Showing 213001 words to 216000 words out of 328222 words

Chapter 72 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

fada bashi bane nadamarka mai magani ta fada.
Kinga idan abinda ya kawomu har an gama a barmu mu tafi don dan uwana dake can
kwance ba lafiya munzo nan da sunan wunine don bamuzo da niyar kwana ba nan da
zaria akwai nisa sosai don haka zamu koma yanzu .
Ya fada yana kokarin mikewa tsaye don duk wanan bashine a gabanshi ba zancen dan
uwansa shine ke zuciyarsa din yana ganin kamar wani abu zai iya samun jafar din
kafin su dawo zaria a yadda suka barshi din.
Ba yanzu ya shirya daukan mataki a gun kawu ba sai bayan komai ya lafa yake son
su tunkari dan uwan mahaifiyarsu din da matarshi.
Don tunda sukai waya da yaya Isah ya sanar mai halin da suke ciki asibiti da
jafar din hankalinshi ya tashi yake ganin ai kamar baida rayuwane sun boye mashine
kawai.
Sai bayan sunyi nisa yake sanar dasu irin halin da akace Jafar din ya shiga
bayansu wanan ya kara daga masu hankali sosai.
ZARIA
Tun bayan faruwan hakan muna dakin zaune nida mama da inna don ita umma ta koma
gida don basu watsewa su bar gidan ba kowa sukace.
Inda yaya isa ya gargada yan uwa yace su koma gida ayi masa addua tunda likitoci
sunce ba zasu bar kowa ya shiga ba kuma dakin da yake kwance din.
Bayan na idar da sallah magaribane inda nake zaune makure a cikin damuwa wayata
dake cikin yar jakata ta dauki kara na dauko ina dubawa abin mamaki dan uwana
Dagene ke kirana a lokacin.
Na dauka murya ba dadi ina amsawa yake fadin yaya yaji muryata haka kamar banda
lafiya ?
Ban iya bashi amsa ba sai kukan dana fashe dashi lokaci guda a cikin harshen
fulatanci nake masa bayanin halinda mijin nawa yake ciki.
Wai tsaya Anini ko dai zancen mijinkine naji hardo da nayi da baffa dazun nan
yake fada min yaji hardo ya bugowa baffa waya suna zancen don ya bashi wani makari
da zai masa amfani dashi.
Asalin maganin baffa ya dauke daga kakansu shi kadai kedashi a hannunsa yanzu
nan dai yake fada min a ranan idan baffa ya fita yawon darensa zai shiga ya dauko
min tun da safe zai shigo mota yazo zaria dashi .
Naji dadin hakan sosai don nasan tunda yayi alkawari har in ya samu daman daukowa
zai kawo din naja bakina nayi shiru don ba abinda zan fadawa wani bane zancen daya
shafeni ni kadaine wanan saiko yar uwata.
Karfe goma yaya Auwal yace na fito mu tafi su saukeni gida don zai mayar dasu
mama da inna gida a lokacin ba zan iya rokonsa ya barni ba .
Saidai furucin mamane yasa naji sanyi don ita ke fadin Auwal kubar yarinyar nan
ta zauna kusa dashi don ko dazun daya rikice badon itaba bamu san yadda zamuyi ba.
Taje dai ta shirya ta dawo nima zan tsaya a nan din tare da ita ya kasance ta
samu mace a kusa da ita sai yaya Isah yace amma mama kinga,,,,,,,
Abinda na fada ke nan isah kubar yarinyar nan a kusa da mijinta har in kuna skn
ganin cigaban lamarin nan ga dan uwanku.
Hakan da mama ta fada shine yayi sanadin zamana da ita a kusa da yaya din ko wani
lokaci don mama irin matan nan ne masu tsare gida ga bada umurni ga iyalinsu wanan
yasa take jan girmanta akoda yaushe.
A can gidan su Jafar din kuma tun bayan barin su asibiti da suka isa gida
Nusaiba ke ta kuka tana waya da yan uwanta tana fadin cewa an kita ana son hada
mata kai yan uwan jafar sun tsaneta suna kinta.
Da korafin yayi yawa uwar tace taba Asmau waya zasuyi magana shine Asmaun ke
fada masu abinda ya faru uwar tayi masu fada dukkansu kamar yadda ta saba tace ai
dole zasuce hakan tunda kuna nuna kamar baku damu da halinda yake ciki ba a yanzu.
Ta yaya zaku tsaya karamar yarinyar har tazo ta fiku iya fallako ta karbe maku
miji kuna gani ai ba sunce bane inda suke ganin kauna suke jin taushi tunda
rayuwansa ake nema a yanzu koma meye ku bari gobe zamu shigo ai.
Da haka suka samu ta hakkura don cewa tayi da zata dawo gida tunda an nuna mata
kiyayya a nuna bata da amfani ga jafar din.
Ranan sunyi shirin da suka jima basuyi ba a tsakanin su don sunyi zama na
shawaran kan abinda zai fitar dasu daga kallon tuhuman da yan uwa suke masu din.
Su mama basu dawo Zaria ba sai karfe biyu saura na dare ina zaune a dakin da
hasken wayata ina karatu mama tana kwance a gefena suka shigo don basu nufi gida ba
asibitin suka nufo kai tsaye .
Jin an turo kofa yasa na dago kai ina duban kofan dakin sune dasu yaya suke
shigowa hakan yasa na dan taba mama da barcin ba nisa yayi ba a lokacin ta tashi
muna masu sannu da zuwa.
Suka amsa da tambayan ya mai jikin aka basu amsa da saukin tun dai dazun din
barci yakeyi a hakan yadda yake bai kara wani abuba kuma har wanan lokacin.
Iya ta karaso tana fadin Allah ya baka lafiya jafaru ubangiji ya tada kafadan ka
a cikin mu suna amsawa da amin kafin ta juya gun mu tana fadin Salamatu ashe kina
nan mama ta amsa da ehh iya zuwa gidan ai baida amfani gara na tsaya a nan din tare
dasu.
Rahamatu kina zaune baki barci ba ke nan ta juyo kaina tana fadan hakan cikin
nuna kulawa nan mama ta karba da fadin .
Ina ai yar nan akwai kokari ko dazun din daya rikece itace tayi namijin kokari
akansa kafin likitocin su iso tayi dubaran datse hakoran nasa da cokali daya taune
harshen nasa ai duka don ba mai dabaran hakan acikin mu kowa ya rude.
Nan tashiga rabtabo masu labarin yadda abin ya faru zaune habu yakai a gefen dan
uwan nasa ya zuba mashi idanu yana kare masa kallo a cikin tausayi.
Can ya juyo yace ko dan kokon daya dan karba yanzu ya daina sha ke nan ko mama
tace ina ai tunda sukai mai alluran nan ya samu barci hakan nan daka ganshi yake
tun dazun din.
Saida kyat suka samu suka bar asibitin don mama data matsa masu suje gida su
huta tunda muna nan asibitin mu hakan yasa suka tafi.
Har iya dake son hutu a lokaci tabisu zuwa gidan yaya habu duk a nan suka kwana
ranan sai kawu da suka sauke gidanshi har lokacin ya kasa furta komai a garesu.
Tun da asuba na jona ruwa na gyarawa yaya jikinsa da taimakon mama na samu na
tsabtace masa jikinsa muka saka mashi wasu kananan kaya sai ya fito dan few dashi
don rama da yanayin jikinsa yayi.
Nabi dakin na gyara na fesa kamshi da yaya Auwal ya sayo ayi amfani dashi na
gyaro har ban dakin koda suka dawo daga sallah sun samu har nagama komai a lokacin.
Lokacin kuma yaya habu yayi sammakon zuwa asibitin shima don duba dan uwan nasa
daya kwana dashi a rai.
Ásmau ce data kira layina tana tambayan ya mai jikin nake fada mata idan zasuzo
suzo da koko don Allah ban jira me zatace ba na kashe wayan.
Sai wajajen takwas suka shigo asibitin da yaransu mun gaisa lafiya suna muna ya
mai jiki mama ta amsa da sauki nan rake fadin .
Tunda kunzo sai ku kamawa yar uwarku taje ta huta ke Asmau saiki zauna dashi zuwa
karfe biyu sai ita nusaiba ta karbe ki zuwa yamma don ita yar nan ta huta don
batayi barci ba a jiyan.
In yaso zuwa dare saita karbe ki atakaice dai mama ta raba muna wanan
taggadaman a tsakanin mu ke nan kuma hakan ya zaunu saidai ina jin hakan na fara
haraman zuwa gida don ina son dama gyara jikina robona da wanka tun da zan fito
gida zuwa wajensu a jiyan .
Ina saka hijjab nake jin suna zancen bashi kokon dasu da mama dubu na gama
kimtsawa na dauko jakata ina fadin zan tafi sai anjima bisa ga umurnin mama duk
suka juyo suna kallona zaki gidane naji mama dubu ta fada .
Ehb zanje na dan watsa ruwane mama na bata amsa take fadin ibrahim yana kusane ya
kaiki zan fita ko zan samu wanda zai saukeni na bata amsa sai naji tace min to
indai babu kowa saiki dawo habu ya saukeki ko ?
Nayi masu sai anjima na fita daga dakin cikin sanyin jiki cike da mamakin sanyi
mama a kaina lokacin ina fita na hadu dasu anty Barakha da yan uwanta nan muka
tsaya muka gaisa suna tambayan jikin dan uwan nasu.
Muryan Asmau naji tana kirana hakan yasa muka isa tare dasu take fadin mama ke
magana dani nashiga take fadin kada ki tafi ai ki tsaya abashi kunun nan don kece
kikafi sanin yadda yake kamawa idan anbashi.
Hakan yasa dole na kwabe hijjab dina na muka soma kamashi don mu dagoshi dole
saida na dan hau gadon na rungumeshi duk sun zuba min ido na soma da kiran sunanshi
a hankali ina mashi sannu.
A lokacin su yaya habu suka karaso dakin suma sai yayi kamar ya bude idonsa ya
kalleni nace ka daure ka dansha koko koda kadan ne don Allah yaya ?
Wani irin ajiyan zuciya ya sauke lokaci guda duk hankalin kowa ya dawo kanshi da
sauri ya habu ya karaso yana tambaya hankali tashe da yaya dai ?
Murya a kare nake fadin ajiyan zuciya ya sauke na kallo Asmau da jikinta ke rawa
nake fadin ta bani kunun ta miko min na kara fadin ka karba yaya don Allah kashe
kada ka zauna da yunwa haka tunda bai shiga ta roban da ake baka din.
Bskin nasa naga yana bukatan a kara wankewa hakan yasa na nuna mata ruwa ta miko
min na diba a hannu ina dan wanke bakin nasa .
Ya kara sauke ajiyan zuciya a hankali nake fadin ya taune halshesa ashe jiya har
yaji ciwo a bakin muka gama na bashi kunun ya karba sosai kamar cibi biyar aka samu
yasha ya habu yace in barshi hakana zan saukeshi a jikina yayi alaman a,a .
Ita Asmau ke fadin kamar ya girgiza kai fa nace hakane ya habune yace ki zauna
dashi haka yake nufi.
Nan anty barakha ke fadin Allah sarki yasan itace ta rikeshi ke nan ya habu yace
ya sani sosai idan tayi mai magana ai yana nuna ya ganeta.
Ikon Allah ai dole inda zuciyarsa take ke nan dole ya shedata ai mama dubu ke
fada hakan ta matso tana fadin sannu jafar ya jikin kai ya kara dagawa a cijin
karfin hali.
Suka shiga gaidashi daya baya duk daba amsawa yakeyi ba sun dai gaidashi din ne
kawai irin na al,ada da akeyiwa mara lafiya.
Yaron Asmaune aka shigo dashi yana rikici suyi lalshi yaki shiru mama ke fadin
ta fita waje dashi.
Hakan yasa na karbeshi daga inda nake zaune daidai fuskan uban na nuna mashi shi
ina fadin ga baba yana gaida kai yaya sai kawai ya bude idanunsan tarr akan yaron .
Da karfi saare ke fadin wallahi yaya ya bude idonsa hakan yasa duk suka matso
garesa a cikin farin ciki sai kuma ya mayar da idonsa ya lumshe a hankali.
A hankali ya habu ya leko yana fadin J ya jikin sai ya kara bude idon ya sauke
ga dan uwan nasa ya sake sake lumshesu ya bude ya kafawa Habu din ido na wani dan
lokaci.
Likitocine suka shigo dakin suka sameshi a hakan sunji dadi sosai a yadda suka
sameshi hakan yasa aka rage a dakin harni a lokacin na samu na fice na nufi gida.
Ban dawo asibitin ba har yamma don saida nayi barci bayan nayi wanka na kwanta
na samu barci sosai sam na manta da zancena da dan uwana Dage saida kira ya shigo
min a wayata yana fada min gashi ya shigo zaria hakan yasa na tashi da sauri ina
salati.
Kwatace yayi min inda yake maigadi na tura yazo dashi tsamo tsamo don da
ganinsa a tsorace yake saida ya hangoni tsaye kofan gidan mu ina dakon dawowansu
hankalinsa ya kwanta.
Nan falona muka zube na bashi abinci yaci yayi wanka saida akai sallah muka samu
kebewa dashi ya soma yi min bayanin abinda yazo dashi din .
Haka kuma ya sanar dani cewa sammako zaiyi ya koma washe gari don gida ba a san
nan ya nufo ba yazo min da abubuwa masu amfani sosai.
Nayi godiya nayi mai alheri iya abinda zan iya wanda yake ganin kamar na
tsomashi a aljanna ne tare mukaje asibitin dashi da yaya habu dana kira nayi mai
bayanin komai .
A saibitin ma ya habu bai boye ba don yace hardon mune ya toroshi ya kawo muna
maganin da za ayi amfani dashi ya fadawa yan uwansa haka tare suka koma zai kwana a
wajensu dasafe ya sakashi motar farko ya koma gida suma sun mashi alheri ya tafi.

Kuyi hakkuri din Allah ba yawa anty Samira gashi da fatan kinyi hakkuri da kanwarki
hakana yanayin jikine ya kawo hakan.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join
my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

6️⃣8️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA bWANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Duk saurina ban manta da zancen maganin dana hada na ruwan dokin da Dange yayi min
bayani ba a kwanaki bamu samu amfani dashi ba yayi wanan tafiyan daya dawo a cikin
rashin lafiya.
Rashin lafiyan daya zamowa kowa a cikin family na tashin hankali don ga mutum
kwance sharkaf baida wani moriya ba umm,uuumm asalima baisan a hanlin da yake ciki
ba na tsawon kwanaki.
Za a iyacewa dai kamar ya shiga common ne ko kuma jinnu sun shafeshi kamar yadda
hausawa kefada in mutum yashiga irin wanan halin da ba asan kansa ba.
A iya binciken asibiti sunce su basuga wani abinda ke damunsa ba saidai suna
hasashen ko kwakwalwansane ya tabu ko kuma ya bugu a kai hakan ya sameshi.
Bayan hakan su basuga komai a tare dashi ba bayanin da sukaiwasu yaya Habu ke
nan a karshe irin hakan wai amma zasu ajeshi acigaba da bincke ko za a gano inda
matsalan yake.
Jin hakan yasa hankula ya kara tashi sosai ga yan uwa kowa ya saduda a yanzu don
irin hakan yana da wuya ace mutum ya mike sai yawancin rai da rabon mikewa din.
Kowa kika gani fuska ba annuri don labari ya karade kowa ga abinda likitoci
sukace game dashi din sai koke koke ke tashi tsakaninsu.
A cikin irin hakan ne na karaso asibitin tunda na tunkaro naga yanayin
fuskokinsu sai jikina yayi sanyi na rasa wanda zan tambaya meya faru dakin na nufa
da sauri a zatona ko ya cikane na gansu a hakan .
A yadda na barshi haka nayi arba dashi kwance shambal saman gadon ba motsi na
gaidasu a tsatsaye na karasa bakin gadon ina kallon numfashinsa dake sauka wani
iri.
Muryan mama tudun wadace naji a gefena tana fadin yana nan ai a raye saidai
lamarin nasame keta kata muni kamar dai wanan ciwon bana asibiti bane.
Bana asibiti bane mama na fada ina juyawa wajenta rabin da take na sake gaida
ita da wuni nakai tsugune cikin girmamawa muka gaisa na aje jakata a gefe daya inda
nata yake .
Ta cigaba da fadin ni lamarin nan yana ban tsoro dazun don yadda gaba daya
yanayin jinyar tasa ya canza a yanzu yana sauyi da kamar iska ko hannu a lamarin.
Binshi nayi da kallo a yanayin da yaken tacigaba da fadin ni a ganina kawai abar
asibitin nan a koma gida dashi zaifi idan an koma sai a surka ayina gatgajiya dana
asibitin.
Abu daine da baka da iko a kansa da ina da ikon da zan fada aji dana bayar da
shawara a kwasheshi zuwa gida ayi na gargaji yafi zaman asibitin nan da akeyi a
cikin duhun kai.
Ni tunda naga sun kwashi jiki sunyi tafiyan nan shekaran jiya nasan akwai inda
suka tafi game da lamarin jikin nan nasa amma kin san ba fada muna kome ke akwai
cokon lamarin zasuyi ba nidai abinda nagani kawai su kwasheshi a koma gida aje ayi
na gargajiya zaifi wanan zaman da akeyi nan.
Mikewa nayi daga inda nake tsugunne a kusa da mama din zuwa bakin gadon ina
kare mashi kallo zakice ba Jafar din nan bane da kikeson karawa kallo duk ya fita
hayacinshi.
Ga kamsuba da suka fito mai a fuska yayi wani baki sai dogon hancinsa kawai zaki
hango zaram bandashi ba wani abu daya rage a cikin jikinshi.
Abin dai dana saba nayi mai addua donshi duk wani mosoyinsa zai mai a lokacin
donshi yafi bukata garemu.
Yayin da zuciyana yake wani irin halbawa a cikin fargaba da tashin hankali don
gaba daya nikan na sallama a raina mun rasa yaya a wanan lokacin don gara wancan
ciwon na baya yana a cikin hankalinsa wanan kam baisan wanda yazo ba baisan wanda
ya tafi ba.
Sai bayan tafiyansu mama dan yanzu dagani sai maman tudun wanda da iya muke
kwana su yaya kwana biyu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login