Showing 210001 words to 213000 words out of 328222 words

Chapter 71 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

Rasa me zanyi nayi saina tuna da dan anty salma ya samu attack irin hakan yadda
mukai masa a abuja da sauri na juya na dauko spoon na nufeshi ina kokarin bude
bakinsa na tura spoon din ya datse tsakanin harshensa da hakoransa.
Kanshi yana saman jikina muryata a cikin tashin hankali na soma fadin don Allah
ku rike min kafansa daga mama din har ita saiban sun kasa hakan shigowan Maria da
Anty Barakha ya taimaka min suka rike kafafuwan nasa dake halbawa.
Innalillahi nake maimaitawa saiga likitocin sun shigo a rude nurse suna fadin a
rage daga dakin a fita don koke koke da yai yawa a lokacin dakin duk kowa na tsaye
cirko cirko a cikin tashin hankali.
Ruwan sanyi ko kankara nake fada ina nuna hanyar waje likitan ya kamo hannayesa
yana dubawa har lokacin yana kwance shambal a jikina.
Ruwan da nake fada din suka miko min a daidai kanshi na manna ruwan sanyin lokaci
guda ya sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi ya daina wanan gurnanin da yakeyi
da farko.
Dukkan mu matansa mu ukku muna tsaye a dakin a cikin tashin hankali har likitocin
sukai mashi abinda zasuyi din ganin ya lafa suka soma magana a cikin fada.
Ba mun fada maku a daina shigowa ba haka da yawa dakin muna son ganin
farfadowansane a ko wani lokaci zai iya yuyuwa yana jin komai saidai nisan fita
hayacinsa da yayine ba zai bari a fahinci hakan ba zai iya jin wani magana da zai
iya daga mashi hankali kuma har hakan ya faru kunga ciwon yana son canza sabon
sallo kuma ke nan.
Na yarda da maganan ka likita don matar nan tasace ke sa insa a dakin lokacin
da abin ya faru kaga ke nan zancen ka gaskiyane ke nan a nan mace ke fadan hakan.
Kuka saiba ta saka mai karfi tana fadin don kawai ba a kaunata za ace nice nayi
sanadin hakan ya faru ya zata fada min magana inki ramawa don ina tsoronta ko me ?
A nan kowa ya raina mata wayau don fahintar itace silan faruwan hakan ashe a
lokacin da mama ta fada.
Anty barakha ke fadin indai hakane aisai duk su fita wallahi tunda ba zaman Allah
da annabi sukeyi a nan ba zasu kashe muna dan uwa da bakin kishinsu kawai ?
Ya zama dole duk su fita likitan ya kalleta yace ita wanan na zaune bida gadon
data bashi taimakon gagawa ina matarshi ce ?
Yana da kyau a barta a kusa dashi na fadawa brother nasa dazun don tana
taimakawa sosai wajen abubuwa da dama ko yanzu badon tana wajen ba da zaiji ciwo
sosai wallahi.
Don zai iya fadowa daga gadon haka kuma harshensa zai datse din ya ja masa wani
matsala babba kuma sabo amma taimakon data bashi din ya taimaka muna sosai a yanzu
wajen magance matsalan don haka abarta a tare dashi please .
Amma kowa ya fita daga dakin nan a yanzu sai mutum biyu kawai za a bari a ciki
tare dashi da zasu zauna su duba halin da yake ciki.
A daidai lokacin kuma su yaya Auwal suka shigo a rude don an kirasu a waya ana
sheda masu halin daya shiga din a lokacin suna wajen karbo maganin da ya habu yai
magana a kai.
Ankara masu bayani ya isah bai tsaya likitan yakai karshe ba ya soma magana yana
fadin amma na fada ai kada wanda ya shiga bayan amarya saike mama din me za a barsu
su shigo har haka ya faru ?
To ya zanyi inyi magana yarinya tana batun zagina don kawai na fada mata gaskiya
ku yanzu ai ku tsawata mata ta daina kila amma halin yarinyar nan ai baiyi ba
wallahi.
Kishi har mutum yana kwance gadon asibiti ba zaki saduda ba yanzu da likita daku
kuka fada ai zata fahinta ko ?
To kuji don Allah duk wanda yazo ya gaidashi ya fita don ba zamu hanaku shigowa
duban mijin ku ba amma a shigo a tsanake a fice daga yau don ba zamu lamuci rashin
hankali ba a nan lafiyan dan uwan mu muke duba a yanzu ba kishin banza ba a nan.
Wanan abinda ya faru yasa jikin kowa sanyi har saiban da take jin take gani
mamata lauya mata laifin komai a kai duk da tasan ba gaskiya bane nice dai na fara
gasa mata magana gashi kuma Asmau taki magana har lokacin sai kukan da take faman
yi akan laluran mijinta din.
Basu jima ba ganin ya samu barci ya koma normal sukayi sallama suka koma gida
nikan ina asibitin tunda naga maman tudun wada ta kama min na samu shiga a
idanuwansu kishi ke nan dama.
Da kwatance kawu dauda suka tsaya a wani gidan zana dake can dan gefen garin
wajen dake dauke da wasu manyan itatuwa dake karawa mazauna wajen ni,ima.
A gaban gidan ya tsayar da motarshi yayin da mutanen dake zaune a innuwar suka
zubo masu idanu suga masu fitowa daga motan.
Kawu ya fara fita har hulansa na faduwa kasa kafin ya bude bayan motan iya ta
sako kafa ta fito tare da mama shi yaya habu shine ya fito karshe suka nufi wajen
mutanen bayan ya rufe motar tashi da key.
Kawu ya fara gaidasu suka amsa tare da masu sannu da zuwa da yaya hanya bayan
gama gaishe gaishensune yake fadin don Allah Tuni fa da cewa matar kamar yadda ake
kiranta dashi a wajen.
Wani daga cikin mutanen ne yace wai Tuni kan ai ta dade da barin mu saidai yarta
kudidi ke aikin a yanzu tana ciki in wurinta kuka zo?
Innalillahi iya ta ambata tare da fadin shike nan dauda son kanka ya halakamu ga
baki daya yanzu kuma ya habu yacewa mutumin kana nufin bata raye yanzu ita tuni din
?
Ai kaji me nace yau shekara kusan biyu ke nan da rasuwanta ai amma yarta na ciki
itace ta gajeta ga aikin yanzu aifa shike nan kuma kai habu namu ya samemu kuma a
yanzu iya ta kara fada a rude mama kan hawayene suka soma zubo mata lokaci guda
takai tsugunne a waje daya cikin tashin hankali.
Dayan mutumin ke fadin ku karasa ciki koma meye yarta kudidi tana nan zata
saurareku ai don ganin yadda fuskokinsu ya nuna damuwa da tashin hankali lokaci
guda jin mutuwan tsohuwan da sukayi.
Yaro aka tura yayi masu iso da matar da aka kira da kudidi din ta dan jima bata
fito ba don tana ganawa da wasu bakin a lokacin .
Yayin datayi masu ison su shigo kawune ya fara shiga dakin da take karban
bakinta sai iya sai mama dubu habune yayi karshen shiga dakin da sallama a bakinsa.
Neman inda zai zauna yayi ya kai tsugune don ita wace suka zo wurinta din tana
neman wani abu a lokacin don haka ta basu baya ba zasuce ga fuskanta ba .
Lokaci guda gabanshi ya fadi yayin da yai arba da wanan matar mai maciji a
kwalla na shekarun baya ba zai taba mantawa da fuskan wanan matar ba.
Ba annuri a fuskan nata gata saye cikin bakaken tufafi irin na mutanen dauri
tun daga sama har kasa sune a jikinta.
Yau Allah yayi kun samu zuwa ke nan abinda ya fito daga bakinta ke nan lokacin
data juyo garesu shiru dan dakin yayi na lokaci guda.
Ta mika hannu ta dauko wani dan kwarya ta girke a tsakiyarsu tana fadin tabaci
ke nan tunda na ganku nan kai habu aina fadama dole saika nememu dama tun abu
baikai haka ba har kun bari komai yakai ga lalacewa.
Sunan habu data kirane ya basu mamaki gaba dayansu har habu din da har lokacin
kallon mamaki yake binta dashi .
Kawune yayi kokarin soma magana cikin wani murya ta dakatar dashi da fadin kai
mana shiru don Allah kome ya faru laifinkane .
Da yar uwarka kazo nan neman sa,a kayi dace an karbama anyi a cikin sa,a amma
ka bata komai da hannunka saboda son kai irin na yan adam daka sawa kanka a
rayuwanka.
Kaki yar uwarka kabi ra,ayin matarka duk da gargadin da mahaifiyana tayi maka a
wancan lokacin akan yar uwarka da kake son cin amananta.
Amma ka yarda ka,biyewa matarka kuka cutawa yar uwarka duk irin biyayyan da take
maka kaida matarka amma kukai amfani da biyayyanta kuka cuta mata ba tare da sanin
taba.
Naso na taimaka tun abin nan bai kai haka ba amma shu,umar matarka ta hana hakan
a lokacin don bata bar yar uwarka a banza ba ita da zurianta.
Kai kanka kasani kasan irin yadda take duke kan wa yan nan mutane duk akan abin
duniya kuke hakan duk da kusan cewa karshen hakan ba zai maku dadi ba nan gaba.
Yanzu ba wanan ba kun zone akan dan uwaka dake fama da jikinsa ko habu ?
Saita kada kai tana bata fuska kafin tace shi an riga da an sameshi saidai ba
yadda akaso samun nasa ba.
Don ansone ayi mashi karaf daya wanan karon saidai hakan bai samu ba saboda wani
dalili kai haba kasani na fadama wanan yarinyar da ka aura tana da wani siri a tare
da ita.
Hakama ita wace ke tare da dan uwar naka naga kamar yar uwar matarkace ita tana
da natukar kokari sosai don Allah ya kyauta zamata tare dashi matuka da komai ya
jagule akansa wanan karon don
Abin nasa yayi masa yawa gida ajefeshi haka wajen neman halak dinsa a jefasa, ga
makiya yan hassada suyi masa yawa, haka kuma a gidan matansa basu barshi ba.
Ta sake girgiza kai tana duban wanan faifai din gabanta data rike tana fadin
yanzu ba lokacin wani bincie bane dole bakin rafi zamu a fara bada sadaka .
Saidai idan karyan nan yaki tafiya ya tsaya a waje daya haka na nufin sadakar
bai karbu ba ke nan saidai mu zurwa sarautan Allah ido gaskiya.
Amma da zaran an saka wanan kwaryan ya tafi yabi ruwa insha Allahu wanan sadakan
ya karbu ke nan don haka sadakan zai kasamce biyune a yanzu.
Da wanda zamuyi don dan uwanka dake fama da lalura a yanzu sai kuma naku kaida
sauran yan uwanka da a yanzu ba aikai gareku ba.
Don haka dole muyi gagawan yin riga kafin akanku kamar yadda al,adan abin yake
murya iyace ya katse matar da take fadin.
Aah, Ikon Allah inda ranka kasha kallo dauda nan kuma ka kawo yar uwarka da zurian
ta don son kai irin naku dauda ?
Tsohuwa kiyi halkuri ayi wanan hadayan kafin komai ya kai ga jagulewa a yanzu
daga baya mayi duk wanan bayanin daku a tsanake.
Ta juya gun mama dubu tana fadin kece zaki saka komai a cikin kwaryan nan zaki
saka da niyar fansan rayukan yayanki daga mutanen ruwa masu bada sa,a da
yarda,,,,,,,
Kallon juna sukayi tsakani mama da iya har habu sai matar tace shi yasan komai
don shi ya dauki alkawarin hakan garemu tun farko.
Dole mama ta mike ama fada mata duk wani abinda zatayi suka dauki kwaryan dake
da abubuwa a cikinsa hardasu masa kosai alawa ayaba sukari da turmin zani zuwa
bakin rafi .
Tun bayan isarsune wajen dole mama dubu din ta taka zuwa ciki ruwan tana bin
matar da kwaryan farko wanda zata fara sadakan dashi akan jafar din .
Gaba dayansu gabasu na faduwa wajen son ayi abin cikin sa,a ba tare da an samu
matsala ba matar ta karbi kwaryan ta fara jera kirari tana daga kwaryan sama tana
saukewa .
Suna tsaye suna kallon ikon Allah a gefenta can ta mikowa mama dubu tace tayi
niyar ga sadaka ta kawo masu idan sune sanadin rike danta jafar tana rokon da su
sakeshi ta biya sadakan da suke binta akanshi .
Saidai yadda ta aje kwarya a saman ruwan ko alaman motsi baiyi ba hakan yasa
gabansu ya fara faduwa cikin tashi hankali.
Wanda hakan ke nufin cewa da alama jafar din yana da wuya wanan abin ya barshi
hakan na nufin dai sai abinda ya fito daga Allah gareshi kuma.
Anyi anyi kirari kwarya yaki matsawa daga inda aka ajeshi hakan yasa aka miko
mata na sauran yaran nata wanda shima yake da nasa kalan tarkacen abin mamaki a na
dorawa a saman ruwan kwaryan ya soma tafiya yana bin kabin ruwa da sauri.
Gani hakan yasa habu dake tsaye gefe daya bakinsa dauke da addu,oinsa ya tako
daga inda yake zuwa wajen kwarya farko da aka aje don jafar din ya cira shi ya
daga yana fadin ka tafi kaima kamar dan uwanka ya dora saman ruwa suka bishi da
kallon mamaki.
Suna jin tausayin irin halin dayake ciki da har baisan abinda yakeyi ba a
lokacin ciki yardan Allah sai kwaryan ya fara dan juyawa sannu a hankali saman
ruwa ya soma tafiya shima .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/17, 08:36] Buhainat: [3/18, 8:26 Yamma] Seenabu Makawa: Open this link to join
my WhatsApp Community: https://chat.whatsapp.com/JeOQfGohQLdKTUlsWMqXoZ
[3/18, 8:28 Yamma] Seenabu Makawa: {2\23\ 3:14 Yamma}seenabu Makawa
MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,,

6️⃣7️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Dan uwa murfin jallo inji manya wasu sukace rabin jiki kuma don hakan ne ya kasance
ga habu lokaci guda don ganin kwaryan da ake nufi ta jafar taki motsi yasa ya dinga
karanto addua da sunayen Allah mai girma sai gashi a fusace ya daga kwaryan ya tura
ya fara tafiya saman ruwa cikin yardan ubangiji.
Abin mamaki suke kallo daga iyayyen har mai maganin sun zubawa ikon Allah ido
suna bi da kallo tun wanan kwaryan yana kokarin turjewa ya tsaya a waje daya har
yakai ya fara dan tafiya da sauri sauri yana bin igiyar ruwan kamar yadda dayan
kwaryan ya mike tsaye yabi ruwa suna kallo.
Lai habu kakai shu,umin yaro iya ta fada daga gefenshi hakan yasa ya dan kallo iyan
yana fadin komai zanyi akan dan uwana iya.
Amma baka ganin kayi kasada da shiga hurumin daba naka ba habu iyan ta kara
fada a hankali yayinda duk hankalinsu yake kan kwaren dake saman ruwan suna
tafiya .
Kaga wanan abin kamar rayuwace malam habu haka ruyuwan bawa yake a wajen
ubangijin mu shi ciwo ba mutuwa bane wani lokaci.
Wahala kawai bawa yake gudu da fitinar ciwo don sai kaga mai lafiya ya tafi ya
bar mai jinya a kwance inda rabon mikewa sai majinyacin ya mike shi wanda yake
tsaye yakai kwance.
Kallonta iya tayi kallo dake nuna akwai magana ke nan ga wanan zancen nata bata
kula ba tana surkullensu na yan bori har zuwa lokacin da ta dago garesu tana fadin
da alama dai sadaka ya karbu ke nan sai dai ayi fatan Allah ya tsare.
Akwai abubuwa da ya kamata ace kun sani tun wajen amsan maganin nan wanda nake
ganin kai malam dauda ya sani a lokacin.
Kawu dauda yana jin hakan ya gyara tsayuwanshi yana dan kame kame ta karbe da
fadin baida matsala tun lokacin da abin ya damu maman mu ta sanar dani komai akan
haka har zuwan da matarka tayi daga baya tana neman a bata aikin a mayar dashi wani
nau,in sai daga bayane hakan ya damu maman mu kuma bayan tayi aikin abin ya koma
yana damunta wanan yasa na fita neman ku don kwantacen da matarka tayi muna a
lokacin . shi nayi amfani wajen nemanku nazo har zaria din a wajenta naji komai a
cikin hikima don yadda najata a jikina sosai a lokacin.
Naso ace kunzo lokacin da mahaifiyar mu take raye saidai hakan bai samu ba don
kaddara ya riga fata a cikin lamarin.
Kai yanzu ga yar uwarka bata san abinda kai da matarka kuke shiryawa akanta ba
duk dadewan nan ya kamata ace ka fito fili a yanzu ka sanar da ita manufarka a
kanka dakai da matarka.
Me zai fada a yanzu ai gara kawai yayi shiru don hakan ma ai maganace don jin
baida amfani a wajen mu yanzu tunda ko yanzu Allah ya baiyana muna nufinsu a kanmu.
Ban taba zaton hakan ba yaya ko mutuwa nayi na taso akace kaine kayi min hakan
akan zuri,ata zance kazafi akai maka don a shiga tsakanina dakai.
Wai sai gashi da raina da lafiyata hakan ya faru yau a gabana yaya ka kasa mussa
wanan zancen da aka dade ana fada min ina fadin karyane zalla zumuncine kawai a
tsakanin mu.
Ashe abin ba haka bane yadda na dauka kai a wajenka da wani manufa ka ke nuna min
zumuncinka a kaina don kawai,,,,
Kukane yaci karfin ta wanda yasa habu ya taso daga inda yake yazo ya rike
mahaifiyar tasu da komai yake iya faruwa da ita a lokacin don yadda yanayinta ya
nuna a lokacin kamar bata cikin hankalinta.
Shima kawu dauda din sai fadi yake na dade da nadaman haka Dubu tun bayan dana
fahinci cewa kamar yaran nan sun gano irin abinda Hafsatu ke izani inayi akansu
din.
Tundai ma shi Habu da har ya fara fitowa fili yana fada min magana a fakaice
wanan yasa na fara neman mafita daga kaidin ita hafsatu na yanke shawaran in kara
aure,,,,
Daga baya ke nan dai dauda kaji kunya wallahi ka rasa wanda zaka zallunta sai
yar uwarka akan abin duniya me yaran nan suka rageka dashi a matsayin ka na kawunsu
?
Malam dauda kadai fadane amma hakan bashine nadamarka ba ko in fada a nan gaban
kowa wanan abinda ka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login