwadayi yake mutuwa wanan kudan da alama kan a
kwadayin za a mutu don an fada ruwa tsundum .
Kudaje dai don ba kuda bane kawai mai kwadayi akwai sauro mai dafi yasha jinin
na tare dashi acan ake makeshi wajen kwadayinsa .
Wanda bai ko fara allon sa ba balle ya biya shikewa mai sauka shagube ai gara da
wanda ya sauke yafi wanda bai gwada saukan ba.
Ai Gara da kudan ya san dadin kwadayi don dai ya lasa din koda pdll
Qwya mutu, don ba duka kuda bane suke mutuwa a wajen kwadayi.
Balle shi wanda ko masunsuni bashi da yaje zagin mai kamshi,daji bai ga ma cin
wuta balle aiwa kututure barka da arziki.
Me kike nufi da hakan amsan zancen ku na baki indai kwadayi ya shigo dani gidan
dan uwanki ai gara dani na lasa keko dako gidan da zaki baki sani ba fa ?
Kina nufin bata aure ke nan kome duk yadda kikace inma haka kuka dauka don ba
wace zatace cas bance da ita kule ba a cikin ku.
Salatin da Anty barakha ta saka yasa mu kallon kofa ta karaso tana fadin wanan
wani irin rashin hankalone mijin ku na kwance haka a wani hali kuke haka a gabanshi
don Allah ?
Anty yarinyar nan yar rainin wayauce daga muna magana da ta sako muna baki a
zancen mu tana son fadawa mutane maganan banza don tana ganin yanzu daidai take da
kowa a gidan nan ?
Haba dai kamar ya daidai take da kowa dama ai daidai taken da kowa tunda itama
aure take kamar kowa a cikin gidan za ace ba zatayi magana ba kuma idan ya
shafeta ?
To shike nan dama kuke nuna mata hakan shiyasa take kokarin dagawa mutane kai
bar ganin a kwanaki kin shanmace mu kina ganin kamar kinci galabane a kan mu
lokacin ?
Ko zaku gwadane a yanzu ko zaku rama duk macen datace zata sakani gaba a gidan
nan mu zuba da ita ban shiga tsabgan kowa a cikin ku ba balle mace tace zata fada
min magana na kyaleta ?
Abinda kowan ku ke takama dashi shine miji nima ina takama dashi a yanzu don
haka kikai min ba daidai ba sai dai muji zafin a tare dake wallahi.
Ramaah ki kyale zancen nan ku duba bawan Allah nan a kwance a tsamanin ku baya
jin abinda kukeyi ne don baya iya fadane kawai amma yanzu yaya yana fahintar komai
da akeyi gabansa.
Anty Salima idan kwadayi yasa na auri yaya itama kwadayinne yasa ta auri mijin
kawarta ai don ta fini zalama tunda ita tanace saida ta aureshi .
Dani dake waye makwadaicin a yanzu ciwo kuma Allah ne ya dora mashi shi kuma zai
yaye mashi aduk lokacin da yaga daman hakan gareshi ita kuma Saare rashin sanin
zafin dan uwanta yasa har take furta hakan gareni a yanzu.
Idan fitsari banzane kaza tayi mana aiko ida nufi bajintane ga mai rabo aurena
da dan uwanki nufin Allah ne a garemu mu biyun duka inma cutane ni kuka cuta da
mugun nufinku a kaina daya koma min hakan a yanzu.
Don haka ni ban raina kyauta da baiwan da Allah yai min na matsayin mata ga yaya
ba duk da halin da yake ciki a yanzu kuwa.
Lafiyanshi najawa ba abin duniyan dayake tsone maku ido ba don ban taba saka abin
duniya a raina ba aure nayi da yaya na tsakani da Allah ba don komai ba iyauyena
sun amince dashi a gareni a matsayin miji nima na amince da hakan don bansan baiwan
da Allah yai min na dalilin hakan ba ?
Ku dake ganin kwadayi ya kawoni na aureshi yau gashi ya fada jinya a halin rai
kwakwai ku hakan yaiwa dadi har kuka fada baki sake don ba Allah a zuciyarku.
Haba don Allah ina wanan zance ya fito haka kuma lafiyan ku kalau kuwa muna da
mutum haka a gaban mu har kuka samu wajen fitina haka don Allah ?
Asmauce take fadan hakan a cikin zafin rai na juya gateta a zafafe ina fadin anty
Asmau matukar Nusaiba bata rike girmanta a kaina ba nima ba zan taba girmamata a
idona ba har ita da Saratu zasu zauna suna sakar min magana don ina tsoron su in
kyalesu niba irin wace zata zauna kiwa abinda ranki yake so bane.
Ya isa hakan tunda sunyi shiru kadama ta bari don Allah taci gaba tunda ita tafi
kowa baki dama dan kauye ai bai iya wayewa ba aka ce .
Allah sarki dadin abin kowa asalinsa kauyene abin bukata shine ilimi koda yake
ba abin mamaki bane don kince hakan tunda baku tsaya kun ilimantu ba dole kuyi
halin marasa hankali.
Wanan maganan dana fada shiya harzuka su muka koma cacan baki da karfi dasu har
mutanen gida suka farga da abinda ke faruwa a lokacin .
Anyi daidai maman tudun wada ta dawo suka shigo suna salati da tambayan meke
faruwa nan suka so juya zancen da cewa nice na jawo fitinan nan mama take fadin.
Assha Rahama ina ganin ki mai hankali ya kuma haka a gaban mara lafiya kuke
jidali haka cikin rashin hankali nan nima na mayar masu da yadda suka tsokaleni na
kasa hakkuri.
Tir da halin ki Saratu halin nan naki baiyi ba wallahi ko dai me kikayi Jafaru
dan uwankine na jini baki kuma da kamar shi yarinyar nan kowa ya sani tana iya
bakin kokarin ta wajen kawar da kanta ga duk wani fitina ga zancen nan.
Amma saida kuka san hanyar da kuka bi akaji bakin ku haka hatta kayan amfani ina
kule ke Nusaiba kwashe abinki kikeyi don kada tayi amfani dashi saida ta sayo nata
ta aje a nan .
To tsaya kuji wallahi daga yau tunda ciwon yaron nan ba damuwanku, yayi ba gaba
dayan ku banda shigowa gaisuwa ku duba shi kada wace ta kara zama a wajen nan tunda
ba damuwa da ciwon nasa kukayi ba.
Na dauka abinku na lokacine zaku saduda ku natsu ta dalilin wanan abin daya samu
yaron nan sai gashi rashin hankalin ku yafi haka ashe.
Ke kuma ki koma can gidan ki idan kinso kizo ki dubashi ki koma kullum inma ba
zaki zo ba dai kiyi zamanki a dakinki ba sai kinzo ba.
Mama dubu ce ke fada cikin bacin rai damu duka ina yunkurin mikewa naji dayan
maman tana fadin ai idan wanan yar mai kulan ta barmu zance ya baci don ko gyaran
wajen nan da take wuni yi a kullum ya ishemu balle irin dawainiyar da takeyi da
yaron nan .
Ba wanu zancen raba kwana tunda rabon baida amfani mu dake nan da ita zamuyi ita
su kuma da rana su dubashi dama ba yau ba na jima ina son yin wanan maganan.
Don da gaiya za a shigo a bata wajen nan sai a barta da gyaransa ni abinku yana
daure min kai yau ko auren kiyayya kukayi da yaron nan ai kwa tausaya masa halin
nan da yake ciki haka ?
Ai wa yan nan banjin zasu canza halinsu don na dade da fahintar hakan garesu ba
kurciya bane ba kishi bane kawai dai rashin hankaline ke damun yaran nan iya ta
fada.
Tun wancan ciwon nasa na farko na dade da fahintar hakan tun karkice wanan
Nusaiba sam kwakwalwanta baya ja karatunsu da suke kurin sunyi baida amfani a
wajensu .
Yau yaron nan koba mijinsu bane suke ganinsa a wanan halin ai duk mai hankali
zai kara tsoron ubangijinsa ga hakan amma sam babu wanan a garesu sai sha,anin
gabansu sukeyi cikin jin dadi da walwala kamar babu fitina irin haka a gabansu.
Ku in kuna da hankali abin bakin ciki da tashin hankalin babba ya sameku a yanzu
don bamu kadai wanan abin ya shafa inma kuna ganin mune da hasaran hakan kuje kuyi
tunane kun fimu hasara kuda yake mijin ku.
Ba kamar ke Nusaiban nan da wanan sakariyan mara hankali Saratu wace bata san
ciwon kanta ba ban taba ji ko ganin dan uwan dakewa dan uwansa wanan halin da sunan
so ba .
Idan kinayi don wani manufane na zuciyar ki saiki matsa kiyi tayi dan uwankine
dai jafaru kafin kisan Nusaiban nan Jafar kika taso kika sani ta dalilin shi kuma
kika san Nusaiban .
Kuka saratun ta fara sosai amma mama bata saurara mata ba daga mu har mama Dubu
harma Salima duk mama din ta hada ta zagemu tas iya na tayata.
Wanan ne dalilin da aka daina robon kwanan da akeyi din inda mama ta kafa dokan
cewa sai su shigo su dubashi da rana zuwa goman dare bata bukatan ganin kowa a part
din kuma.
Daga wanan ranan komai ya sauya haka shima mai jikin a dan ganin sauki sosai ga
lamarin nasa don dai yanzu alaman sauki yana baiyana a gareshi .
Matsalan dai shine har zuwa yanzu din bai magana ba kuma motsi zai daiyi alaman
yana son abu da idanu .
Masu magani kuma kasuwan su ya bude a dauko wanan yayi bajintarshi wani yazo
abu dayane ban fasa yi mashi amfani da maganin gidan mu ba din wanda daga iya sai
maman tudu suka sani sai kuma ya habu da mahaifiyarsu.
Kawuma yana zuwa dubanshi sai dai yadda iya kan zage tana nuna masa bacin rai
yasa ya daina zuwa sosai yanzu din don ko yazo daga waje yake tsayawa wani lokacin
bai shigowa.
A cikin hakane wata rana ya habu ya shigo yana fadawa iyayyen nasa matsalan da
aka samu da dukiyan yaya din dake can ikko .
Ida yace zaije da kansa ya gano halin da ake ciki duk da bawai yasan komai bane
akan dukiyan nasa amma dai zaije da kansa shida yaya Auwal zasuyi tafiyan sai wani
abokin shi jafar din.
Sun je din sai dai basu gane komai ba don da alama kamar dai dukiyan na shirin
salwanta sun dawo a cikin bacin rai suna bayani ga iyayyen nasu kan abinda sukaje
suka sama a can din.
Wanan ya kawo cecekuce ga yan uwa inda wasu ke ganin kodai ya habu yabi bayane
ya karbe dukiyan ba da sanin kowa ba.
Wanan tsegumin daga yan uwansu na dakinsu ya fara fitowa har maganan ya dawo
kunnen iyayyensu ranan maman tudu tayi fada sosai inda taketa ta,alka laifin hakan
ga mama akan duk ita tayi sake da har hakan ke faruwa.
Hakan yasa ya habu din yayi fushin zuciya yake fadin har na nan arewa da yake
kulan mashi dasu zai dawo da dukiyan a tara a waje daya.
Ana cikin haka Allah ya jefo Yazid a wani dare ya iso zaria dashi da iyalinshi ni
dai ina zaune ina murza mashi magani a kafa naji ihu a cikin gida.
Saida na saurara nagane ba fada bane wai ashe murnan zuwansune sukeyi saigashi
anzo fadawa iya zuwan nasa iyan ta fita ta bar mu dagani sai mama tudu dashi.
Ki natsu ki kara mayar da hankalin ki kinji yar nan insha Allahu ladan ki yana
ga Allah shine kadai zai saka maki da alherinsa Allah ya tayar da kafadan mijinku
lafiya.
Nagane dani take yasa na amsa da amin tacigaba da fadin a kullun nikan ina gani
sauki a cikin lamarin yaron nan kibar wa yan can marasa hankalin suje suyi ta gulma
da zasuyi iya ka su zageni shine kawai amma ni ina da hankali ba zan bari a batawa
yaron nan maganin saba.
Ba tauyeki nayi na dora maki laluran nan ke kadai ba nasan kece kadai zaki masa
abu tsakani da Allah uwarsa ma ta sani amma tana jin tsoron magana yasa na ari
bakinta nayi hakan.
Sallaman bakin nasune ya katse mata maganan take masu sannu da zuwa sau daya na
dago kai na dubesu na mayar da hankali wajen abinda nake masa.
Ya karaso yana fadin ya subbahanal dan uwa kaine a cikin wanan halin innalillahi
wa inna alaihim raji,un maman tudu take fadin ai kaga sauki a yanzu yazid.
Nan na juyo ina mashi sannu da zuwa ya amsa har lokacin hankalinsa yana ga dan
uwansa dake kwance sambal a saman katifa
Suna da matukar kama da yaya habu har kamar tasu ma ya baci don sai kace ko
tagwayenesu da yaran nasa biyu sai matarsa da gabinta irin bakaken larabawan nan na
sudan akwai kyau sosai gareta gaskiya.
A nan dai muka gaisa da ita din don itama hankalinta na kan dan uwan mijin nata
dake kwance nagama na gyara wurin na kwashe kayan zuwan kitchen .
Nafito na samu iya ta dawo falon suna kara gaisawa yana zaune daidai satin kan
dan uwan nasa dake kwance .
Naji yana tambayab koya ganesu ita mama din ke fadin ya gane ka baka ga yana
kallon ka ba yana murmushi.
Wanan matarshi ce yake tambaya mama take bashi amsa da itace matarshi ta ukku
sauran fa ya tambaya take fadin suna part dinsu.
Zasu shigo yanzu tunda sunji kazo yake tambayab yanzu wani mataki ake ciki
dashine mama munyi waya da habu yace min yana kaduna tun safe.
To yazid matakin ke nan mu zubawa sarautan Allah ido kome Allah yayi daidaine
don asibitin da kansu sun bamu shawaran agwada na gargajiya a gani suna zuwa kuma
nan gida ana dubashi ko wani lokaci halin da muke ciki ke nan a yanzu.
Wa iyazu billah ya fada yana girgiza kai ya mayar da kallonshi ga dan uwansa a
lokacin ne matan yaya jafar din suka shigo yi masu sannu da zuwa ita Saiba ke
fadin ashe kuna hanya bamu sani ba ?
Yace mun taso tun shekaran jiya yau muka taso sai yau muka samu karasowa sannun
mu da wanan halin da dan uwa ya shiga ciki suka amsa da sannun mu dai din .
Kalman data fito a bakinsa shine shi kawu din yana zuwa dubab shi har yanzu iya
ko kun hanashi zuwa don in ina nan ba zaizo ba ?




ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join
my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

7️⃣0️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Da zafinsa ya dawo kasan ba irin bakuntan nan wai ya dade baya gida din nan sam shi
baiyi hakan ba da ganinsama karatu ya hudashi sosai magana kadan zaice Allah yace
Annabi yace yanzune zai katse mutum shi ba ruwanshi.
Iyaka dasu gaisu idan sun shigo ban dogon motsi ballema yasan dani a gidan har
kishiyoyina duk sun kama kansu dashi suma.
Kannesu ma sun kama balle mu din yana da kwana biyu da zuwa yayiwa Saratu tas a
gaban kowa yake fadin tayi hankali yana da labarin komai akanta fa don haka ta
shiga taitayinta dashi.
Akan zancen abincine da yace matarshi bata cin tuwo kada a kawo masu sai saratu
din tace ita din yar gidan uban waye ta tashi ta girka mana da kanta ita tuwo mama
tace tayi shi kuma zatayi ta dafa ta kai masu..
Shine ya biyota har part din da abincin ya kwashi fadanshi yace kuma ta tashi ta
girka masu wani


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login