Showing 30001 words to 33000 words out of 328222 words

Chapter 11 - Murfin Jallo Dan Uwa By ZAINAB IDRIS MAKAWA

yakai kwana bakwai a wajen wani cup har yayi huhuna da abinda
akaci cikinsa aka barshi nan kaya saman lafiyayyen kujeran dake falon kayan yayansu
da nasu abin ba tsarin fada wallahi.
A kitchen din naga tashin hankali don tukwane abincin ne a girke da ruwa da
ruwa duk sun yi babu kyau gani a wajen hakan na tsaya saidana wanke tukunyan da
zanyi amfani dashi lokacin na dora girkin .
Ban iya sakewa kitchen da kazanta haka dole na shiga wanke kayan dake tare a
kitchen din ina mamakin yadda mace zata samu daula haka kazanta ya hanata
gyaranshi.
Lafiyayyen shimkafa da miyar kaza na hada masu fridgen din nan nasu dankare yake
da nama haka store dinsu kayan abinci a dankare kamar sun lalace a wajen gyara
sosai na tsaya nayi masu tsakani da Allah ga yarta dake ta kuka na dauketa na goya
ta a bayana yarinyar tayi barci haka kuma nake wanan uban aikin da ita a goye a
bayana.
Banji kyashi ko kiuya yi masu aiki tsakani da Allah ba inayi ina gyaran falon
ina duba girkin daya gauraye gidan ba wani abu bane girki kamar mace ta tsaya ta
soya kayan miya yadda ya dace .
Haka tayi amfani da sanadarin girki na zamani ko na gargajiya da muka sani wanda
nagani a kitchen din shi nayi masu amfani dashi a lokacin.
Na bude miyar naga ko ya isa daukewa saiga dayan matar ta shigo kitchen din
ksllon mamaki take min kafin ta karaso gabana tana fadin .
Banyi mamakin ganinki a nan ba tunda har ga yar gida a bayanki yau nagani nidai
ki gama ki fito muna dashi in diba na amsa da fadin.
Ba aiki ya kawo ni nan ba zuwa nayi in taimaka mata idan wace ta sani na girka
ta fito sai ta baki daga haka ban kara tankawa ba kuma.
Huumm,ummm kama kanki yarinya bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane nan ba
wurin raininki bane ko yarki bata isa ta kawo min rashin mutunci ba balle ke ?
Muryan Asmaun mukaji a bayan mu tana fadin sannu da aiki Ramaah yauwa sannu anty
na kammala na fada ina kokarin fita daga kitchen din.
Ai da kice min munyi sabuwar yar aiki a gidan nan Saiba ta fada sai naji Asmau
na fadin .
Yar aiki kuma ina take kafin ta gano me take nufi sai tace haba dai kanwar
tamuce kuma yar aiki daga taimako ?
Ninaje gun yar uwarta na rokota tazo ta kama min kaina yana damuna da ciwo ga
zazzabi kada mu zauna da yunwa.
Ki duba irin aikin da yarinyar nan tayi muna kamar ba mutum yayisa ba cikin dan
kankanin lokaci haka ga kuma gitki .
Yarinyar tayi kokari gaskiya wanan matsalankice Asmau banga abinda zaisa na ja
wa yanda sabodasu akaci min mutunci a gidan nan.
Kitchen din na dawo ina fadin karbeta zanje nayi sallah ta mika hannu ta karbi
yarta daga bayana zan fice take fadin zoki dibi abincin mana ?
A,a akwai abinci wajen ,,,,,
Dakata don Allah Asmau nifa ban son kaskanci ki bari in diba inyaso idan na
diba sai ta diba din wani kallo nayi mata na wuce zuwa part din iya din.
Koda na koma suna zaune da anty da Yanda a falon suna hira na shigo na fada
saman kujera sai iya ke fadin har kin hada nace nagama iya.
Ai yanzu dai sunga ranan dan mutum ke nan yaro dama ba a haifeshi don mutum
daya ba yau da babu zaman mutunci ai ba zata zo neman alfarma haka ba.
Ina jin tsohuwar saidai na kasa magana saboda maganganun da Saiba din ta fada
min duk da ban kyaleta ba nima amma sai nake ganin ta shammaceni ai a lokacin data
fada min magana irin wanan .
Asmau ta shigo da abincin a cikin kula tana fadin ga abincin Ramaah kinki
tsayawa ki dauko a,a ba zanci ba na fada ina gyara zama .
Tace saboda me ko akan maganan da saiba tayi zakiki karban abincin aiba ita ta
sakaki ba nuce na roka kiyi min kuma nagode da abinda kakai min.
Ita haka halinta yake bata da tunane sai ta dauka kowa bai isa ba ita kadaice ta
isa a gidan nan shiyasa ko yaushe kuke jin fadan mu da ita a gidan nan ai.
Ba ita ta sakani ba ai balle ta dameni na fada ta dan juyo tana kallona sai kuma
tayi murmushi a fuskanta tace.
Yadda kikayi ai naji dadin hakan Ramaah tayine don kada gobe ki kara taimaka min
kiyi fushin zuciya akaina haka take min wallahi.
Duk wanda taga ina abin arziki dashi duniyan nan Saiba na bakin ciki da maishi ko
gaisuwa batayi da kai indai ina hurdan arziki ki da mutum.
Aiko zata wahala wallahi indai Ramaah ce dama bata nuna hakan ba da dukkanku
kunji dadinta antyna ta fada tana dariya.
Daga wanan ranan da haka ya faru muka dan fara shiri da Asmau a gidan har antyna
suna dan biye juna sama sama .
A cikin wasa Asmau zata jani zuwa wajenta muyi gyaran daki haka yarta a yanzu
yarinyar tayi mugun sabo dani sosai idan ta ganni ta fara washe baki ke nan tana
miko min hannu tana son in dauketa.
Idan na bushi iska zan shiga wajen anty Asmau din mu dan taba hira sama sama da
ita wanda hakan tun yana ba Saiba haushi har tazo takan dan saka muna baki a cikin
maganan mu din wani lokaci.
Wani lokaci kuma kamar bata san da Allah ya ajeni ba takeyi ranan da yan iskan
nata suke kai saidai tayi ta jan tsoki tana jin haushi ta nuna cewa bata son zaman
mu a lokacin.
Wanan yasa ban faye damuwa da ita ba ban kuma fasa shiga ba idan na bushi iska
ranan da ba karatu sai hakan yasa shakuwa sosai yashiga tsakanin mu.
Saidai matsalan ta shine kazanta da kuma rowa tana iya hanawa mutane abu koda ba
zatayi amfani dashi ba zata bar abin ya lalace saidai ta zubar dashi a karshe.
Amma yana da wuya tace maka gashi a cikin dadin rai saidai in rabon mutum ne ya
ratsa a gareta sai dai kuma anan saiba gaskiya a dan shigan da nakeyi ita saiba
tasha bamban da Asmau din.
Don saiba ko bakaga abu ba zata iya cewa dake idan zakici abu kaza akwaishi a
kitchen ko kuma idan kun zauna kuna hira ta dauka abin ta mikama shi a gadarance ta
juya bambamcin su ke nan.
Sakin fuska sai Asmau kyauta kuma Nusaiba amma wajen kazanta gaskiya a ganina
kamar suna kwatawa duk da ance wai Nusaiba tafita dama a wanan fammanin.
Nasan matan hausa sun camfa mu matan fulani da iya yi da kisisina da makirci
wanan kirarine da akewa matan fulani dake auren kado wani lokaci.
Wanda a wurin mu abin ba hakana bane na dauka iya kamun kaine da sanin darajan
aure wanda ake ganin hakan kamar wani kisisinane nasu sukeyin hakan.
Ko a yanzu gidan nan haka suka fara radawa yar uwata don tsananin bin dokan
mijinta da kiyayyewa da takeyi.
Don duk umurnin da mijinta ya bata bata taba ketareshi tana kuma kafa,kafa da
duk abinda ya gargadeta dayi wanan yasa suka saka mata suna zundenta.
Don yana da wuyane ka shigo ka sameta a waje ko kaga gilmawanta a haraban gidan
idan har ba wajen iya zata shiga ba.
Duk shigan da nakeyi wajen su anty Asmau bata hanani saidai ita ta kama kanta
kamar yadda mijinta yace kada yaga tana shiga wani rikici yazo ya faru sunanta ya
fito a cikon case dinsu.
Hakan yasa nima takan ja min kunne a duk lokacin da taga kamar nayi zurfi a cikin
sha,aninsi zata taka min burki da jan kunne kada in yarda wani abu ya fito ace
nice na fada.
Hakan kesa in kara kama kaina dasu saidai a danyi hiran yaransu ko hiran film
iyakata dasu ke nan suma din kuma sun fahinci haka a gareni.
Hutu muka samu na dogon zango haka yasa muka samu wanan irin zaman da ko yaushe
kana gida da sunan hutu saidai a wajena abin ba haka yake ba.
Ranan tunda na tashi nayi irin aiyukan dana saba yi a gidan gyaro ko ina na
cikin gidan da waje bangaren yayata da kuma bamgaren iya kamar yadda na saba a
kullum.
Duk da su Anty Sare suna gida a lokacin ban damu da sai sun tashi sunyi ba
Allah baisa min kallon irin hakan ba a rayuwata kace baka abu don wani baiyi ba .
Wajen yayata na koma don yanzu dasu anty Sare suka dawo hutu tare da ita nake
kwana idan mijinta baya gari.
Don cikin jikinta dake bata matsala tana yawan zazzabi da amai da sauran laluran
masu shigan cikin .
Haka kayana har wanan lokacin a wajenta suke sai na amfanina na yau da kullum ne
a wajan iya.
Kwance na sameta falonta na zauna a wajenta gaidani tayi da aikin yasa na zauna
ina dariya nake fadin ina aikin a yanzu Yanda ?
Ramaah kinsan abinda ke damuna yanzu ta fada hakan yasa na sake kallonta ina
girgiza kaina alaman a,a a gareta.
Nisawa tayi tana fadin wallahi baffan mu nake yawan mafalkinshi sosai Ramaah a
kwanakin nan yana yawan zo min a cikin mafalkina kamar yana kokarin aikata min wani
mugun abune nake gani kinsan baffa mugun mutum ne Ramaah.
Baki addu,ane idan zaki kwanta anty tace inayi kuwa sosai Ramaah ai duk dare ya
habu sai ya tunana min da addua idan zan kwanta kina jinsa ai wani lokaci.
Tunane na shiga yi don sanin da nayiwa baffa mutum ne mai kyashi da hassada
kashe mutum a wajensa ba wani abu bane shi da bakinsa zaki yana ikirarin sai yaga
bayan mutum idan dan wani abu ya hadashi da wani.
Balle mu da akai rabuwan tashin hankali dashi zai iya cewa zai dauki fansa yanzu
akan yar uwata din dan abinda ya faru kafin aurenta.
Hakan yasa na dago ina fadin anty yanda mu kira hardo mu fada mai yafi abar
zancen nan don kinsan hardone kawai maganinsa shi kadai naga baffa yana tsoro a
cikin yan uwa.
Dan murmushi ta sauke a fuskanta tana fadin Ramaah ban son saka kowa a cikin
lamarin nan ni nasan baffa yana wani shiri a kanmu Ramaah ko ince a kaina don ni
kadai nasan yadda nake ji tun zuwana gidan nan a wahalce nake kai safe idan na
kwanta.
Dan dama idan habu yana garin nan nakanji saukin lamarin amma duk da hakan wani
lokaci kuma sai nayi wanan mugun mafalkin nasa.
Nasan ba zata taba fadawa wani halinda take ciki ba koni din a yanzu data
fadawa Allah ne ya matsi bakinta har ta sanar dani din tunda duk dadewan nan bata
taba sanar dani komai ba.
Saidai na fahinci tana cikin damuwane sosai a lokacin danafi saka ran akan zaman
gidan nan ne ko kuma rashin sabo ke damunta tunda nasan bata da matsala acikin
lamarin aurenta.
Don haka nasan ba zata fadaba ba kuma zatayi komai ba saboda alkunya irin na
fulani data gado.
Shiru nayi ina nazari kafin na mike na shiga wanka ba tare dana kara mata
maganan komai ba abin mamaki kodana fito daga bayin na samu ta dawo cikin dakin ta
kwanta da alaman tsoro ko wani abu yana damunta.
Bandai yi mata magana ba balle ta fahinci hankalina yayi mugun tashi a lokacin da
abinda take ciki din tana kwance har na gama shirina kafin ta mike ta shiga ban
daki don kewayawa.
Hakan ya bani daman samun abinda nake so na dauki wayanta na dannawa mijinta kira
na fice daga dakin yana ganin kiran ya daga wayan yana fadin .
Maria ya akayine na amsa daba ita bace yaya nice Ramaah sai naji yace Ramaah
lafiya ina yayan taki kuma meya sameta ?
Ba komai yaya saidai yana gab da faruwa amma zurfin ciki irin nata ba zata fada
ba balle a dauki mataki nan na kora masa abinda ta fada min bai ko bari nakai
karshe ba naji yace ina zuwa zan koma kira .
Ashe hjynsu mama Dubu ya kira hankali tashe ya fada mata abinda ke faruwa nan
itama mahaifiyar nasa hankalinta ya tashi sosai dajin hakan.
Bansan ya sukayi ba dai sai ganin hjy din mukayi gidan lokacin da na gama wayan
na mayar mata bina tayi da kallo na mika mata wayan take tambaya wana kira nace
kawata bata damu ba ta karba kawai ta koma ta kwanta.
Nima ganin hakan sai ban fita ba zauna da ita ina janta da hira inda naga ta dan
sake muna zaune mukaji sallaman mama tare da iya a part din.
Hakan yasa muka fito muna masu sannu da zuwa idon mama dubu yana kan sarakuwar
nata cikin tausayi take tambaya da fadin .
Maria meke damun kine yaya kike ganin shi a mafalkin naki ido takai gareni na
dukar dakaina kasa hakan yasa mama dubu fadin .
Aimu ta kyauta muna data kira Habu ta sanar dashi yau wa take dashi garin nan
daya kaiki maria yar uwarki kar kiga laifinta irin wanan abin ba a wasa dashi tunda
kunsan halin mutumin nan .
Bari kawun ku ya karaso yanzu ki shirya kuje da Iya kafin ya iso ki tashi ki
shiga ki shirya idan ya karaso sai ku tafi ba magana takeyi ba ita.
Saidai ta mike don bin umurnin sarakuwar nata nan iya ta soma magana tana fadin
yanzu yar nan duk sabon dake tsakanin mu irin haka ya faru dake gamu a gida daya ki
kasa fada min ?
Wancan cikin na farko ya zube kin samu wani kuma lalura ya shigeki irin hakan ba
zaki fada ba yar nan asan abin yi akai ?
Kawu yai sallama suka shigo da anty Sare data rakoshi ina jin suna gaisawa nima
na gaidashi na shiga daki wajenta na sameta ta saka hijab saidai ta kasa fitowa
falon ta samesu.
Juyowa tayi ta kalleni tana fadin yanzu abin nan da kikayi Ramaah kin kyauta ke
nan don Allah zaki tayarwa mutanen nan da hankali haka Ramaah wanan yasa ban fadawa
kowa halin da nake ciki nake bari a zuciyana.
Hawayene ya zubo min lokaci guda na soma fadin Yanda idan ban fada ba ki halaka
ina kallo kuma na sani baffa mugune komai zai iya aikatawa akan kuma don ya fadi
hakan kuma mun sani.
Muryan mamace dake fadin idan kun shirya ku fito mana kuje maria hakan yasamu
fitowa falom muka samesu take fadin sai sun dawo iya zancen nan kada ya fita a
cikin gidan nan don Allah.
Bana son azo a wuya zancen ta wani tsiga kin dai san halin yaran nan matan
shiyancan yanzu ne da sunji zancen zai juye zuwa wani daban.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
[5/19, 21:37] Buhainat: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/K44JhTApwmM4gU33AbpqHC


MURFIN JALLO DAN UWAN TAFIYA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

1️⃣2️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257
NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A
WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA
YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


(Ikon Allah )abinda malamin ya fada ke nan ya dago kai ya kalli kawu dauda da iya
da suke zaune gabanshi cikin damuwa tare da son sanin ainihin abinda ya kawosu.
Ga mamakin kawu dauda dake sauraren malamin zancen Yanda ce ya kawosu saiga
malam ya fara wasu zantutuka na daban da bai shafi ita Yanda din ba sai yayan mama
dubu.
Yana faman fadin umm,umm subbahanallahi Allah ya kyauta ya dago kai yana ajiyan
zuciya yace wanene fari dogo haka matashi a gida ?
Su biyune guda yafi guda haske a cikinsu dan tsayi kawu dauda ya kallo iya kafin
ya mayar da kallonshi kan malamin yana fadin mun ganesu yayan mune saidai don Allah
malam idan akwai wani matsalane a game dasu abari mu gama na wanan yariyar a yanzu
kafin a furta nata take mutumin ya fahinci me kawu yake nufi.
Sai malam yayi murmushi yana fadin gaskiyane ita wanan da tana tabuwa malam
dauda aida tuni an gama da ita ko saidai labari to saukin abin dai yaran nada
tsarin ubangiji a jikinsu.
Saidai ayi ta raunana cikin da take samu amma ba ita ba wanan hayaki zan bata da
rubutu yanzun nan ta shaye insha Allahu ba abinda zai faru da cikin jikinta data
sauka lafiya kai malam dauda kazo nan ka sheda min daga wanan karon za a daina
bibiyanta amma turene da akai mata na iska da suke son lalata cikin jikinta din .
Zata dage kuma sosai da addu,a shi kansa wanda keyi yasan yaran suna da wani
baiwa da Allah yai masu wana da wuya a iya cin masu da sauri barma yar uwarta da
tafita karfin tsari a tare da ita.
Ya dai bata abinda zai bata sun aje zance kawu zai dawo karban abu yake fadin
ai matsala da sakaci yakai ga hakan amma yaran nan da nake zance uwarsu ce da
laidin komai don akwai wata mace dataso taimaka mata amma ya kasance uwar bata
mayar da hankalinta ba.
Sam kawu baison zancen a gaban yar uwata hakan yasa ya kau da maganan akan zaije
ya dawo sukai mashi godiya tare da dan bashi abinda zai bashi na goron sadakan
taimaka masu din suka bar wajenshi suna godiya.
Hankali iya yai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login