Showing 198001 words to 201000 words out of 328222 words
Chapter 67 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA
WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Yan gidansu dana hango a wajen yasa na doshi emergency din kai tsaye takawa nakeyi
amma bansan inda nake takawan ba har nakai wajensu.
Suna min sannu da shigowa ga kallon tausayi karara a fuskokinsu inda nikan har
lokacin zuciyana sai harbawa da take min tana wasi wasin ko waye a wajen ?
Ganin yar uwata dake cikin taron yan uwa yasa na dan fahinci bata ita bace kuma
ba mijinta bane ras naji lokaci guda da matansa da suka iso a daidai lokacin suma
hankali a tashe.
Wuni sukayi don na tsaya gaidasu yaya isah dake tsaye suna magana da ya Habu
suka amsa min hayaniyar da saiba keyi tana fadin akan me ba za a bari mu shiga
muganshi ba ?
Wanan yasa ya habu katse maganan da yakeyi ya doshi wajen hankali a tashe yana
fadin ke Nusaiba kada kiyi kokarin daga muna murya wajen nan fa ?
Kowa da kika gani wajen nan abu daya ya kawomu nan saboda shi muka zo nan din
kowa kuma yayi hakkuri yabi dokan likitan .
Ko in an barki kinshiga suna aikinsu da abinda zaki mashine a yanzu wanda yafi
nasu din don haka kada ki kawo muna rigima a wajen nan don Allah ?
Har na taka nakai inda su maria suke tsaysaye din cikin damuwa a cikin yare nace
yayane ko ta amsa min da shine tana rike hannuna .
Cikin yare take fada min in natsu in kwantar da hankali Allahne mai komai kada
inyi abinda zan zubarda imanina a gaban mutane don Allah.
Yanzu likitocin nan suna dubashi ne su can sunce basu ga komai ba shine nan
suke nasu kokari ko zasu gano abinda ya sameshi din.
Ajiyan zuciya na sauke ina bin bangon dake bayanta nakai tsugune a wajen tare da
noke kaina cikin gwiwana salima ta dafani tace kiyi hakkuri ki natsu kinji Rahama
don Allah.
Kamar dai irin ciwon nan nasane na baya ke son taso mashi amma wanan karon ya
canza sallo ne yazo mai da wani nau,in kuma .
Ruwan dake hannunta na mika hannu na karba na dan tsiyayya na shafawa fuskana
ban sauke idona akan kowa ba sai mama dake zaune a kasa tayi tagumi a cikin tashin
hankali.
Kallona ya koma kan saiba dake fada har lolacin saidai ba cikin daga murya ba
haka nayi tabin mutanen wajen da ido ina nazarinsu daya bayan daya a takarshe idona
ya tsaya kan Saare dake magana tana murmushi na juyo a hankali na dubi yar uwata
ina fadin .
Akan me zasu kawoshi asibiti Yanda bayan sunsan ciwonsa bana asibiti bane komene
ai mama ta sani da kawu .
Maman dana ambata da kawu yasa salima kallona itako maria sai fadi take ta fada
min kada inyi wani abinda zan jawa kaina matsala fa.
Koma meye ga yaya Habu nan ai dole zai dauki mataki ba zai kyalesu ba shima don
haka inyi shiru kawai don Allah.
Itako salima din cewa tayi dani ai mama tunda taga halin da aka iso dashi take
zaune wajen nan bata daga ba don baki cewa yana da rai fa ko motsi yaya baiyi
Rahama idonsa a kafe suke waje daya.
Innalillahi na ambata a cikon tashin hankali ganin an bude kofan yasa kowa kallon
likitan daya kira ya habu suka nufi hanyar office dinsu dashi.
Ya dan jima a wajensu ya dawo tare da likitan lokacin ya habu din kewa yan
uwansa bayanin abinda likitan ya fada.
Su maza suka fara shiga saibama ta kusta sai naji maria ta rike min hijjab dina
na dago na kalleta don na yunkura na tashi nima tsaye lokacin.
Ki bari su shiga ai dole ya habu ya bari ki shiga ki ganshi a natse wanan yasa
na tsaya ba don naso ba zance kusan mune karshen shiga wajensa din.
Kuka masu kuka keyi irinsu saiba sai da wasu yan uwa tunda naga yanayinsa naji
duk jikina ya mutu a wajen muryan ya lawal naji yana fadin tun a can fa haka yake
bai motsi bai komai ko ka nuna hannu da alaman ma bai san kayi ba.
Komai ya bace min akai sai wanan kalman ta (Lillahi ma,fis samawati wama fil
ard) shine abinda ya fado min a zuciyata lokaci guda nake faman nanatawa a
harshena.
Na doshi wajen gadon da yan uwa da matansa suka zagaye ku dan bata waje ta isa
wajensa don Allah ya habu ya fada daga bayan mu hakan yasa wasu juyowa suna
kallona.
Har na karasa ban iya furta komai ba sai wanan kalman daya tsaya min a saman
baki don komai ya bace min a lokacin.
Shi din ma daddy Abuja ya koyar damu hakan aduk lokacin da wani abin damuwa ko
furgici ya shigemu dashi na taso a bakina don haka kila yayi saurin zuwa min a
kaina ayan karshe a cikin bakara.
Tsaye nayi ina mai kura mashi ido tare da nanata kalman a cikin bakina sannu a
hankali na kara matsawa kusa da iya ina fadin sannu yaya Allah ya baka lafiya ya
sahalema wanan halin daka tsunci kanka a cikinsa.
Magana nakeyi amma abinda iya da yaya Isah suka fada lokaci guda yasa nayi shiru
na kurawa bakinsa din ido don cewa da yaya Isah yayi wallahi ya amsa mata adduan
nan da amin.
Wallahi bakinsa yayi motsi kuma wallahi amin yace da sauri mazan suka matso
sukace yayi magana fa kace iya tace kwarai ya amsa nima naji hakan wallahi.
Dama likitan yace a gwada kawo mai na kusa dashi agani ko za,a samu reaction
indai hakane kuwa dole Rahama zata tsaya kusa ke nan .
Yaya Auwal ke fadin hakan ki kara magana mugani ko zaiji don Allah yaya isa ya
fada daga gefena din.
Saida na dan kara matsawa kadan na rankwafo nace yaya kana jin mu don Allah idan
kana ji ka dan nuna alaman hakan ?
Nakai hannuna na shafa fuskansa a hankali yayi wani irin ajiyan zuciya mai karfi
da kowa ya firgita saina fashe da kuka na kifa kai a jikinsa.
Ku dagata kawu ke fadi daga inda yake tsaye muryan iya ne tace ku barta dashi
hakan na dan lokaci mu gani ?
Hawaye yakeyi fa yaya isah din ya fada hakan yasa wasun mu da dama kara kuka a
dakin har iya duk dauriyanta saida ta fashe da kuka ta soma fadin.
Allah ya saka maka Jafaru ga dul wanda ya sakaka cikin wanan halin ubangiji
yabi maka hakkinka akan mai shi ga alamu sun nuna karara akwai wani boyayyen lamari
a cikin matsalanka.
Duk wanda ya sanka yasan a yan watanin na baka daidai kamar kulum kana yawan fada
min iya banda lafiya ni kadai nasan yadda nake ji a jikina .
Iya bana barci wani lokaci har tunane gushe min yakeyi iya ina jin na kusa barin
ku wallahi tana kuka sosai take fadan hakan.
Iya ki daina wanan maganan don Allah ai sai a dauka ba ayi imani da Allah ya
kawo mashi hakan ba imani ya kamata ace munyi ayanzu ba irin wanan zancen ba don
Allah ?
Me kake son in fada akan abinda nasan shine sila akan matsalan yaron nan dole in
fada tunda abu ko yaushe sai kara gaba yakeyi akansa.
Kiyi hakkuri iya in sha Allahu za a dauki matakin hakan ya habu ya fada nikan a
hankali nayi kokarin dagawa daga jikinsa amma sai naji kamar hannunsa dake sarke da
nawa ya dan rike hakan yasa na dan dago ina kallonshi.
Tabbas hannun nasane ya rike min nawa a hakan da yake din na bishi da kallo
kamar yana son kifta idanunsa saidai ya gaza hakan a lokacin .
Na fahinci yana kokarin yi min yadda yake min ne lokacin da yake da lafiya idan
mun kasance a hakan dashi nayi yunkurin dagawa daga jikinsa zai rikeni ya hanani
wani lokacin yace mu tsaya a hakan dashi shine yanzu abinda yake kokarin yi mi a
lokacin.
Muryan Asmau naji a bayana tana fadin sannu yaya J Allah ya baka lafiya jin
hakan yasa na dan dago ina fadin ga anty Asmau nan yaya tana gaida kai.
Hannuna na zare na hada da nata dana kamo na daga daga wajen takai zaune inda
na daga tana mashi makamancin abinda nayi mai din a lokacin.
Idanuwa kur akan mu dakin yayin da saiba ta karasa itama ta zauna kamar yadda
Asmau ta zauna din tana maganganu gareshi.
Dole kowa zai tausaya a wanan halin ga dan uwa a cikin wani hali babu mai halin
ko ikon kwatosa daga jerabawan nan sai Allah sarki buwayi gagara musali kafai yakai
ya kwato maka dan uwan daya fada cikin irin halin nan.
Kuka ka munyi shi har mungaji mun godewa Allah mun koma muna rokon Allah ya
bashi lafiya sai dare karfe tara na bar asibitin zuwa gida.
Koshi yaya habune da yai tsaye a kan mu cikin daure fuska yake fadin duk mu fito
mu wuce a kaimu gida babu wace zata tsaya a nan cikin mu .
Za a bar iya da yaya Auwal da yaya isah su zauna dashi a ranan naga dadin
kyautatawa yan uwa da yaya J keyi don suma sun nuna mashi kauna kwatankwancin yadda
yake nuna masu din.
Tare da yanda muka bar asibitin a motarsu suka saukeni gida tana ban baki da
lurar dani na dangana nayi aikin hankali.
Don taji an fara surutu da tsegumi wai duk halinda yake ciki saida nazone yayi
motsi har aka gane wani abu a gareshi.
Kinga ke nan suna nufin wani abu ke nan a kanki yanzu kwarai kuwa nima naji suna
fadan hakan wai badon zuwa ta ba ko motsi baiyi ba tunda suka daukoshi tunma a can
din da hakan ya sameshi Nasir kanin su yaya din daya dauko mu yake fada.
Maria tace na kula suna son kawo wani zance ga hakan sai tace amma ai yaya Isah
yace itace ya kamata ta zauna tayi jinyarsa idan hakan ya taso .
Saidai sunsan wanan matar tasa yar kaduna zatayi fitina akan hakan amma yaya Habu
yace a barshi da ita kawai yanzu naji suna maganan idan anga asibitin baiyi sai a
koma gida a cigaba dana gargajiya.
Sun dan jima a gidan wajena muna magana kafin suja mota su tafi maigadi ya
tareni yana fadin ashe abinda ya faru ke nan ?
Yaso ya bisu zuwa asibitin sai yaga ba kowa a gidan Allah ya bashi lafiya ya
tada kafada na amsa da amin nashiga ciki.
Habi bata gida nasan tana gidansu donshi na shiga dakina kai tsaye wanka nayi na
fito na gyara jikina a yanayin da nake ciki banko tuna da abinci ba a ranan .
Tea na hada da niyar insha kada in kwanta da yunwa saidai na kasa shan koda rabin
kofi ne a lokacin don bakina da nake jin ba dadi.
Ina ganin kamar ko wani lokaci zasu iya kirana suce min ya cika a yadda na barshi
din ga gidan ba kowa sai hakan yasa tsoro ya kara shigana duk da maigadin mu yana
daga wajen gidan a lokacin falo na dawo na zauna a cikin zulumi ina jan tsabaha
tare da tunanen yanayin da yaya din yake ciki.
Daga karshe dai na mike na rufe kofa na koma cikin daki bayan na kashe wuta ko
ina a gidan ina cike da zullumi a zuciyana.
Alwala na dauro nazo nayi sallah nafila nakai wani lokaci ina nemawa yaya sauki
a wajen Allah kafin dan barci ya saceni zuwa dare kuma na falka ban kara runtsawa
ba har safe ina idar da sallah na fito zuwa kitchen abinci lafiyayye na hada inda
shi kuma nayi dabaran dama mashi kunu ko za a samu ya dan sha.
Karfe bakwai har nayi wanka nashirya na fito na kulle gidan na doshi asibitin
gabana sai faduwa yakeyi.
Tunane kan nayisa kala kala a zuciya yau idan na rasa yaya yaya zanyi da
rayuwata ina zan shiga a duniyan nan mutumin da nake mafalkin shimfida rayuwa mai
inganci dashi nan gaba gashi kuma Allah ya jarabeshi yana cikin halin hau,ula,i a
rayuwansa yanzu.
Zance nice ta farkon isa kota biyu na samu su yaya na ciki suna tsabtace masa
jikin daya bata Allahu akbar bansan lokacin da kuka yazo min ba.
Sammakona yasa na samu daman shiga gurinsa kai tsaye yana kwance kamar yadda muka
barshi dai a jiyan dan bambanci sun sauya mashi kayan jikinsa zuwa jallabiya
tufafin nasa da suka cire mai yaya isah ya miko min na karba.
Iya tashigo tana fadin ga abin karyawa nan tazo muna dashi shikan ai ba abinda
zai iya ci a hakan da sauri nace na dama koko ko zai dan karba a gwada a gani.
Shawaran hakan suka karba na hada kunun na dan fifitashi saidai mazane sun rasa
dabaran da zasuyi su bashi.
Nice dai cikin karfin hali na gwada karban kofin a hannun yaya na doshi gadon ina
sunkuyawa nace sannu yaya ya karfin jikin kuma Allah ya bako ikon cin jerabawan nan
.
Suka amsa da amin amin yaya ka dansha koko gashi na dama maka koda kadan ne don
Allah cikin ka babu komai a cikin sa cikin ikon Allah sai yai kamar ya lumshe
idanunsa a lokacin.
Na dibo na fara dan dago kansa a hankali ina dura mashi kokon yana shiga cikinsa
har muka samu ya dansha kamar spoom biyar haka dai suna fadin Alhamdullahi wanan
dabaran yayi kuwa na shan koko din.
Iya ke fadin aiko yunwa ya isheshi mutum kwana nawa cikinsa babu komai a lokacin
su mama suka shigo dukkansu da kishiyoyinta aka fara gaisawa.
Yaya Auwal ke fadin amarya tayi dabaran bashi koko ko zaisha gashi ko mun samu
cikin ikon Allah ya dansha din sai mama tace nima nayi tunanen hakan a raina.
Nan yan uwa suka fara cika dakin da abinci da kayan dubiya ina zaune a gefe
takure har kishiyoyina suka iso saidai su Maria sun rigasu isowa tana fadin mun
biya mu daukoki maigadi yace muna kin fito tunda safe ai.
Kafin na amsa iya ke fadin zuwata ai yayi muna rana tunda an samu ya dansha
kokon data damo mashi ta bashi ya karba sosai yasha.
Irin maganganun nan da ake fada akaina mai kamar da ana yabona shine ke kara
hadasa min kiyayyana a zukatan wasu a wajen irin kishiyoyina da su Saare dake gani
iyyye iyye ne kawai irin nawa da son nuna ni din watace datafi kowa.
Itako iya kamar zuzuta zancen takeyi a lokacin don suji haushi don sai kara cusa
magana takeyi tana fadin ai ko dazun da yarinyar nan ke mashi addua ya karba.
Muryan ya habune ke tambayan kawu ya fito akace bai karaso ba tukun yace iya
tazo suka fita ashe zancen zuwa wanan wajen yai mata.
Take fadin ya kamata kan aje din aiko wancan karon banso ya tafi tafiyan nan basu
je ba amma da yake Dauda munafukine sai yakawo uzuri ga tafiyan yace wai yana
gudawa lokacin.
Koma dai meye yau din nan iya nake son muje din don nayi mafalki jiyan nan ba
dadi wallahi ciwon nan haka zaita bibiyan mu bawai Jafar kadai ba kowan mu sai
hakan ya nadesa idan har ba a dauki mataki ba.
Ga zancen nan ba kowa ya kamata yasan dashi ba tunda ba zancen da za a fito a
fada a fili bane har wani yaji abune daya shafe mu mu kadai wanan.
Amma saidai naga kamar dole a fasa din don yau idan kawu ya kawo min uzuri
wallahi za a jimu dashi a wajen nan wanan yasa na kiraki iya.
Wanan shine daidai na rasa me dauda kewa noke noke ga zuwan nan gashi har ankai
ga yadda ba ason akai din dole kayi masa jam ido ko zuwan zaiyi amfani a dace.
Har ya juya ya dawo yana fadin sai kuma kula dashi ina son aba Rahama daman
hakan ta dinga bashi kulawa idan tana kusa tunda yana jin muryanta yana bada
responding kinga hakan ai alaman saukine.
Shina fada jiya da dare ko yau kuma muga alama hakan don tabashi koko yasha da
kanta hakan za ayi yanzu dai idan mun dawo idan babu cigaba nan asibiti sai mu koma
gida dashi iya.
Aje ayi na gargajiya a gani don ko lokitan nan dan Zamfara shawaran daya bani ke
nan jiya yace abin nasa kamar akwai sihiri a cikinsa din haka sai mun hada dana
gargajiya.
Kawune ya doso wajen da matansa biyu sai dan amaryan nasa dake dauke a hannunsa
iya ta kallesu taja tsuki tana fadin babu komai yanzu a cikinsa banda tabara akan
wanan auren da yake ganin yayi.
Suka karaso suna gaisawa tare da tambayan ya mai jiki din yace da sauki zai
shige iya race barsu su shiga kaika tsaya muyi magana dakai ke hansatu idan kin
shiga yi min magana da Dubu ina nemanta nan.
Lokacin ne kuma muka fito dakin nida maria muka kebe muna magana dan nisa dasu
sosai saidai jin yadda ya habu ke daga murya yasa hankalin mu ya koma akansu.
Duk da bamu ji sosai amma na fahinci zancen tafiya sukeyi nasan kuma can din inda
nakwana da tunane suke shirin zuwa.
Sai lokacin nakewa maria bayanin komai tayi mamaki kwarai dana san hakan nace
shiya fada min komai wallahi kamar yasan hakan zai faru dashi har dalilin dawowan
iya wajena saida na bata labari.
Take fadin kinga bambancinsu da ya Habu ke nan