Showing 159001 words to 162000 words out of 328222 words
Chapter 54 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
zancen salima
na jiya don Allah Rahama banson kina damuwa da irin maganganun su don su basu dauki
hakan wani abu ba.
Da mai mata da mara mata dukkansu biyun zaman lafiya akajawa ba wani abuba don
haka kiyi zamanki a dakinki lafiya da mijinki Rahama.
Itama Salim din nayi mata fadan irin wanan magana tace wallahi bata san zai bata
maki rai ba don haka kiyi hakkuri don Allah dai.
Abin tsaman dana dauka na juya dankali na aje ina fadin la anry wallahi ban
dauki wanan maganan nata wani abuba sam wallahi.
Ita ta tayani karasa aikin har na samu naje nayi wanka da wuri na samu na fito
a daidai lokacin da yaya Habu yayo sammakon zuwa gidan.
Na gaisa dashi kana na nufi dakin yaya don in fada mashi zuwan yaya Habu din
kwance na sameshi yana barci dama yace min barci yake son ya samu ya danyi don ya
gaji da yawa.
Gashi kuma ya hana kanshi hutu da dare saida na yabawa aya zaki duk wani
gajiyansa ya rage saukewa a kaina cikin daren.
Na rasa yadda zanyi na tayar dashi hakan yasa na kai zaune a gefen shi a hankali
nakai hannuna saman wuyanshi na shafa kana na mayar da hannun akan kirjinsa.
Firgigit ya bude idonsa ya sauke a kaina ya dan motsa yana mika yake fadin
wallahi nagaji Rahama banda time din hutu a can koda da darene balle da rana.
Yaya habu ne yazo yana falo na fada tare da kura mai ido naga ya danyi tsuki
yana fadin karfe nawa yanzu na bashi amsa da almost to nine fa ?
Kai ya fada sai ya mayar da idonsa ya lumshe zakai wankane kafin ka fita yaya na
tambayesa ?
Ya bude idonsa yana fadin naso hakan amma bari na ganshi tukun in dawo ya kara
kallona yana fadin har kinyi wanka ke nan ?
Nayi ina shirin tafiya school ne yanzu abinci na falo na hadama ko bari na hada
ruwan wankan kadin ka dawo don nasan fita zakuyi kila ?
Na fada ina mikewa ya miko min hannu wai in dagashi dan murmushi nayi din nasan
ina ni ina iya daga mutum kamarsa amma banki ba na mika mashi hannun nawa ya jawoni
da karfi na fada mashi a jiki ya rungumeni.
Bai sakeni ba saida ya dan jahagulani ta hanyar kiss na samu dai ya sakeni yana
fadin barin je naganshi tunda korata akayi jiya aka nuna min ba a maraba dani nan .
Na samu na mike tsaye ina fadin ba hakana bane yaya tsoron shiga hakkin da ba
nawa ba nakeyi ga hakan baidai yi magana ba ya mike shima.
Nakai kofan bayin naji yace nasan abinda nakeyi sarai Rahama duk abinda kikaga
nayi ina da dalilin yin hakan so ki barni kawai na fiki tsoron hakan a zuciyana.
Ni dai banyi maganan ba na shige bayin na fara gyarawa don amfanin da mukayi
dashi da safe na wanko na fesa kamshi na hada mashi ruwan dumi na fice zuwa dakin
shima na gyara shi fes kafin na fito daga dakin.
Tsabta da yake so a zuciyarsa yakai karshe don haka nima nake ban son kazanta ko
kadan abu kadan na kazanta yanzune zai tayar min da hankali har tsikan jikina sai
ya dinga tashi kan hakan.
Tare na samesu suna karyawa dasu don harda Nura ya shigo ashe nasan Nuran tun
ban auresa ba don yana da wuya idan yana gari bai tare da Nuran abokinsane sosai
shakikinsa.
Hakan yasa na tsaya gaida Nura zan shige naji yaya din ba fadin Rahama karfe
nawa zaki shiga school ne ina son yin amfani da motarki idan ibrahim ya saukeki ya
dawo zan fita da ita don nawa ba zasu shiga ba yanzu sai an wanke min su.
Yanzun nan zan shirya in tafi don test zamu rubuta yau Ok ya fada idan ya
saukeki sai ya dawo ya daukeni ni dai na shige daki abina.
Na karasa shiri daidai yaya Ibrahim yazo don bai saba time gaskiya inba lokacin
da yakai mama kaduna dauko Saiba ba shine na biyo motan su Nuratu na dawo gida don
basu dawo garin ba sai bayan isha,i a ranan.
Nayi tuya na manta da albasa don da ta buga zata kaduna yaya Habu yace yayi
tafiya shine mama tace zatabi motar haya yaya habu din yace ta kira ibrahim yazo ya
kaita.
A hanyarsu ta dawowane mamake tambaya dama makulin motar tana hannun ka ke nan
ibrahim yace ehh mama kinsan Amaryan yaya ke amfani dashi ita ake kawai school da
motan .
Nan saiba taji wani sabon malolo ya tokareta a makoshi har suka kawo zaria bata
kara magana ba sai ajiyan zuciya da take saukewa lokacin.
Haka shima yaya daya shiga motar ya tayar yake tambayab ibrahim din da zai
sauke ya akayi yaji motar a haka don indai iyaka school da yake kaini ai baci ace
tana wanan karan ba ?
Ya ibrahim din yace ranan da nakai mama kaduna da zata dawo da Saiba shine naji
tana wanan kara na so nakaita wajen gyara naji kuma tabar kara yasa ban kai ba
gashi kuma yau tanayi again.
Da wanan motar kaisu kaduna ina motar dana aje donsu a can yace to ban sani ba
nidai mama dince ta kirani inzo da mota in kaisu kaduna ita da saratu shine na
dauki wanan na kaisu.
Baiyi magana ba ya saukeshi shida Nafisa ya wuce da salima gida sai ganinsa
sukayi kwatsam don ba wanda yasan da dawowan shi a gidan.
Part din iya ya nufa tana zaune ta gashi tare da salima hannu ta fara tafawa
tana fadin lale lale da Jafaru yaushe garin inji maki bako saukan yaushe jafaru da
safen nan haka ?
Iya jiya na dawo ta amsa da to sannu da zuwa yaya can ta dai shiga tambayansa
irin na al,ada yana amsawa da alhamdullahi.
Ga uwar taku ko yau zasu dawo sun tafi sokoto duba yar nan da take aure can tun
shekaran jiya ko yau zasu dawone oho ?
To sun tafi duba hauwa ke nan don yar wajen mamace ke aure a sokoto din akaiwa
aiki wajen haihuwa shine suka tafi dubanta sai suka samu tana jin jiki suka kara
kwana.
Nan dai iyan tayi mai bayani ya mike yana fadin barin leka wa yancan ingansu ai
ba gidan nan ka kwana ke nan ba ?
Yace a,a iya wancan gidan na sauka yanzu shigowata kenan nan din a daidai
lokacin Saratu ta fito daga daki tana fadin sannu da dawowa yaya.
Au ke kina ciki ke nan jelar mama aina dauka tare kuka tafi dasu mama din ta
amsa da ehh na dan kwantane naji muryan ka nafito.
Kaji makira tana daki tun safe bata lekoni ba da badon yar nan matar habu ba
wana shashashan data kasheni da yunwa a gidan nan tunda ba iya girkawa zanyi ba ba
kafa kasani ta fada tana nuna mashi kafan nata.
Saratu din ya kalla yana fadin saratu why zaki barta da yunwa don Allah meyasa
kike hakane saboda Allah ?
Idan wa yancan basu da hankali ko basu san zafin iya ba saratu ke baki sani
bane ashe da gaskiya da ake fadin halaiyarsu kike amfani dashi ?.
Yaya kafa san hali iya da surfa komai akai mata ba ai mata daidai ba ni shiyasa
na kyaleta baki kyauta ba wallahi ya fada cikin daure fuska ya juya yana tsuki ya
fita.
Part dinsa ya nufa suna falo dukkan su a lokacin falon dai kamar kullum kaca
kaca dashi Asmau ta amsa mashi sallama tana mashi sannu da zuwa.
Ya amsa yana tambayanta ya suke da yaran ya dan raba ido ko zaiga yaran bai
gansu ba yake tambaya yaran fa tace suna part din habu ina ji.
Ok bakima tabbatar dako suna can ba ke nan ina zasu yaya banda can tunda get a
rufe yake yaja tsuki ya nufi hanyar dakinshi kai tsaye.
Saiban taja tsuki tana magana kasa kasa har yasa key ya bude dakin ya dawo baya
yana fadin me kike nema a gidan nan ?
Ki koma inda kika fito kinji na fada maki in a serious voice yake magana don bai
nuna wasa ko sanya ba akanta fuskansa a daure.
Ai saika bari mama ta dawo kaji abinda nakeyi don ita taje ta daukoni har gidan
mu Ok zaman mama kikeyi ke nan to ki zauna zamanta din idan hakan yayi maki ya juya
ya shige.
Asmau ta kalleta tace kema da son rigima kike wallahi Saiba meya kaiki yi mashi
tsuki don Allah ta juyo a hasale bayan ta mike tana fadin .
Wa,azi zaki min kome ina ruwanki da zancen mu banda munafunci sai Asmaun tace
a,a meko ruwana a ciki Saiba ni gaskiya na fada maki kibi abin nan a sannu fadan da
yafi karfin ka sai ido ?
ZAMFARA
Tunda komai ya fito fili yanzu ba zancen boyo a wajen mijin anty baraka kuma ya
fito fili yana soyewa da bazawaranshi da ake shirin daura masu aure.
Ranan yarta tazo ta fada mata wallahi ga baba can na gani tsaye da Safiya kofan
gidansu da leda suna hira duk da hararan da yaiwa yar saida ta fada data shigo
gidan.
Zuciya ya dibi barakan ta mike ta yafa hijab ta samesu a kofan gidan tundaga
nisa ta hangoshi ya turo hula gaban goshi kafanshi daya yana ta cikin zauren gidan
daya kuma yana ta waje ya dafa bangon kyauren na gidan.
Yayinda bazawaran nasa ke tsaye daga ciki kadan amma ana hangenta waje ta karaso
tana huci sai jin muryanta sukayi tana fadin.
Macuci azzalumi Allah ya tona maku asiri kaida yar iskan taka yau ya juyo yana
fadin baraka hauka kikayi ko me da zaki biyoni nan da rana tsaka haka ?
Ba hauka nayi ba daga turu na fito ke kuma macuciya mai laluben ramin labewa
ahir dinki da mijina wallahi don ba wajenki a gidan mu.
Dakata baraka ki gyara zancen ki kice mijin mu don ya biya sadakina tuntuni in
baki sani ba ki sani bakinki ya saba da fasin mijin mu a yanzu.
Sadaki ko yaudara kudi garesa balle ya biya sadakinki dashi kudin nawa daya
yaudareni yayi min dadin baki ya kawo maki wai sadaki ?
Masha Allahu in hakane kema kin samu lada ashe tunda kin taimaka za a raya sunnan
ma,akin Allah da kudin ki kai nayi maki murna gaskiya.
Ke sakarai wa zakiwa dadin baki a baya badon baida kudin kika kisa ba sai yanzu
an samu kudin banza za a dauko min wahala.
Ke baraka ki koma gida tun kan ranki ya baci dani wajen nan don zanci maki
mutunci fiye da tsamanin ki wallahi mijin nata ke fadan hakan cikin karfin hali
ganin jama,a sun fara taruwa masu.
Nan dai aka taru aka fara bata hakkuri da ban baki data koma gida tayi hakkuri
har ya dawo gida hakan ba mutuncinta bane gaskiya.
Dole dai ta hakkura ta koma gida din cikin hasala da mijin da bazawaran tashi
tana zage zage kamar mahaukaciya da yawa sun san wanan aure za a daiyi ne amma
safiyama bata da halin kwarai.
Zata dai bata masu zamane kawai shida matarsa da suke zaman rufin asiri a
tsakaninsu shekara da shekaru ba a jinsu ansan itace yan uwanta ke taimakonta take
rike da gidan tunda shi ankoresa aiki tunda yayi siyansa dake kalubalanta ta
gwaunati aka sallameshi aikinsa yake zaune gida.
Yayinda wasu kuma suke jin haushin abinda safiya din tayi don me zata biyoshi
har waje tana mashi tonon asiri haka a gaban jama,a ?
ZARIA
Tunda ya shiga dakin yake bin ko ina da kallo saboda kuran da dakin yayi duk da a
rufe dakin yake yabar key din a gidana saida zai fitone ya dauko don idan ya barshi
bude har yara suke bari suna shiga mashi suyi mashi barna shine ya soma rufewa ya
wuce da key dinshi.
Shi ta ina zai iya kwana daki haka kaca kaca donshine yasawa Asmau kira da tazo
tana tsaye bayan ta shigo yace ki duba saboda Allah dakin nan yadda ya koma Asmau
saboda kazantar ku ?
Ki duba don Allah Asmau wanan wani irin rayuwane wai kika zabarwa rayuwanki
Asmau ?
To yaya ai dakin a rufe yake balle a gyarama yaja tsuki yace kona barshi a bude
aiba gyarab zakuyi min ba ?
Wanda bai iya gyaran jikinsa bane zai gyarawa wani muhalinsa ki duba yadda kuka
mayar da falon gidan nan don Allah ku bakujin kunya azo a samu gida haka don
Allah ?
Ni idan na saba wanda suke shigowa sun saba da hakanne don Allah baku jin kunya
a rayuwan ku ku ki duba jikinki Asmau son Allah ki dubi kanki ki gani don Allah ?
Yaya ni yanzu bata gyara nakeyi ba nima tawa ta isheni don Allah falo kuma ko an
gyara a bata donshi nima na bari kowa ya zauna hakana in gaskiyane.
Bayan haka meye dalililnku na rashin sawa iya abinci da bakuyi har yanzu ya
kafeta da ido yana kallonta don son jin amsan da zata bashi.
Tayi shiru ya dago yace badake nake bane idan ita Nusaiba bata san darajan iya
ba ke Asmau nace baki sani bane kome ?
Kinsan fa mama bata nan yarinyar nan Asmau kuma yaushe zata iya girka mata
abinda take so wai amma sai lokacin da matar habu tagama girki ta kawo mata
zataci ?
Ke yanzu bakiji kunyar hakan ba Asmau duk wanda yazo gidan nan a yanzu keya sama
amma baki iya tunawa da hakan sai kanwar bayan ku ta tuna tayi hakan ?
Yaya kafa san halin iya da surfa in an dafa abinci tace bai mata ba kuma ai ita
tace a bar saka mata kada ya zama barna bata iyaci.
Shout Up my friend don tace hakan ke baki san tsufa bane ko baki san yakamata
bane ?
Amma jeki ba matsala wallahi kowan ku will regret it don nasan abinyi a yanzu bai
yuyuwa ina kawo komai a gidan nan amma ace ba za a iya girkawa aba kakata for what
reason za zaman kashe jikina a banza.
Kayi hakkuri yaya za a dinga saka mata idan an girka ko bataci din kayi hakkuri
yaja tsuki ya dan kalleta ya juya yana daga filon saman gadon zai kakabd da sauri
tana jan kafan don nautin da cikin yai mata ta karba ya fito daga dakin gidan ya
fice ga baki daya cikin takaicinsu a zuciyarshi.
A ranan mama ta dawo Zarian ita da abokan tafiyanta can family house dinsu suka
sauka ganin Nafisa a gida take tambaya take fada mata ai yaya ya dawo jiya shiyasa
ta dawo gida.
Ko ya dawo aiba gidan zai sauka ba don me kuka dawo yau tayi shiru bata bata amsa
ba don tasan halin mama din haka kuma tana gudun hadin hasumi.
Saiga Nusaiba ta kirata tana kuka tana fada mata abinda yace ta bata hakkuri tace
kar taje ko ina gata nan zuwa gidan ai.
Haka yasa ta kwasa zuwa gidan don ta rutsa shi don saiba bata san fitanshi ba
tace mata yana nan gida lokacin
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: {2\25\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,
5️⃣4️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Shiya daukoni daga school ranan muna hanyane aka kirashi a waya wai mama tana
nemanshi saratu ce ta bugo wayan lokacin ya amsa da Ok ta dawo ke nan ?
Tace ehh sai naji yace da ita gani nan zuwa zan sauke Rahama injuyo sai banji
dadin hakan daya fada ba a lokacin saboda nasan halinta yanzune zata iya juya
zancen ya zama babba.
A samu na yamadidi dani a gari ana fadin magana ba dadi a kaina wanda bai dace
kamar yadda akewa mutum fatan sheri a yanzu don har jira mutane suke wani sheri ya
sameka a fara yawo da sunan ka har garin ku.
Muko fulani kowa yasan mu kunya garemu badai tsoro ba dan bamu jin nauyi ko
girman abu idan mun tashi yinsa kai Aaye muke abin mu ba boyo .
Saida ya kaini din ya sauke ya shiga yaci abinci sanan ya tafi kiran da mama din
ke mashi inda ya samu mama ta hau akansa don abinda saratu ta fadi har yaso zama
fada a tsakaninsu da salima a lokacin.
Saboda lokacin da yace gashi hanya ya daukoni zai kaini gida bayan ta kashe wayan
tace ke mama kinji.
Wai matarsa ya dauko sai ya kaita gida tukun zai zo wai Rahamace yaya yake kira
da matarsa Rahama dai Rahama dai wanan ai abu a fili yake kowa yasan hakan aikin
asirine gaskiya.
Inba asiri ba me yaya zaiyi da Rahama don Allah wanan bagidajiyar yar kauyen yana
da mata kamar Saiba.
Aikin banza aiba wayewa akajawa ba hali na gari jarin mutum a hakan yar kauyen
yake son abinsa don tafi bashi kwanciyar hankali.
Balle ko makiyin Allah a yanzu baicewa Rahama yar kauye don koke tafiki wayewa
sanin da dai kikai mamata yasa kika kirata da yar kauye.
Tafini fa kikace Salima tace kwarai kuwa abu a zahiri ko kina gardaman hakanne
koda yake ba mamaki don kin dade baki ganta bane yasa kike