Showing 75001 words to 78000 words out of 328222 words
Chapter 26 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
suka
dora muna wanan yasa a kullum baffa ke fadin mugaye muke masu bakin jini a haka
zamu kare a kiwo.
Ni nasan Allah yana sonmu shine ya kawo sanadin da bamu hadu da baffan mu ba
lokacin don da yaga yadda muka koma komai na iya faru a lokacin don baffa mugun
bafulatanine sosai shiyasa mutane ke masa lakani da maita.
Mun dawo lafiya baki alaikum da kamar ba zamu samu taro wajen yan gidan mu ba
kome suka gani oho masu saiga Asmau itace ta fara shigowa yi muna sannu da zuwa.
Daga baya Saiba tashigo a yatsene take muna sannu da dawowa ya hanya muka amsa
mata da lafiya kalau.
Acan gida mun shiryawa ummah sosai gaskiya yaya Habu yayi kokari ba kadan ba
tunda ba wani sana,a yar uwata takeyi ba.
Bayan dawowan mu da sati biyune ummah muta tare a gidan sabon mijinta dake
kaduna a unguwar Dosa mama dubu dasu inna sukai mata rakiya a cewansu sunyi mamaki
kwarai ashe mutumin ba karamin mutum bane .
Ita matarshi data rasu ta barshi da yara biyar tsohuwar lauyace mai zaman kanta
haka yayan nasa ma duk karatu sukeyi basu zama a gida.
Nikan sai najiwa ummah tsoron hakan don yan bin nan ba ai masu shigen kutse
haka duba ga yadda mu nan muke fama da facalan yar uwata a wajen kishi.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
2️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Mu dai bamuje kaduna ba saisu mama dubune sukai mana kara ita da kishiyanta inna da
yanzu itace kamar uwar dakimu gidan saboda tana nuna muna kulawa sosai kodon muna
tare da yartane oho ?
Koma meye damunzone gidan zata karbe Abbati tana angonta tana ba,a kasancewa
itace amarya acikinsu.
Wanan yasa muma muke zama a dakinta har dai shakuwa ya shiga tsakaninmu sosai da
ita bamu gane ko mama dubu tana son hakan da mukeyi ko bata so ?
Har dai yakai ya habu da kansa yakan dauki yaron yakaiwa inna shi don yawan
tambayansa da takeyi lokaci lokaci kota niko gari tazo gida tace tazo duba
maigidantane ita da iya.
A kullum kuma inna tana kan muna nasiha game da zama tare zakice ita din yar
uwamuce ta jini donshi shakuwa sosai ya shiga tsakanin mu da ita harma yayanta.
Don haka ta takawa mama wajen rakiyan ummah gidan sabon mijinta akaduna sai
gashi sunje sunga abinda basu zata ba a can din.
Yanzu tsakanin mu da ummah wayane mu duka kowa na kiranta yaji lafiyanta tana ce
muna lafiya kalau wanan ke kwantar muna da hankali.
Gaskiyane da wasu mata idan mazansu sun mutu sun barsu da yaya koda iyayyensu
suna raye suke fadin gatansu ya fadi gatansu ya tafi wanan zancen ba karya bane don
mun gani a kanmu a rayuwan mu.
A yadda hardo ke fada muna a yanzu duk shanayen mune wajen baffa shanayen da idan
da zamu mallakane zasu taimaka muna harmu taimakawa wanin mu a rayuwa.
Sai gashi badon ubangiji ya rufa muna asiri sanadin ya Habu ya auro yar uwata ba
da rayuwan mu a bautan baffa da iyalansa zai kare muna.
Sannu sannu yau nakai UG 3 da dadi da wuya haka karatun ke zuwa min a daidai
yayin da Anty Salima take shirin zuwa bautan kasa a lokacin kuma muka shiga wani
tashin hankali sabo dayafi na baya a gidan rikona inda yar uwata take aure.
Don ko an samu sakon ya Jafar wanan ciwon kan nasa a yanzu ya dawo inda abin har
yafi na farko ga fadan masu fada labari yazowa mama kamar hauka yayi a lokacin.
Innalillahi wa inna alaihin raji,un tashin hakan da muka kwana dashi muka tashi
dashi kr nan a gidan wanda yasa su kawu dasu yaya habu kwasan jiki zuwa garin da
yake.
Da alama ba dadi don duk lokacin da wani zai kira a gida aji halinda yake ciki
amsa dayane shine jikin dai da saukin musulunci za ace kawai amma ba sauki sai a
wajen Allah.
Rana daya naga damuwa karara ga iyalinsa ranan da ya Habu ya kira yana fadawa
mama cewa da wahalan da Jafar yake ciki mama gara a roka masa Allah kawai saukin
mutuwa.
Sai mama ta fashe da kuka kuka mai tsanani dole kowa a gidan kukane na tashin
hankali ba maiba wani hakkuri a gidan lokacin.
Duk muna falon iya gaba dayan mu in banda iyatu dake faman aiyukanta a wajen
gidan nan saiba ke fadin mama ko zamu shirya mujene ?
Ai yanzu ba zancen zuwa bane tunda gida zasu dawo dashi a gwada a gani abin na
asibiti yaki suncesu basu ga ciwon komai a jikinsa ba komai nasa yana lafiya don
haka bana asibiti bane abin iya take fadan hakan ga matar nasa.
Dawowa dashi din garama da suke can labari kawai mukaji bamu gani ba don
ganinsa a irin halin da yake ciki shine babban tashin hankali ga yan uwa da abokan
arzikinsu.
Kai innalillahi tashin hankali baida kyau don ciwon maimakon aga sauki sai kara
sabon sallo na ciwo da yakeyi yau ya taba nan gobe ya canza waje duk a jikin nasa.
Idan ya taso yana kugi duk inda mutum yake a gidan yana iya jinsa saboda zafin
ciwo a yadda naji har salinta jikinsa ya farayi yana saba irin na macizai.
Haka na shirya na bar gidan a cikin damuwa ganin mama yadda take kuka a gaban
kawu da iya tana fadin wanan wahalan yai yawa in tafiyane Jafar gara katafi ka huta
da wanan wahalan haka.
Duk da nake yarinya banji wanan adduan ta mama yai min dadi ba musulumi sauki
aka sanshi dashi da nema a wajen ubangiji ba zancen baki ba.
Masu fadan hakan bawa yasan abinda zai tar a gurin Allah ne shidai bawa ya nemi
sauki koma meye a wajen ubangiji shine mafita.
Har nakai school da wanan zancen nake a zuciyana a karo na farko da kusan
shekara biyu ke nan da zuwan mu gida ban taba gwada kiran layin Dage ba sai a ranan
naji ina son kiran Dage in sanar dashi halinda dan uwar mijin yayata yake ciki don
mutumin arzikine sosai ya J komai mutum zai iya masa don ya cetoshi daga wanan uku
ban da yake ciki na bautan ubangiji .
Gashi ashe sakacin su yasa basu koma can wajen wancan malamin daya taimaka masu
ba da farko tunda sukaga sauki suka fita batun koda kawu ya koma yace ba abinda zai
iyayi yanzu da ace tun wancan lokacin sun dawo sun karbi abinda yace din da sun
bashi goron sa da wata kila hakan bai faru ba a yanzu don an riga da ancin masa ko
ciwo yayi nisa wanan zancen tunda kawu ya dawo ya shedawa mama ta fita hankalinta
ga baki daya.
Cikin ikon Allah ina danna kiran layin ya shiga bai dauka ba har kiran ya katse a
kasa nake tafe hakan yasa na kara danna mashi kira a karo na biyu.
Sai gashi naji an daga ana faman fadin Alo alo alo murmushin karfin hali nayi
ina fadin who is speaking au kafirata ka kirana ashe ?
Naji Dage din na fadan hakan na sake sallama don na fahinci zai iya kashe wayan a
lokacin ya amsa sallama yana fadin wake magana ?
Nace budurwankace ta birni da kaba layin wanka koba dage bane yace kwarai kuwa
nine Dage nace to ni aljannace na kirakane muyi soyayya shiru yayi da har yasa na
daga wayan na duba koya kashene a lokacin.
Sai naji yana fadin Aradu Ramatuce oho yar nema ja,ira sai yau kikaga daman
kirata watau ?
Ina gwada layinka Dage baya shigane nayi mai karya yace kai kinshan me Ramatu
kudin da kika ban ardu kudin albarkane ai watau da wanda kika bani da wanda kika ba
inneje na hada suk na sawo muna dan karo mace dana miji Ramatu bakiga yadda suka
haifa muna diya ba wallahi kowa sai magana yakeyi nashe wa tsayahu wanan karon
zumuncine tsakanina da Ramatu.
Dariya na kwashe dashi na katseshi da tambayan mutanen gida har baffa yace kul
ardu kun kuru da baku samu baffan nan a gida ba lokashin .
Yayi cizon yatsa yashe ai zaku dawo shi za a kawowa shegan taka ita maria harda
haihuwa da kado ko ?
Gabana ya fadi nasan za a rina dama indai baffa ne da suke kira da magajin tauri
duk wani maison maganin tauri yazo yaga baffa ya warke.
Dage akwai wani bawan Allah dan uwan mijin maria da akaiwa makaru nan dai na
tsaya nayi mai dan bayanin abinda nasani game da ciwon yaya din.
Kai amma ke Ramatu a kwaiki da shirme wallahi ina wanan garin dana fara baki shi
zaki dinga mashi hayakinsa haka kuma.
Ki samo magarya kunne gomasha bakwai kada ki dada daga hakan a samu dutsen tama
kinshanshi ko nace a,a amma zan nema yace kwara ukku kacal a saka kasan tukuyan a
tafasa a tare saiya dahu sosai a sauke ya huce a diba hannu uku asha sai ayi wanka
da sauran .
In Allah ya yarda da zakuga sauki zan binciki baffa nayi mai karyan wani nason
taimako a waje na bashi dan kudi sai ya fada min wanin.
Bari na turo ma kudi a wayan ka ka sayar ka bashi ba sai ka taba naka ba Dage ayi
haka kuma Ramatu haba dai ka barshi kawai nayi niyane ai.
Wurin mai shago na tafi na bashi kudi ya turawa layinsa lokacin haka ake tura
sakon kudi sai gashi ya kirani yana fadin arradu Ramatu kinyi lafiya kun ketare
kaidin baffa shima baffa yana fada gaba dayan ku kunfi karfinsa ai.
Ya gwada sa,ansa akanku ya kasa cin maku tunma ke yace ke iblishiyace da zaki kai
wani lokaci a wajensa da kin kwance masa karfinsa.
Haka dai muka rabu dashi yana ta shirmensa na tare abin hawa zuwa gida saidai
kuma me a gidan dai badadi don wani tashin hankali na dawo na riska inda mama
tayiwa matan jafar kaca kaca a ranan .
Wai suna gudunshi suna kyamarshi don haka mama tace sai subar gidan ita zatayi
jinyar danta in da rabo in yaji sauki su dawo mashi amma yanzu kan sai sun bar mata
gidanta.
Tunda babu wace keda hankalin da zata kula dashi iyakarsu su dan shigo suyi
shaaaa su fice babu mai zama ta kula dashi a cikinsu.
Hakan ya farune da Asmau ta shigo dakin da yarta yana dan cikin hankalinsa ya
mikawa yar hannu da tazo wajensa sai uwar taki bari yar taje.
Shi jafar din ya dubi matar nasa yana fadin inku kuna kyamana a haka har da
yayana zaku hana su rabeni Asmau ?
Kawu da mama na zaune lokacin da hakan ya faru mama tace sun ma isa sunce suna
kyamar ka jafar ?
Yace aigata nan idan akwai wace ke yarda ko gadon nan ta taba haka nake fama idan
baku kusa kona kirasu basu zuwa su taimaka min komai zasuyi min a wullakace suke
min shi suna gudun su dauki cuta a jikina.
Wanan ya harzuka mama ta soma bala,i da tashin hankali har haka ya faru ita
saiba sai ta fake da tayi yaji ta kwasa ta nufi kaduna wai mama na yawan takura
mata .
Ita Asmau bata tafi ba shine mama tace har ita din ta tafi duk mai zaginta ya
zageta amma basu zama a gidan.
Nima na kula da hakan a lokacin saidai sanin halinsu yasa ban dauki hakan wani
abuba tunda haka yake zaune da abinsa.
Na rasa yadda zanyi in aiwatar da maganin nan ga yaya j ina zance dasu na samu
wanan abin ina part din mu mama ta kira waya da inzo mu kula mata da Jafar zasu
tafi wani waje ita da kawu.
Don a lokacin ita Saare tana school ita kuma Salima ta wuce bautan kasa saini da
Nafisa ne a gidan muka shiga part din nasa tsit don matan gidan da basa nan kwana
biyu.
An dawo da Asmau mama tace taje ta huta kawai haka ba yana nufin zata raba mata
aure da mijinta bane bata dai son ganin su gidan a yanzune.
Lalai ankai hali dubu makura mace mai hakkuri ta iya yanke wanan hukunci don haka
kawu yace suje din kamar yadda tace har ta huce.
Anty Nafisa tashi mu shiga dakin yaya ayi komai a gabanki don Allah akwai taimakon
da nake son yi ban samu daman hakan ba a gidan nan .
Kallona tayi a tsorace tana fadin me zakiyi Ramaah nace zo muje anty Allah ya
gani taimako zamuyi da zuciya daya.
Dakin muka shiga da sallama ya kwance gwanin ban tausayi muka gaidashi ya amsa
muna da kai dakin ya danyi shiru gabana sai faduwa yake ina kuma kare mai kallo
nace yaya don Allah ka fahinceni.
Akwai wani magani da aka bamu a gida nake son in jaraba mu gani amma ina tsoron
hakan bansan me zan fada ba yasa yanzu na sameka ga anty Nafisa don Allah yaya ka
daure ka dinga sha koda ban kusa anty Nafisa zata baka zamu fadawa iya kuma.
Maimakon ya amsa min sai hawayene ke zuba a idonshi na fito da kullin maganin
muka zuba mai a kunnu bai ki ba yasha muka kara kwantar dashi.
Mun jima a wajen zaune sai sha biyu su mama suka dawo gidan kawu ya sauketa ta
samemu a dakin wajensa zaune bamuyi barci ba.
Mu muka taimaka mata tayi mashi komai a ranan daman dana samu kuma weekend ne
don haka yasha maganin kusan na kwana uku ina bashi a boye.
Mu gyara dakin mama tayi mai wanka kafin ta fito na kwashe zanin gadon na
shimfida wani na feshe dakin da kamshi.
Zakiga ya sauke ajiyan zuciya idan ya zauna na hada mai kunu ina bashi mama
tashigo tana saka min albarka tare da fatan alheri a gareni.
Take fadin Rahama indai ba karya nakeyi ba kamar jikin jafar yana saba (salinta
) alaman hakan kuma meye ?
Mama duk ta rude daka ganta bata cikin hankalinta nace mama kila hakan wani
sallon ciwon ya canza kuma ?
Naji sauki sosai ya bamu amsa da fadan hakan yana gyara kwanciyarsa ya habu ya
shigo dakin nayi saurin gaidashi yana tambaya ina Nafisa mama ke fadin yanzu take
nan tace iya tace tayi mata shayi .
Ya karasa bakin gadon yana fadib J ya karfin jikin naka ya bude ido ya dubi dan
uwan yayi dan murmushi kadan hakan yasa ya Habu din yakai zaune.
Mama bari naje na gaidasu iya na fada ina fita tace kima huta tunda ga Habu ai
kafin kawun ku yazo ya kama min nima na dan jena huta.
Bayan fitana yake fadin yarinyar nan habu yace wa Ramaah ya gyada kai alaman
eeh saiya lumshe ido yace me tayi yaya yace kirki don bai dogon magana.
Sai Habu din ya danyi murmushi mama daga gefe tace meyace wai Rahama yake fadin
tana da kirki aini har tausayi ta koma bani yarinyar arzikice sosai wallahi.
Barci nayi sosai don kwana mukeyi gadinsa a gidan daya motsa dayan mu dake
falke zai tambayeshi me yake so ?
Hakan yasa har zuwa school na dan dauke don maganin da muke gwadawa wanda dagani
sai anty Nafisa dashi muka sani haka kuma yana sha sosai idan mun bashi din kuma
yana shan wanda su mama keyi mashi.
Hadari aka hada sosai a garin hakan yasa mama cikin damuwa ga yaya Habu ya tafi
kaduna tare da kawu gashi ance kada a dage rana ga karbo maganin fita nayi kamar
zan shiga cikin gida na fice bakin get ban samu abin hawa ba haka nayi ta sauri
saida na kusa isa na samu mai keke ya karasa dani gidan mutumin.
Na karbo haka na biyo ruwa da iska na iso tsamo tsamo da maganin gidan nakaiwa
mama mamaki tayi sosai ta shiga yi min fada yadda na iya fita a cikin hadarin nan.
Nace mama gani nayi lokaci zai wuce bai sha ba kuma ga ruwan nan ba a san lokacin
da zai tsagaita ba.
Maza kije ki kwabe tufafin nan kada sanyi ya kara kamaki mura ya sauka maki kin
daiyi kasada wallahi bin hanya haka a cikin ruwan nan .
Dakin ta shiga tana fada yake tambayan meye mama din tace yar nan Rahama ashe ta
fita a cikin ruwan nan ta tafi karbo maganin nan dana damu akansa.
Baiyi magana ba sai zuwa can yace mama yaran nan suna matukar kokari sosai
wallahi a raye suke kwana gidan nan.
Aini ban iya cewa komai a yanzu saboda ko yaran nan su saratu ba zasuyi min
wanan dawainiya haka ba wallahi.
Bayan kamar kwana biyu jikin nasa yayi sauki sosai a lokacin ya dan harda
tafiya ba tare da an rikeshi haka kuma kumburin kafanshi ya fara sucewa kafan yana
fadawa don yayi kamar turmi a lokacin ba dadin gani sai walkiya da yakeyi kamar zai
fashe.
A takaice bawan Allah nan yasha wuya fiye da tsamani sai zantuka akeyi marasa
dadi game da ciwon nashi kowa da abinda yake fada.
Shi kanshi mijin yar uwata duk ya fita cikin hayacinsa saboda jinyar dan uwasa
din hankalisa duk a tashe yake haka kuma shike gudanar da komai na kasuwancin