Showing 279001 words to 282000 words out of 328222 words
Chapter 94 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
sai shi zaisa hannu don gashi mai karfi ko zai iya fada da ubansa.
Ba hakana bane yaya yayi kuskure don Allah da gani a jigijce yake a barshi yaje
ya huta bari nasa maigadi ya bude mashi dakin baya guda ya zauna kafin asan abinyi.
Da sauri naji yaya din yace No don me zai zauna muna nan baga can gidan ba ya
zauna mana da iya nace don Allah yaya tunda yazo nan din ka barshi ?
Kayi hakkiri ya zauna nan din bai min magana ba na dade a zaune wajen ina
sauraren amsan shi baice komai ba har lokacin.
Haka yasa na mike ina fadin inka gama taso muje kaga inda zaka sauka din na fice
ba tare da nace komai ba.
Shima kuma baice komai ba sai wayanshi da yake duba ya fita batun mu daga bayan
mu akwai dakuna hudu kamar boys quaters a gidan da suke rufe sai maigadi dake dan
amfani da guda don adana abubuwansa.
Tambayasa nayi ina kayanka ko suna can gidan ka bari yace haka nazo mummy don
bai bari na shiga gidan ba balle in dauki wani abu .
Ok shiga kayi wanka ka huta zuwa anjima kazo ka fita nan titi ka samu kananan
kaya ka saya na juya na bar wajen ina jin yana fadin nagode mummy nagode.
Na koma ciki na samu yaya a zaune zama nayi ina fadin an bude mashi dakin
tsakiya zai zauna a cikinsa shiru yayi ba amsa hakan yasa naja bakina nayi shiru a
cikin tsarguwa da hakan da yayi min din.
Kamar daga sama naji muryanshi yana fadin ke har yanzu baki fahinci mutanen nan
ba naga kina kokarin jawo muna yaron nan a gidan nan banson wani abinda zai kawo
muna fitina ko tsegumi ki barshi can ai kakansa tana nan yaje can wurinta ya zauna
mana don me zai nufo nan gidan haka kai tsaye.
Shiru nayi ina nazarin zancensa a kaina tabbas gaskiya ya fada don ba mutanen
arziki bane alheri sai ya zama tsiya a wajensu.
Zama na gyara ina fadin ni naga ba zaizo nan mu koreshi ba ai yaya tunda yazo
din sai ayi hakkuri don kai ba za aga laifinka ba sai nawa tunda yariga da yazo
kayi hakkurin hakan don Allah.
Bai kira yace dasu yaron na gidansa ba hakan yasa hankalinsu ya tashi lokacin da
uwar ta bugo waya tana tambayan ko yaron yazo nan ?
Duk hankalinsu ya tashi haka ba wanda yai dabaran kiransa ni dai ganin har
magariba banga yana shirin komawa gidan can ba sai mamakin hakan da zaiyi nakeyi a
zuciyana.
A bangaren yaya barakha an nemi Aminu a nan gusau ba a sameshi ba har washegari
hakan ya daga mata hankali ta bugo waya nan zaria tana tambaya ?
Mama Dubu hankalinta ya tashi har dare suna buga waya gusau din suna tambaya ko
an ganshi sai ace har yanzu dai ana nemansa ba,a sameshi ba.
Ga jafar da suke sa ran shigowan gidan har goma na dare ba labarin shi hakan
yasa mama sa a duba mata ko yazid ya dawo aka dubo yana gida.
Da kanta taje part din yazid din ta sameshi tana tambayan malam fa don sunan
malam Jafar marigayi da sukai jahadin da,awa a cikin kasa yasa duk wani Jafar
yawanci ake saya sunan nasa a cikin girmamawa ga malam Jafar din dake tashe
alokacin.
Yagane dan uwansa take tambaya donshi ake kira da wanan sunan na malam din take
fadin malam fa yace yana lafiya ta amsa da aina sani tunda naji shiru ?
Tambayanka nayi har yanzu bai shigo ba kai gaka ka dawo gida ko da kansa zai
dawo yau ya kamata ace yana nan ga zancen yaron nan da har yanzu ba a gansa ba ko
za ayi wani abu a nan ?
Mama J aiba zai dawo gidan nan ba yau ban ma tsamanin nan kusa gaskiya kin ga a
yan kwanakin nan yadda ya koma kuwa ?
Dakata don Allah nasan duk bakin ku daya shi zai fara yace bai dawowa gidan nan a
yau da kuwa na sameshi a can naci masa mutunci.
Acan kikace mama kwarai ko kana tsamani ba zan iya bane kagani ya dan dubeta ya
kawar da kai ya soma tafiya yace zaki iya masa hakan nasani to kira min shi yanzun
nan .
Ko kaje kazo min dashi yanzu gidan nan yanzu fa mama gomafa ta shude da nan da
can ai dayane nagani meye ruwanki da zamanshi can din ke ?
Yazid kai abin da nace kada ranka ya baci dani a wajen nan Ok yayi bari na
kirashi naji in zai dawo sai naje na daukoshi din.
Ya kira wayansa bai shiga ba haka yasa ya fada mata gaskiya itama kuma taji
matar computer tana sanar da hakan a wayan .
To kinji wayansa a kashe yake yanzu yaya ke nan kaini gidan idan ku ta shanye
ku aini bata shanyeni ba har ita karamar yarinyar ta isa ita da masu taimaka mata
din kar nake kallonsu.
Bai haifawa jikokin fulani diya ba balle suzo su mallake min yaya da raina da
lafiyana ina kallo shi kuma J far din zaizo ya sameni ai zai jini.
To bari in shirya in fito ya fada ya koma ciki itama ta juya zuwa dauko
hijabinta don tafiya ya shige ciki yana dariya.
Har ta fito yazid din bai fito ba nan kofa ya tsaya yana kallonta yana gyara
rigansa hakan yasata daga murya tana kirasa a hasale tana fadin zata saba mashi fa
idan bai fito sun tafi ba.
Iya dake cikin tana jin sautin muryan mama ta fito tana fadin lafiya anga yaron
ko don tana cikin damuwan rashin ganin yaron a lokacin.
Karan budan kofan da iyan tayi yasa salima dake kwance tana charting ta biyota
tana fadin iya lafiya ?
Iya sai fadi take anganshi ko cikin rawan jiki a lokacin Yazid ya karaso yana
fadin mama shiryawa fa nakeyi don nayi shirin kwanciyane kika zo .
Nace kunga yaron ne iya ta sake fada karo na uku ba a ganshi ba iya gidan Jafar
zamu mama ta dauko shi ya dawo nan.
Jafar kuma ta daukoshi kamar yaya iyan ta tambaya to ni dai tace in kaita ta
daukoshi can din wai nan ya kamata ya kwana a yau ?
Dubu iya ta fada cikin mamaki tana kallon yar nata da wani irin kallon dake
baiyana mamakinta karara ga yar nata dake wanan magana.
A,a iya rashin hankali yake son ya tafkawa mutane waishi ga salamame zaije gun
yarinyar nan Rahama ya tare don rashin hankali ya daukarwa kansa zunubi.
Zunubi a wajenwa Dubu wajen ki ko wajen wa zai dauki zunubin da kike fadi dubu ?
Dubu dubu kanki daya kuwa da yaron nan yayi wata da watanni a gidan nan meyasa
bakice a kwashshi a kaishi can ba lolacin kada ya kwashi zunubi sai yanzu ?
Iya wanan ai lalurane itama din ai tana tare dashi a nan kuma, zaman nan din
aida ita akayishi da yanzu zatace a maimaita mata hakan da akayi ?
Ta fada maki cewa sai an mata maimaicin hakan a gidanta wai dubu meke damunkine
haka wai ?
Kai Yazidu koma dakinka ka kwanta don ba inda zaku a cikim daren nan da wanan
rashin hankali na uwarku don kina mara hankali zaki gidan surukarki da wanan zance
na hauka idan kinje kice masu me yanzu ?
A,a iya ki bari nayi maganinsa tunda yana ganin ya isa ne yanzu har zai kwashi
kafa ya koma can ya tare bai fadawa kowa ba ?
Kamar yaya Dubu don ni ban fahinci wanan rashin hankalin naki ba har yanzu waiko
dubu akwai hankali akanki kuwa ?
A fahintana Dubu kamar kishi kike da yaran nan fa don abin nan da kikeyi bana
kai sake bane dubu ban taba gani ko jin irin wanan rashin hankali naki ba gaskiya.
Iya yanzu sai a kyaleshi yaeinya karama tana juyashi ana kallo ba a dauki
mataki ba jinyar da tazo nan tayi nasa ai yan uwanta dashi ta cuta ga hakan ?
A,a ba juyashi tayi Dubu mulkeshi tayi iyakar juyawa dai ko aiki ya sameki babba
idan kikace kishi zakiyi da matan yayan ki ?
Duniya da mutanen cikinta suna shirin maki dariya jeki dan mutuncin dake gareki
a idanun yarinyar nan ya zube aikin banza aikin wofo kawai da rashi kamun kai ?
Kai yazidu koma wajenka ka kwanta ba inda zaku ni naga rashin hankali yau a
filin Allah ashe ke ba zancen yaron nan daya batane ya dameki ba shirmenki kike a
zuciyarki ?
Yau ni naga hauka na rubutawa a jarida Dubu baki tsoron bakin duniya ko wanan
halin da kikewa yayan mutane ya tambayeki nan gaba ?
A,a iya don Allah abar zancen nan baikai har kiyiwa yaran nan baki ba a gareni
yaje ya zauna tunda ya zama sallamame a wajenta.
Karamar yarinya kamar wanan yau zata juyawa Jafaru hankali yana wanan abin a
gaban kowa iya dole inyi magana abin yayi yawa dama an fadi matan fulani haka suke
idan sun shigo waje.
Kai Yazidu dawo ka kaita ta dauki matakin da zata dauka iya ta katse mama din
dake magana ta juya tabar wajen yazid kuma bai ko juyo ba ya shige part dinshi.
Washegari da safe kodana tashi kamar kullum na hada mai abinda zai rike mai
ciki kafin mu gama breakfast ya dan kwanta.
Hakan da nake mashi ba karamin kara mai lafiya yake masa ba ga sunan Allah da
zaibi jikinsa da ruwan zamzam ga kuma kuzarin da jikinsa zai dauka yana daga cikin
abinda Yazid ya hango na annuri a garesa yake fadin yaga ya canza mashi lokaci
guda.
A gurguje nake aikina ba don wani abu don kawai nasawa raina cewa suna iya zo
min gida a ranan don Aminu dake nan wajen mu.
Mun gama na jera mai a kasa don na fahinci a yanzu yafi son ci a kasan don kamar
baijin dadin zama saman kujera yaci abu a yanzu da baida lafiya din nan.
Na gama na shirya kaina na umurci biba data jetayi wanka har tace ta dauki
abincin Aminu takai mai ne da sauri na juyo nace a,a ki barshi nan kitchen har ya
shigo.
Ba son komai nace haka ba saboda ban manta wani case din daya faru akan wata uwa
dake tura yarta kaiwa saurayin gidan abinci ba.
Amma haka mutumin yayi amfani da wanan daman ya batawa wanan matar yarta akaita
case din karshe dai an cuci yar da uwar don har yakai ga dirkawa yarinyar ciki dole
aka haifi dan hakana kuma yarinyar karamace sosai a lokacin.
Wanan ya tsaya min a rai yasa nake kafa kafa da yar mutane ban yarda ko maigadi
tayi wani dogon mu,amula dashi iyaka gaisuwa a tsakaninsu.
Gareku mata wanan abin ya faru da gaske wallahi mutum koke kika haifeshi yanzu ya
zama dole a gareki ki saka ido ga mu,amulansa na yau da kullum Allah ya tsare ya
kare amin.
Wasu dogon riga na saka a jikina _onion_ colour da adon zaiba har kasa anyi
rigan mai dagware a sama kamar alkyaba yana daga cikin dinkin da anty salma tayi
min na aure a Abuja.
Zaune na samu yaya a dakin na shigo ina fadin ka tashi ashe yake fadin yazid ya
tayar dani da waya wai yaron nan sun dauka ya batane ashe basu san yana nan ba ?
Aminu na fada cikin mamaki yace shifa kiji ba yace muna ya tafi can ba ashe
karya yakeyi ke nan nan yayo direct wajen mu.
Ikon Allah amma cewa yayi ai yaje ya samu baka nan ace kana nan yace karya
yakeyi yanzun ka fada masu yana nan dai ko ?/
Na fada masu ya fada a sanyayye nasan zasu shigo yanzu ai tunda sunji yana nan
amma Aminu bai kyauta ba daya dagawa mutane hankali haka ?
Bar dan iska kilama abinda ya fada karyane barshi kawai bari suzo din muji ai
nasan za a fada masu abinda yayi ya gudu nan yau din nan zai bar min gidana.
A,a yaya na fada da sauri ya katseni cikin tsawa da fadin ke karki tsoma min
baki cikin maganan su ki barni kawai dasu.
Nayi shiru kafin nace wanka zakayi ke nan yace haka naso na mike zuwa bandaki na
hada mai ruwan wanka ya mike ya shiga saida ya gama na cude mai jiki da ruwan addua
ya saka kaya muka fito falo.
Mun zauna ke nan na zuba mashi ya fara ci biba tana gefe daya tana cin nata don
sosai muke sakewa da yarinyar harshi sukan dan taba hira wani lokaci da ita.
Muka ji sallaman Salima shigowa gidan ashema dukkansune tafe sai Asmau ce sai
matar Yazid suka bari a gida lokacin.
Ban daina mika mashi fruit din dana gyara ya zama juice ba da nakeyi na amsa
sallaman nata ba tare dana juyo ba suka karasa shigowa gidan gaba dayansu.
Nagama na dago ina fadin sannuku da zuwa ina kwanan ku a cikin jam,i bansan
waya amsa ba ko wanda bai amsa ba a lokacin don na basu bayane ina zaune amma naji
muryan yazid.
A,a a a mutumina inafa zaka koma gida wanan riritakan da yar nan keyi shine ka
gudu ka barni ba azo cin dadin amarcin dani ba ?
Iya ba gaki kinzo ba yanzu saiki zauna muci dadin yanzu kada in kwareki kaidai
tunda ina da rabo a cikin na yanzu sai in zauna inci amma zan barwa amaryaka aronka
kwana biyu ai don tasan ina da kara amma fa a tuna damu muma kada a shagala suka
kwashe da dariya.
Ai fakaice baiyi iya gara ki fito mashi fili tasan yabar wasu a gida ba nan
bane kawai gida a gareshi don shi naga hanyar konewa ya zaba yanzu.
Bani ganin hakan cikin zuria,ata insha Allahu daidai lokacin namike a kusa dashi
zuwa gaban mama na durkusa har kasa ina gaida ita.
Kamar dole ta amsa min ba kin dawo lafiya na juya wajen kawu na gaidashi sai
iya dake fada na rike hannunta sai lokacin ta dakatar da zancenta take fadin.
Ke dai yar nan kin dawo lafiya yaya kika bar yan gidanku duk suna lafiya dai ko
naso nazo banda wanda zai kawoni in maki sannu da zuwa.
Iya ba komai na fada ina mikewa tsaye na nufi hanyar dakina muryan ya J naji
yana fadin ina kuma zaki ?
Daki zan tafi har ku gama na bashi amsa sai yace abincin fa wazai ban kizo ki
zauna muci kema baki karya ba ai bari dai ku gama na fada.
Kizo ki zauna nace me zamu fada wanda ba za aso kiji ba iya na fadin zo ki zauna
abinki ai ba komai zamuyi ba ballema ina zata iya ?
Yadda yake magana hakan yasa na dawo na zauna a inda na tashi duk suka zuba muna
ido gashi sai magana yake min a cikin rashin damuwa da suna wajen a lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/25, 12:44] Aisha Srtr Mt: MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
8️⃣7️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Aminun yana inane mama ta kawar da shirun dake falon kaina a kasa ya J yace da ita
ga uwarshi nan itace ta bashi mafaka a nan .
Don ni tun jiya da yazo gidan nan ban yarda dashi ba koransa nayi don yadda yazo
min nan a gigice sai hakan bai kwanta min ba.
Itace ma ta saukeshi ta bashi wajen kwana a nan gidan dan idan tannei zai koma
tun a jiyan ai da bai kwana a gidan nan ba .
Wai dama ita Rahama tasan yana nan shine bata kira ta sanar da mutane ba don
isa kuma ta ajeshi tabar mutane suna wahala hankali tashe ?
Ke zanci abu kazan ubanki wajen nan ke meyasa kike yar iskane wai kamar kinfi
kowa baki ban hanaki idan manya suna magana ki tsoma baki a ciki ba ?
Me kika dauki kanki ko kin fi wanan biyun ya nuna salima dani baki da suka kama
kansu agaban manya basuce komai ba ?
Na dago kai nace ya Yazid don yaya ya kori Aminu ni sai na yarda ya bar nan din
a yadda na ganshi nasan inda zai nufa kuma idan ya bar gidan nan ?
Kwarai kuwa kedai yar nan kinyi daidai haka ake son macen arziki ta kasance dama
ta kula da mijinta da kowa nasa wanan shike nuna halin alherinta .
Bar sakaran nan da bata san komai ba sai rawan kai da iya makircin banza meye na
ganin laifin yar mutane a nan daga ta taimaka muna da bata rikeshi ba yanzu har
muzo a sameshi nan.
Bakin saratu shi zaija maki matsala bansan irin bakin wanan yar ba a rayuwana
yaron nan a nemansa an kuma ganshi a inda ya dace .
Barta kawai dai idan itace mai mugun halin nan irinsune masu iza dangin miji
nisa da dan uwansu wanan zata iya