Showing 87001 words to 90000 words out of 328222 words
Chapter 30 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
shan magani bayan maganin na rage yawansa nace kuma ya kare a karshe
don haka na daina wanan sintirin na kama kaina.
Idan na fita tun safe ban dawowa gidan sai ana gab da magariba zan shigo inyi
sallah in kwanta sai kuma da safe idan zan fita zan lekasu inmasu ya maijiki wata
ranama don sammakon dana tsiri yi nakan samu yana wanka a lokacin bai fito ba na
gaida mama in juya abina infita.
Itama Nafisa ta tafi bukin dangin mamanta a kauyen nan zaria din wani gari da
ake kira da fanbeguwa mahaifiyarsu yar can garin ne sun kuma kwasa sunje buki.
Sai ya koma daga mama sai yan mantata suke faman dawainiya dashi don sune dama
doleshi ai mu karan taimako mukayi masu amma Saare bata gane hakan ba.
Duk da ya danji dama yana iya wasu abin da kansa don bawan Allah nan Allah ya
bashi karfin halin ciwo da dauriya a kwancen dayaji dama a haka yake gudanar da
bussiness dinsa abinka da rai da guri.
Amma sai hakan ya zama gajiyarwa ga kannen nasa dukkansu kowa na korafi a gefe da
basu samun hutu ko kadan daga ayi wanan sai gyaro wancan mama ke sakasu.
Anty salimace tashigo part din yar uwata a gajiye tana zama take fadin wayoni
maria bayana zai tsage ?
Anty maria take fadin garin ya ke kuma ta dan kai kwance tana fadin ke matar
yaya kinsan irin wahalan da mukeyi kuwa mama bata bari mu huta sam wallahi dakin
dan zauna yanzune zakiji tace tashi kiyi wanan ko dauko abu kaza ki gyara.
Duk wanan mai bakar aniyarce Saare taja muna haka wallahi ni nasan Ramaah da
Nafisa fushi sukayi din abinda saare din ke masu.
Ai wani abu tayi masune maria ta tambaya tace bata fada maki ba ko dadina da
Ramaah ke nan ai bata faye irin surutun nan ba ita.
Maria ta sake fadan wani abin ya farune tsakaninsu tace ai kinsan halinta da
sakin magana Nafisa kuma ta nuna mata ko ita waye.
Nasan hakan da Ramaah ta gani yasa dauki zancen ta daina shiga itama tana aikin
ladanta gabadaya ko dazun nan wallahi saida yaya yayi min zancen sun daina shigowa
kome ya faru ?
Sam bata fada min komai ba wallahi kinsan halinta da zurfin ciki ai haka kuke
fulani sai dai in kun tashi fada baku duban bakin gatari kuke sarawa.
Au sheri zaki min ke nan kuma yanzu ai naga kema da baki iya hakan ba da yanzu
kin bar gidan nan akan sherin matan gidan nan.
Nice na fado falon da sallamana ina ganin ta nayi murmushi na karasa shigowa ina
gaidasu da gida suka amsa min take fadin.
Cigiyar ki nazo yi Ramaah yaya yace kun dauke kafan da part dinsa bai san
dalilin hakan ba a yadda na kula kuwa hakan ya dan dameshi.
Ni kuma aiko dazun da zan fita nashiga mana da safe yanzun nan kuma dawowana ke
nan ai ban zama yanzu zamu soma exam yasa hankalina ya dauko.
Kyaleshi kinji kinsan halin yaya J ai da damuwa da wanda ya damu dashi yanzu
dan kulashon da kukeyine yaga kun daina shine yake wanan magana shi haka yake da
damuwa da mutane shiyasa ake saurin kamashi.
Dan kallonta nayi na kau da kaina gefe ina wasa da Abbati daya zo ya fada jikina
ban jima ba na mike da yaron zuwa ciki.
Nasan dai ta fita tunda naga anty Maria ta shigo dakin gab da magariba take
tambayana meya hadani da Saare na dago ina fadin Saare kuma ?
Yaushe ba abinda ya hadani da ita take fadin in daiyi sannu ita ba don mama da
ya habu ba ba zata yarda ina sintiri a part din yaya J ba.
Tunda tasan halin matanshi ba mutuncine dasu ba hakama Saare din na dai share
zancen zuwa don ban bata amsa ba.
Saidai a kasan zuciyana ina tunanen me akace ya hadani da itane wai tunda bakina
da nata dai bai hadu ba duk bare baren da takeyi a kaina din.
Tunda bata nuna dani takeyi ba akan me zan tsaya nuna mata nasani balle yanzu
dana kama kaina da shiga part din da sunan jinya.
Shima kuma addua muke mashi Allah ya bashi lafiya ya mike don ba mai fatan ya
tabbata a hakan da yake din.
Na share hakan kwana biyu kuma ranan weekend na gama wanki nayi wanka sai gata
again wai yaya J yana kirana.
Saida na shirya naje suna falo zaune na shigo nake gaidasu da kwana suka amsa
min yake fadin Rahama lafiya kwana biyu na daina ganin ki ?
Ita Nafisa ance tayi tafiya amma ta dawo jiya sai a lokacin ma nake jin cewa su
Nafisa din sun dawo daga tafiyan.
Nake fadin ba komai yaya exam zamu soma yasa ban zama yanzu exam zai hanaki
shigowa ki duba yayan ki Rahama ?
Sai nayi kasa da kaina bance komai ba don mama data kura muna ido tana sauraren
mu itace ta kawar da zancen tana fadin yace kiyi mai irin ferfesun da kikayi ranan
ya tsaya kuma tareki da tambaya.
Wayyo Allah da mama ta sani ko shi yaya din da basu sakani wanan aikin Allah
bai hada jinina da kifi ba duk bafulatanin asali haka yake inba mu fulanin zamani
ba .
Sam bafulatani bai cin kifi ace zaki dauki spoon ki motsa miyar kifi ki kuma
dauka ki motsa miyar naman dashi ko one spoon kikai a bakinki a ranan idan kin soma
amai kamar zaki amaye duk hanjin cikiki.
Amma don kawaici da alkunya haka na mike zuwa kitchen din nasu na soma aikin
hada ferfesu din ina gamawa na bude fridge an kawo kifi mai yawa da gani sabon
zubawa ne ballo na wanke na hada.
Ban fito ba saida na kammala komai na zuba na nufo falon dashi na samu mama bata
nan ta fita saishi da wani abokinshi a falon suna hira.
Sallama nayi na aje tare da gaida abokin nasa ruwa naje dauko mashi naji bakon
na fadin kai mutumina wai dama kayi sabon aurene ban sani ba ?
No wander naga alots of changes a tare dakai da kuma yanayi yaushe ka auri wanan
african queen din banda labari ?
Yanzu daka sani ai bai baci ba gashi kun gaisa amma gaskiya ba ganin fuska ba
wanan karo kan ka tsaya ka zabo abinda ya dace dakai.
Allah ko ya fada hangoni dayayi tafe ruwa na dauko masu da drinks na aje gaban
bakon daketa faman sabarin baki ga abokin nasa.
Godiyana ga Allah banyi kwaron hannu na dafa kadan ba tunda nasan mama da
yaranta na wajen sai kuma Allah ya turo wanan bakon nasa yazo.
Furcina yasa bakon dan kallon mu da nake fadin nagama yaya shike nan ko akwai
wani abin naji yace jeki Rahama zan nemeki idan mun gama.
Zo amarya mana kada ki tafi ban sayi baki ba bayan abincin da kika karrama ni
dashi haka tun ban ciba kamshi ya danne hancina kudi ya dibo daga aljihunshi ya
miko min na dan dubi yaya din yai min alaman dana karba.
Naji bakon na fadin kai akwai irin matan nan har yanzu ashe gaskiya J ka dace
kwarai wallahi kudin ma sai ta tambayi izzinin ka zata karba ?
Gaskiya kayi dace Allah yasa abin yacigaba a haka ni abokinsane sosai tare muka
taso dashi saidai bani zama a nan yanzu shine ya rabamu har baki sanni ba na mika
hannu kawai ina fadin wawa sai zuba yake haka na tsani namiji irin haka wallahi.
Na fito na hango Saare tsaye kofansu tana waya ban sake kallonta ba na shige
part din mu da kusan a jere suke a barin dama dana yaya J din sai dai akwai dan
tazara sosai a tsakanin su.
Inda part din su mama ke barin hagu yana kallon nasu yaya din da wanan dayan part
din da ake cewa part din yaya yazid ne shi ko yaushe yana rufe saidai da yarsu tazo
daga zamfara kwanaki aka bude mata ta sauka ciki da yaranta.
Sai tsakiya dake da fili tsakanin gidajen duk girman wanan filin da haka nake
tashi in shareshi tas amma yanzu na ba kaina lafiya ko ita wace akace yar aikin
bata iya sharan wajen yanzu sai almajiraine ke zuwa kwana bibiyu suna sharan wajen.
A basu abinci da kudi garama namu part din muna sharansa har wajen gidan mu zaki
gashi tsab dashi saidai a tsarin ginan yanzu na ya J yafi sauran girma don filin
dake bayanshi an hade dashi anyi gina da aka karawa wajenshi girma sosai donshine
nasa part din ya fita daban dana sauran.
Ina zama saare na fadowa part din saida gabana ya fadi dana ganta na dauka wata
tsiyar tazo yi min sai naji tana fadin .
Ai bansan kina part din nan ba Ramaah dana shiga me kika bar su yaya sunayi da
zaki fito nace kila abinci zasuci na dai dafa mashi taliya fara da ferfesun kifi
yace ayi mashi.
Wai kinsan wanan yaya mansur din abokin yaya saurayinane kuwa ya tambayeki ni ko
ince kinji suna magana a kaina don Allah ?
Wallahi banji ba ni ina kitchen na gama na aje masu na barsu suna hira a wajen na
fito sai naji tace barin koma na gani ko sin gama ?
Har ta gama surutunta ta fita maria bata daga kai ta kalleta ba sai bayan ta
fita taja muna kofa maria din tayi tsuki tana fadin wahalalla kawai.
A haka zata kare ance ko saurayin arziki bata dashi ina ganin shine na Abujan
data lekewa tana so din nan yazo ?
Itama ke sonshi mama bashi ke sonta ba aiko akwai aiki wallahi gara kaso wanda
ke son ka ba wanda kake so ba anyi ma kina so yana so yaya aka kare balle wanda
kake cusa kanka wajensa.
Kudin daya ban na aje ina fadawa yar uwata din abinda yace nace shifa ya dauka
aure yaya yayi sai zuba yakeyi harda miko min yana fadin gashi na sayen bakine
tunda bai san lokacin da akai buki ba.
Maria tace don bai sanki bane yasan duk kannensu ai ba zai dauka kema a gidan nan
kike zaune ba aje kudin nan ki nunawa mama tunda ta dalilinsu ya baki shi.
Mama kuma na fada ina kallonta tace to Ramaah ina gudun abin maganane wallahi
kada yaya ya fada masu abindake nan suce kuma wani abin.
A,a wallahi saidai inba yaya din inji me zaice ai dukkansu kyaleni sukayi a
kitchen suka fita da bakon yazo don me zan basu nikan ba zan bata ba don tsab zata
karbesu wallahi.
Nafisa fa tace in anyi muna abin arziki mu daina nuna mata tunda karba takeyi
bata bamu sai naji tace ke Nafisace Ramaah ?
Waima ko sai yaushe zasu dawone mutumiyata naji kewanta sosai wallahi na zata
kwana biyu zasuyi kawai a can ai sai gashi suna batum share kwana goma.
Sun dawo jiya naji mama tana fadin ance sun dawo tana garin nan yana da wuya
dama ta dawo gidan nan gaskiya don anty saare din dake gida yanzu nasu baizo daya
ba.
Don cewan da takeyi wai don kwadayi an mamaye komai anayi ta ina za a bari matan
yaya su dawo a yanzu shine sukai fada har tayi fushi lokacin ta kwashi kaya zata
koma gida saida akaiwa Saare din fada.
Kingani ko dama saida nayi wanan tunanen a raina don wanan abinda kukeyi za a
dauka da wata manufa ake hakan kinsan mutane yanzu da sheri.
Yar uwarsu ke nan Nafisa sun fadi hakan a kanta ina gake da ba yar uwarsu ba ai
sai sufi camfaki ga zancen don Allah kadai yasan irin abinda take fadawa matanshi
yanzu tunda suna tare.
Banjin tsoron duk abinda ta fada saboda nasan ban aikata hakan don kudi ko don
wani abuba saidai ban jimirin daukan wullakaci a kan hakan yasa na kama kaina tun
bata kawo kaina ba.
Ita din yar uwar ya Habu banson nayi rikici dasu don yana mijinki idan nayi
hakan bartabanki ne zai tabu a wajensu.
Shiru tayi min cikin damuwa ta kasa ban amsa ga zancen ganin haka kawai na mike
nabar falon da kudin a jikina don ba zankaiwa mama din ba kome za ayi kuwa tunda
nice akaba.
Ranan ya Habu ya dawo daga tafiya ya dawo da abin arzikinshi kamar yadda yake
akida wajensu duk garin da sukaje zasu sayo abinda ake amfani dashi garin.
Za ,a sayo azo dashi gida ayi amfani dashi saidai gajiya ya hana a raba ba sai
washegari ya fito dashi daga motansa .
Nice ya kira na dauka zuwa part dinshi danasu mama duk da ina kyautata zaton
mama tana part dinsu ya J a lokacin.
Iya na sama zaune na gaida ita da kwana ta amsa tana fadin yar nan za,ace baki
gidan nan wai meke faru hakane kun dauke kafanku gaba daya da wajen nan.
Babu komai iya ina nan saidai a yanzu ban faye zama ba ina zuwa makarantane kin
sani ai.
Kayya yar nan akwai dai abin da akai maki kika dauke kafanki haka ni zuwanki
yafi min zuwan wa yan nan marasa lissafin ai ki fada min idan an maki wani abin ne
na dauki mataki kan maishi .
Nace iya ba komai karatune yasha min kai duk kwanakin nan sai naga ta yafutoni da
hannu alaman in matso kusa da ita na je din kuma ta tausa murya tana nuna min dakin
su salima tace.
Ita wanan sakariya tun jiyan ta shige daki bata fito ba wai abokin yayanta take
so kiji min ja,iba baki bari a nemiki ba sai kece mai neman miji don sakarci irin
na saratu.
Iya tana sonshine tace jam,jam ai mace takan jira furtawan namijine ba ita ta
nuna hakan ba shine yayanku Jafaru yayi mata tas jiya da dare ta shige daki tana
fushin banza.
Ni dai na fita ina dariyanta don yadda tai maganan sai kayi dariya tana kallon
labulen dakin zakice saarece a wajen tsaye lokacin.
Nasan takaicin hakan tsohuwar taji yasa take neman abokin hira ta amaye abinda
ke cinta a zuciya don basu shiri da Saratu sam suna konewa junan su mai ko yaushe.
Ban,san ya akayi ba na dawo daga school na samu Asmau uwargidan ya J ta dawo
gidan inda na gane hakan yarta dana gani tare da Abbati a part din mu nake
tambayan ita dawa tazo maria tace min ita da uwarta sun dawo dazun ita ta kaduna
iyayyenta sunce sai karshen sati zata dawo.
Nasan suna kara shiri irin nasune don ance ba karamin shige shige suka iya ba ko
wanan dawowan nasu yabawa kowa mamaki don haka kawai akaji mama tace su dawo
dakunan su.
Ance ya j din ya nuna bai son dawowan su amma mama tace aiba tafiyanshi sukayi
ba natane don haka dole su dawo dakunan su.
Sun dai muzanta na fada ina nufar dakin mu naji tace dani ga wanda yasan hakan
ba ai tun karfe biyu tana gidan nan wajen salima nake jin tace Saiba basu gama
shige shigensu bane a can.
Amma wai mijin yace idan ta wuce gobe ba dai gidansa ba nasan zata dawo ga
goben itama ke nan gamu dai gani ai duk fa sun lalace ba kamar yadda suka tafi ba
daga ita har yar nata .
Ban fito ba ban kcuma da niyar zuwa yi mata sannu da dawowa ina daki ko falon
yar uwata kika shigo ba zaki ganin ba don ban zama a falonta sai daki saboda ya
habu dake garin.
Kamar yadda yaba da umurni sai gata tashigo garin wajajen karfe biyar na yamma
bata dade da isowa ba ni dawo daga school motan gidansu dana hangone yasa na gane
cewa Saibace ta dawo.
Haka kuma na samu anty Nafisa itama ta dawo gidan nayi mamaki kwarai data dawo
gidan a lokacin a zatona ba zata sake dawowa da sunan zama ba.
Wai ashe shi yaya Jafar da yaya Habune da sukaje gidan suka dawo da ita nayi
mamakin jin ya Jafar din ya fita a ranan zuwa cikin gari dashi da dan uwansa lalai
sauki ya samu sosai gareshi tunda har ya iya fita zuwa cikin gari.
Ina sallah magariba naji shigowan su anty Salima da Nafisa part din mu suna
dariya ban fito ba saida na idar duk da naji suna tambayan ina nake ?
Suna dariya wai iya tana can tana sakin magana hakan yasa suka gudu zuwa part
din mu kafin ta hada dasu ta zage.
Daga kofa na tsaya ina fadin anty Nafisa munyi fushi ta juyo tana fadin kada ki
fushi Ramaah kina raina wallahi wayarkice ko yaushe mutum ya kira zaijita a kashe.
Haka dai yaya yace dazun salima ta fada dazun ya kira layin ki wayar bata shiga
ai yace bai ganki ba duk kwanakin nan nace kina nan sammako kiyi kina fita zuwa
school.
Yadda maria ta kalloni yasa na kawar da kaina gefe daya nima dai naji zancen
wani iri balle yanzu da matanshi suka dawo gidan hakan zai iya kawo zargi a
zukatansu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,
3️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN