Showing 21001 words to 24000 words out of 328222 words
Chapter 8 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
ukuba da tsagwama ga yunwa da
wahala daya juye masu kamaninsu a lokaci guda.
Dan wayan dataje dashima garin baffan ya karbe ya sayaryan suturunsu duk sun
koda a karshe dole suka koma amfani da irin wanda mutanen wajen suke amfani dashi
suka saje dasu baka gane sun taba rayuwan Abuja a baya.
Irin wanan labarin da Yanda takan ba Abubakar a cikin waya shine suke tsuma
zuciyarshi yana jin yana son ya taimaka masu duk da yasan karfin sa baikai ba amma
zai gwada sa,anshi ya gani ko Allah zaisa a dace.
Da haka kuma ta kara shiga ransa sosai yake matukar jin ko ta halin kaka saiya
taimaki rayuwan Yanda din inma da son samu gaba dayansu zaiyi sanadin dasai sun
dawo cikin gari da zama amma kuma ya kan tambayi kansa da taya haka zai faru ?
( IKKO Ikon Allah )
Tafiyan jirgine yayi don haka bai huta ba washegari ya fita wajen business dinsa
yabar zancen da sai Meimbe ta nemasa da kansa don har yanzu bai kai ga yanke
hukunci ba duk da malam na kusfa ya gaya masu akwai alheri tattare da wanan abin
saidai zai dan fuskanci baraza amma kuma ya bashi addu,a tare da ruwan rubutu
dayasha tun a wajensa.
Haka kuma baiyi sanyi a gwiwaba tun dawowan nasa yana duk abubuwan da kawunan
nasa suka bashi shawaran yayi don rigakafi a rayuwansa.
Har wani annashuwa yakeji don abubuwa yanzu sai budewa sukeyi tun dawowanshi
daga gida kofofin samunsa kamar an bude mai yake gani duk abinda ya taba cikin
yardan Allah zaiga nasara akan abin.
Haka saida ya tabbatar da matansa sun horu sosai kafin ya fara daukan wayansu
koshi saida iya ta kirashi tana sheda mai zuwansu Asibiti da Saiba da aka tabbatar
da tana da matashin ciki a jikinta na wata biyu da kwanaki.
Kamar yadda iya ke fadamai tun bayan barinshi gida bata da lafiya wanan yasa ya
kira Asmau ya fara jin lafiyanta kafin ya kira saiba din a gurguje suka gaisa yayi
mata ya jiki ?
Zata fara kawo mashi kissa yace aiki yakeyi zai kirata idan ya gama shine farkon
da har yake saurarensu idan sun kira wayanshi din koshi ya kira yaji lafiyan
jikinsu.
Tunda ya tara guzame a gidansa don ko,wacesu tana dauke da cikinsa a yanzu ya
zama dole ya kulasu haka kuma duk sati yana turowa ko wacensu kudi a account dinta
don bukatun yau da kullum irin haka na mata.
Yau ya kasance saura kwana biyu ya cika sati biyu da dawowa gidane suka hade
miss meimbe a wani shago itace ta fara hangoshi ta nufi wajenshi cikin sakin fuska
tana fadin kai kayi wuyan gani fa ?
Shima murmushi yayi cikin dan basarwa yana fadin mun daiyi wuyan gani koda yake
naje gidane kinsan mutum mai iyali sole inayi ina leka gida.
Dariya ta kwashe dashi tana fadin kajika sai kace wanda ya aje mata masu mata a
gida sune bini bini suke zuwa gida lokaci lokaci ba irin ka yaro karami ba.
Dariya zancenta ya bashi yake fadin nine yaro karami nida keda mata biyu a gida
zaki kalleni kice min yaro.
Dariya sosai ta kwashe dashi tana fadin abinda kakewa kanka fata kenan ka fada
ka aje mata biyu kamar yadda ku musulmai kukeyi ?
Sam kai baka dace da tara mata ba lover boy kada ka tauye kanka sa yawa mana
mace daya is ok for you ku more rayuwanku da lokacin ku.
Wani kallo yake mata kafin ta tsaigaita da maganan tana kallonshi itama tace iam
tell you gaskiyata ke nan har zuciyana na fadama saboda kai din mai tsadane zanso
naga wanan mace mai sa,an da zata aurenka ?
Me kika daukenine mrs na fada maki matana biyu wallahi kuma ko wace a yanzu tana
da ciki da zata haifa min baby.
Kallon serious tayi mai tana fadin kacire wasa abinda naga ya dace dakaine na
fada sai yayi murmushi don yasan ba zata yarda da yana da mata ko bama mata ba a
lokacin.
Can ta dan tsagaita dariyan ta saita kanta ta soma fadin ina ta nemanka naji
shawaran daka yake don broda ya kirani yace ina guy din don kaya sun fara yawa yana
son a fara plan din turawa arewa din.
Shima Jafar din gyara tsayinsa yayi ya soma fadin eh to gaskiya ban tsayar da
maganan zanyi ko ba zanyi ba a yanzu saina gana dashi yayan naki na fahinci wasu
abubuwa daga bakinsa.
Wanan baida matsala don yana Nageria yanzu haka kaga bari na nemesa sai muji
time din da zamu samesa don gaskiya mr handsome ina sonka da wanan business din don
ba karamin samu zakayi a cikinsa ba yafi wanan buga buga din da kukeyi a yanzu.
Tana magana tana dauko wayanta a cikin handbag dinta a lokacin ta soma dialing
din number dan uwan nata kira kusan zai katse ya daga yana fadin sorry sister ina
meetinga ne a yanzu.
Dama broda guy din nan danayi ma zancenshi shine yake son ka bamu time da zai
gana dakai yake fada mata zai shigo lagos next tomorrow idan ya shigo by 4 pm zasu
iya ganawa dashi a ranan.
Suka danyi yaresu inda take kara rokawa mr handsome dinta alfarma a wajen yayan
nata tana yabawa har yayan ke fadin tabari din yazo din da alama guy din yasan
kansa tunda har ya nemi su fara ganawa dashi.
Abinda baiso shine cuta da cin amana idan haka ya faru ba zai dubi alakansu ba
zai dauki mataki mai muni akan ko waye.
Tace by god grace hakan ba zai faru ba son ta yaba da halinsa sosai sun dade
suna business dashi ta fada mai hakan don ya yarda.
Kai ta dag ta saukewa Jafar kallo tana fadin munyi sa,a basai muje can ba zai
shigo lagos banda gobe kaga zamu sameshi 4 o,clock ku gana dashi don forget with d
time ta kara fada suka taka zuwa bakin motarta tashiga ta wuce.
Shima motanshi dayazo da ita wajen ya nufa ya shiga ya nufi inda zai tafi tare
da tunanen yadda abin nasu zai kaya saboda zuciyarshi ta shiga wasi, wasin don
imani da tauhidi dake yawo ajinsa na adduan iyayye.
Kamar yadda suka aje time karfe biyu yana fitowa sallah ya kirata karo na farko
yana tambayanta ko brother din nata ya samu shigowa lagos din tace zata kira ta
tambaya taji.
Ba a dauki wani lokaci ba ta turo mai sakon wajen da zasu hadu zuwa wajen yayan
nata yaci gaba da harkokinsa na yau da kulum a lokacin.
Sai bayan ya fito sallah a masallaci mafi kusa ya shiga mota ya sameta tana
jiran sa hakkuri ya bata daya tsaya sallah ne a masallaci tace ba matsala tana gaba
motanshi nabin nata a baya har gidan dan uwan nata dake wani unguwar masu kudi anan
kusa da ruwa.
Kai tsaye ganinta security suka barsu suka shiga gidan don tayi masu bayanin
tare suke yaji mamakin girman wanan gidan haka yasashi nasa wanan yayan nata ba
karamin mai kudi bane ashe.
Sun samu waje sun faka motocinsu wajen suka fito zuwa cikin gidan shidai yana
dauke da addu,a a bakinshi don zuwa yanzu sai tsoron zuwa shi kadai ya darsu mashi
a zuciya yana tuna addua shine mafita koda yazo da wani din ba zai iya mai abinda
Allah zai yi mai ba ya fara jero duk abinda ya sani a bakinsa.
Wasu kulka kulkan mutanene ta gani suna gadin gidan bai damu ba saboda addua
yasa ya daina jin tsoro a yanzu.
Sun samu yana meeting da wasu yan kabilansu kana ganinsu kaga manyan matasan
arnakun kasan nan ya fake da waya da wani abokinshi a lokacin.
Ya fahinci duk wanda ya fito yaga Meiarbe sai yayi mata kirari da bata girma
irin tasu na iyamurai da sukeyi bayan sun fitone akai masu iso zuwa ciki don yayan
nata ya hangota daga waje yasan sun iso ke nan.
Addu,an da Jafar ya doshi wajen dashi yasa suna shiga yaga mutumin aiba wani
babba bane can yanda ya zata don irin matasan daya ganine a waje yanzu.
Hannu ya mikawa Jafar din su gaisa baiki ba ya mika masa yaga zalla nagartan
jafar daya hango a yaron lokaci guda.
Bayan sun gaisa yake tambayanshi daga ina yake ya fada mai kai tsaye daga zaria
yake yana zaune nan lagos.
Ya dan kara kallon Jafar din dake zaune a cikin ladabi kafin ya soma magana
yana fadin quity sure kayi min haka nake son dama matashi mai lokacinsa wanda zai
iya bada karfinsa ga aikin mu ba ya zauna ya tura ai masa ba.
Saidai kota fadama harkan mai zamu soma a yanzu mutane da dama daga arewanku suna
son wanan harkan ban basu daman hakan ba don ina jin tsoron hurda hausawan ku
saboda basu da amana.
Kai jafar ya dago ya kalleshi yacewa Jafar din gaskiya na fada nagwada aiki da
mutanen ku a baya banji dadin hakan bane.
Allah sarki malam bahaushe da abaya iyamuri ko bayerabe suke tsoron koyi masa
kallon banza balle fada a yanzu zamani yazo da iyamuri zai fito fili ya fadi magana
akan bahaushe sune ke fadin basu yarda da bahaushe ba suda muke kyama sosai.
Saida wasu marasa zuciyan bahaushe da suka batamu a wajensu sun ari rigan
bahaushe sun yafawa kansu suna yaudara suna batawa hausa asali suna da akidarsu ta
yaudara a yanzu.
Kada ka damu you are lucky tunda autace ta kawo ka nasan idan bata yarda dakai
ba zata kawoka har wajena ba zan barka hakan don nasan tunda kace kana son ganina
kaima kana da abinda kake son fada a kaina.
Zama Jafar din ya gyara ya soma fadin najo duk abinda ka fada saidai ina son
jin ainihin yadda kake son sana,an naka ya kasance a arewa idan zan iya zan karba
da hannu biyu inma godiya idan kuma naga ba zan iya ba zan fada tun a wajen nan ka
neme wani don addini mu bai yadda da wasu tsare,tsare ba a cikin sana,an mutum.
Kallon guy din chibuza yayi yaro karami yasan kansa akan addininsa abinda bai
taba jin manyasu sun fada ba Allah Allah ma suke ai signing din contract dinsu su
farawa mutum yaudara shi gashi yazo masa da nasa tsarin akan addininsa yanzu.
Ehh to ba wani abu bane ya soma mai bayani akan yana bukatan gina gidajen mai a
arewacin Nageria din shi Jafar duk zai kula da wanan bayan haka akwai motoci da
zasu shigo wa yanda zasu dinga sintiri kai mai kuma duk zasu tsayane akarkashin
kulawan jafar din da komai illa iyaka shi nasa balancen zasuyi yana turo mai kudi a
wajensa eather shekara ko bayan duk wasu watanni haka yadda dai abin ya samu
karbuwa a wajensa.
Ajiyan zuciya Jafar ya sauke don jin ba wani abinda zai soki addininsa ko
rayuwansa nan gaba donshine ya amince suka tsara yadda abin zai kasance tare da
musayan secret number da zasu dinga magana a tsakaninsu.
Ya gargadi Jafar sosai da bai son yawan magana inda yace koda ba,a aka sunan
yadda za a fahinci nasa bane shi wanan ba matsalan shi bane kada dai a samu kuskure
a cikin harkan .
Budan bakin Jafar yace wanan kada muyi fatan haka mu nemi sa,a a wurin ubangiji
ya dafa muna kan lamarin da muka dosa .
Iyawan mutum ko kwazon mutum baiyi kamar na Allah ba da komai yake a hannunsa kai
chibuza ya daga yana yaba nagartan Jafar a zuciyarsa.
Dafa Jafar din yayi yana fadin idan ka rike gaskiya zamuji dadin juna sosai
dani dakai don a wanam harkan kadai zamu tsaya ba a sannu zanyima hanyar
international business .
Sun rabu cikin jin dadi da fatan nasara a tsakaninsu sukai sallama akan in Jafar
yagama nazari zai nemesa yaji inda za a fara.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1f
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Kamar yadda yake dan adam bai gani bai tofa nasa ruwan a cikin lamarin da bai
shafeshi ba shike faruwa yanzu akan Jafar .
Wanda yasan jafar yasan mutumne daya taso da kwazon nema saidai ganin rufin
asirin da ubangiji yai masa lokaci guda yasa mutane nata tofa albarkacin bakinsu
akan cigaban daya samu inda a yanzu ya gyara gidansu da suke zaune a cikinsa don
haihuwan matansa yaiwa kowa part dinta amma falo na tsakiya babba haka bangaren
Abubakar da zancen Aurenshi yanzu kowa ya san da yana neman aure a Cameroon .
Don har manya su kawu sun shiga zancen zuwan farko baffa yake amincewa da zancen
saida suka biyu ta Alh can abuja ya fito masu ta bayan gida a dan Nageria ya hadasu
da hakimin garinsu shiya aika masu da sammaci aka nemosu har can inda suke zama
akan human right tayi karan baffa din.
Tsoro da gudun wahala yasa baffa cewa ya yafe yaran su koma nan kauyen su gidan
hardonsu don zaman kaka yake ga yaran.
Yace su zauna anan tunda shi baida iko dasu dama taimakonsu yakeyi ai tunda
naggen da ubansu yabari a yanzu sun zama nasa tunda shekaru ya kora shike kula
dasu.
Hardo yaso yayi magana amma sai su Abubakar sukace ya kyaleshi daha baya za,ayi
wanan zancen yanzu zancen yarane da uwarsu su samu freedom ayanzu akeyi.
Abubakar bai tsaya dogon nema ba irin na barna lokaci a dade da budurwa ana
shan soyayya daga shiga rayuwansa ya fito da zancen aure.
Inda mama Dubu ta kama mashi tana kuma tayashi da addua da shawara wanda a yanzu
kowa yasan da zancen bafulatanan ruggace yake son ya aura.
Inda wasu ke ganin ya rago kamarshi dan boko dan gaye mai jin lokacinsa zai buge
ga auren yar daji jahila mara boko wace bata waye ba ?
Sun manta kida Jahilace haka Allah ya tsara idan itace matar da zai aure din ba
(makawa ) inkiyan kauyen zee makawa) sai ya aureta.
Allah yayi za ai abin a gabar da dan uwansa ke cikin tashen Naira Allah da
yardansa yadda aka saka watan auren lokaci yayi akasha buki.
Bukina mai kama da dunkula irun ta fulani ba wani shagali aure kawai aka daura
aka dunkulo amarya sai yan rakiya da hardo yabayar mutum biyu sai kanwata da zatazo
zama da ita don ta samu wani a kusa da ita cikin garin da bata san kowa ba .
Hardo ya roka kuma anyarda mai da hakan gidan su Abubakar din mama tace dama tana
da niyar hakan a zuciyarta don ta samu na gida a kusa da ita.
A bangaren matan yaya jafar kuma sai dariya sukewa Abubakar a fakaice tunda
Saiba dake fadin duk bakin ransa da jiji dakai a bafulatan daji ya kare ashe.
Ga mata birjit a gari amma ruwan ido ya kaishi daji auro bafulatana saidai basu
fadi a gabanshi saidai a bayanshi basu kadai ke wanan zancen ba harda matan gidansu
gidan mahaifinshi.
Suma sunata sakin irin zancen nan da fadin magana akan fulani abindai kamar yadda
aka saba tsegumi akan ko wani irin aure wanan ma a tofa iya tofawa da za a iya.
Mutum dai bai isa ya hana abunda Allah ya nufa ga bawa ba saidai gajin hakkuri
namu na yan adam yakansa mu daukanwa kanmu zunubi a cikin rashin sani.
Ita kanta maria bata taba zato ko tsamani haka zata samu gidan Abubakar din ba
don ya nuna mata shi baida komai a lokacin nemasa da ita.
Sai gashi hadaden gidan dataga an kawota ciki ya tsinka mata zuciya ta kara
godewa Allah daya duba mairaicinsu ya fitar da ita daga kuncin bautan da sukeyiwa
baffa.
Sai addiua take wanan auren ya zamo mai dorewa a gareta don baffa yai mata baki
da cewa indai auren kado ne taje ya bata shekara tasan baffa mugune na bugawa a
jarida.
Don ko yan uwansu kaf fulani tsoronsa sukeyi abu dayane ke razana baffa shine
hukuma baison abinda ya dangantashi da hukuma.
Don bai kaunan ya cire nagge daya balle fiye da dayan a cikin garkenshi ko
yaushe a cikin lissafin garensa yake a tsakar dare bai barci nan zaita sintiri yana
kidayan shanun dake garken sa.
Yana kuma surukullensa a ciki yanawa mutane aiken shirin daya saba wanan tunane
data shigane yasa har bataji sallaman su saiba ba da suka shigo ganin amarya da
safe.
Sai da yar uwarta ke fada mata a cikin hausa anty Yanda ana maki sallama fa ta
zabura tana fadin wa ,alaikis sallam.
Kallon juna sukayi suna fadin tubarkallah amaryan ke nan ta fito tana masu sannu
da zuwa sai yar budurwan dake tare dasune da ba zata gime mata sosai ba take fadin.
Anty maria wanan matan Yaya J ne ana suke gidan suma ina kin gane yaya J babban
yayan mu na dakin mu sune matansa.
Cikin fara,a da yar kunya ta sake dago kai tana masu sannu da zuwa tare da
gaidasu tana dan kare fuskanta don kallon kurullah da suke mata.
Ba zakace ita din bafulatan daji bane yadda suke fada don dinkin da anty fadila
tayo mata daga Abuja sune jikinta a lokacin dinkin dakosu basu saka irinsa ba dogon
rigace da yaji duwatsu kamar sarka ya danne a jikinta sai dogon gashin kanta daya
sha gyara an daureshi a waje daya yana kyalli a jikinta.
Mikewa tayi tana fadin bari tazo taji saiba ta