Showing 243001 words to 246000 words out of 328222 words

Chapter 82 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

da shirun namu da yake fadin agaida mama din ni dai bance komai
ba don nashiga na samesy zaune da saratu suna magana da ita da saratu nagaida ita
naga ta amsa min a dakile.
Na saba da hakan da mama ke min tun abun yana damuna har yanzu na share na fitar
da komai a raina abu dayane kawai ina kare abinda zaisa ta taba min mutuncina.
Iyakarmu gaisuwa inma tazo waje ina kokari na kaucewa wajen don gudun samun
matsala a tsakanin mu a bakin maman tudu na kara fahintar wasu halaiyan mama din
daya kara sa nake taka tsantsan da ita.
Mun jima a tare dashi dakin zaune kafin Anty Asmau ta shigo da yara suka zauna
suna hira hakan ya bani dama samu na mike nabarshi dasu na fara gyaran part din
dana gama kuma wanka naje nayi na fito.
Saida darene mama ta samu daman yi min fada sosai kan nayi hakkuri da yar
uwata kada na yarda aji kan mu har a gane muna da matsala tundai saratu taji zancen
zai juya wani abu na daban a bakinta .
Na fahinci ba saratu ba har salima mama tudu ta tsana acewarta mahaifiyarsu ta
sagartasu sunki aure suna abinda suka ga dama a cikin gida zaune.
Dole washe gari na shirya na tafi saidai ban barta ba don yadda nayi kuka itama
saida na sakata yi don na fada mata abinda ke zuciyana.
Inda ta nuna ba hakana bane wai mijinta ya hanata fita saboda matsalanta yasa ta
kiyayye dole dai na zage nayi abinda ya dace ace nayi a wajen duk da karfin hali
nakeyi a lokacin.
Saidai nasha zunde da sheri a wajen yan uwansu a ranan kowa da kalan sherin da
yake min akan cikin dana samu a yayin jiyar miji ni dai nawa kawai murmushi.
Ban dawo gida ba kamar yadda kowa ya zata daga gidan ya habu gidana na nufa a
ranan a can na kwana don ina son gyaran gida nida Anty Nafisa da wata yar yaya
Auwal mukazo gidan muka kwana.
Koda mama ta kirani a waya nace dasu gani nan gidana mama ina son inyi gyaran
gidan ne duk yayi kura yana bukatan gyara take fadin ga mijin ki nan yana fada dake
hakan baisa na dawo ba a ranan saidai nayi mata bayani maganinsa daya dace a bashi
na shafawa kuma su san yadda zasuyi.
Ba komai yasa na koma gida ba sai gulman da akai min kan wai ina ha,intar
kishiyoyina na fake ga sunan jinya na karbe masu miji dama mu fulani haka muke da
kwatar maza .
In badon cikin daya baiyana min a jikina ba da ba,a gane muna cutasu gashi najawa
Saiba saki saida ya fara samun lafiya nasa an sake ta saura Asmau itama in batayi
hankali ba korata zanyi in zauna ni kadai kamar yar uwata.
Naji dacin wanan maganan sosai da naji hakan yasa na yanke shawaran komawa
gidana tundai da naji ance Asmau dince take fadin wai sun zama yan kallo yanzu basu
gane komai a gun yaya din dul na tare komai banson kowa yazo kusa dashi saini kadai
ashe mun san abinda mukeyi ni dashi ?
Nasha alwashin duk abinda za ace saidai ace don ba zan koma gidan ba kuma zan
dai dinga zuwa in dubashi a can din iya abinda nasa a raina ke nan.
Washegari na tashi da aikin sosai su anty nafisa suka tayani a yadda na fahinta
kamar ta samu manemi a yanzu din don bini bini sai ya kirata a waya sun dade suna
hira dashi.
Misali karfe biyu na rana mama ta kira waya tana fadin har yanzu bamu gama bane
karya nayi mata nace mama gaba daya gidan yayi kura saida muka fitar da koma ana
kakabewa .
Da dare kuma ta kira tana tambaya nace mama ina ganin sai gobe don da sauran aiki
ban koma ba dai har kwana uku gana hudu nayi abinci da safe na shirya zuwa gidan.
Acikin kwaliyata na shiga da basket din abincina tiwon semo da miyar egushi
nayi dayaji nama na aje basket din a wajen su mama da iya.
Muka gaisa tana min sheri tace kice kin koma gidane da wayau yar nan daga zuwa
suna saimu nemeki mu rasa ?
To meya rage yaya tunda sun gama aika aikansu dashi kuma ai saita koma gida
tayi jinyar cikin yanzu kuma ?
Tana jinyar ciki ita daya ga miji a nan na mike ina murmushi zuwa ciki na samu
yayi fushi sosai dani hakan bai dameni ba na gaidashi da kyar ya amsa min .
Duk daya ban tausayi nasan banyi daidai ba don ko kallon dakin kawai da nayi
dakin ma kansa yayi missing dina don sai ince bai samu gyara ba daya kai sau biyu.
Har wani dan bashi dakin keyi a lokacin zaune nakai ina gaidashi bai amsa ba ya
kyaleni nima nayi shiru muryan mamace ke kirana tana fadin kizo ki dibarwa mijinki
abincin nan nasan zaici sosai tin shekaran jiya yake maganan tuwo gidan nan an kasa
yi mashi.
Na mike naji yace No ki barshi ba zanci ba nayi murmushi ina fadin yaya fushi
kakeyi dani ke nan bai daiyi magana ba harna fita.
Na debo abincin a plate zuwa gabanshi na aje yadda yake kallon abincin yasa na
mike na koma na debo ruwa a gabanshi na zauna na fara dibowa ina bashi da kyar na
samu ya karba bayan ya gama fadanshi cikin zafin rai yana fadin nasan inba niba
wazai samu yana taimaka mashi yadda nake mashi ?
A tausashe na soma magana ina fadin yaya ka tuna bafa ni kadai bane matan nan
suna da hakki a kanka tunda yanzu ka dan samu lafiya har kana dan iya mikewa ya
kamata suma a basu hakkinsu ladan nan kowa fa yana son samunsa don Allah kayi
hakkuri in zauna gida itama ta dan taba ta samu ladan hakan .
Na jima da loman abincin a hannuna saida na gaji nakai bakina na sake debowa na
mika mashi ya karba ya kumaci sosai ya gama na kwashe kayan.
A wurin mama nake jin cewa ashe zuwan da Yazid yayi shiya turashi ya daukoni sai
yaje ya samu muna gyaran gidan da gaskiya ranan tace dani.
Ranan munga tashi hankali ai na zata ai inkin dawo zaiyi fada sai kuma naji shiru
koda yake dubu ta taka mashi burki ai tayi mai tas tace ya barki mana idan zaki
koma can ne ki koma da yake fadan mu nan ba mutane bane a tare dashi ?
Ko ita Asmau bata iya mashi komai da kike mashine ta dai kwana nan din sau biyu
jiya banga tazo kwanan ba wai danta baida lafiya tace .
Oho dai na fada a raina ba dai zan zauna ba kuma a nan na wuni na gyara masu ko
ina tas na shiga wajen kowa da yamma kuma nace ni zan tafi kada yamma yayi min.
Kallona yayi Asmau tana zaune ba daman yayi wani abu yace saida safe kawai saiga
iya take fadin yanzu dai kinyi hijara ke nan kardai kin gudu ke nan fa ?
Iya gara ingudu inbarwa anty mijinta tunda ya samu sauki a yanzu itama ta samu
nata rabon na tare waje da sunan jinya na hanasu ganawa da mijinsu yadda suke so .
Kamar yaya kin hanasu ganawa da mijinsu yanzu ko da aka ga idanunsa sun bude
aka san wanan da kikai wahalan ki a lokacin wayace zai kama maki hakan ?
Gulman nan yazo kunneki ke nan don wanan dama kika koma can ke dai ai gulman nan
ya jima da fita gidan nan yanzu da kika tafi din waya iya abinda kikeyi masa din
ina zaune yake cikin takaici da kazanta kawai ya isheshi gidan nan .
Zai dai tattaro ya cin maki can mamaku ma tace gida tayi tunda Allah ya kawo
sauki na hanata tafiyane don in kun tafi gaba dayan ku abin bai dadi gara dai ta
sauna har akwana biyu.
Banda gulman me suka iya sunan son miji ne kawai abaki amma babu hus a garesu
mutum bai kula da kansa ba balle wani saida yazid yayi cin mutunci yadda suka bar
gaban gidansu da kazanta dazun .
Murmushi nayi na saba gyalena ina fadin ni zan tafi shiru yayi kamar bai jini ba
a raina nace kaji dashi ba dai zan zauna ba din a kara zagina duk a yanzu dai zagin
bai kankaruwa a gareni ba riga dana shafawa kaina wanan kuma ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[5/17, 08:44] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

7️⃣6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Haka abin ya kasance duk da ya nuna baison hakan dana yankewa kaina amma saina dake
da safe zan shigo inyi mai duk abinda na sabayi idan yamma yayi kafin magariba
saimu koma gida da Biba ko anty Nafisa.
Tun yana daure fuska idan nazo har yakai ya dan sake ya fara daina hakan da yake
min ina daga ciki tare da mama nake jin hiran mutanen gidan dake zaune falon da ake
jinyasa din salima ke fadin.
Kefa Asmau na kula kwanan nan sai wani sheki kikeyi kina wani budawa meye sirin
hakan kuma ?
Koda yake duniya taki yanzu an watse an bar maki miji ke kadai kina shanawa ba
dole kiyi sheki ba haka ?
Wani anbar mata miji a ina saida aka gama abinda za ayi don dai ita bata san
zafin kanta bane ai ina zan zauna mace na shigo min gida tana min feleke da yanga
ana iskanci da sunan jinya wallahi ba a haifi wanan yar ba tukun .
Komai sukayi ai don kansu saratu balle ma me akeyi duk abinsu dai basuyi da
ranana balleni kome zasuyi yanzu ai na saba da ganin hakan akan mutumiyarki Nusaiba
bai kuma daga min hankali ba balle wanan din.
Sai naji salima tace ballema me akeyi maganan kice dai kawai saratu da wani
tashin tashin dinki can daza ki kawo za,a hanata zuwa duba mijintane kuma ?
Wayace za,ya hanata yanzu don Allah ni dai banson abinda zai hadani da wanan yar
kauyen yarinya dake ganin daidai take da kowa yanzu gidan nan.
Jin nayi shiru ina saurarensu yasa mama soma fadin zaku fara takale takalenku ko
ku jawa kanku zagi a karshe a juya maganan kuma .
Ko yaushe ina muku fadan irin wanan maganan dabai shafeku ba amma baku jin
kashedin da nake maku ina ruwanku da shanawanta yanzu kuma ?
Sallon ku hada wani fadan kuma kenan a yanzu tsakaninsu ana zaune kalau maman
tudun wadace take fadin hakan a garesu rai bace.
In sun jawo magana ai suji dashi ni ina ruwana tunda ban aikesu ba sun daiji
abinda yazid ya fada game dasu ai ya karya yarinya ba wani abu bane wajenshi.
Ballema mama waye zai dauki zancen su tunda ba sakarai nake ba kawai dai magana
ce mukeyi sai kawai saratu din ta mike tana guna guni ta fice .
Ashe fadi take don an mayar da mutum baiyi aure ba za a dinga mashi abinda akaga
dama karya ta fada ba cin amanan akeyi ba inba hakaba ya akayi tayi ciki yanzu ?
Na jima a zaune nayi shiru kaina kasa gaskiya wanan mace tana son shiga min
rayuwa duk dana tattarata na watsar gefe daya iyakata da ita gaisuwane wata rana
kuma bamu ko gaisawa din da ita haka zamu share juna.
Tace ita danyar kai nace na fita muje zuwa sai hakan da nake mata kuma a yanzu ya
koma bata haushi tana jin kamar ta shakeni ta kwantar.
Wai ashe bayan tabar part din takoma nasu shine taje ta kira saiba a waya tana
labarta mata duk abinda aka fadi abu ga mara hakkuri saiga saiba din ta kira Asmau
tana zagin ta.
Muna ciki din mukaji Asmaun na fadin ita saratun din tace hakana wai meyasa
saratu keda tsegumine wai ?
Shiru daga ita har mu wajen yayi can ta soma fadin Nusaiba na fada din ina
ruwana da duk abinda zasuyi ke bakiyi min wanda yafi wanan din bane aiba karya na
fada ba ko ?
Mama tudu ta mike ta isa tana fadin wai meye kuma yanzu ita yarinyar nan dan
maganan nan saida ta kira yarinyar nan tun ba a bar wajen ba ta fada mata ?
Anya kuwa saratu kanta daya kuwa da wanan halin ke mara kunya an fada din ai idan
bakiyi ba ba zata fada ba ai wanda ya mutu akewa karya.
Mikewa nayi na fara hada kayana don tafiya kallona yayi yana fadin ina kuma zaki
yanzu na amsa da gida rai bace ban yarda na kalleshi ba.
Abin yana ban haushi duk da nasan yana cikin halin ciwone a yanzu amma kuma a
yadda na fahinceshi shine gaskiya duk cikinsu kamar kannensa sunfi raina shi don me
zatayi ta min hakan ko watan mu ya kasa daukan mataki idan kuma ka dauka da kanka
abin ya zama laifi a gun mahaifiyarsu.
Ganin ban kulashi ba yasa shi fadin ke Rahama kada ki bari raina ya baci dake
gurin nan badake nake magana bane wai ko sunyi dakene yanzu ?
Jin abinda ya fada yasa na kara dagowa na dubeshi cikin mamaki banga laifinshi
ba kila son yana namiji yasa bai fahinci zancen daga farko ba.
Ko kuma wata kila baiji farkon maganan tasu bane sai tsakiya yasa yake fadin
zancen bai shafeni ba ai ni dai na hada kayan na koma falo na zauna na barshi nan.
Tunane nakeyi a raina ya zama dole nasan yadda zan daukarwa saratu mataki ta
daina aibantani ga bakinta a yadda na fahinci maganan ta dai shine.
Ina fakewa da cewa ina jinyar yaya ga hakan na shammaci abokan zamana ina kwana
da miji ni kadai har ciki ya shiga ba yau ta fara fadan hakan ba karo na biyu ke
nan da irin hakan ya faru.
Wata rana muna zaune a haraba ana hira ake bada labarin wata wai bata da umma
asalinta me saratun zata fada daga inda take zaune tana dakilan waya sai cewa tayi
ai ance basu bane shegu.
Shegu suna gidan aure inda ake daukan kwanan wata a samu ciki a haifi mutum wanan
dan da aka haifa ya zama shege sune shegu na asali da akasani ba wai wanda aka
haifa a wajen iskanci ba haka ?
Wanan abin ya tsaya min a rai tun lokacin duk da maman tudu ta tsawata mata don
ta katseta da fadin to malama inji wano nafsin ya baki wanan fatawan kuma ?
Kinhanki saratun nan a yanzu kan gaskiya baki iya zama babban gidan mu saidai ki
koma rabe rabe a nan tunda har kin san wanan kikaki kawo miji kiyi aure ki huta.
Ai mama Allah ne bai kawo mijin bata fada cikin tsigar rashin kunyarta datakewa
mutane nan mama ta rufe ido tayi mata tas a lokacin tace sai inci ubanki wajen nan
niko uwarki bata fada min maganan banza haka ?
A wanan lokacin har mama tayi fushi tana fadin gida zata koma bata zama tana
kallon wanan fitsaran haka saida sukai ta bata hakkuri shine yazid ya kusa halakata
din a lokacin sai kuma wanan karon da ta sake maimaita abin shigen hakan.
Tunda na zauna a wajen baiyi magana da kowa a cikinsu ba ga Asmau sai maimaita
abinda Saiba ta fada mata takeyi amma hakan baisa na tanka masu ba don zuciya daya
zo min a lokacin.
Ba karya nasan ina da wanan zuciyan wanda idan nace zanyi magana a lokacin
tabbas hakan zai iya jawo muna gagarumin rigima a ranan.
Saidai kashh jin yadda Asmau ta matsa da zancen har take fadin indai don wanan
da akeyi yanzune ai ba ai komai ba balle ko a gabana akeyi hakan bai taba damuna
ni.
Ai yin ma isace idan fitsari banzane kaza tayi mana Allah ne sheda ta koda hakan
ya faru nasan kaddaratace a hakan amma a cikin kiyayyewa nake don ni din ba jahila
bace kamar wasu nasan abinda nakeyi ban shiga hakkin kowa ba har na samu wanan
cikin .
Da za a zauna ana fada min magana inma shegen ne nayi tare da yayanta muka aikata
hakan don ba zina naje waje nayi ba balle a zauna a fada min magana haka kamar nice
farau.
Sai a bari tunda yaya yana kwance nayi cikin idan na haihu aje asibiti a auna dan
idan ba nasa bane sai a ban in tafi da abina .
In kuma nasane zan shayar daku mamaki a gidan nan don sai nayi karan saratu a
wajen hukuma na bata min suna da take kokarin yi a gidan nan.
Yau dai ko saratu kishiyatace ya tsaya a hakan irin abinda take min kawai ta koma
can gidan takama daki daya mu zauna a matsayin kishiya da ita insan zaman miji daya
mukeyi da ita a gidan nan.
Naji ina cin amanan su saidai zaki bada dalilinki gobe gaban Allah don ba yafe
maki zan taba yi ba saratu sai kin fadawa Allah cin amanan da kika sheda nayi masu
a gidan nan.
Ke kuma Asmau indau zuwa duban yaya da nakeyi gidan nan ne na daina daga yau ba
zan sake leko gidan nan da sunan gaidashi ba balle na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login