Showing 99001 words to 102000 words out of 328222 words

Chapter 34 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

, , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Wasa wasa zancen sati biyu yake batun sharewa bai gida run bayan tafiyan wuni dako
kila ya kwana yabar zaria dashi sai gashi kwanansa goma sha biyu da tafiya .
Wanda yai daidai da tafiyana don tafiyana kwana goma sha,ukku ke nan yanzu hakan
yasa matan yaya din a cikin damuwa .
Ga iya dake sake masu zancen cewa saboda bakin ciki sun kora mata jika ya tafi
shida ba lafiya ya isheshi a jiki ba amma masifansu yasa yabar gida dole.
Irin wanan maganan da iya keyi yasa Nusaiba ta fito fili ta nuna damuwanta ga
tafiyan nasa inda itama ta fara nuna damuwanta ko waya basu samun shi gaba daya ya
daina amfani da sim din da aka sanshi dashi da farko .
Daga Abuja ya wuce matatar mai don yin wasu cikin takardu daya dade yana neman
daman cika hannu a cikinsa.
Sai gashi kwatsam an kirashi yazo ya cika takardan an bashi daman yin hakan a
lokacin don shi ya kwasa zuwa fatakwal din.
Kwanasa hudu ya gama abinda ya kaishi daga can ya nufi lagos a lagos din ya samu
aiyuka da yawa da suka shagal dashi wanan yasa su a zatonsu suke ganin ya bar
gidane saboda matsalan daya faru din.
Saidai Habu yana da labarin komai da yake gudanarwa don ya sanar dashi abinda ya
taso masa don haka duk surutan da akeyi ido kawai Habu din ya zuba masu baicewa
kowa kala ba.
Nikan na zata ya hakkura da zancenane don jinshi shiru da nayi har anty salma
namin sheri wai na kore yayana da hali ya kama kansa dani.
Har take cewa Ni dama nasan za,a rina wai ansaci zanin mahaukaciya don matansa
sun riga da sun girgizaki dashi Ramaah.
Dama kuma ance kuskure daya mutum keyi a rayuwansa mai ban haushi don haka shi
tun farko yayi kuskuren rashin daukan mataki a lokacin.
Saidai ni a waje ke Ramaah irin matakin da yake son dauka din shine ake kira da
gyaiyya don yafi wanda kika so ya dauka zafi don shi naso ki nuna masa aiba komai
har su fahinci akwai kauna a tsakaninku ta gaskiya.
Amma yanzu ai ba zasuji haushin komai ba tunda basu san kunyi hakan dashi ba
kuma bame fada masu balle hakan ya damesu.
Ajiyan zuciya na sauke ina lumshe idona a lokacin banjin komai a raina saina
daukan fansa matukar ban dauki wanan fansan a garesu ba ina iya hade zuciyata duk
sanda nayi arba dasu kuwa.
Idona da suke a lumshe na,dan bude ina kallonta nace wanan saiba din ko don ita
da saare zan iya hakan a yanzu anty .
Nafisa ke fada min sunce wai kunya yasa na bar gari wai da bakinsu suke fadin
sherinsu yayi aiki saura anty maria komai dadewa sai sunsa tabar gidan nan.
Kutumuu,lesi ai uban kuturu yai kadan wallahi gida kuma zaki koma cikin sa
tsunbul ba maria ba har ke sai sun gani a gidan tsakiyansu kuwa.
Munyi hakan da kwana biyu na gaji sosai ranan don practical din da mukayi a
training center din mu donshi ma na kwanta da wuri ranan.
Misalin sha biyun dare a daidai wanan lokacin wayata dakr ajiye a karkashin filo
ta dinga kara da alama kirane ke shigowa a lokacin.
A cikin barci naji sautin karan yana shiga kunnena tare da verbiration din da
yake fita daga wayan.
Dan guntu tsuki naja tare da mika hannu cikin magiyan barci saboda dadin barcin
da nake ji a lokacin.
Jikina gaba daya tsami yayi nakai hannu na dinga lalubo wayar kasan filo ba tare
dana tsaya duban mai kiran nawa ba na kara a kunnena bayan na dauka.
Muryan yaya na tsinkayo yana fadin Ramatu Rahama tabbas kinci sunan ki don na
fara sheda hakan a gareki.
Ai na zata ba zaki daga wayan ba saboda dare yayi duk da dai dare baiyi ba a
wajen matafiya ni gani nan yanzu haka airport ina jiran Jirgin mu ya tashi.
Kalman da yake fada din yasa na gane yana shirin tafiyane wani waje lokacin
shirun da yaji nayine yasa ya kara fadan hello kina jina kuwa ?
Da kyat na iya bude bakina da yai min nauyi na amsa da ina ji yaya Allah ya
tsare hanya aje lafiya a dawo lafiya Allah kuma ya bada sa,an tafiya.
Masha Allah nagode kwarai Rahama kece kadai na kira a duk yan uwa ina sheda maki
zancen tafiyan nan don ina kyautata zaton jin hakan dama a gareki.
Rahama ke din Alherice a gareni sosai na fahinci hakan a yan kwanakin nan tabbas
akwai alheri a taraiyana dake Rahama domin naga hasken dake tunkaro rayuwata tun
zancen nan bai kankama ba sosai a tsakanin mu.
Kiyi hakkuri da yayanki Rahama ki karbi bukatata dani dake din taraiyan mu akwai
alheri sosai a cikinsa in sha Allahu zakice na fada wata rana.
Kinsan meyasa nace hakan a gareki dole kinsan ina da dalilin hakan dana fada don
kuwa nina san irin farin cikin da Allah ubangiji ya jefani a cikinsa cikin yan
kwana kin nan.
Rahama abinda na dade ina mafalkin samunsane Allah ya banshi a wanan lokacin .
Don haka zuciyana taban ke din alherice a garemu baki daya don bani kadai ba kowa
dake kusa damu wanan alherin zai shafa insha Allahu.
Kalaman dayake fada min sunyi matukar daure min kai a lokacin saboda ban
fahinceshi ba sam don haka sai nake fadi a yar siririyar murya da Allah ya kara
tabbatar muna da alherin ya amsa cike da jin dadi da amin Rahamata.
Sai naji abin wani bambarakwai a kunnuwata wai nice yaya yake kira da Rahamarsa
haba dai maza ashe haka suke saboda soyayya sai babban mutum ya zamo yaro a
gabanka.
Akwai wayewan kai a yar fahintan da naiwa rayuwan mutum biyu a yanzu ma,ana miji
da mata ko saurayi da budurwa.
A tsakaninsu akwai kyautatawa da burge juna a lokacin taraina koda akwai sabanin
hankali idan Allah ya hada wanan burgewan yana nan a zukatansu.
Jin nayi shiru na shiga dogon tunane yasa yake fadin kina jina Rahama ina son
dana dawo wanan tafiyan in sha Allahu za ayi komai a tsakanin mu.
Fatana ki kwantar da hankalinki ki cire wani shakku da tsoro a zuciyar ki kada ki
tsaya duban rayuwan wani ki duba tamu da nake kokarin ginawa a yanzu.
Sam ban yarda da tsarin anty Salma na cewa ki zauna a hostel ko a kama campus ba
nafi bukatan kai tsaye ki dawo Zaria a matsayin matar jafar.
Gabana naji ya fadi da wanan kalman da sauri na tareshi da fadin a,a yaya don
Allah kayi hakkuri ban taba wanan tunanen ba kuma ba zanyi a yanzu ba.
Kai din a yayyuna nake daukanku yaya ba irin wanan zancen a tsakanin mu don Allah
kamar yadda ka fada a baya ba a daukan hukunci a cikin fushi yaya.
Haka kuma matanka basuyi karya ba yaya kaidin ba tsaran aurena bane sun fadi
gaskiya da sukace naje na nemi daidai dani dan daji.
Nima ai daga dajin asalina yake ko habu bai fada maku asalin mu daga kauye
mahaifin mu ya fito yazo nan zaria ba.
Sun san kin fisu da komai Rahama hassadan hakan yasa suka sakaki a gaba har
sherinsu ya haska min hanyan da ban gani da farko saida kalamansu ya haska min
hanya sun kwakwasa min kofa da zan bude sabon shafi a rayuwata.
Don haka a cikin kalamina Rahama ba gudu ba ja da baya don a shirye na fito da
makamaina kan mai uwa da wabi zanyi lokaci guda.
Kasake nayi ga bugun zuciya dake harba min lokaci guda tunane barkatai suka taru
min a kasan zuciyana .
Tabbas idan na samu yaya a miji na more a rayuwata saidai bahaushe yace ana barin
halas don kunya dolene naki karban tayin yaya a kaina don tsira da mutuncin yar
uwata dake aure a gidansu .
Yau badon hakan ba kai tsaye zan amsa tayin nasa sai dai wani sashe na zuciyana
yana mai ban shawara da mai zai hana inbi shawaran anty salma ko girgiza imanin su
indanyi.
Muryanshi naji yana fadin zan barki Rahama an fara sanar muna da mu karaso kusa
jirgin mu yana kan layi.
Saina samu muryata da fadin to yaya Allah ya kaika lafiya ya bada sa,ab tafiya
amin Rahamata in kuma dawo lafiya in sameki a shirye da tarona.
Muka kashe wayan da karfin gaske nake jin zuciyata ta bugawa hakan yasa na sauke
ajiyan zuciya ina lumshe idanuwa tunane barkatai nayisa a lokacin kan in yarda ko
kada in yarda .
Washegari da safe haka na tashi ina jin zuciyana tayi min nauyi don kwana
tunanen dana zaunayi dogon riga dinkin dinkin atamfa mai A sharp na saka a jikina
sai dan karamin gyale dana dora a kaina .
Abujane fa birnin taraiya Abuja ko dame kazo anfika saidai kayi naka banjintar ka
bari wani yazo da tasa kalan .
A falo na samu anty Salma zaune tana ba yaranta abinci tun daga fitowana take
fadin oya zo na zata ai kina kwancene wanan dan naki dan rigima wai ba zaici abinci
ba haka zai tafi school da yunwa.
Murmushi nayi na karasa na karbi abincin a hannunta ina lalashin yaron kafin ya
soma karba yaci daga hannuna har suka gama na rakasu har bakin mota suka tafi.
Falon na dawo don sai goma zan fita tana waya na kwashe kayan zuwa kitchen nakai
na fito bayan mun gaisa da yan aikinta dake dauka ni din yar uwatarcen ta jini
kamar yadda take fada a kaina din
Don haka suke kirana da small hjy zama nayi a gefenta din ta juyo tana fadin
kai Ramaah wai kinga yadda kikayi wani fresh dake kuwa wanan aiko yau kika koma
zaria ba zasu ganeki ba
Waini kan ya zancen mutumin nakine kwana biyu banji zancensa ko kin fita
batunsane wai gaskiya Rahama ina sonki da guy din nan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,

3️⃣5️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Bayan sati biyu da hakan shigan bazata yayi masu don da safe yashigo gidan wanda
ke nuna a garin ya kwana ke nan don duk wanda yagashi a zaria karfe takwas na safe
haka yasan a cikin garin ya kwana.
An kasa samun wanda zai tambayeshi ina ya kwana sai iyace take fadin amma a garin
nan ka kwana Jafaru.
Ya bata amsa da eh iya cikin gari na kwana nashigi da darene sai kawai na sauka
wancan gidan nawa.
Kana da wani gidane dama Jafar ban taba sani ba kowama bai sani ba iya idan ba
yanzun din da nake fada maki ba amma na dade da ginasa ai komai kuma na saka a
cikin gidan.
Ina son in kai amaryata can ta zauna ita kadai sai masu tayata aiki kawai a gidan
kinga na samu gidan hutu ke nan .
Can zai zama Abuja kenan yaya nan kuma gidan kwamacala ya zama lagos ko don
lagos shike daukan duk wani kwaram da amma.
Salimace take fadin hakan a cikin barkwanci ga dan uwan nata data dauka zolayan
iya yakeyi ya fadi hakan.
Saiba dake zaune ta tsoma bakiga zancen da fadin babu wata shegiyan da zata
shigo muna gida iyamu, mun isheka rayuwa muma din ya aka iya damu balle aje dauko
wata.
Ta fada tana turo baki dake nuna tana cike dashi har lokacin gashi ya sharesu
kusan wata daya ke nan yanzu ya dawo kuma ba wace ya tsaya kulawa a cikinsu.
Itako Asmau sai cewa tayi ai lagos din ma ba laifi indai zaka zauna lafiya ko a
lagos ai akwai more rayuwa sosai ma don yafi wani wajen sau dubu.
Salima tace amma ai kusan cewa Villa shiyafi dadi ko ?
Don gaka ga gidan kudi kullum kana jin kamshin bugunsu haka kuma shine headquater
da kowa ya sani dai dole yaya ya tare da amaryansa Villar ku kuma kuna nan da yara
kuna kwamacalan ku.
Dadin abin dai ba a canzawa tuwo suna haka kuma baka zama da miya ba tuwo don
shine abokin hadinsa mu din dai mune dai ba wata yar banzan da zata sake shigowa
gidan nan da sunan matan aure a part din nan sai dai can gaba kuma .
Wayanshi dake kusa dashi ya dauka cikin rashin damuwa da zantukan da sukeyi
lokacin can a ka daga yake fadin kai Habu kana inane wai gani gida zaria ?
Ina nan kano tun shekaran jiya ana karasa sauke maine har yanzu to idan an gama
kazo gida don ba dadewa zanyi ba zan koma .
Ina tafe yau din nan in sha Allahu zuwa yamma Habu din ya fada yace Allah ya
kawo ka lafiya yana kashe wayar tasa ya aje gefe daya.
Sai lokacin iya ke fadin da alama dai wani tafiyan zakayi ke nan kuma Allah ya
tsare muna ku Jafar a duk inda kuka nufa din ya amsa da amin iya.
Yanzuma akwai abinda nashigo yi a nan zaria don da baku ganni maza ba saboda
aiyukan da suka taso sosai a yanzu sai iyan ta karba da madalla haka muke son ji ko
yaushe aiki ai alherine.
Ta juya ta kalli salima data rakota tana fadin to ke zaki zauna nan ne kuna cika
baki ko zaki maidani wajena don naga baku karasa cacan bakin naku ba har yanzu.
Ehh lalai ma Iya cacan baki kika dauki zancen mu ashe yanzu akwai wata wace
zatayi gigin shigo muna gidan nan da sunan kishiya ?
Au kina wasa wuka a gaban doki ne don yaji tsoro ko to jafaru ba raggon maza
bane yana da ikon cikawa da biyu a rana daya.
Yadda aka auroki kika shigo kika hana wata rawan hantsi kema haka za a dauko wata
a kawo bayanki don ba a haifi namiji don mace daya ba dama.
Tashi muje yar nan ta dubi Salima bayan ta gama maganan daya harzuka Saiba din
data gane nufinta ta zata asirin da take bankawa jikan nata yana tasiri akansane da
har bai iya daukan wani kwakwaran mataki akansu.
Jafar yasha yiwa iya korafi akan Saiba ko ince ya kawo mata karan sai ba din kan
barbade barbade ga abinci ko cusa abu a gabanta bayab sun gama sunna ya ga abin tun
yana mata fadan hakan dagashi sai ita har yagane hakan yabi jikinta ba zai iya
lamuntan hakan gareta ba yakai karanta wajen iyan akan a tsawata mata ta daina
wanan halin.
Wanan yasa ciwon sa na farko harda zargin saiba din saida sukayi wanda dama
hakane ga mace mai hadawa da surukulle wata rana har abata abinda zai cutawa abokin
zamanta cikin rashin sani da sunan taimako a gareta.
Ya Habu bai shigo gari ba sai wajajen la,asar ya dan gauta ya iso tun
shigowansa gidan ya hango motan dan uwansa a kofan part dinsa.
Nasa part din ya tsayar da motarsa ya shiga ciki inda ya samu matarsa da dansa
don ita ba ma,abociyar son shiga jama,a bace wanan ya kara mata bakin jini a gidan
suka kara tsanarta.
Don sun dauka daukan kai take masu don tana ganin kamar ta fisu wanda ba haka
bane haline saika zauna da ita na wani lokaci batace dakai kalla ba saika gaji kayi
mata magana.
A part din iya suka hadu da dan uwan nasa sun dan zauna na lokaci kafin suka
mike da sunan zuwa wajen mama dake can tudun wada family house dinsu ita da Saare
da Nafisa.
Tun zuwa sunan matar yaya sani basu dawo gidan ba suka zauna can din wanda ita
Saare bata so hakan ba amma mama Dubu tace ba zata koma gidan yayyun taba sai tare
da ita wanan zaman takuran Saare take cikinsa duk kwanakin.
Motar Habu sukai amfani dashi suka fice gidan a hanya Habu daya kula da rashin
sakin jikin dan uwan nasa yake fadin kace kana son ganina J ?
Haka kuma tun shigowana part din iya na kula da dan fadawan da kayi don kayi
rama sosai a yadda na barka wani abin ya farune kuma ?
Ya dan juyo daga barin kallon titin da yake yana mai dan tsurawa dan uwan nasa
idanu na dan lokaci kafin ya mayar a hanya yaci gaba da tukin da yakeyi.
Yayi wanan magananne don yadda yaga damuwa karara a fuskan dan uwan nasa don bai
saba ganinsa a hakaba ko da yaushe yana a yanayin nishadi da walwala .
A hankali J din ya kwantar da kansa jikin kujeran mota yana sauke ajiyan zuciya
tare da lumshe idanunsa yace.
Bari Habu ina cikin wani dan cakwakiyane a kwanakin nan duk da kaima nasan abin
zai shafe ka duk yadda ka kauce kuwa .
Subbahanallahi mene wanan abin J jikin nakane ya kara tashi kuma again ya
girgiza kai yana fadin ba jikin bane Habu rigima dai na fada a ciki lokaci guda.
Habu ya jinjina kanshi yace ina saurareb ka nasan dai duk rigiman da zaka jawo
ba wanda zaiyi kasa da martaban mu bane a idon mutane in sha Allahu.
In Allah ya yarda ba irin wanan da kake nufi bane habu rigiman soyayya na fada
lokaci guda ka kangani a haka na rasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login