Showing 60001 words to 63000 words out of 328222 words

Chapter 21 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

haka balle ga yaro karami.
Shine yana jin banda waya yaga rashin dacewan hakan gara ina da waya a hannuna
aji halinda nake ciki a nan yayi shawaran saya min waya din sai ya ga wa yanan
kayan kuma ya hado min dasu.
Yarinyar ba laifi gaskiya tana da dadin zama ga tsabta ga ladabi ga hsanin ya
kamata bata da hayaniya ko daukan magana duk abinda matansa keyi bai taba jin yaran
sun tsaya sun mayar masu da martani ba koda agabansu akai abin.
Hakan yasa yake ganin girma da kimar sarakuwar tashi da kanwata duban irin simple
rayuwan yaran yakan burgeshi wallahi tundai tsabtansu da wanan yakewa matasa gori
wanda sukuma suke kara jin kiyayyan yaran a zuciyarsu.
Haka ya kama hanya bayan ya saukeni tare damamakin wani irin halakace tsakanina
da mutanen nan haka ?
Don da ganin gidan ba gidan karamin mutum bane dole akwai wata halaka mai girma
a cikinsa koma meye ya godewa Allah da bai ajeni a wullakace ba.
Gara da Allah ya bashi dubara danyi min sayayyan nan da yayi don a ganni a cikin
mutuncina da kima ba zaiji dadi su ganni cikin irin suturan da habu ya barni ina
sakawa duk dai da baisan daliliba amma dai babu wadatuwa gareni gaskiya.
Yasan haka halin dan uwanshi yake tun suna kananunsu habu bai damu da wani
rigimar duniya ba kan shima bai fitar da kanshi kunya balle wani.
Wayanshi dake karane ya katseshi ya dauko yana duba dan uwan nasa da yake
tunanene ya kirashi yana mashi ya hanya ?
Alhamdullahi Habu na sauketa tun dazu na saya mata waya don ta rike don nace ta
kira idan da matsala tace bata da waya a hannunta.
Why habu zaka kasa saiwa yarinyar nan dan waya koda karamace da zata rika meyasa
kake hakane wai ?
Yaran nan kaika daukosu a karkashinka suke a gidan nan da anga kana darajasu da
ba macen da zata nemi tozarta makasu a cikinsu.
Bai kamata irin hakan na faruwa ba marayune fa Habu kasan yawan ladan da zaka
samu a wanan taimakon da kayi gaskiya banji dadin hakan ba wallahi na dai saya mata
da wasu kaya tunda banyi tsamanin ta samu dinkin wa yancan ba da zata saka.
Shiru Habu yayi yana saurarenshi na dan lokaci saida ya kare magana yake fadin
Nusaiba ta kira wayan kane ?
Nusaiba wani abubya farune kuma dazun dai da zan fito tazo tana min rubbish
akaina ban tsaya kulata ba don bata da hankali nake gani.
Bata dashi kan akan ka dauki Rahama yau tashigo wajen su mama tayi tijara iya son
ranta katse dan uwan yayi da fadin What ?
For what reason zata samu mama to Salima dai bata kyaleta ba itama bata kyale
salima din ba sunyi ba dadi a gaban mama wanan yasa na kasa hakkuri na kiraka .
Irin wanan abin yana taba mutuncin mahaifiyar mu sosai don bata magana su kuma
sunga ko sunyi ba mataki kake dauka ba yasa suke cigaba da hakan tundai ita Nusaiba
din.
Saiba saiba takai karshena wallahi amma bari laifin mama din ne dake hanani
daukan mataki akansu kome sukayi mama tace inyi hakkuri haka mata suke basu da
tunane komai girman su zankiraka habu ina zuwa don Allah ya fada a gagauce ya kashe
wayan.
Me wanan yarinyar take nufi danine wai yana neman layinta data kirashi danzun
yana zancen zuci a fili ta dauka ni dan iskane irinta kome yaji ta dauki wayan
cikin basarwa tana fadin hello J.
Ke Nusaiba yanzun nan ki tafi gidan ku kada ki bari in dawo zaria yau in sameki
idan ba haka ba wallahi saina katse duk igiyan dake tsakanina dake a yau din nan
ya kashe wayansa yana huci bai jira cewanta ba.
ABUJA
Ina saka wayan a caji aka shigo na juyo yar aikin antyce wata yar budurwa mai
guntun buje da ganin shigarta nagane ita din yar aikice agidan .
Abinda basuyi muna ba ke nan a lokacin sam ba a gane cewa mu yan aikinsune kuma
ta gargadi mama dake katobaran fadawa mutane hakan.
Ranan da hjy taji tayi fada da mama sosai take fadin mu bamu daukeku a yan aiki
ba a yan uwa muka daukeku kowa kuma yasan abinda nake fada ke nan don kun zama yan
uwa a wajen mu yanzu.
Tun wanab lokacin ummah bata sake wanan katobaran ba tana kafa kafa da abinda ke
batawa hjy rai akai zama lafiya sosai a tsakanin mu.
Wanan yasa na nasa a raina cewa yarinyar nan ta huta indai har anty Salma ta biyu
halin hjy mama da yan aikinta zataji dadi sosai a wajensu.
A falo na samu anty salma din tana waya alama tayi min da hannu inzo na karasa
ta nuno min fuskan wayanta dake hannunta.
Fuskan hjy mama a cikin massalaci zaune ga larabawa suna gittaiya mama kinga
Ramaah kin yadda ta girma ta zama big girl yanzu.
Mama ina wuni Ramaah ta lafiya lau ya kuke yaya yanda da jikinta yaya yan uwanku
na amsa da Alhamdullahi.
Ya ibada mama tace Alhamdullahi gamu a cikinta aini mamakin ganin yadda Ramaah
ta girma nakeyi mama din ta katseta da fadin anyi sallah ki bari zan kira ku
anjima.
Ta kashe wayan tana fadin yau mama zataji dama ace tana garin nan ta ganki
murmushi nayi ina dukar da kaina kasa.
Take tambayana ya jikin Yanda da sauki ko babu dai wani matsala dai ko na amsa
da taji sauki sosai lafiya na barta jiya muna asibiti tare a can na wuni dasu.
Ta koma tambayana karatu nake fada mata nagama secondry school yanzu gaba zaki
ko sai nayi murmushi ban bata amsa ba don banda abinda zan fada mata lokacin.
Duk da nasan ana zancen zuwana gaba din amma ita ban fada mata komai ba tunda
banda tabbaci akan hakan yanzu saidai abinda shawara ya yanke a kai.
Tunda su Salima na karatu ni kuma yanzu rikona ya dawo hannun yaya Habu nasan
yana da wuya ban je higher institution da nake son zuwa ba.
Zamana gidan anty sallama a ranan ya tuna min abubuwa da dama a rayuwana wanda
yasa jikina yayi sanyi don tuno da mahaifinmu da zaman Abuja da nayi.
Zaria duk yadda Saiba taso ta kira mijin nata yaki daukan waya don yayi blocking
dinta a lokacin karshema kashe wayan nasa yayi don mama ta fara kiranshi tana son
taka mashi burki.
Wanan karon yasha alwashin sai ya koyawa Saiba hankali sai ta gane ita ba kowa
bace in ma rabuwace ai a rabu din ya gaji da wanan irin halin nata na rashin kwabo.
Bata kara sanin da gaske bane saida ya Habu ya dawo yana fadin yace ta fita
gidan kafin ya dawo har in ya dawo ya sameta gidan wallahi kowa yayi mata tsaye yau
sai ya raba igiyar auresu ga baki daya.
Iya najin hakan tace maza ki tatara ki nufi gidan ku kada kaddara ya zaunar dake
yazo ya aikata abinda ya fada zaman ki gidan nan ya kare maki.
Babu yadda ta iya don mama tayi shiru batace komai ba a wanan zancen hakan ya
kara tunzurata ta shirya kayanta a cikin yar karamar jakka ta nufi kaduna.
Ana magariba tana sauka gidansu cikin tashin hankali ba wanda yace mata komai
don ta samu ana hada hadan shan ruwa a lokacin.
Baya bata da kadan don ko tana fita ba,a jima ba ya iso gidan bai tsaya ba ya
sauke abinda ya sayo a hanya ya nufi cikin gari don samun sallah a unguwarsu inda
suke shan ruwa.
Maigadi ya jido kayan zuwa part dinsa dana iyayyenshi iya take tambayan maigadi
ina Jafaru ?
Yace ya fita yanzun nan kayan kawai ya sauke ya juya ya fice daga gidan ba zai
shigo ba ai tunda yasan abinda ya aikata uwar ta fada.
Keko meya aikata kuma ba zancen ki bane asalima nasan saboda ke yaron nan yake
son daukan mataki tunda kinji wayan da sukayi da dan uwasa don haka ki sa masu ido
kawai yayi iko da iyalinshi.
Yarinyar nan tana bukatan gyara a gaban mu tazo tana zagin yarinyar nan koke
maisa ya dauki matakine kan abin nan data aikata ai.
Shawaran Iyan mama tabi don koda Jafar din ya dawo batayi mashi zancen ba shiru
tayi har ya gama hiranshi da iya ya nufi part dinshi.
Takaicine ya kamashi yadda ya samu fslon nasu a ya mutse ga kujerun falon da
basu dauki wani lokaci ba a gidan har sun fara ya mutsewa da auren Yanda ya sayo
masu shi da akai gyaran gidan.
Abin takaici ranan daya shiga falon Habu yaga nasu zakice ranan aka kawo masushi
part din don komai ba suyi ba sai walkiya da sukeyi.
Takaici ya kara kamashi haka ya taka zuwa dakinsa ga wani bashi dake tashi ba
alaman ma tayi wani soye soye don shan ruwa a ranan.
Yana gab da shiga dakinsane yaji muryanta a bayanshi tana fadin ai kadowone ashe
na dauka ba yau zaka dawo ba ai naga Saiba ta tafi kaduna da yamman nan ?
Bai tsaya bata amsa ba ya murda kofan dakin ya shiga ya rufo sai lokacin ya
shaki kamshin dakin don ko yaushe shike tsayawa ya gyara abinsa yadda yake son
ganinsa.
Kayan jikinsa ya rage yashiga wanka yaso ya kwana a Abuja saidai saboda ya kure
saiba ya dawo zaria a ranan tayi arziki daya dawo ya samu tabar gidan don daya
shayar da ita mamakinsa a ranan.
Why zata zargesa da irin wanan mumunan abin ta rasa wanda zataiwa sheri irin
wanan saishi kuma ?
Dashi dan iskane yadda take zato akanta zai fara nuna halinsa ai amma sai ya
juya abin zuwa aure a tsakaninsu tabbas itace da farko ta fara nuna mashi so da
kauna .
Don tun bai gane ba har yazo ya fahinci me take nufi da farki yaso ya guje mata
amma ta hillanceshi da dadadan kalmanta har yaji ya kamu da kaunanta itama saboda
yadda take matukar bashi kulawa zakice ko itace matar nasa duk a lokacin ta fake ga
besty dib Asmau take masa wanan.
Tsoki yaja lokacin daya murda famfon ruwa ya kare hakan ya tabbatar mashi da ta
kasa fita ta kunna ruwa ke nan a ranan .
Dole yayi amfani da ruwan roban da suke tarawa acikin kyankyami saboda ruwan ya
dade a rufi bayan ya fitone ya shirya kansa bai fito daga dakin ba nan ya zauna
bakin gadonsa yana waya da wani mutumi da zasu hadu dashi a Onicha.
Tashi yayi ya sakawa kofan key yana mai jin haushin matan nasa aransa a haka
barci ya daukeshi don koda Asmau tazo tana murda kofan duk yayi barci a lokacin.
Sai tsakar dare da yunwa ya tayar dashi irinta wanda ya wuni da azumi a cikinsa
hakan yasa dole ya fito ya duba falo ko zai samu abincinsa aje sai dafa duka da
ganye.
Kitchen dinsu daya dade bai shiga ba ya nufa a can ma ya kwammace da bai shigo
kitchen din ba a lokacin don kayan takaicin daya sama a kitchen din.
Drinks ya dauko a fridge sai bread dashi yai sahur ya kwanta cike da takaicin
duniya akan matan nasa.
Idan kaga Asmau a zahiri zaka dauka mace ce mai tsabtan bala,i don iron yadda
jikinta yake ashe abin ba hakana bane halittace kawai a hakan .
Ita kuma saiba datayi mai dadin baki tana da dan dama saidai ba sosai ba ga kuma
cin mutunci har na tsiya a bakinta.
Abin yana daure mashi kai yadda mace tayi boko zata tsaya tana wanan kazantar
haka sai wace batayi karatu an koya mata tsabta ba tafita.
Da safe kuma asubanci yayi yabar garin zuwa Abuja inda ya shiga jirgin zuwa
Rives don haka koda mahaifin Nusaiba ya nemeshi baya gari bai sameshi ba.
Saarece wajen binciken ta ta dauko kayan nan da matan ya J suka dawo min dashi a
cikin kayana tana nunawa mahaifiyarsu.
Tana fadin wai mama kinsan yarinyar nan ashe bata dauki ko tsinke daga cikin
kayan nan ta tafi dashi ba.
Yanzun nan ina neman gyalena na gansu a kayan ta yadda aka bata haka ta ajesu a
nan din bata dauki ko tsinke daga cikin kayan ba.
Haba dai Saare yanzu bincike kikai mata a kayanta kema kinsan babu gyalen ki a
kayan Ramaah wace take hada muna kayan mu itace zata daukar maki gyale kuma ?
Mama yarinyar nan tana min katsalamdan a ciki zancena kwanan nan wallahi idan
tana min hakan za a jimu da ita.
A cikon takaici mama ta juyo tana fadi rufa min baki mara hankali ai gaskiya ta
fada inba rashin wayau da tsegumi ba meya kaiki cikin kayan yarinyar nan yanzu don
Allah.
Wanan wani irin dabi,ace Saratu ina kula dake a gidan nan idan nabi ta naki
yarinyar nan so kike ki hadani da yaran nan sam bansan meyasa kike haka a kansu ba.
Haka yarinyar nan dake asibiti tun tana tambayana ke har tagaji ta kyale ta daina
tambayanki kwata kwata a yanzu kinki zuwa ki gaida ita.
In habu ya gane wana halin da kika tsiru nasan ba zaku kwashe dashi da dadi ba
tsorona Allah a yanzu kada sunan ki ya fito cikin zancen yarinyar nan Nusaiba.
Don ban tantama idan ba kece kika fada mata cewa yarinyar nan zatabi yayan ku ya
sauketa a Abuja kika haddasa wanan fitinan a tsakanin su.
Kallon uwar tayi tana fadin haba mama ni ina naga Nusaiba a ranan balle in fada
mata ga Ramaah zatabi yaya idan ma kece ai ji zamuyi don Nusaiba fada zatayi kin
sani.
Wanan ai shashancine jafaru din ta zarga ko wanan yar komu ta dauka bamu san
abinda mukeyi ba lamarin wanan yar yana ban mamaki ke kinyi kwancen mijin nan
hannun kawarki kuma ki koma kina nuna kowa bakya son yai mu,amula dashi saboda me
hakane wai ?
Har kizo kina neman batawa mutane suna akan abinda bashi ba isan wani yaji wanan
shirmen ai zancen zai juya wani abu daban kuma ?
Iya na sauke zancen mama ta dauka da ai yanzu tagani nafi da son ya gani ko yaji
ya dauki mataki da kansa kada ace na zubawa yara ido na hanashi zaman lafiya da
iyalinsa amma yanzu ai zata gane uwa nake ga jafar.
Tsuki iya taja tana fadin yaushe kuma ai tun za a ake shiri ba sai anje ba kin
rigada kinyi kuskure tun farko ya kamata ki nuna ke uwace agaresu .
Amma haka kike shaye duk wani wullakanci akan yaran nan kuma ki hana mijinsu ya
dauki mataki akai waike kada a zargeki.
Yo an dade ba a zarga din ba da wanan halin da yaran nan suke sakaki ciki a
kullum wana karon dake dasu kunkai yaron nan makura don haka ki barshi ya dauki
matakinsa ido kawai zaki zuba masu tundama baison zancen dake iyace tasa mama a
gaba cikin fada ganin yadda ta daga hankali wai ga sallah ya gabato ga azumi ya
tura yarinya gidansu.
Abuja
Rayuwan gidan anty sallama rayuwace ta turai tsantsanta don sai ankai karfe dayan
rana kowa na dakinsa kwance ba a fito ba.
Sai hakan ya zama min bakon al,amari a wajena don saboda wahala da jikina ya saba
dashi na ba hutu gareni da zaran karfe hudun asuba ya buga.
Don hakane a bangarena ba barcin na koma ba don ban saba da hakan ba idona biyu
ina dai kwance ina faman tunanen duniya.
Hakan yasa na jawo wayan nan na kunna ina shige shige a cikinsa har na fara gane
kan wayan don ban san kan waya ba a lokacin gaskiya.
Ban kuma damu da insani din ba don waya bai gabana a lokacin tunda nasan ba zan
mallaki waya a lokacin ba kila sai gaba kamar yadda anty Yanda tasamu sanadiyar
yaya Habu.
Amma sai gashi nice da wanan wayan dake hannuna da yazo min a bazata wayan da
kana kallonsa kasan babban wayace ba karamar waya bace bakace wulk da ita.
Taba can tabo nan har na gano abubuwa da dama game da wayan na shagala sosai a
lokacin har anty sallama ta shigo dakin bansan lokaci yayi ba na yarda da wasu ke
fadan waya kanin shedan .
Tabbas haka yake don ko sai gashi ya mantar dani duk wani irin damuwan dake
zuciyana lokaci guda har na shagala da dakilanshi.
Ramaah aina zata har yanzu barci kikeyi muryan anty salma naji a tsakiyan dakin
har ta karaso bakin gadon da nake kwance rub da ciki.
Na dago ina aje wayan tare da gaida ita da kwana duk da wunine lokacin ba kwana
ba amma tunda ban gaida ita da safe ba dole na kira hakan da kwana.
Lafiya Ramaah ta fada tana zama tare da tambayana i hope ba matsalan komai dai
nace a,a anty.
In kina da matsala fa kiyi magana flee free don Allah nan gidankine fa idan kina
da damuwa ki fada kawai nasani ?
A,a ba komai tace Ok akwai wasu perfume na dade da sayan su da kayan kwalliya
ban amfani dasu ina maji har na aurena akwai a ciki idan kin fito sai ki duba ki
zabi iya yadda kike so kiyi amfani dashi.
Kinsan ni nafi son naga mutun so clasic ba irin yadda kika koma din nan ba anyi
mace haka duk da azumine babu dan gyaran jiki haka Ramaah ?
Ki gyara jikinki tsab ki saba da hakan ko har kin manta da tarbiyan mamace wai
kinsan mama fa idan taji baka kamshi ko falonta baka shiga mata.
Dariya na danyi ina fadin komai na rayuwan mu a baya ban manta dashi ba anty
saidai a can gida rayuwa ta juya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login