Showing 195001 words to 198000 words out of 328222 words

Chapter 66 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

ina mata
addua Allah ya kwatota daga kaidin da take ciki a yanzu duk wani abinda za a fada a
yanzu banzane don bai tasiri azuciyarta don tana ganin ita daidai take.
Amma kaga Dauda da matarsa hansatu ka barsu nan inda ka gansu su dade sunawa
uwarku bandan kasa.
Yanzune abin yake yawo akanta haka kuma yar nan matar Jafaru itama da akwai wani
shu,umancin datayiwa Dubu a zatona wanan abin shine duk ya rikita kanta a yanzu
din.
Kaga kuwa wanan abune dake son addu,a don ba yarda da hakan zatayi ba koda an
fito mata fili an lurar da ita zata iya mussan hakan mutum abin tsorone.
Ni kaina a lokacin ai hafsatu bata barni ba nasan komai ido na zubawa gudunsu
tunda yadda suka so dai bai samu ba.
Sunyi hakane don ku da yan uwanka ya kasance duk wani nema naku yana a hannusu
sai yadda sukayi daku da uwarku din sai gashi ku ba a kama kuba ita abin yafi shiga
jikinta.
Nina sani iya don ko kowa bai yarda ba nina yarda kawu zai iya hakan fiyema da
hakan sai yayi don irin yadda yake muna wani lokaci sai mutum yakai zuciyarsa nisa
don azauna lafiya.
Yanzu dai zan bargidan ba zan zauna ina gudun zuciyarsu ba ninawa yana baci a
kullum don haka zan kwashe kawai na bargidan ina ganin shine mafita a wajen mu baki
daya.
Ita kuma saratu kai salima na fadawa yaya su fito da maza a daura masu aure kowa
ta kama gabanta zaman ya isa hakana musanman ma saratu da duk wani fitina itace ke
kawoshi a gidan nan kuma mama bata yarda da hakan .
Yanzu da safen nan saida muka kwasa da ita wai mun kadarwa saratu bamu kaunarta
abu kadan ace saratune har tana batun yi min kuka fa iya wai akan saratu.
Sai naji iyan tace kafadawa uwar taku zancen tashin naka yace ehh to cikin fada
na fadi amma ina ganin bata dauka da gaske nakeyi ba.
Don kyata da bala,i irin nata wai a falona Nusaiba zataje fada duk sun fasa min
kayan falo amma duk mama bataga laifin hakan ba sai fada rakeyi wai Rahama tazo har
gida tayi masu rashin mutunci.
Me yaranan suka tarewa mama haka don Allah iya ta nisa tana fadin habu kayi
hakkuri na fada maka inda matsalan yake don haka addua zamu bita dashi a yanzu.
Ya juyo wurina yana fadin ke kuma baki da hankaline da kika biyewa haukansu
Rahama idan suka illataki fa badon Allah ya doraki akansu ba yadda ake fadi sun
tarar maki ai saisu nakasaki a banza tunda ba wajen hukuma za a kaisu ba a daukar
maki fansa.
Don haka daga yau ki kama mutuncin ki dama ita abinda take nema ke nan abinda za
ayi ta bata maki record a idon mutane ba haka kikaga yar uwarki tana zama dasu ba.
Bayan haka ke kinsan yadda akai auren ku da J dole haka ya faru tsakanin ki dasu
don ma ita Asmau a yanzu ta daina saka kanta cikin iskancin Nusaiba don na kula ita
a yanzu bata irin abubuwan nan don haka kada nakara jin hakan daga gareki.
Duk abinda zatayi ai yanzu tunda ta gwada ba sa,a a wajenta aiba zata kara bari
su hada jiki ba kuma da dai ace ta samu sa,antace bata da sauran numfashi kuma a
gidan nan yanzu.
Sai Allah ya kawo saukin abin kika rijayesu don haka yanzu iskancin zai rage
akanki saidai ta fito wani hanyar kuma nan gaba.
Ai tasha fadancewa saita wullakantani dake a gaban kowa amma ban taba tsayawa na
kulata ba ina jiran ranan da zata kawo iskancin ta akaina ta gane kurenta bata san
naki dan maline ba don nafiki hauka kyalesu kawai nakeyi.
Maria data karbi zancen iya take fadin hakan sai iyan tace gara dai kada akai
ga hakan ai yanzu na fada maku zasu shiga hankalinsu sosai tunda basu sha da dadi
ba.
Na daiyi fama da tsamin jiki tunda jikin a yanzu ba wahala irin da can baya
inda gadan gadan ya Habu ya shiga gyaran gidanshi da zai koma da iyalinshi.
Unguwa dayane amma akwai dan nisa da inda nake saida yayi wani dawowan ya samu
mama da zancen tarewansu gidan akan ga gobe.
Me kake fada Habu zaka kwashe ka koma gidanka watau ban isa da kaiba yanzu saida
yaran nan sukai nasaran raba min kanku a gidan nan ?
Wasu yara kuma mama ta kalloshi a yatsune tana fadin wasu yara banda shu,uman
yaran nan da kuka dauko min a gida ?
Dama gurinsu kenan su raba min kan yayana gashi ko sunyi nasara na farko a
gareni shigowan yaran nan cikin ahalina bai haifar min da komai ba sai tarin bakin
ciki da takaici .
Kowa yasan asalin nono dama daga ruga yake ashe gaskiya ake fada akan fulani ba
a fadi karya ba duk wanda ya auri yar filo sai yabar kowa nasa gashi kuwa nagani a
kaina.
Saita fashe mashi da kuka ya mike ya fice daga dakin bata kara ganinsa ba saida
yammane saratu ke fada mata da gaskiya yakeyi fa tafiya zasuyi don ashe har sun
kwashe duk wani abin amfani nasu sunkai wancan gidan.
Ranta ya baci ta mike tsaye da sauri saratun ta tareta tana fadin mama kada ki
fita don yaya ya ganeni zaice nice na fada maki.
Yace mana idan yace fa shi har ya isa ince ban yarda da hakan ba yace min don me
koshi jafar daya dauki wanan yarinyar ya kaita can tunda abin ya zamo iskanci ai
nan zai dawo da ita dole yanzu.
Tunda tana ganin hakan da yai mata kamar tafi kowane a yanzu har take iya ganin
zata tako har cikin gidan nan taciwa mutane fuska jiransa nakeyi ya dawo garin nan
ai,,,
Sallaman ya Habu dake shigowa dauke da dansa a hannunsa sai maria dake bayanshi
sabe da jakarta na hannu shiya saka suka juya suna kallonsu.
Zama yayi yana gaida ita ta amsa a dakile kafin yace yaune zamu tafi wancan
gidan mama na fada maki zamu koma gidana to yaune komawar tamu insha Allahu.
Kai habu saboda ka auro yar gwal mai takobin raba zumunci zaka ture dokana kace
zaka bar gida don ra,ayinta tunda su da manufa suka shigo cikin mu dama ?
Meye laifin Maria anan mama tunda ba itace ta gina min gida ba ninayi ra,ayin
hakan don haka a barni da shawarana don haka nake son tsarina.
To ba zaku ko ina ba kaji na fada maka wace zata iya zama a nan ta zauna wace
bata iyawa kuma hanya a bude yake ta fice ta kama gabanta.
Ashe gaskiya da ake fadin dangin filo dangin bala,i yanzu don matarka har zaka
iya kyatare dokana don kada ranka ya baci.
Mama ba ra,ayinki nazo nema ba a yanzu don na riga dana gama shirina ba zan bar
iyalina gidan nan kina kallo ana ci mata mutunci ba tare da daukan mataki ba.
Yanzu zanyi abinda ya dace a zauna lafiya kuma zakice ban isa ba a zatona hakan
abin farin cikine a wajenki ai mama tunda har Allah ubangiji ya hore muna muhalin
kanmu haka da taimakon dan uwanmu dake son cigaban mu a rayuwa.
Ashe hakan ke a wajenki ba abin godiya bane yau don danki ya samu farin ciki
mama kinfi bukatan ganin rayuwan mu ko yaushe a tauye ?
Habu ni kake musayan harshe dani yau haka kan wani tsari da aka doraka sama yace
ba wanda ya dorani na fada maki ra,ayin kainane hakan.
Banda ra,ayin zama a cikin yawa haka shima jafar din da aka tauye ya zauna ai
banga wani abin karuwan daya samu ba ga haka.
Abinda yakamata ace kin dage akansa mama kin kasa dage muna akan masifan dake
bibiyan rayuwan mu ki sa kawu gaba zuwa garin matan nan dayaje ya karbo maki
haihuwa kin kasa haka mama kin tsaya ana zugaki a kan mu don mu lalace .
Ba laifi idan yau kin min baki kan na bar gidan nan na koma muhalin kaina na
zauna don in samu zaman lafiya a rayuwata.
Kullum kana wajen aiki hankalinka ba a kwance ba kana tsoron abinda zaije ya dawo
na samu Allah ya hore muna kuma zakice baki yarda ba sai dai kiyi hakkuri donnni na
tashi ke nan bafasawa zanyi ba.
Haka kuma dolene muje wajen nan a wanan karon abada duk wani abinda akai
alkawari bayarwa don dan uwanmu dake cikin matsalan rayuwa.
Zuwa lokacin kuka sosai mama takeyi akan ya daina amma ya tsaya sai daya gama
fadin abinda ke bakinsa ya kallo maria yana fadin tashi muje.
Maria kinyi nasaran rabani da dana yau har yakai habu bai saurarena sai ke
hakan bai maki ba kin shiga kin fita kin cusawa Jafar ra,ayi akan yar uwarki to ki
saurari shirina yadda kika rabani da dana haka kema zaki rabu dashi indai harni na
haifeshi.
Tsoro ya kama maria din dajin furcin mama ga kowa dake gidan tsaye an fito haka
ya cusata mota ya shiga yaja motar suka bar gidan .
Nan suka shiga bawa mama hakkuri mai sunan zugi suna fadin aidama haka aka
tsara tunda anan idon kowa na kansu ba a samu yadda akeson a mulkesu ba yanzu ko ai
shike nan sai dai mama din tayi hakkuri.
Jin irin abinda saiba ke fadi har tana cewa su dai da aka mayar shakatafi ai an
tauyesu an hanasu walawa din ga yan kauye don samun waje sunzo sun karya dokan da
aka kafa kuma ba ai komai ba.
Haba keko Saiba wanan maganan bai dace ba mana samunefa koshi ya J ai
ra,ayinsane zama a nan din don kowa yasan yana da halin hakan baidai da niyar
dagawa nan din ne kawai.
Ai dole kice haka tunda bake bace akaiwa hakan kuma ai aure zakuyi indai a
tauye mutum ne kowa ai zaije gidan mijin ya gani takecewa salima.
Shiko habu suna barin gidan ya hau maria da fada don me zata tsaya taki shiga
mota karshe ya gama fadanshi ya kira dan uwansa yana fada mashi sun bar gidan zasu
koma sabon gidansu lokacin.
Murmushi J din yayi yana fadin Habu baka jin magana meyasa ka zabi fushin mama a
kanka tunda tace bata yarda ba ai saika saurara har lokacin da zata amince din da
hakan gare mu.
J nifa ban iya daukan wanan abunda kake dauka a rayuwanka idan ba badin gidan
nan nayi ba za a samu rigiman da sai Allah zai iya maganinsa don raina ya gama baci
da yadda mama takewa iyalina kasani.
Ko yanzu ai laifin maria din ta gani which means kaga da ita dai take adawa
badani danta dana ce zan bar gidan ba irin wanan ne zakuce nayi hakkuri in bar yar
mutane a gidan nan ?
Maria tana da zurfin cikin tsiya da ace Rahamace zata iya zama dasu din hakana
amma maria zurfin cikinta yayi yawa wallahi.
Duk abin nan maria bata san gidan ba tunda bai taba kaita tagani ba saida suka
shiga karamin get din gidan da hasken wutane ko ina a gidan tarara ta bude ido tana
kallon mamaki.
A ranta take tambayan kanta yaushe har yayi wanan gina haka bata sani ba bata da
labari a bakinsa ?
Bin ko ina take da kallon yadda gidan ya tsaru dan maidaidaici dashi komai na
more rayuwan zamani ansa harda filin tsakar gida da wajen aje mota ba abinda ya
kara burgeta irin hasken da gidan yake dashi wadattace.
Saida suka shiga ciki ta kara tsunkewa da lamarin yadda komai ansaka ashe ya
jima yana shirinsa ba tare da kowa ya sani ba ke nan .
Bayan sun natsune tayo min text tana fada min sun tashi a family house gasu
sabon gidansu yanzu haka zaune.
Ina falo zaune da iya ina cin abinci sakonta ya shigo min na bude lokaci guda
nake hamdalla suka kalloni nace iya wai yaya Habu ya tare sabon gidansa yau din
nan.
Habu fa kikace ta tambaya cikin mamaki nace yanzu maria ta aiko min da sako hakan
yasa na daga waya na kirata .
A cikin yare nake mata murna tare da tambayan ya haka ya faru tace kedai bari
kawai Allah ya rufa min asiri yau Ramaah .
Zagi da mugun fata nasha shi nidake a wajen mama na katseta ina fadin ga iya na
mikawa iya wayan ta dauka tana fadin maria kun tashifa naji ance ?
Tace wallahi iya ina zaune dazun da yamma yace min na shirya kayan mu ya kwasa
saida ya dawo yake fada min nafito mu tafi.
Akwai magana ashe Habu yakai dakare ya shamaci kowa dayin haka idan ya fada
yasan ba barinsa zasuyi ba aiya kyauta daya fito mata ta hakan yanzu ai kowa zai
gane gaskiyan abin ku dai kara hakkuri ku zauna lafiya da mazajen ku.
Shiya karbi wayan yana fadin tsohuwa me kike fada ina nan shigowa da safe ai bamu
da nisa daku da safe zanshigo in baki labarin komai.
Ja,iri bakajin taro duk tangwanka da mukayi saida ka nuna halinka na gagare ka
gudu kabar uwarka can ?
Dariya yayi yace dolene iya matukar ana son zaman lafiya tunda Allah bai hana
muna abinda zamu kula da rayuwan mu ba akan me za mu tauye kanmu haka.
Sundan jima suna wayan wanan yasa ban samu wani zance da maria din ba don dare
yayi lokacin da tunanen abinda ta fada na kwana a raina.
Gaskiyane idan akace mutum yayi hakkuri wani lokacin hakkuri ba cutarwa bane ga
bawa yinsane keda wahala.
Da ace ban biyewa Saiba nabi zugin ziciyana ba da duk hakan bai faru ata sanadina
ba tunda ashe dama ya habu yana da niyar tashi gidan lokacin.
Amma yanzu nasan danice mama dubu zatayi kuka nice sanadin komai da har haka ya
faru danta yabar gidan a sanadiyar abinda ya faru a part dinshi damu.
Sam ba za a gano gaskiya ba nice dai laifin zai koma kaina zata kara tsanata
nida yar uwata fiya da wanda take muna a baya.
Don haka zan koyi hakkurin nan da kowa ke fasin muyi hakkurin saidai nasan hakan
yana da wuya ace na iya gaskiya akan cin fuskan da saiba ke kokarin yi min a
kullum.
Washegari duk da ina son shiga school amma na daure banyi sammako ba don zuwa
gidansu Maria din da mukeson yi.
Shi yaya habu din yazo misalin karfe tara ya daukemu nida iya don habiba ta wuce
ita tunda safe iya kuma a can zan barta gidan awajensu.
Gida yakai gida Allah yasa da nisan kwana akaiga wanda yafi hakan gaba iya ke
fadi na amsa da amin muka shiga ko ina yana nuna muna nan nabar iya na fito ya
ibrahim yazo ya daukeni zuwa school.
Muna hanya yake fada min yayanshi yace ya kamata na koyi mota idan ya dawo zai
koya min donshi zai fara aiki dasu zaman garin a yanzu zaiyi wuya a gareshi.
Dan murmushi nayi ina fasin kyaleshi ya ibrahim kullum haka yake fada amma ya
kasa tsayawa ya koya min din ya zata ko ba zan iya bane.
Na cirewa kaina damuwan dana so sakawa zuciyana kan mama tunda kome nayi dai ba
haske zanyi a wajenta ba tunda ta nuna bata kaunana da danta.
Ni kuma gani a yanzu son danta ya kamani ta yadda nake jinshi a wani bangaren na
zuciyana dadin abindai ba a waje daya muke rayuwa ba balle in shiga takuranta.
Koma waje dayane tunda ba zamanta nakeyi ba zan kauda kaina ga duk wani cin
fuskan da suke min a yanzu din kan mijina.
Miji daine Allah ya nufi aure a tsakanin mu dashi ba soyayya mukayi ba amma
fahinta da kulawa yasa muna kaunar junan mu.
Don haka rabamu a yanzu ganganci a wajen mama don nasan hakan zai haifar da
abinda yafi na yaya habu a tsakaninsu.
Sai dare iya ta dawo koshi da kwantancen da nayiwa Habiba ne taje gidan ta dawo
da iyan don yaya habu din ya fita tun safe ya shiga kano.
Nazata mama zatazo gidan a ranan sai gashi har dare banganta ba kuma bata kira
waya ba don haka nima na watsar da zancen komai a raina.
Anyi haka da kamar sati kwatsam ina hanyar school naga yaya Habu ya kira layina
na dauka da mamakin dalilin kiran nawa lokacin na dauki wayan.
Muryanshi ba dadi yake fadin Rahama kina school ne na amsa da ehh yaya amma gani
hanya dawowa na jira yaya ibrahim ban gansa ba na biyo yar kura.
To kizo nan teaching hospital ki samemu idan kin shigo muna dakin maza ki kirani
zan fito abinda ya fada ke nan ya kashe wayan.
Innalillahi na dinga maimaitawa a bakina tare da tunane barkatai a lokaci guda
ina fadi a gigice asibiti kuma wake can asibitin kuma yanzu ?
Gabana ya fadi don tunowa da yaya J da nayi rabon da muyi waya dashi kwana ukku
ke nan kuma kona kira wayansa baya shiga na dauka baya wajen service ne.
Mai keke nayiwa magana ya wuce dani cikin asibitin tunda dama daga school nake
muka doshi hanyar shiga asibitin gabana sai faduwa yake min.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join
my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/22, 10:45 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

6️⃣4️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login